Novel Document

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novel

A hankali motar da shigo layin dai dai wani katafaren gate ta tsaya, yanayin yanda take fidda wani Dan Kara alamune dake nuna motar tayi dogon zangon tafiya, direban Bai Danna Horn ba bara a kaiga bude gate din gefen wata bishiyar dorawar tururawa ya karasa da motar, wasu dattawa ne su buyi suka fito daga bayan motar yayin da wani matashi ya fito daga mazaunin direba, Mika yayi dareban tare da salati.Kofar gidan suka nufo da kafarsu Dan matshin be yayi nocking kamar day biyu kafin wani dattijo ya leko ta wata karamar kofa jikn gate din.Da sauri ya bude kofar Yana fadin “A’a Alhaji barkan ku da zuwa kin Sha hanya sannunku” tare da Basu hannu sukayi musabiha suna fadar “wlh kuwa malam Sani ya muka sameku?”.Cikin fara’a yake fadar “Alhamdulillahi”.Kafin yayi gaba Yana cewa “Bari nayi Muku iso gurin Alhajin Allah ya taimaka Yana nan”.Harabar gidan suka shiga suka rufawa malam Sani baya zuwa bangaren Mai gidan inda yake ganawa da bakinsa.Lokacin da suka karaso gurin kofar shi Kuma Malam sanin ya fito Yana fadin “Bismillah ku shiga, sannunku”.Yayi gada da sauri Dan cika umarnin Alhajin na Kiran babban Amininsa na kankankan Malam Bukar.Da sallama suka shiga falon, Masha Allah komai najin dadin rayuwa akwai shi a falon tamakar fadar wani sarkin. Cikin fara’a da sakin fuska Alh Jafar Mai Yadi ya nufo bakin nasa Yana fadar “A’a! Alhaji Sulaiman kune haka cikin wannan ranar ga nisa”.Amma kasan zuciyarsa mamaki ne fall a cikinta shi dai yasan ba wani abu daya taso da zai kawosu a irin wannan lokacin a kalla suna da sauran kwanaki uku kafin duzo duk da sun bada duk abinda ake da bukata lokacin kawai ake jira. Amma dai ko meye Allah yasa Alkhairi ne.Bayan gaishe gaishe na al’ada daya daga cikin ‘ya’yan Ahj Jafar ne yayi sallama ya shigo Yana gaishe da bakin Yana aje musu lemon da ruwa ya fita.Wani matashin ne shima ya shigo da manyan warmers da wata yarinya da basket Mai dauke da plates da cokula da cups Suma suka gaishe dasu suka fita.Tunda aka Fara shigo da wannan karamar arzikin Alhaji sulaiman ya sadda Kai kasa zuciyar idan tayi dubu to a bace take.”Bismillah kuci abinci kafin mu shiga sallah tunda Azzahar ta gabato”.Alh Jafar ya fad’a Yana nufar kofar fita.Bayan fitar Alhaji Jafar Alhaji Ismail ne ya kalli Yayansa Alhaji sulaiman “Nifa duk na rude wallahi har na rasa ta inda zamu Fara fad’a musu irin wannan magana duba da irin karamcin wannan bawan Allah”.Ya fad’a yana Jan siririn tsaki.Dan matashin daya tukosu ne yayi magana “wlh Daddy naso kun hakura da zuwa ita Hajiyar tazo da kanta ta fad’a musu abinda ta kulla, ni ban taba ganin irin wannan ba anyi Abu cikin mutunta juna har an kawo wannan gabar Amma Rana tsaka irin wanna ta taso Babu Dadi ni wallahi tausayin Musbahun nakeyi ya shiga wani hali Amma ita ko a jikinta”.Shi dai Alhaji sulaiman Bai Kara magana ba haka Bai ko kalli abincin ba duk da yunwa da yakeji leonm da ruwa kawai ya sha, Alhaji isma’il da Al-Amin ne sukaci abincin suka fita zuwa masallacin kofar gidan.Tare suka shigo gidan bayan idar da sallar har da Malam bukar domin shine limamin masallacin.Sabuwar gaisawa suka karayi Amma wannan lokacin Al-Amin Bai biyosu ba.

Alhaji sulaiman ne yayi Qarfin halin Fara magana Yana kallon Malam Bukar “Dan Allah malam ayi hakuri da abinda mukazo dashi WALLAHI badan Nan gidan bane Babu abinda zai Kara dawo Dani garin Nan”.Yayi shiru ya kasa karasa maganar saboda wani abu daya tsaya Masa a makogwaronsa yana masa tukuki.Shima Alhaji Jafar wani abune ya tsirga masa har tafin kafarsa ga wata irin faduwar gaba taba gaira ba dalili.Shiru falon ya dauka na wucin gadi kafin Malam Bukar ya magantu “Alhaji ka Fadi ko menene ba wata matsala ita rayuwa ba yanda Bata zuwarwa bawa ko Dadi ko akasin hakan, Kuma duk musulmin kwarai ai yasan kaddara, ba damuwa ai and Zama daya”.Alhaji Ismail ne ya karbi maganar ganin yayan nasa bashi da niyyar cigaba da maganar.”Ayi hakuri Malam kan maganar auren yaron gurinmu ne da yarinyar gurinku, wata fitina ta taso yau kwana uku kenan ana Abu daya mahaifiyarsa ta kafe kaida fata Bata amince ya auri Zahra ba duk yanda mukaso gyara abun ya gagara karshe ma cewa tayi idan har Musbahu ya auri Zahra Bata yafe Masa nononta daya sha munyi munyi da fad’a Mana dalilinta na wannan cin zarafin Amma ta kekashe taki fad’a karshema abun ya zamar Mata lalura kamar ta jinni”. Tunda ya Fara kora bayani Alhaji Jafar ke maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, domin duk wani karfin gwaiwarsa ya Kare wannan wace irin musiba ce kullum idan auren yarinyar nan ya taso sai an Sami wani akasin ya taso shi Lamarin Nan ya rasa yanda zeyi dashi.

Malama Bukar ma rasa abin fad’a yayi duk wani kuzarinsa ya Kare.Yayin da su Alh Sulaiman suketa nanata ban hakuri.Cikin muna juriya da dattako Malam Bukar yace “haba Alhaji ba komai kasan komai nufi ne na Allah Daman Bai Qaddari shine mijinta ba, Allah yasa hakan yafi musu Alkhairi su duka’.Gaba data suka amsa da Amin.”Amma dai Abu baiyi Dadi ba wallahi ba Baki nayi musu ba Amma kafin a Sami Mai nagaratr yarinyar Nan zasu Dade suna nema” cewar Alhj Ismail.Har gurin mota suka raka bakin, har suka daga bakinsu Bai Dena bada hakuri ba.Bayan tafiyarsu falon su Malam suka dawo jiki a sanyaye duk Lamarin ya cakule wannan wace irin kaddara ce ke bibiyar karamar yarinya haka aure dai dai har uku ana fasawa. Cikin nuna damuwa Alhaji Jafar ya kalli Malam Bukar yace “malam inshallah Allahu wannan karon zan aurar da Fatima tunda Naga lamarin bana arzki bane ko meye in Sha Allah sai Naga bayansa’.Tunda Alh ya Fara magana Malam Bukar ke girgiza Kai shima lamarin ya kaishi makura yasan lamarin yarinyar akwai magauta a cikin Amma ganin an samu rata Mai yawa a tsakani ya dauka abun ya wuce ne.Cikin nuna alhini Malam ya kalli amininsa yace “Dan Allah Alh kayi hakuri kada kayi Abu cikin fushi da kace zaka aurar da ita kada azo ayi aikin Dana sani”.Kujerar dake daura da Malam din ya zauna kafin ya sauke ajiyar zuciya.”Ko daya banyi fushi da ikon Allah ba kawai dai na gaji da wannan wasan ne kullum na Zama karamin mutum saina Raba I.V na daurin sure azo ace an fasa wasu ma sai su zageni ace Dan bani na haifi Fatima ba na saka ido ana Mata wannan cin zarafin wlh da banyi alkawarin daina hada auren zumunci ba da yau ba sai gobe ba zan aurawa Abdul Hakeem ita. Amma yanzu ma Bata baci ba ka nemi shawarar Mahmud na Nan gurinka idan ya amince na bashi auren ta”.Cikin kaduwa Malam Bukar ya kalli Alh Jafar yace”Wane Mahmud din, ba dai na Nan gurina ba?”.Cikin yadda da Kai Alh Jafar yace “shifa nake nufi ko akwai wani Mai wannan sunan a gurinka?”.Gargiza Kai Malam din yayi tare da fadar “Babu, Amma Alhaji al’marin Mahmud ba boyayye bane a gurinka kada duniya ta zagemu fa”.Gyara Zama Alhajin yayi kafi ya fuskanci amininsa sosai.Wallahi Malam bana gudun duk abinda za’a fad’a na yaba da nutsuwarsa idan kaga ba’ayi ba to shima Allah Bai nufi mijinta bane Amma na jima Ina yiwa ‘ya’yana sha’awarsa”.

Kai kawai Malam yake jinjinawa shi lamarin duk yazo Masa a baibai ya jima Yana nazari akan lamarin Fadima kullum Abu daya yake gani mijinta ba Nan kusa take ba bil hasal ma wani lamari yake gani Mai girma dangane da mijin nata da wani irin Haske Amma koda Wasa Bai taba fadawa Alhajin ba sai dai Yana yawaita saka almajiransa gurin yi Mata addu’a.Sun jima suna kullawa da kwancewa a tsakaninsu daga karshe suka tsaya a malam ya tambayi ra’ayin yaron idan yana so la’ba’as._______A hankali take sakkowa daga stair din tamkar wani dawisu Tasha make-up da wata gawon Mai azabar kyau Sai karamar pos a hannunta daga bayanta ‘yan Mata ne su biyu ko wacce Tasha nata gayun, tun kafin su karasa sakkowa kamshinta Mai saka nutsuwa ya gauraye ilahirin falon. Falon a Cike yake da jama’a kowa ka gani ta amsa sunanta sai tsirarun yara.Da sauri wata ta matso gurin su tana rangada buda, tana fadar “Masha Allah Amarya Allah ya kade hau da bala’i ya bada zaman lafiya, Hajiya Zahra sukari bayi farin banza, jikar hardon fulanin Mubi jikar larabawan Jodan da larabawan madinatul munawwara kaga musu kyawun asali Amarya a gidan Mushahu alherin Allah yakai Miki”.Wata daga cikin matan dake zaune ta tashi ta shiga zubawa marokiyar kudin ita Kuma tana Kara Koda Amarya Zahra.Aunty Hasana ce ta fito daga wani Dan korido ta karaso tana kallon kanwar ta ta, tana Kara tasbihi ga ubangiji daya halicci wannan kyakykyawar surar.Hannaun Zahra ta rike tana kallon Baba Tabawa Mai aikinta yanda ta zage tana jero kirari kamar wata marokiya.Dan murmushi tayi tana fadar “Masha Allah, Baba Tabawa yaushe Kika Zama marokiya bani da labari?”Dariya tayi tana fadar ” ai ko ban iya ba na koya mu Abu namu bikin uwar dakina guda kinsan biki na d farar kaza balbela ba gayya ce ba, yakuwar kan kabari kenan bakin cikin ‘yan taushe, murucin kna dutse Baki fito ba sai da kika shirya”Dariya sukayi gaba daya, har gurin da zasuyi bridal shower din kawar Aunty Hasana da Baba Tabawa suka raka Zahra.Sun chashe, sunyi hotuna kamar ba gobe sai dai duk Wanda yasan Zahra yasa Bata cikin walwala haka nan take Jin wata irin faduwar gaba da rashin dadin zuciya, Amma ita kanta Bata San taka maimai me yake damunta ba gashi tun jiya take neman wayar Mushahun ta kasa samun shi, haka ta abokinsa Deeni itama shiru a yanda sukayi dasu yau ne ranar da zasuzo Dan har hotel din da zsau zauna sun Kama mukullan ma suna hannun magaji.Dadin dadawa yau sukayi za’a kawo ya’yan yayar shi da wasu cussing dinsa.Sai gurin karfe Tara suka Gama shagalinsu, Zahra Bata koma saman ba inda akayi musu masauki Sai ta nufi bed room din Aunty Hasana na kasa dakin, ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta yake tashi ga danyi AC ya gauraye dakin. Head din ta cire ta aje kan bed side locker kusa lamp, gadon ta hau ta kwanta lamo kamar ba mutum akai Dan ko kwakwkwarwn motsi Bata sonyi wata irin kasala ce ta sauko Mata.Ta jima a dakin kafin taji alamun bude kofar Bata daga Kai taga ko wanene ba kamshin da taji ne ya sanar da ita Auntyn ce.Kusa da ita ta zauna tana Kai hannu jikin.wuyanta tare da tambayar “me yake damunki? tun safe Ina Kula da mood dinki Sam bakya cikin nutsuwa”.Ta fad’a tana kafe Zahrar da Ido.Yunkurawa tayi ta tashi zaune tare da fadar “Nima bansan me yake damuna ba wlh Aunty Sam bana Jin dadin zuciya ta sai zafi take min Kuma gabana sai faduwa yakeyi”.Ta karasa fad’a tana shashhshekar kuka kasa -kasa.”Meye Kuma abin kuka? keda zakiyi farin cikin Allah ya kawo lokacin bikin ba kamar lokutan baya ba da aka dunga samun akasi”.Kanta ta kifa a jiki Auntyn taci gaba da kukan ta marar sauti.Bata hanata sai tayi Mai isarta kafin ta Sami zarafin magana.”Aunty wlh Ina ji a jikina kamar wannan ma za’a Sami matsalar kinsan jiya saida nayi irin mafarkin da nakeyi idan za’a fasa aurena”. Ta fad’a tana Kara goge kwallar data ciko Mata Ido.Kallon ta kawai Aunty Hasana take ita fa lamarin yarinyar Nan Yana Bata tsoro kada fa namijin Aljani ya aure ta suna zaune Basu Gane ba.Karo biyu ana saka bikinta abun Yana lalacewa toga wannan ma, itama fa kawai daurewa tajeyi tunda Zahra ta fad’a Mata Musbahun Bai kira ba Bai kumazo ba ba wani Kuma nasa da yazo alhalin ba haka aka tsara abunba, Amma sai tayi ta maza tace.”Haba Zahra ya Zaki ringa fadar irin wannan maganar kiyi addu’a ba abinda zai Sami aurenki wannan karon sai Alkhairi, Ina ga da abinda ya hanasu karasowar har yanzu ki jira zuwa gobe Mana maza kiyi sallah kici abinci a sakonki can ki dauko zuwa an jima sai kiyi amfani dashi.

Novel TitleAuren Huce Haushi 2 Complete Novel
Author Maman Fatimah
GroupHausa Author Forum
GenreLove Story
Published Date01/04/2025
File Size600MB
Format SizeTXT
Book Price 500
Phone Number08055362975

Back to top button