Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 26 Hausa Novel

Ihu take yi sossai na neman agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ƙasan ranshi, Mommy da ta shigo da gudu ne ta riƙe belt ɗin a tsorace take cewa “SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa fa kake yi wa wannan duka kaman wanda ya kama ɓarawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?””Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi kaɗan na mata ko kallon banza ta sake yiwa Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ƙasa ƙasa da ita, marasa kunyar yara kawai…”Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi zaune.”Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?”Sadiqa da baƙin ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba laifi ta bugu ta ce “Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba’a je ko ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida ba, ni zai daka? Akan Sabreena da take ƙanwar ƙanwar bayana?”Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa da kuka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan ɗan ta? Ko ci kanku bata ce ba.Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yake faruwa ita bata gane komai ba, Sabrina ta sauƙo tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta ɗora mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba.”Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?”Mommyn ta faɗa cikin mamakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin?”Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama wani iri ga faɗa da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai yanzu?”Samha ce me maganan zuciyarta har lokacin yana bugawa “Nima na kasa ganewa Samha kaina ya kulle tamau, kwakwalwana ba ya tunani daidai… Amma bari iyayen nata su zo mu ji me kenan?”A parlorn suka cigaba da zama chan kuwa sai ga Gaje da Yaya sun shigo, yanayin shigar tasu ma ba yadda suka saba zuwa ba a raɓe a raɓe a baya suna tsoro kar su yi ma mommyn ba daidai ba, kai tsaye suka zauna cikin kujerun parlorn yaya yana cewa “Hajiya Hussaina ashe ana nan, barka da gida””Sannunku da zuwa”Ta faɗa tana ta kallonsu kaman sabbin halitta yadda suka shige cikin kujera duk ba haka suke yi a baya ba, bata gama mamaki ba sai da Sabreena ta zo da gudu ta rungume Gaje tana musu oyoyo “Masha Allah, Amarya kin sha kyau da kamshi””kai Gaje, Baba sannu da zuwa”Ta faɗa tana daga jikin Gaje dake ta riritata.”Barka dai ‘yar arziki irin albarka, ya sabon wuri? Babu takura ko?””Ah baba wa ya isa ya takura ni ni da gidan mijina”Suka yi dariya.”Yana zuwa ya gaishe ku, sa kaya yake yi””Ah ba komai ai muna nan”Mommy tana zaune tayi tsamo tsamo kaman ruwa ya daki babban zakara har Saleem ya sauko ya zo ya tsuguna suka gaisa da su Gaje sai albarka suke sa mishi kan ya miƙe ya kalli Sabreena yace”Na fita”Da sauri ta miƙe ta bishi muryarta na fita a lokacin da take cewa ka zo min da… Sai dai bata ƙarasa da karfi ba, bayan ya fita ta dawo ta saka su Gaje gaba banza suka yi da su Mommy kaman Allah bai halicce su a wurin ba, wasu irin hawaye ne ke zubowa Sameera tana ambaton sunan Allah kan ta tashi ta shige ɗaki tana fashewa da kuka.Samha dai da mommy sun kasa magana, suna kallo har ta musu iso dining suka ci suka yi nak suka dawo parlorn, mommy ta kasa shiru tace “Yaya…!”Kallonta yayi “Menene yake faruwa ne? Na rasa gane kan Sabrina tunda aka yi auren nan, ɗazu fa har sa wa tayi Salim ya daki sadiqa abin da ba halinshi ba, ba haka na saka shi ya aureta su zauna ba ba zan zuba idanu mu cigaba da tafiya a haka ba, Salim ko kallon mutunci ya daina min daga aure? Me hakan ke nufi?””Hajiya Hussaina ke fa kike ɗaukar abu da zafi, yaro yayi sabon aure ai ba za’a saka musu ido ba, tarbiya daidai gwargwado mun ba Sabrina kuma idan Sadiqa tana mata gani gani da a matsayin ta na yayarta yanzu yayansu take aure ya kamata su san maganan da za su dinga faɗa mata ina ga hakan sai a zauna lafiya”Mommy ta saki baki da hanci tana kallonsu. Sabrina tayi murmushi tace “Abin da mommy ta kasa ganewa kenan, mu ajiye batun nan ku tashi mu je ku kalli sashena”Basu bi ta kan ‘mommy ba suka bi bayan Sabrina, numfashi ne taji bata iya ja da kyau Samha ta riƙe hannunta”Mommy…! Mommyyyy!!”Hankali tashe take kiranta kiran ya fito da Sadiqa da Sameera ruwa suka dauka suna shafa mata a fuska har ta Fara sauƙe numfashi da ƙarfi, me su Yaya suka yiwa yaronta? Sai yanzu tunanin za su iya cutar mata dashi ya zo mata innalillahi kawai take ta maimaitawa a tsananin tsorace.Su kam suna hawa Sabrina tace “kun yi min komai iyayena, ba ni da abinda zan saka muku kun ba ni wannan daula da dukiyar sai yadda naga dama zan juya shi, a yanzu ma ina ragarwa uwar ne saboda wani dalili nawa amma itama nan kusa za ta gane ta ɗauki goruba ne ta damkawa kuturuwa don kwace saleem a hannuna sai mutuwa”Dariya suka sheke dashi Gaje tace “Ke gidan nan fa duk na mijin ki ne kina da ikon yin yadda kike so, sai na ga kaman wannan sashe yayi muku kadan kenan ku suka raɓa ba ku kuka raɓa su ba”Hakane kuma gaskiya Gaje, kai Sabrina ta gyaɗa “Zan san abin da zan yi akai, amma ko za ku dawo nan ɗin ne?””Ta ya kenan ‘yar albarka?”Baba ya faɗa, ta saki murmushi “Kar ku damu na san yadda zan yi saleem yayi musu korar kare a gidan nan”Hira suka cigaba da yi wane sa’anninta ba iyayenta ba duk wani tuggu sun haɗa shi a ƙarshe baban ke cewa “Ai duk yadda za mu yi mu yagi rabon mu kan a je lahira za mu yi, ko a gaban Allah laifin mu kadan ne ita ta ga dama ta bamu hanya zuwa cikin gidanta shekara nawa ina faɗi tashi akan ya kula ki sai da na hakura na cire rai kwatsam ta dawo da zancen ashe muna da rabon dangwalar arziki mu ma, bari mu je mu fara tattare”Sallama suka mata suka bar gidan ransu kal…****”Saleem…”Ya kira sunan yana zama gangar shi, buɗe rinannun idanunshi yayi ya zuba su kan Rayyan ɗin ba tare da ya ce komai ba, duk wannan ɗin ba halin Saleem bane na Rayyan ne hakan ya sa Rayyan ɗin ya ɗan damu. Yana zaune kawai ya ga Shigowar saleem ɗin office ɗin kuma bai ce mishi komai ba bayan sallama ya samu wuri ya kishingida.”Menene? Me yake damunka?””Ni ma ban sani ba Rayyan, kawai ina jin ƙunci ne raina babu daaɗi zuciyata na mini zafi ba na iya bacci””Saleem kana karatun Alqur’ani?”Ya girgiza kai don ya fi 2weeks rabon da yayi karatu in ba a sallah ba.”Alqur’ani wani dafa’i ne na yaye ƙuncin zuciya saleem, idan ka ga ba zaka iya bacci ba kayi ta nafilfili kana karatun za ka ji sauƙi, ka fi kowa sani na har a yanzu bana bacci kaman na mutane amma da na riƙe ibada ban zauce ba… Ka roƙi Allah ya yaye maka dukkanin damuwowinka”Kai ya gyaɗa, Rayyan bai kara cewa komai ba ya tashi yayi playing karatu a office ɗin ya je ya ɗauko ruwa ya kawo mishi ya ɗan sha tare da kwanciya a three seater abin mamaki tun karatun na shigar shi har bacci mai tsananin daaɗi da natsuwa ya ɗauke shi ba tare ma da ya san yayin ba.Saleem ya yi baccin Awa biyu cip kan ya farka har lokacin Rayyan na office ɗin yana wani aiki a system ganin ya farka ne ya mishi sannu, kai ya gyaɗa ya miƙe ya shige toilet da ke ta tashin kamshi wanke fuska yayi tare da alwala don ana ta kiran la’asar, bayan ya fito Rayyan ma ya rufe duk abin da yake yi don baya tunanin daga masallaci zai dawo office ɗin ya shiga bayin yayi alwala ya fito yana gyara hannun lafiyayyar farar shirt ɗin shi da ya ɗora akan navy blue wandon jeans, rigar suite ɗin ya dauka da briefcase ɗinshi suka fice yana kulle office ɗin. Sai da ya zube abubuwan a mota suka isa masallaci suka yi sallah.”Za ka iya driving ɗin ko in mayar da kai””No zan iya”Ya faɗa a hankali.Da kallo ya bishi har ya shiga motar shi ya bar wurin, ƙasa natsuwa yayi da yanayin saleem ɗin duk sai ya tsaya mishi, da wannan ‘yar damuwar ya nufi gida horn yake dannawa a kofar gidan da gudu aka wangale mishi gate ya cusa motar ciki, idanunshi ne suka faɗa kanta sanye take da wani stylish crepe Adire ta haɗa shi da matching colour purple na Jersey, daga inda yake yana hangar labbanta dake shekin man baki sossai tayi kyau amma shi ba kyaun yake gani ba.Dr. Sulaiman dake tsaye yana mata magana ya ɗan zubawa idanu kan ya ƙarasa parking ɗin ya sauƙa sai ya ɗauke kai kaman bai san akwai halittu wurin ba, tafiya yake kaman ba zai taka ƙasa ba har ya ɗan gota su Dr. Sulaiman ya taso”Assalamu Alaikum warahmatullah Dr. Rayyan”Sai da ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan ya ɗan waigo ya kalleshi ba don ya san muhimmancin sallama ba babu abinda zai sa ya amsa, hannu ya miƙa mishi suka gaisa ya juya ya shige ciki fuskar nan kaman an mishi mutuwa.Sai da ya ɓace ta sauke numfashin da ta riƙe Dukda ko kallon inda take bai yi ba, kwarjinin shi ya matuƙar cika ta ta tabbatar haka Sulaiman ma don babu wanda baya shan jinin jikinshi a duk sadda Rayyan ya matuƙar tsumewa, ita dai ta san Rayyan ba ya rasa nasaba da sarauta.”Afeefah me kika ce?”Dr. Sulaiman ya faɗa “Zan tambayi Mammi in shaa Allah in ta amince tunda gobe half day juma’a sai ka zo mu je in na tashi school””Toh shikenan, ga wannan”Ya miƙa mata leda kin karɓa tayi sai da ta ga ranshi ya ɓaci kan ta amsa don bata yadda ta iya.Kai tsaye wurin Mammi tayi don ta bata ledar ba ma ta bukatar buɗewa kan ta kai mata, da kuwa ta san abinda zata tarar da bata shiga ba faɗa sossai Rayyan ke yi na shi baya son tarukuce idan abinda zata yi kenan ta tattara ta bi samarin nata yaushe har ta tafasa da zata ƙone? Haka ta ga Abeeha na yi? Toh shi ba irin tarbiyar da yake ba ƙannenshi ba kenan in kuma tana gidan dole tayi abinda ta ga su Abeeha na yi.Jikinta rawa ya ɗauka, Mammi ta riƙo hannunshi “Duk faɗar nan na Sulaiman ya zo ba tare da ka sani bane? Kayi hakuri ni ce na mata izinin fita ba haka kawai tayi fitan gaba gadi ba kuma ko mintuna biyar bai kai ba idan nima na yi laifi sai in ji…”Shiru yayi bai ce komai ba.Tana tsaye a gefe kaman yajin kosai kafafunta kaman za su kayar da ita saboda yadda suke rawa don mugun kallon da ya aika mata, ledan hannunta ya kalla”Ba kin ga kalar rainin da bana so ba Mammi? Mun ce ba mu dashi ne da zai kunso koma menene a leda ya kawo mata? Ko ta tambayi abu ba’a yi mata ba?””Saraki…! Bana so! ka ga bana so don Allah, ka duba yadda ka firgita ta? In kuma hankalina kake so ka ɗaga ka cigaba”Da ɗan faɗa tayi maganan, haushin kanshi ya ji ina ma ruwan shi da zai damu da tarbiyar ta? Shi ba wani tsiyar yake dubawa ba sai kar ta lalace da tara samari tun bata kai lokacin ba, Miƙewa yayi ya nufi fita daga ɗakin ranshi a haɗe fuskar nan murtuk, wani irin chill abu ne ke bin jikinta na tsoro, bata san me yasa shi baya wani damuwa da damuwarta ba a ranta take jin kaman bai yi na’am da zamanta a gidan nasu ba, ita idan ba don mammi ba wlh ko inuwa ba zata so haɗawa da shi ba bare har magana, gashi nan tana ta aikata laifin da zai ji haushinta.Kamshinshi ne ya daketa a sadda ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba ta lumshe ido sai da ta tabbatar ya tafi ta sauke numfashi ta isa wurin Mammi tana jin hawaye na tsinke mata “Mammi ki yi haƙuri ban san ba’a haka anan ba, na fita ne ba don wani abu ba sai don Roƙon da Dr yayi ta min a kan ko ba zan ɗauke shi Masoyi ba in ɗauke shi wa da zan iya neman abu a wurinshi yayi min, ya ce min Mamanshi ta damu tana so in je ta ganni ta ji lafiya ta don kaman ‘ya itama ta ɗauke ni wlh ba ni na roƙe shi ba Mammi kin ga da kyar na karɓa har saida ranshi ya ɓaci…”Dafa ta Mammi tayi “Natsu Afeefah! Ki natsu kar masifar Saraki ya dame ki, haka yake wlh kin ga su jidda basu isa su kula saurayi ba sai ya fara zuwa ya ganshi yayi bincike ya amince mishi kan ya zo idan yayi bincike bai mishi ba ko wayanshi suka sake ɗauka mai karbar su a gidan nan sai ya shirya, na sani a yanzu babu zancen aure tsakanin ki da Sulaiman shiyasa na bari kika fita, kuma ai ba’a mayar da hannun kyauta baya… Goben ki shirya sai ku tafi da Abeeha in ta dawo school ku gaishe da mahaifiyar tashi kinji?”Tsoro ne ya sake rufe ta jin yana duka, itama kenan zai iya bugun ta in tayi ba daidai ba”A’a Mammi ba sai na je ba, zan bashi uzuri…””Kar ki wani damu zan mishi magana”Ledar ta ajiye don ji take ko abin ciki bata sha’awar gani, hankalinta ba’a kwance ba ta tashi tayi ɗakinta ko da ta shiga sai da ta sakawa kofar key don ji take kaman zai biyo ta ya cigaba da faɗa.

Back to top button