Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 11

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

D’ago kanta ta kalleshi, da Idanunta wanda lokaci daya yanayin cikinsu ya sauya, musamman yadda maganar da taji ya fito daga bakin Abban ya daki zuciyarta  matuka gaya.

Abba Kabir kuwa ganin ta d’ago kanta ne yasa shima ya zuba mata ido, fuskarsa sam babu alaman wasa. 

Hakannne kuma yasa ta maida kanta k’asa, tare da d’an lumshe Idanunta, a hankali ta soma wasa da y’an yatsun hannunta.

Yayinda takejin zuciyarta na dan bugawa.

Dai-dai lokacinne kuma Aunty Dijat ta bud’e kofar d’akin ta shigo. 

Yanayin yanda tagansuda dinne kuma ya sakata sakin murmushi, tare da karasowa ta zauna  akusa da Jannart din.

Kallon Jannart din Aunty Dijat tayi, tare kuma da bud’e bakinta da niyar yin magana.

Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir saurin d’aga mata hannu alamun dakatarwa. 

Kallonsa Aunty Dijat din tayi, lokaci guda kuma itama ta sauke kanta k’asa.

Hakanne kuma yasa gaba ki d’aya d’akin ya dauki shiru, babu abunda ke tashi sai sautin fitan numfashi, da kuma ajiyar zuciya da suke ta saukewa dukansu akai akai.

Almost 10mn kafun Abba Kabir din ya sake d’ago Kai ya kalli Jannart, cikin tausayawa da kuma danne abundake cikin zuciyarsa yace.

“Jannart kinji abunda nace, Ina fatan bazaki bijirewa umarnina ba kamar yadda kika al’ƙ’warta min.”

Kai Jannart din ta d’ago Ahankali ta kalli Abban nata.

 Domin sai takejin maganganun nasa tamkar wani abu na daban, wanda bata tab’aji ko sanin akwai shiba.

Ita dai tasan kalmar Aure, amma batasan haka kalmar kan zuwarwa mace cikin zuciyarta ba, batasan ya rayuwar cikinsa yake ba.

Saidai koma meye ta sani bazata tab’a bijerewa umarnin Abban nata ba.

Idanunta tasake mayarwa k’asa, kana kuma Cikin sanyi ta jinjina masa Kai, alaman “Eh.”

Ajiyar zuciya mai k’arfi Abba Kabir din ya sauk’e, cikin kuma son sake tabbatarwa kansa amincewarta yace.

“Jannart duk da cewar bani nahaifeki ba, amma matsayin uba nake awajenki, haka kuma Kallon y’ata ta cikina nake miki, wannan yasa bazan tab’a yi miki dole ba, shin kin amince da hukuncin dana yanke akanki?”

Kanta ta sake jinjina masa, tare da bud’e Labb’an bakinta da takejin sun danyi mata nauyi a hankali tace.

“Eh Na amince Abba, duk hukuncin daka yanke akaina dai-dai ne.”

Numfashi Abba Kabir din ya fesar, tare da sake gyara zamansa.

Kana yace.

“Alhamdulillah naji dadi kwarai, Insha Allahu kuma yanzu akwai shirye shiryen da zamu fara, Domin banason lokaci ya ja da yawa.”

Kanta ta d’an langwabar gefe, kana cikin yanayin sanyi tace.

“To Abba, amma akwai abunda nake shiryawa, saboda ranan alhamis dinnan, zanyi wani program, Dan Allah Abba kabani dama, nasamu nayi shirin nan, Idan yaso daga baya komai ma sai ayi.”

D’an murmushi Abba Kabir din yayi, tare da cewa.

“Karki damu Jannart, shirin da nakeyi akannaki ma zaikai har bayan alhamis din, saboda haka kina da ishashshen dama na y’an wasu kwanaki.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e, tare da d’an sakin murmushi, saboda yanzu ta danji sanyi acikin ranta, Yayinda ta kuma k’ara samun hope akan cewar Lallai lailai bazata rasa aikinta ba.

Aunty Dijat kuwa Kallon Jannart din tayi, Yayinda takejin tasananin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarta.

Lallai Tabbas tasan cewa, Jannart din bata san komai ba, aharkar auratayya sai abunda ta karanta a musulunce, wanda hakan yasa dole tana buk’atar  mai taimaka mata. 

Sanin wasu abun a zahiriyar rayuwar duniya more Especially aure.

Tasan Jannart cikekkiyar janitalauce, sabida kan haka aka reneta aka bata tarbiya, bin umarnin na gaba da ita, ya zama komai na rayuwarta bata da zabin kanta ko ra’ayinta sai abinda manyan ta suka faɗa, shiyasa suke sarrafa ƙwaƙwalwarta sun hanata yancinta sun dakufeta bata da wani abu sai amsar umarni daga garesu.

Shiyasa ta kasance mai sauƙin kai da rauni kana ga tarin haƙuri. 

Wanda suke tasirin hanata tsayuwa kan ra’ayinta.

Hannunta Aunty Dijat din ta rik’o, kana cikin tausasawa tace.

“Naji dadi da kika amincewa maganan auren nan Jannart, Domin kuwa aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, acikin aure akwai abubuwa da yawa, farinciki da kuma akasin haka, amma ni naji ajikina cewar auren da zakiyi shine zai zame miki Tubalin farin cikin ki, Rayuwa zata sauya miki Jannart, zaki zamanto Mace mai y’anci, k’uncinki zai gushe, Yayinda haske zai bayyana acikin rayuwarki Insha Allah, sannan kuma ako da yaushe kiyi riko da addu’a, Domin abubuwa sukanyiwa bawa tsanani ne Idan yana wasa da addu’a, Addu’a makamin mumini ne Jannart, musamman gake, da ace bakya sakaci da addu’o’i da ko Junaid da yake yawan musgana miki, bazai tab’a samun daman fuskantar ki ba, saboda Allah zaina baki kariyarsa akoda yaushe.”

Kai Jannart din ta jinjina, cike da gamsuwa da maganganun Aunty Dijat din kuma tace.

“Insha Allah zanna rik’o da addu’o’i, Nagode sosai Aunty Dijat.”

Murmushi Aunty Dijat din tayi, tare kuma da cewa.

“Ba komai Jannart, Allah Ubangiji ya kawo mana saukin damuwarmu.”

Da Ameen suka amsa dukansu, Yayinda Jannart din kuwa ta d’an kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, ganin lokaci yaja sosai ne kuma yasata, d’an mikewa tsaye.

Tare da Kallon Abban nata tace.

“Abba zan tafi wajen aiki kada nayi latti.”

Kai Abba Kabir din ya jinjina, had’e kuma da mik’ewa tsaye yace.

“Allah ya kiyaye hanya Jannart ya kuma Kareki aduk inda kike.”

Da Ameen ta amsa, tare kuma da daukar jakarta, ta juya ta fice daga cikin dakin.

Sam bata damu da maganan auren da Abban yace zaiyi mata ba, saboda batasan menene zata tsinta acikinsa ba, wannan yasa ko tambayan wanda sa’a aura mata din da kuma sunansa batayi ba, Ita dai ahar kullum tamkar rak’umi da akala take, duk inda aka jata zuwa zatayi.

Saidai kuma tana da tabbaci  cewa Abban nata bazai yi abunda zai cutar da ita ba.

Koda ta fito compound din gidan, kaitsaye wajen motarta ta nufa.

Tana shiga cikin motar kuwa Drivern yaja suka tafi, Yayinda kattin guard dinta suka rufa musu baya. 

Kaitsaye hanyar tashar tasu ta Arewa24 suka nufa.

Jin yanda suka mik’i titi ne kuma yasa ta, jingina bayanta da jikin kujerar motar, tare da lumshe Idanunta.

Ahankali ta sauk’e wani irin ajiyar zuciya, Yayinda kalaman Aunty Dijat kuwa suka shiga dawowa cikin kanta filla filla.

“Aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, Aure shi zai zame miki tubalin ginuwar farincikin ki.” 

Abunda kwakwalwarta ke maimaita mata kenan, wanda kuma har yanzu ta kasa warware kalaman.

Meyasa Aunty Dijat din tace aure zai zame mata tubalin farin ciki? Menene acikinsa? Wacce kalan rayuwa ce zatayi, har kuma ta samu farinciki bayan zata zaune akarkashin wani ne wanda bata saniba bai santaba.

Ya yake irin Yah Junaid da Daddy ne ne ko irin Yah Azeez da Abba? Wai shin menene ma  manufar auren nata da Abba bai gaya mataba?

Tayiwa kanta duka way’annan tambayoyin da ko kusa bata da amsarsu, ba kuma ta da mai amsa mata su yanzu.

Batasan komai akan hakan ba, ba ta kuma tab’a tunanin hakan acikin kwakwalwarta ba, shiyasa takejin duk wata kalma da ta shafi aure, amatsayin bak’on abu. 

D’an numfasawa tayi, tare da watsar da duk wani tunani dake cikin ranta, dai-dai lokacin kuwa suka iso babban parking space dake cikin tv station din. 

Bayan Baba Ado ya gama dai-dai-ta parking din motar ne kuma ta fito, kaitsaye ta nufi cikin gidan tv’ nasu. 

Ahankali take taka k’afafunta, Yayinda kowanni taku da zatayi yake dauke da jan hankalin mai Kallon ta. 

Azahirin gaskiya kuma awajenta tafiya takeyi normal, Yayinda duk wani mai Kallon ta kuwa, ke ganin tafiyar tata tamkar tafiyar hawainiya, saboda komai nata na dabanne, tana da wani irin tsarin halitta mai matukar burgewa, wanda kuma ko ita kanta batasan cewar tana dashi ba.

Tura kofar babban office dinnasu tayi ta shiga bakinta dauke da sallama.

Jin Sauti da amon zazzakar muryar nata ne kuma yasa, duk mutanen dake cikin office din juyowa suka kalleta. 

Wani dogon tsaki Asiya taja tare da kauda kanta daga kallonta.

Ita kuwa Jannart Sam hankalinta ba a kanta yake ba, duk da irin Kallon da taga tanayi mata kuwa Amma bata damu ba.

Fuskarta d’auke da murmushi ta k’arasa wajen, Aysha Lawal da kuma Salman wanda suke zaune awaje daya suna duba wasu takardu. 

Murmushi Aisha Lawal din ta sakar mata, tare da cewa.

“Jannart Idi Saleh Dakata yau kinyi lattin zuwa wajen aiki, saboda haka sai munciki tara.”

Murmushi mai kama da dariya Jannart din tayi, har saida fararen hak’waranta suka bayyana, hakan kuwa shiyasa  dimples dinta duk suka lotsa.

Kafad’an Aysha’n ta d’an buga, kana cikin muryata da babu hayaniya sosai tace.

“Kai Aysha kwata-kwata fa mintuna 10, na kara akan yanda nake zuwa kullum.” 

“Eh duk da haka dai.”

Ayshan ta fad’a tana murmushi.

Jannart kuwa zama ta d’anyi agefe dasu, tare da dawo da Kallon ta ga Salman Wanda ya  saki idanu da baki yana Kallon ta.

Had’a idanu da sukayi ne kuma yasa shi saurin janye idanunsa daga kanta.

Itakuwa Jannart batare da ta fahimci komai na daga Kallon da Salman din keyi mata ba tace.

“Good morning colleague.”

Gashin kansa ya d’an Sosa kana awayance yace.

“Morning Colleague, fatan kin tashi lafiya ya jikin naki.”

“Da sauki sosai, Domin nama warke yanzu babu wani abu dake damuna.”

Jannart din ta fad’a tana me ajiye Jakarta,

Adai-dai lokacinne kuma Hajia Rabi’ah da Aunty Fauziya D Sulaiman  suka shigo, cikin sashin su Jannart din.

Ganin Jannart din da sukayi acikin office dinne kuma yasa, Aunty Fauziya D Sulaiman sakin murmushi, kana cikin jin dadi da kamala da mutuntaka tace.

“Masha Allah gaskiya Jannart ansamu lafiya, tunda har an fara fitowa office.” 

Murmushi Jannart din tayi, cikin kuma jin dadin kulawan da yan office din nasu ke bata tace.

“Alhamdulillah my Aunty Fauziya naji sauki, kuma Ina saka rai da fatan cewa Insha Allah Gobe ma zan gudanar da program dina.”

Kai Aunty Fauziyan ta jinjina, tare kuma da matsowa kusa da Jannart din sosai.

Cikin yin k’asa da murya irin ta maganan sirri tace.

“Masha Allah, amma Jannart kinaga kuwa Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din zaizo.”

Kanta tad’an langwabar tare kuma da juyawa, ta kalli Salman wanda shidinma kuma Kallon ta yake. 

Kai Salman din ya jinjina mata, cike dason bata karfin guiwa yace.

“Karku damu Insha Allah Zaizo.”

Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da daura hannayenta akan kafad’an Jannart din.

Murya atausashe tace.

“Karki damu Jannart, ko da ma ace bai samu zuwa goben ba, ai kina da sauran chance harna tsawon one week, Insha Allah kuma muna saka ran dacewa.”

Kai kawai Jannart din tad’an jinjina, tare da komawa ma zauninta ta zauna, lokaci daya kuma duk jikinta yayi sanyi, domin tasan gobenne kawai last hope dinta, kasancewar bata da tabbacin cewa, wani satin zata kasance available, musamman ayanzu da Abba Kabir yake kokarin fara shirye shiryen b’oyeta.

“Yah Allah Kabani sa’a.”

Tafad’a k’asa-k’asa, tare da maida idanunta ta lumshe, saboda gaba daya yanzun ta karaya da komai.

 Salman kuwa daya karanci tarin damuwa akan fuskar Jannart din, ji yayi komai na Office din baya yi mishi dadi,  duk yanda yaso ya daure zuciyarsa akanta kuwa baya tab’a iyawa.

Haka yake d’agowa time to time yana satan Kallon ta.

Itakuwa Jannart samma batasan yanayi ba.

Aysha Lawal ce kawai take lure dashi, fahimtar abunda ke ran Salman din agame da Jannart dinne kuma ya sakata sakin murmushi.

Batare kuma da tace komai ba taci gaba da ayyukanta.

Haka dai Jannart ta kare gaba d’aya wuninta a office din, duk yanda kuma taso kawar da fargaban dake ranta ta kasa.

K’arfe 5 dai-dai tayiwa su Salman da Aysha  Sallama,kaitsaye ta wuce gida. 

Koda suka iso gidan nasu, haka ta fito daga cikin mota gaba daya duk jikinta asanyaye.

Direct falonsu ta nufa, inda tana shiga cikin falon kuma wayarta dake rik’e a hannunta ta soma kara. 

Kallon ta ta mayar kan screen din wayar.

Lokaci daya kuma murmushi ya bayyana akan fuskarta, saboda sunan Yah Azeez da ta gani.

Picking call din tayi, tare da kara wayar akan kunnenta.

Sallaman da tayi dinne kuma yasa Daga can b’angaren Yah Azeez ya amsa mata, tare da cewa.

“My y’ar k’anwa Jannatuwa, bari na fara bada hakuri kafun ki shigo da korafin rashin kiranki da wuri da banyi ba.” 

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan shagwab’e fuska, tamkar Yah Azeez din yana ganinta. Tace.

“ai saura kad’an nayi maka fushi Yah Azeez, kuma da baka kirani yau ba ko hmmm, ko kakira bazanji rarrashi ba.”

Murmushi Yah Azeez din yayi, cikin tsananin so da Kaunar yar uwartasa yace.

“I’m sorry Jannart wallahi aikine yayimin yawa kuma na kira sau biyu Mom ke ɗagawa tace kina bacci, yanzu ya jikin naki, Ina fata kinji sauki sosai.”

Kanta ta jinjina had’e da cewa.

“Naji sauki sosai Yah Aziz, Domin yau har wajen aiki naje, yanzu shigowa ta ma gida.” 

“Masha Allah Lallai jiki yayi kyau, To Allah ya kara afuwa, sannan kuma ki kara hakuri kinji Jannart, Insha Allah watarana sai labari, komai da Junaid keyi miki zaizo ya wuce, kuma Allah zai saka miki akan duk wani cutarwa da Junaid keyi miki, shima kuma zai ga sakamakon abunda ya aikata.”

Idanunta ta d’an lumshe, saboda har acikin zuciyara taji sanyi da dadin kalaman Yayan nata, inama da ace shine akusa da ita ba Junaid ba, Lallai da taji dadin duniya, Domin ko ayanzu  da baya kasar, yana iyaka kokarinsa wajen bata kulawa, da nuna tausayawansa agareta. 

Numfashi ta d’an fesar kana  Asanyaye tace.

“Nagode Sosai Yah Azeez, kuma Insha Allah zan kara hakuri akan wanda nakeyi.”

Murmushin Jin dadi Yaya Azeez din yayi, Domin dama yasan tuncan k’anwartasu mai biyayyace, akan duk wani abu daka umurceta. 

Still cikin nuna kulawa yace.

“Yauwa y’ar k’anwata, yanzu fad’Amin akwai wani abun da kike buk’ata ne, ko kud’i sai na tura miki ta account, ki saya duk wani abu da kikeso.”

Murmushi tayi, hadi da cewa.

“A’a Yah Azeez bana buk’atar komai.

Domin last week Abba Kabir yayimin shopping, sannan kasan akwai kudi da yawa a account dina, ko salary na Idan anturomin bana sayan komai dasu.”

Ajiyar zuciya Yah Azeez din dake kan wayan ya sauk’e.

Nandai suka d’an tab’a hira kafun daga bisani sukayi sallama.

Bayan ta kashe wayar nata ne kuma ta lek’a kitchine ko zata ga Momy, saboda tunda ta shigo babu motsin kowa agidan.

Ganin kitchine din bakowane kuma yasa kaitsaye ta wuce bedroom dinta, saboda tanason yin wanka Tsarkin data samu.

 Akwai kuma wasu bayanai da zata had’a acikin system dinta. 

Acan B’angaren Dr. Rayyern Muhammad Mai-nasara kuwa zaune yake akan wata had’add’iyar royal chair, Yayinda yake sanye da wani had’add’en suit mai kalan ruwan k’wai ajikinsa. 

Daga gefe guda kuwa drinks da kuma Chocolate d’insa ne, sai kuma  sabuwar wayarsa Iphone daya k’ara saya, dake rik’e ahannunsa.

Inda kaitsaye ya shiga cikin contact d’insa, yana neman wani numbern tsohon abokinsa, Salisu, saboda yanason yiwa Salisu din ta’aziyya kasancewar yaji labarin rasuwar Baban shi. 

Yana cikin tsaka da duba contact dinne kuma, idanunsa suka sauk’a akan numbern Salman.

Numbern da Idan bazai manta ba, sune wanda suke son ganinsa, ya kuma yi musu alk’awari zuwa.

Saurin sanya hannunsa yayi ya dafe kansa, saboda sai ayanzu ne ma abun ya fad’o masa, gaba daya kwata kwata ya manta ma dasu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da dan cije Labb’an bakinsa.

Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Allah Nagode ma daka tunatar dani, Allah kada ka bani ikon daukan al’k’awarin da bazan iya cika shi ba.”

Jawo wayarsa yayi ya duba date da kuma rana.

“Today is Wednesday, gobe ne al’k’awarin dana d’auka kenan zai cika, Insha Allah zanyi kokari naje, kodan yaronnan ya tsira da aikinsa, ya kuma samu abunda zai ciyar da iyalansa.

Tabbas zanyi cancelling duk wani schedule dina na Gobe, har sai na samu naje tv station dinnan, bazan tab’a zama mai karya alk’awari ba Insha Allah bazan zama sanadin rasa aikinsa ba.”

Ya fad’i hakan, yana me mik’ewa tsaye, tare kuma da d’aukan laptop d’insa.

Kaitsaye ya koma wajen zamansa da yake na musamman, acikin katafaren office din da yake new company’n’ sa. 

Tahir Quest Palace.

Riyyam nsra ne kwance akan makeken gadon dake dakin hotel din, wanda kuma yanzun gama wayarsa da Mammy da kuma Zaiton. 

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da juyowa ya kalli, matashiyar budurwar dake kwance agefensa. 

Almost 1hour kenan yanzu da zuwan ta wajensa, wanda kuma itama sun had’u ne da ita anan Tiktok,  Yayinda itama take cikakkiyar celebrity ce a Tiktok din, sannan kuma yar asalin Nigeria ce cikin Kano tayi shuhura a iya tiƙa rawa da bin waƙa, ga iya sa fitinennun suturu masu bayyana tsiraici hakan yasa kasuwarta ke ci. 

Idanu Riyyam din ya zuba mata, Domin kuwa Wannan shine Karonsa na farko daya fara mu’amala da wata mace y’ar Nigeria. 

Yarinyar dake kwance agefen nasa, kuwa ganin irin Kallon daya ke mata ne, yasa ta kashe masa Ido, tare da turo masa kirjinta gaba, wanda ko kaya babu ajikinta.

Hakan ya faru ne kuma saboda sheke ayarsu da sukayi ita da Riyyam nsra din.

Wani irin nishadi takeji acikin zuciyarta, kasancewar Riyyam din yayi mata hundred percent. 

Shikuwa Riyyam da baya gajiya da tab’ewa, hannunsa yasa ya shafo kirjinta, cikin kuma yin k’asa da murya hadi da kashe mata idanunsa yace.

“Are you ready?.”

Idanu ita dinma ta kashe masa, hade da jinjina masa Kai alaman she’s ready. 

Batare kuma da ta bari ya kawo kansa ba, ta hade bakinsu waje daya. 

Akaro na biyu kenan yanzun da suka sake shigewa duniyar Mazinata, duniyar da muninta ya wuce misali, kyamatacciyar duniya marar kyaun gani mai cike da masifu wanda duniyar TIKTOK ya zamo kawali’unsu.

Bayan Riyyam din ya fito awankane kuma, ya shirya kansa cikin shigar daya saba yi ta kananan kaya. 

Wayarsa dake aje kan table ya d’auka tare da Kallon yarinyar da take kokarin saka kayanta. 

Bandir din fararen y’an one one k dake hannunsa ya cilla mata. 

Tare da d’alewa saman table din ya zauna, hakanan yakejin wani irin haushi, takaici, da kuma kunci acikin zuciyarsa, Yayinda yaji ko ganin yarinyar baya mason sake yi.

Sometimes kuma baisan Meyasa yakejin hakan ba, aduk lokacin da yayi sex da mace, bayan ya samu biyan bukatarsa sai yaji duk duniyar ma batayi masa dadi.

Itakuwa Yarinyar ganin da tayi mood d’insa ya sanja ne, yasa ta tattare kudin daya watso matan ta zuba acikin Jakarta. 

Bayan ta gama kimtsa kanta ne kuma tayi masa sallama ta tafi.

Kamar kuwa dama jiran tafiyan nata yake, Domin tana tafiya shima ya rufe dakin.

Bayan ya bada key din a reception ne kuma, kaitsaye ya fito daga cikin hotel din.

Taxi ya tara, tare da fad’awa mai taxi din ya kaisa can cikin Nassarawa G.R.A din.

Acan b’angaren Rayyern kuwa bai baro Companyn nasu ba, har saida ya kammala duk wani abu da yakeyi. 

Koda ya fito daga cikin company din kuma, kaitsaye motarsa ya shiga. 

Inda suka nufo gida. 

Isowarsu bakin gate din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowar Riyyam nsra din acikin taxi. 

Ganin motar Rayyern dinne kuma yasa Riyyam sakin murmushi,

Bayan ya biya mai taxi din kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin gidan.

Kasancewar tuni motar Rayyern din ta shige ciki. 

“Baba Maud’o barka da gida.”

Riyyam din ya fad’a alokacin daya bud’e karamar kofar gate din ya shigo.

Baba Maud’o dake zaune kuwa, ganin Riyyam dinne yasa kashi sakin murmushi. 

Cikin kulawa kuma yace.

“Yauwa barka dai Riyyam, tun safe yau baka zoba sai yanzu ka samu zuwa kenan.”

Kai Riyyam din ya jinjina tare da cewa.

“Eh, yau din nayi bacci sosai, kuma abokai na sun kawomin ziyara shiyasa Banzo da wuri ba.”

Kai kawai Baba Maud’on ya jinjina, Yayinda shikuwa Riyyam kaitsaye ya nufi inda motar Rayyern yake. 

Yana zuwa wajen kuwa Rayyern na fitowa daga cikin motar.

K’arasowa Riyyam din yayi, cikin sauri yace.    “Oyoyo Hamma Rayyern sannu da dawowa.” 

Ya k’are maganan yana me rungume Rayyern din. 

Rayyern kuwa zame jikinsa ya d’anyi, tare da jinjina kansa alaman yauwa. 

Kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa, kaitsaye duk suka nufi babban falon gidan.

Yayinda afakaice kuma Rayyern ke Kallon Riyyam din, Domin hakanan yaji zuciyarsa na raya masa wani abu na daban, dangane da Riyyam din musamman kamshin turaren jikinsa da yaji wanda ya tabbatar turaren matane. 

Shigowarsu cikin falonne kuma yasa.

Hankalin Mamy dana Ramadan harma da Abba ya dawo kansu. 

 Ganin Rayyern dinne kuma yasa Abba sakin murmushi.

Yayinda Riyyam kuwa ke biye dashi abaya.

Karasowa cikin falon sukayi suka zauna.

Inda Riyyam ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba da Mamy, fuska asake duk suka amsa masa.

Rayyern kuwa da ya Zauna akan kujeran dake gefen na Mamy.

Kallon Abban nasu yayi tare da cewa.

“Abba Mamy barka da gida.”

“yauwa Rayyern barka dai ya company’n.”

Abba ya tambaya.

“Alhamdulillah Abba komai yana tafiya dai-dai an kusa gama haɗa komai.” 

Rayyern din ya fad’a yana me d’an gyara zamansa, tare kuma da sauk’e idanunsa akan, Riyyam wanda yaje ya manne da jikin Ramadan. 

“Masha Allah Allah ya taimaka.”

Abba da Mamy suka hada baki wajen fad’an hakan.

“Ameen.” Ya amsa still yana mai Kallon Riyyam.

Kwarai so yake ya fahimci yaron, saboda yarda da abunda zuciyarsa ke gaya masa, yanaji ajikinsa cewar yaron kamar yana bin mata, musamman Idan akayi duba da irin rawar kan da yake dashi, ya cika rawar Kai da yawa.

Janye kansa daga Kallon Riyyam din yayi, saboda bayason yana shiga abunda bai shafesa ba. 

Ramadan kuwa dake rik’e da wayarsa d’ago kansa yayi ya kalli Rayyern din. 

Cikin sigar lallashi hadi da roko kuma yace.

“Yauwa Hamma Rayyern dama kai nake jira ka dawo, please Hamma Rayyern Dan Allah ka fito da mata kasamu kayi aure, kaga Abba yace bazanyi aure ba harsai kayi, ni kuma Allah yanzu aure nakeso nayi, bana son na rasa  Rayhanna please Hamma na.” 

ya k’are maganan yana me d’an langwab’ar da kansa gefe. 

Shikuwa Rayyern d’ago kansa yayi, da kuma fuskarsa wacce ta sanja kala zuwa yanayin bacin rai. 

Wani irin kallo ya watsawa Ramadan din, cikin hade fuska yace.

“Rufe min baki Ramadan  kada fa ka tunzura min zuciya Kaine zaka tsaramin yanda zan tafiyar da rayuwata? Ko ka fini sanin abunda nakeyi ne, da har zaka zo kana cewa wai nayi aure! Kai ubana ne!? ko yayana!? kama fini sanin abinda ya dace kenan?.” 

Rayyern din ya k’are maganan cikin fad’a. 

Wanda hakan yasa Ramadan Dan sunkuyar da kansa, cikin yanayin sanyi kuma yace.

“Ayyah Hamma Rayyern kayi hakuri Insha Allah bazan sake ba kaji kayi haƙuri.” 

Kai Rayyern din ya kawar, Yayinda Abba da Mamy kuwa suka kalli junansu. 

Ramadan kuma mik’ewa tsaye yayi, tare da kama hannun Riyyam-nsra suka fice daga cikin falon. 

Fitansu daga cikin falonne kuma yasa Abba d’ago Kai ya kalli Rayyern din. 

Yayinda su Ramadan kuwa suna fita, kaitsaye wajen Baba Maud’o dake zaune abakin gate suka nufa. 

Ganin su dinne kuma yasa Baba Maud’o sakin murmushi. 

Bayan sun zauna akan dogon bencin da Baba Maud’on ke kaine kuma.

Baba Maud’on Ya kalli Riyyam-nsra tare cewa.

“Riyyam ya mutanen can k’asar taku, da su Mammyn ka da Zaiton.”    

Murmushi Riyyam-nsra yayi, tare da gyara zamansa ya kalli Baba Maud’on cikin kuma jin dadi yace. 

“Munyi waya dasu dazu kowa da kowa yana nan lafiya, sunma ce na gaishe da kai, saboda na tura musu hotonka, har Zaiton tana cewa wai itama zata zo ka nad’a mata irin abunda kake sawa afuskarka, wai zatana boye fuskarta saboda Samarin dake damunta.”

Yar dariya Baba Maud’o yayi, tare da jinjina kansa.

Cikin jin dadi yace.

“To shikenan Idan tazo zan koya mata yanda ake na dawa, ai rawani ne ba komai ba, nadashi kuma ba wahala.”

“To Baba Maud’o nima dai ai watarana zaka koya min ko, sai naje na koya mata.” 

Kai Baba Maud’on ya jinjina alaman.

“Eh.” Daga haka kuma suka ci gaba da hiransu.

Ethiopian.

Adai-dai lokacin ne kuma Mammy dake zaune akan sallaya ta kurawa, hoton dake kan screen din wayar nata idanu, wanda kuma hoton Baba Maud’o ne da Riyyam ya turo mata. 

Azahirin gaskia ba kuma tana Kallon hoton da wata manufa ko tunani bane.

Kawai dai tana mamamkin irin shigar da taga mutumin yayi ne, saboda su anan basu tab’a Ganin irin shigar ba. 

Ajiye wayar nata tayi tare kuma da watsar da duk wani tunani dake ranta, kaitsaye ta mike daga kan sallayan ta shige kitchine. 

 Acan falo kuwa Abba dake Kallon Rayyern d’an gyara zamansa yayi.

Tare da  fuskantar shi kana cikin yanayi masifa faɗa da kuma umarni yace. 

“Uhmmm RAYYERN kenan.

Saboda kawai yace maka kayi aure shine kake daka masa irin wannan tsawan? Da ɗaga jijiyoyin wuya.

To shi meyene laifinsa, saboda kawai yace ka cika martabarka, ka kuma raya sunnar Annabi Muhammad SAW shine, yayi laifi?”.

Ya ƙare mgnar tare da tsareshi da idanun 

Da dole yasa RAYYERN yayi ƙasa da kansa.

Shi kuwa Abba kwaffa yayi tare daci gaba da cewa.

“Yoh wai kai azatonka da tunaninka haka zaka ta zama babu aure ne, saboda kawai kaga na zuba maka ido tsawon shekaru, kayi tunani da hankalin ka fa Rayyern, ayanzu Kai ba yaro bane, Domin kuwa kabawa shekaru 30 baya, shin kana tunanin banason yin aurenka ne? Ko atunaninka bana da buk’atar Ganin aurenka ne?  To kasani duk da cewar nasan tabbas na sakar maka ragaamar komai, na tara maka ayyukan da sukafi karfinka, bawai Ina nufin ka zauna haka babu aure bane ba wurin aiki kawai nake son ganin kamalarka ba harda aure,  Tabbas banajin dadi aduk sanda ka nuna cewar babu maganar aure kwata-kwata agabanka, kaine babba akan Ramadan, ya kuma zama dole kayi aure, Domin duk wani Namiji mutumcinsa da Darajarsa bata cika ko a idanun mutane, har sai in yana da aure, komin dukiya da mulkinsa kuwa, aure shine abunda ke maida Rabi ya dawo Guda,  ka d’aga mutumci da darajarka ta hanyar yin aure,  Allah dakansa zai dubi al’amuranka, amma ace akoda yaushe Kai baka da zance sai na cewar bakason aure…”

D’an gyara zamanta tayi, tare da sake fuskantar cameras din dake shooting fuskarta.

Ajiyar zuciya ta d’an sauke tare da nemo jarumtarta dake suɓuce mata,

cikin Taushi da kuma amon  muryanta zakin tace.

“Assalamu Alaikum Masu kallonmu, sannunmu da arzikin sake saduwa, acikin shirinmu mai farinjini wanda mukeyi Domin farincikin ku, wato Bak’onmu na Mako, To ayau dai shirin namu ya gam da katar yayi babban kamun  gayyato muku wani babban bak’o, wanda nasan idanuwanku  suna cike da dokin ganinsa. Wannan bako kuwa ba kowa bane face. Dr…!”.

Sai ta kuma datse sunan tare da sakin murmushi.

Wanda hakan yasa kab masu kallo suka ɗokanta da son jinnwayene baƙon makon.

Mayafin kanta ta ɗan gyara tana mai jin harshen ta bazai iya furta sunansa ba, cikin nitsuwa ta tare da lumshe taci gaba da cewa.

“Sanannen mutumin da sunansa yayi shuhura acikin kasarmu Nigeria dama wajenta baki daya, nasan da yawan masu kallo basu tab’a Ganin wannan bak’on namu ba.

Dan yauce rana ta farko daya amsa gayyatar wata kafar sadarwa ta jarida, da TV. Alhamdulillah sai namu a yau.

 Kasancewarsa Babban Doctor kuma babban d’ankasuwa da duniya ke damawa dashi, saboda haka yau dai gamu gashi, zakuma mu haska mukushi, inda zai fayyace mana koshi din waye.” 

D’an tsagaitawa da maganan nata, tayi tare da juyowa Ahankali ta fuska ce sa.

Cikin muryarta mai taushi tace.

“Doctor barkanka da zuwa, barkanka kuma da shigowa cikin wannan tasha tamu mai Al’barka, da fari dai munaso ka gabatar da kanka ga masu kallonmu.” 

Numfashi ya d’an sauk’e, batare kuma da wani sakin fuska ba, ya dago da kansa ya d’an kalli cameran a fakaice, cikin muryarsa da ako yaushe yake kara bayyana asalin wanene shi yace.

“Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.” 

Ya k’are maganan atak’aice, Cikin kuma halin nitsuwa. 

Kai Jannart din ta jinjina, tare da hade yatsunta awaje daya, cikin tsananin kwarewa da sanin makamar aikinta tace.

“Masha Allah to Dacta, yanzu dai ka gabatar da kanka awajen al’umma, saura kuma mu shiga cikin shirin namu ka’in da na’in,.

Dai-dai lokacin kuma aka ɗan ɗauke fuskokinsu aka sa ɗan sautin tambarin tashar Arewa 24 din.

Kana aka dawo dasu.

Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi a fakaice kana a hankali tace.

“Shin amatsayinka na cikakken Likita, wanda kasa keji dashi, wacce irin shawara zaka bawa al’umma dan kula da lafiyarsu da matakan kariyar riga-kafi?.

Sannan kuma ya kake Ganin irin yanda al’amarin k’asarnan yake, ma’ana irin halin da al’ummar k’asar take ciki, da kuma irin k’alubalen da muke fuskanta more Especially wurin kiwon lafiyar kananan yara da mutanen karkara da tsofaffinmu, Sannan wani irin hanya da kuma mataki zamu bi, Domin mu samu nasara akan yaƙar cututtukan dake addabar al’ummar ƙasar mu?

Then menene matsalarmu aharkar malaman kiwon lafiya?”.

Kanshi ya ɗan kauda gefe tare da yamutsa fuska, ɗan gajeren tsaki yaja.

Ji yadda yarinyar nan take zuba babu ƙaƙƙautawa kamar carbi ya tsinke ko numfashin bata ja.

Ta wani jero min tambaya kusan goma, a dungule.

Ni Radio ne ko ni parrot ne da zan iya haka.

Duk yayi tunanin cikin second 5.

Numfashi ya ɗan fesar kana cikin haiba da dakewar murya yace.

“Privet Hospital!!!

Sune matsalan kiwon lafiyar kasarmu.

 Domin sune suke dak’ushe asibitocin gwamnati,  har suke zama ba masu inganci ba.”

Ya fad’i maganan kai tsaye, batare kuma da wani dar ko shakka ba.

Jannart kuwa Kai ta d’an jinjina, tare da sake rik’on wani farin card dake hannunta, saboda acikine duk wani tsare tsaren tambayoyin da zatayi masa suke. 

Kanta ta d’ago daga Kallon takardar da takeyi, still kuma Cikin muryarta da akoda yaushe take fitar da daddad’an sauti tace.

“To Dakta. munji abunda kace. Kuma al’umma zata iya gamsuwa da hakan.

Toh amma kamar wani mataki za’abi, Domin asamar da ingancin asibitocin Gwamnati da kiyaye lfy?.”

Numfashi ya ɗan fesar a hankali kana yace.

“Dole gwamnati ta tsaya ta gyara asibitotin ta, ta ingantasu hade da kawo nagartattun kayan aiki, da kuma kwararrun ma’aikata, baya ga haka kuma ta rika biyan likitotin isassun kudaden da zasu iya biya musu bukatunsu, saboda mafi akasari acikin kasar bawai Nagartattun Doctor’s dinne  bamu da suba, kawai dai basa samun yanda suke sone, hakanne kuma yasa suke fita wasu k’asashwn suje su fara aiki Acan, ko kuma kowannensu saiya zaga gefe yaje ya bud’e asibitin kanshi, saboda baisamu yanda yake so a gwamnati ba, wannan dalilin yasa ayanzu asibitocin gwamnati suka lalace suka zama kara zube,, Domin anriga da ancire  Tubalin abunda aka gina asibitin akai haka yasa duk mai ƙarfi da yar wadata bazaibi ta kan asibitin gwamnatin ba, wanda kuma da al’ummar ƙasa aka ginasu.

Sannan yana da matukar muhimmanci ga  iyayen yara  suke kula da tsabtar jikin raya da muhalli da abinda zasuci domin shine babban rigakafi.”

Ya k’are maganan yana me gyara zaman necktie din dake wuyansa. 

Sosai yayi masifar kyau yadda yake dan jujjuya fararen yatsunshi

Inda Jannart kuwa ta ci gaba da cewa.

“To Doctor yaya za’ayi agyara matsalar Government Hospitals din domin in ƙantasu ta yadda al’ummar ƙasa zasuje garesu da kekkyawan yaƙini!?.”

Dan muskutawa yayi still kuma cikin rashin tsoro ko fargaba cikin yaƙinin da Kekkyawar manufa yace.

“To Da farko dai asibitotin gwamnati abunda zai gyarasu abu maisauki ne!?”.

Da sauri ta ɗan fuskanceshi tare da cewa.

“Duk da lalacewar da sukayi gyaran mai sauƙin ne? Ta yaya ko kuma ta ina gyaran zai fito da sauki!?”.

Cameras din ya ɗan kalla kana ya gyara zamanshi tare ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin masakaicin amo yace.

  “Idan har gyara akeso ta yadda zasu in ƙanta tofa dole daga kan, Shugaban k’asa, Governors, Ministers, senator’s har zuwa kan ciyamomin kana kama daga Sarki, Waziri, Galadima, Wambai, Chiroma, Durbi, Garkuwa, Ɗan buram, Majidadi, Ma’aji,  dama duk wasu masu fad’a aji, na siyasa da masarautun gargajiya. suyi kokarin daina zuwa asibitotin kudi, ko fita kasashen waje Dan duba lafiyarsu, su tsaya su ingata asibitotin Gwamnati, ta hanyar dasu kansu asibitotin zasuna basu Kekkyawar kulawa, 

Ya zama asibitin da Sarki zaije.

To shi fadawan sarki zasuje.

Kana asibitin da shugaban kasa zaije ya zama shine na talakawa, ta hakane zai sa shugabanni su san halin da asibitocinsu suke ciki, da inƙancin likitocin da kayan aikin.

Haka zai sa a kula da in ƙancin asibitocin.

 Domin duk wani asibitin gwamnati matukar akwai ingantattun Doctor’s da kayan aiki da watar tsabtacewa.

Toh  dai-dai yake da duk wani asibitin kudi, hakanne kuma zaisa asibitotin kudin su dakushe, su durkushe.

saboda yawnacinsu bawai anginasu Dan taimakon al’umma bane, anginasu ne kawai saboda neman kudi irin na yaki haram yaki halal, tayanda talaka bazai tab’a amfana dasu ba sai dai su cika aljihunsu.”

Da sauri Jannart ta juyo ta kalleshi.

Ido cikin ido sukayi da juna,

Bakinshi ya taɓe tare da yimata wani irin munafukin harara, hakane yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta 

Kai  ta jinjina, cike kuma da gamsuwa da kalaman nasa tace.

“Tabbas maganarka tatafi Kan hanya mai kyau, sai-dai kuma amma baka ganin yin hakan zai dakushe mutane da dama, musamman ga masu privet hospital kamar yanda ka fad’a!!!.”

Kansa ya d’an girgiza, sannan kuma akaro na farko da tun zamansa awajen ya dago kansa da nufin  ya kalleta da kyau dan tambayar da tayi masa.

Saidai ko secan daya bai dauka yana kallontan ba yakau da kansa gefe.

In don’t care manner yace.

“Hakan ba wata matsala bace ai, Domin bani da yakinin cewa yin hakan zai tauye musu hakkinsu”.

Da sauri ta kuma cewa.

“Toh kuma kake bada shawara a rushe asibitocin?”.

Wani irin kallo ya ɗan watsa mata.

Sabida ta mishi tambayar cikin gajin haƙuri irin nasu na ƴan jaridu.

Dan bata tsaya taji ya dasa Ayaba.

Koda yake haka suke.

Yan jaridun suna jin daɗin jefowa mutun tambaya kamar sauƙawar aradu ko kuma titsiye.

Cikin tsare fuska yace. “Dama meyake sawa su bude nasu asibitotin?”.

Ya mata tayarma tare da tsareta da ido.

Yar-yar haka taji tsikar jikinta na tashi.

Haka yasa da sauri ta kauda kanta gefe.

Shi kuwa kai ya jin jina tare da cewa.

 “Baki sani bako?

To bari in gaya miki…”

Ya kare mgnar yana mata hararan ƙasan ido kana yaci gaba da cewa.

“Dama rashin samun isasshen abunda zasu rufawa kawunansu asirine, saboda sometimes acikin asibitotin Gwamnatin, gwamnati bata biyansu al’bashi akan kari, baya ga haka kuma bata basu isassun al’bashin da zasu dauki nauyin iyalansu sabida gwamnatin tayiwa malaman jinya dana makarantu riƙon sakainar kashi Alhamdulillah gwarama wannan gwamnati da muke ciki.

Duk da haka ana buƙatar ƙari.

Domin duk lokacin da Gwamnati ta fara biyansu isassun al’bashi, To ba wani abu da zaisa suje su bude privet Hospital toh ko sunje sun buɗewama wa zai je musu in dai asibitocin gwamnatin nada inkanci , Domin ak’asarnan ba yawan asibiti muke da bukata ba, ingancinsu kawai shine abun buk’atar mu, tayanda  talaka da maikudi da fulanin daji zasu samu gamsashshiyar kulawa, batare da nuna wani banbanci ba!!!.”

Ajiyar zuciya Jannart ta sauk’e, kana kuma cikin yanayin nutsuwa tace.

“Mungode sosai Dr. inafatan kuma Gwamnati zataji shawarar daka bada kuma tayi aiki dashi, yanzu kuma zamu shiga babi na biyu. wanda ya shafi b’angaren kasuwanci kafin mu dawo nan a likitance.

Yah Salam shine abinda ya faɗa a ransa.

Sabida ya lura yau bakinshi sai yayi tsami sabida magantuwa da wannan fitinenneyar yarinyar take sashi.

Kamar a tsakiyar kanshi yaji ta kuma cillo mushi tambaya.

 “Shin Dakta wacce irin shawara zaka bayar, agame da yanda sha’anin saye da sayarwa ya zama acikin k’asarnan,  misali ta yanda ayanzu kayan abinci yayi tsada sosai, akullum wasu daga cikin yan kasuwa k’ara farashin kayansu suke,  rayuwa tayiwa talaka tsada, manyan y’an kasuwa da kamfanoni sun had’e kai da baki  waje daya, Koda yaushe farashin kaya hauhawa yake,  tayaya ne za’a samawa al’umma sauk’i, musamman manoma, wanda sune ma suke noma abincin amma kuma Idan ya shigo kasuwa sai yazo yafi karfinsu, shin wacce shawara zaka iya bawa manoma?.”

Numfashi ya dan fesar ta bakinsa, saboda yanda yaji labbansa sun soma gajiya da yawan motsasu da yake.

Hakanne kuma yasa batare daya dago ya kalli ko cameran ba, saidai atausashe yace.

“Shawarar da zan iya bawa Manoma itace, duk wani manomi Idan har ya noma abunda zaici, To kada yayi gangancin saidawa, har sai ya tabbatar daya ware ishashshen abincin da zai isheshi, har na tsawon wata shekarar da zai sake noma wani abincin, kafun nan sai yazo ya saida wanda zai sayar, saboda gudun kada ayi  gaban mai haƙar rijiya. kai ka noma ka gama shan wahala, sannan kuma ka tattara ka sai dashi lokacin da yake araha, bayan y’an wasu watanni sai yayi tsada, ga kuma wanda kake dashi ya riga ya k’are ga damuna ta sako sama ruwa ƙasa ruwa, fita nemowar ma wata rana sai ya gagara, kaga kenan nakan daka saida shi zaka sake zuwa ka saya, akan farashi mai masifar tsada,  kenan Kai Manomi kaine ka wahala a banza.

Sannan kuma ya kamata manyan kamfanoni su dinga tausayawa talakawa, su daina yi musu irin wannan hawan k’awaran, zuwa su sai abincin manoma tun yana gona basu shigo dashi gari ba su kuma manoma ku farga da wannan sagegeduwar da akeyi muku.

Sannan kuma su manoman kansu, su daina sayarwa masu manyan kamfanoni abincinsu tun yana gona, saboda wasu tun abunda suka noma yana yabanya suke saida shi, atunaninsu ko da ace abun da suka noma din baiyi kyau ba ko sanadin fari ko tsuntsaye ko kwari ko tsutsa, su dai sun samu kudi, da yawan mutane basu san al’barkar dake cikin kayan gonansu ba, saboda haka yana da kyau, ka dinga girbe abunka kana gyarawa da kanka, ka kididdige abinda ka samu ka ware na buƙatunka kafun ka mik’ashi ga wasu, sannan kuma duk wani manomi yayi kokarin saida abincin daya noma, akan farashi mai kyau, saboda ko yaya guminsa ya keci.

 Domin shi kadai yasan wahalar daya sha wajen noma ta, sannan yanzu Idan akayi dubi, gaba daya manoma da talakawa su suke shan wahala, musamman Idan aka shiga cikin damuna, haka komin ruwa da iska zasu tsaya neman abunda zasu rufawa kansu asiri suyi noma dan ciyar da al’umma duk kudinka fa, in manomi baiyi noma koda kuɗin ka bazaka samu abincin ba, shin zakaci kuɗin naka ne!!!?.  Sannan ku kuma y’an kasuwa da kamfanoni masu karawa kayan abincinsu kudi, ba komai kuke ciba face *RIBA* haramtacciya, wanda kuma kowa yasan hakan ba abubane mai kyau bane,  ga wanda suke sayan abinci su b’oye sai yayi tsada su fito dashi, suma duk Allah naganinku, kuma Allah da kansa baya tausayawa wanda baya tausayin na kasa dashi.”

Kai gaba daya mutanen dake boye abayan cameras din suka jinjina, hatta MD da kansa shima ya samu cikakkiyar gamsuwa da bayanan da suka fito daga bakin Dr. Rayyern din. 

Ba kuma a iya cikin tv station din ba, har acikin gaba daya k’asar tamu, mutane da yawa dake Kallon Live Program din sun samu cikakkiyar gamsuwa, Yayinda kalaman Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya ratsa zuk’atansu, ciki kuwa harda mafiya yawan manoma da suke kallon shirin, sabida Tashar Arewa 24 TV tayi zarran  birni da ƙaune suna kallonta maza da mata manya da yara. 

Adai-dai lokacin kuma Abba Kabir  zaune yake agaban tv yana Kallon shirin,  shi kansa ya gamsu da kalaman Dr. Rayyern din, saidai kuma sosai zuciyarsa ta cika da tsananin mamakin, ganin da wanda Jannart din ke hira yau.

Acan babban falon gidansu Jannart din kuwa, Alhaji Idi Sale Dakata, Dr. Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa ne, zaune sun zubawa babban TV plasma din dake cikin falon idanu. 

Wanda kuma yanzun akayi musu kira na musamman, akan su kunna tashar Arewa24 Dan Ganin hirar da akeyi da Dr.Rayyern din.

Hakance kuma ta kasan a wurare da dama yadda wasu ke kiran wasu manyan ƙasar suna shaida musu su kunna tv tashar Arewa 24 TV suga program ɗin da akeyi da Dr Rayyern Mai-nasara. 

Jin abubuwan da Rayyern din ya fad’ane kuma, yasa Alhaji Abdu Tababa yin k’wafa, kana cikin takaici yace.

“Amma dai wannan yaron anyi d’an iska, mai tsaurin ido, kujifa abunda yake fad’a, wai gwamnati ta rushe asibotin kudi ta inganta nata, Lallai yaron nan bashi da tsoro.”

“To shi nashi asibitin na uban meyene,  shegen yaro mai jajayen kunnuwa.”

Cewar Dr. Lukman da yakejin kansa kamar ya kurma ihu yayi fiffige yaje ya shaƙo wannan yaron.

Yayinda Alhaji Idi Sale Dakata kuwa ya rumste idanunsa, saboda shi ayanzu ko son Ganin yaron bayayi, hasalima gaba daya tunaninsa ya tafi ne akan yanda zai ga bayan Rayyern din, saboda al’ƙawari ne da yayiwa kansa cewar saiya b’atar da yaron daga Doron k’asa.

Acan cikin tashar ta Arewa24 kuwa, Jannart ce ta sake gyara zamanta, batare kuma da ita ma ta d’ago kanta ta kalli Dr. Rayyern MAI-NASARA dinba tace.

“Toh Doctor mu dan koma baya.

Kaba da shawara akan cewar aduk’ar da asibitotin kudi, a tada na Gwamnati, ta hanyar zuba ingantattun likitoti da kuma kayan aiki, To irinku fa masu asibitotin kudi yaya zakuyi kaida ire-iren ka masu privet Hospital’s, kodai kuma zaku dawo aiki a asibitotin Gwamnati ne! Ku watsar da naku asibitocin!!?.”

Cikin gamsuwa da yarda da kai yace.

“Kwarai kuwa, saboda ai hakan bawai gazawa bace, Indai muka had’e hannu da Gwamnati dan musamar da ingantaccen kulawa ga al’umma, To mu hakan kamar alkhairi ne agaremu, ba kuma najin hakan zai tauyemu ko ya ragemu da wani abu.”

Ya fad’a atak’aice saboda ya fara gajiya da amsa tambayoyin yarinyar mai shegen baki cai-cai surutu tuni yawun bakinsa sun kafe. 

Hannunshi yasa ya ɗan shafa sajenshi har zuwa kan lips ɗinshi sabida ji yayi kamar bakinshin yayi tsawo ne da surutu. 

Jannart kuwa, again cikin sanin makamar aikinta tace.

“Amma kamar baka goyon bayan duk wani privet hospital, in na fahimceka.

Kuma  naga kaima kana da naka hospital din, wanda kuma bana gwamnati bane, ya akayi to hakan ta kasance? meyasa baka had’a hannu da Gwamnatinba!? kun ingata Koda asibiti daya ne!!!?”.

Wannan Tambayar  ta saka duk magautan

 Dr. Rayyern Mai-nasara  dake Kallon tv suka saki Murmushin mugunta, saboda atunaninsu yarinyar ta kawosa makura inda bazai iya amsa tambayoyin nata ba Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.

Saida yaji tamkar ya shiga TV ya goya ɗiyar tasa Jannart, sai yakeji kamar dan su tayi mishi wanna tambayar dan ta kure musushi.

Dr Lukman kuwa hannunshi ya dunƙule tare da jinjinawa Jannart harda yimata alamar kiss dan masifar daɗi. 

Ita kuwa Jannart batama san sunayi ba, kuma bada wata manufa tayi tambayarba sai dan dacewar hakan tunda tasan yanada asibitin.

Shikuwa Rayyern ko ajikinsa baiji wani abu ajikinsa dangane da tambayar da Jannart din tayi masa ba, hasalima Dan gyara zamansa yayi, cikin kuma kwarin guiwan da ako yaushe yake tare dashi yace.

“Banyi karatun likita Dan yin aiki akarkashin wani ba, asali Tubalin karatuna shine Idan na kammala na raya  asibitin, dake gine tun kan zuwata duniya.

saboda amfanar al’umma, bawai iya mai kudi ba kawai harda talakawa, saboda babu wani wanda, asibitin Mai-nasara Hospital yafi karfin zuwansa, koda kuwa bashi da karfi, Mai-nasara Hospital muna da foundation na taimakawa marassa karfi dashi mukeyin dukkan taimakon daya dace, sannan kuma Mai-nasara Hospital bawai irin asibitotin nan ne da kowa ya sani ba, Ina da confidence akan Hospital dina, ako ina kuma zan fada batare dajin na fadi ba daidai ba!!!.” 

Kai Jannart ta jinjina, saboda ayanzu kam amatsayinta na y’ar jarida ta gamsu da duk kalaman mutumin, musamman da ta fahimci with full confidence yake magana, ba irin na wasu mutanen ba, da mafi yawancin maganansu Kame kame da kuma k’aryane. 

Domin sometimes ma suna fad’an karyane Dan su kare kawunansu daga titsen yan jarida. 

Daga can gefe kuwa, Asiya ce dake tsaye take ta aikin bankawa Jannart d’in Harara.

 Yayinda takejin wani irin kuna da radadi acikin zuciyarta, Lallai Tabbas taso ace itace ta samu wannan damar, taso ace yau itace akan stage din tare da mutumin da kyau, nutsuwa da kuma haibarsa suka matuk’ar tafiya da hankalin ta,  kana kuma mutumin da take ganin cewa, samun daman magana dashi ma wani matakin nasara ne.

Kamar kuwa yanda Asiya ke jin tukukin bakinciki acikin zuciyarta, haka ma Dr Lukman,  yakejin kamar ya shiga cikin tv’n ya shak’o wuyar Dr Rayyern. 

Abunda yasan bazai taba samun daman aikatashi ba a gaske kenan.

Kallonsa ya mayar gasu Alhaji Idi Sale Dakata, cikin takaici yace.

“Lallai wannan Dr Rayyern din shege ne, ko ta Ina so yake ya tauyeni, bakinsa baya tab’a mutuwa, kowacce tambaya akwai amsarta acikin kansa.”  

Murmushin daya fi kuka ciwo Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, cikin takaicin daya lullub’e zuciyarsa yace.

“Nan kusa wannan bakin nasa bazai sake motsawa ba, wannan alk’awari ne na daukawa kaina.” 

Murmushin Jin dadi Dr Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa sukayi, saboda sanin hali irin na Alhaji Idi Sale Dakata da sukayi, Domin sunsan duk abunda yace zai aikata saiya aikata Tabbas.

Ab’angaren Gidansu Rayyern kuwa, Abba Mamy, Ramadan da kuma Riyyam-nsra ne zaune afalo suna kallon shirin, gaba daya sun bada  hankalinsu akan shirin, musamman ma Abba, da tunaninsa ya rabu izuwa wani waje na daban. 

Kallon Rayyern da kuma yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi yake baya ko k’yaftawa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin abu na daban. 

Su Ramadan kuwa Hamman nasu suka tsurawa ido,suna mai jinjina kawunansu saboda irin amsoshin da Hamman nasu ke bayarwa, yana matukar ratsa zuciyarsu,  acikin zuciyarsu kuwa babu wanda bai yaba da irin kyawun yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi ba. 

Jannart kuwa, akaro na barkatai ta d’ago ta kalli camera’s din dake haska su, mike din dake gefenta ta gyara, tare da cewa.

“Kamar dai yanda kuka sani, ayanzu zamu bud’e layukan wayoyinmu saboda, masu kira.

 Dan fadar ra’ayoyinsu da tambaya, ga numbar layin namu kamar haka…

Tana gama fad’an numbers dinne  kuma ta kunna wata waya mai kaman telephone dake aje agabansu, kan wani had’add’en table.

Aikuwa kaman jira ake sukunna layin saiga kiraye-kiraye suna shigowa. 

Wanda manyan mutane-ne suke kiran.

Numfashi ta ɗan fesar tare da gyara zamanta.

Kana ta ɗan kalli wayar da wani kiran ya kuma shigowa tun kan ta ajiyeta.

Picking call din Jannart tayi, tare kuma da latsawa tasa wayar a hands free. 

Cikin zazzakar muryarta tace.

“Assalamu Alaekum.”

Daga can b’angaren aka amsa mata, da murya irin ta manyan mutane.

Jin hakanne kuma yasa ta cewa.

“Barka da shigowa filin bakon mako.”

“Yauwa Barka dai”.

Aka faɗa daga daya sashin cikin girma.

Ita kuwa Jannart lumshe idonta tayi tare da cewa.

 “Ko zamu iya sanin waye akan layi?.”

“Sunana Alhaji Abubakar Ginsau S.A protocol na gwamna, nakira ne kuma Domin na jinjinawa babban Bak’o DR. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, agame da maganganu masu amfani daya fad’a, Insha Allahu kuma maganan zata isa ga kunnen way’anda ya kamata suji, sannan muna godiya k’warai matuk’a, da irin shawarwarin daya bayar.”

Kai Jannart ta jinjina, tare da dan satan Kallon Dr Rayyern din, wanda ya kauda kansa gefe, kamar baiji ana yabonsa ba.

“Girman kai rawanin tsiya.” 

Tafad’a acikin zuciyarta, Yayinda afili kuwa cewa tayi.

“To S.A protocol muma godiya muke sosai, sannan bakon mu Dakta shima yana godiya.” 

Daga haka kuwa kiran S.A din ya katse, wani kiran kuma ya sake shigowa. 

Cikin tashin hankali Dr Lukman ya mik’e tsaye, tare dasa hannunsa ya dafe kansa, zuciyarsa cike da takaici yace.

“Lallai wannan yaron ya shallake duk wani tunani na, ba a banza ba  ake kiransa da Mai-nasara ba, tunda gashi yayi sara akan gab’a, daga maganansa har S.A da kansa ya kira, ya kuma shaida cewa maganar zata tafi har wajen governor, wannan wanne irin Dan iskan yaro ne? Mai sa’a”.

Cikin tsananin takaici tsana Alhaji Idi Saleh Dakata ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Ai yamafi Dan iska wannan yaron da kake gani Dr Lukman, shegen yaro ne kwance-kwance yake mana, da sannu Idan bamu tashi ba, duk sai yabi ya sare mana duk wani reshen mu, b’arna babba yake aikata mana, batare da ko damuwa da hakan yayi ba, Tabbas kuma ya kafu iya kafuwa, da wayannan kalaman nasa masu ratsa zuciya yake yaudarar mutane, waishi ala dole mai tausayin talakawa, yana abu tamkar Dan siyasan da yake barar neman kujerar takara, hmmmm Lallai zanyi maganin wannan yaron, zan kawar dashi kamar yanda na kawar da way’anda suka fishi tsauri a baya.”

Alhaji Idi Sale Dakata ya ƙare mgnar yana me sakin zazzafan numfashin takaici.

Yayinda Alhaji Abdu Tababa kuwa yace.

“Lallai kawar dashi daga doron k’asa shine hanya mafi a’ala, Idan ba haka ba kuwa duk sai ya fito damu waje cikin rana daga gidajenmu.” 

“Hakan bazaiyi wuba kuwa.”

Alhaji Idi Sale’n ya fad’a yana me mikewa tsaye.

Yayinda acan gidan su Rayyern kuwa, har yanzu su Abba basu matsa daga gun tv’n ba. 

Sunanan zaune kowannensu dauke da farincikin, irin nasaran da Rayyern din ke samu.

Haka ma agidan Barrister Kabir har yanzu shima yana zaune agaban tv’nsa.

Dai-dai lokacin da ake cigaba da haska shirinne kuma, Aunty Dijat ta fito daga daki.

Zama tayi akusa da mijinnata tare da soma kokarin had’a masa coffee.

Kallon ta Barrister Kabir din yayi, kana cikin tausasa murya yace.

“Dijat kalli tv kiga, Jannart da matashin saurayin nan dake zaune agefenta”.

Da sauri ta miƙa mishi cup ɗin tare da zubawa tv ido tare da cewa.

“Masha Allah”.

Kurban coffee’n yayi tare da cewa.

“Sundace ko?.” 

Ware ido Aunty Dijat din tayi ta kalli tv’n, dai-dai lokacin kuwa aka sake matso da fuskokin Jannart dana Rayyern din kusa.

“Masha Allah, ai kuwa Abban Hafeez matukar dacewa ma sukayi, kyau da kyau kenan.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da gyara zamansa a takaice yace.

“Shine mijin dana zab’a mata, kuma shine wanda zata aura amma batare da ta sani ba.”

Ya fad’a yana me karb’an coffee din da aka had’asa masa.

Idanu Aunty Dijat ta d’an zaro waje, cike da tsananin mamaki hadi da zallar farinciki tace.

“Allahu Akhbar, Lallai girman Allah iko da buwayarsa tana da yawa, Masha Allah Lallai Jannart ta dace da hazik’in Namiji kuma jarumi, mai dauke da nagarta, Tabbas ka cika Uba nagari, ai kuwa zamusha biki yaushe ne Auren?”

Murmushi Abban yayi, tare da girgiza mata Kai, Ahankali kuma yace.

“A’a bayanzu zan gaya miki ba, abun namu sirrine.”

Back to top button