Uncategorized

The Governor’s Wife Book 1 Page 2 Complete Novel

 

…… MATAR  GWAMNA….

 *©Azizat Hamza*

“Aseey we are dead”  CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office.

“Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi”

“Dama kin fi kusa da MD ai”

“Kai ka san wannan”

Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.

Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma’aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma’aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa.

Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.

Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.

Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..

***

Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri.

“Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane  ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor”

“Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director”

“Sir???”

“Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs”

Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.

“Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki”

Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.

“Shikenan Sir, nagode”  daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta. 

Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin…

Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta.  Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.

Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?

Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.

Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd  godiya.

“Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?”

“Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci”

“Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa”

“Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba”

“Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi”

Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.

***

Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.

A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.

 Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.

Ya ƙara da cewa ” ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba”

Yallaɓai yai murmushi ya ce “Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya”

“Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya”

“Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi”

Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce “ni zan wuce”

Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.

“Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse…”

Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.

Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan…

***

Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa, 

Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.

“Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu” ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.

“Hansa’u kenan”

“Hajja idan na girma ina son zama kaman ki”

Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa’u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara  goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana’a tunda ta ƙi auruwa. Hansa’u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce ‘yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.

“Hansa’u Malamin Junior ya zo ko?”

“Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje”

“Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita”

“Hajjan mu a kawo mana tsaraba”

Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.

Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma  ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.

Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar ‘ya’yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha’awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.

Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu. 

Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.

Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi. 

Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner.

Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waɗannan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku.

“Ba ki tafi ba?” First lady ta faɗa da mamaki

Hajiya Bilkisu ta buɗe baki cikin kaɗuwa.

“Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa”

 Hajiya Hadiza kenan da wannan magana.

“First lady saboda waɗannan kika shanyani kaman kayan wanki” ta yi maganar tana nuna su.

“Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haɗa taro idan bana gari”

 

“Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai”

“Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?”

Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki.

“Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya” First lady ta faɗa a fusace

Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro.

“Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya”

Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan.

A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai.

Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa.

Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa’anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya.

Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya ɗauketa ba. Ta dai farka tsakar dare  ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba.

***

Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa.

“Hello” ta faɗa da muryan bacci

“Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa”

“Ka manta anyi suspending ɗina jiya”

“Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office…” ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta.

Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira “Mommy” ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki.

“My boy”

“A’a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?” Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su

“Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba”

“Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa”

“Miyasa Junior ke cin abinci shi ɗaya ina Hansa’u?”

“Hansa’u” ta ƙwala ma ta  kira da ƙarfi

“Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg”

“Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House”

Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa’u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah. 

Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke

“And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool ɗin ko?”

Nana ta kalli Hansa’u ta ce ” yanzu Hansa’u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?”

“Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan”

“Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo” Nana ta faɗa da tsawa.

Hansa’u ta ɗauke kwanon ta koma kitchen da sauri.

Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko’ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki.

Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi  a library ɗinsa  ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba.

Ta ci sa’a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai.

“Bilkisu” ya kira sunanta da mamaki.

Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba’in da bakwai.

“Lafiya dai ko?”

“Lafiya Baba”

Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da ‘ya’yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba.

“Saifu ne zai miki kishiya?”

“Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi”

Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa.  Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota.

“Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?”

Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.

“Wace tambaya ce kuma wannan?”

“Baba dan Allah ka amsa min tambayata”

Alhaji Kachallah ya kalli idon ‘yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce ” idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba”

“A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?”

Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.

“Babu yadda za’ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai”

“Bilkisu!”

“Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and…”

Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa  a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi.

Bayan fitar Bilkisu daga falon, Alhaji Kachallah ya faɗa kogin tunani. Ta ina zai fara? Akwai gaskiya a hasashen Bilkisu dole ne ya san yadda zai yi ya shawo kan matsalar tun kafin lokaci ya ƙure a juye ma sa baya.

***

“Miyake faruwa naga kwana biyu ba kya fita”

SSK yai maganar yana zama gefen gadon Bilkisu tareda kissing goshinta.

“Ba na jin fitan ne kawai. Ina buƙatar hutu ne ma”

“Nima ina buƙatar hutun nan Allah. Inaga tunda Gwamna ya dawo why not mu je UK hutu ko da na sati biyu ne?”

“Its a good idea gaskiya. Muna buƙatan hutun nan sosai” ta yi maganar tana murmushi.

SSK bai jima da fita daga ɗakinta ba wayarta ya hau ruri. Madam Bintu ta gani a jikin screen ɗin hakan ya sa ta faɗaɗa murmushinta. Ta yi saurin ɗaukan kiran tana faɗin ” mutanen Turkiyya kin shigo kenan”

Daga ɓangaren Madam Bintu ta ce “na shigo jiya da dare zan shigo wajen ki anjima”

“To sai kin zo”

Ƙarfe biyar da rabi sai ga Madam Bintu a gidan ta.  Hansa’u ta kira ta kawo musu abin taɓawa.

“Har yanzu ba ki rabu da wannan matar ba bayan shirmen da ta yi kwanaki”

“Bintu tausayi ta ke bani Allah. Besides yanzu ta iya aiki sosai ba kaman farkon kawota ba sai dai ba a rasata da shirme kam. Most importantly tana sani dariya and that’s help alot ga mu ma su hawan jini”

“Ok” ta faɗa tana ƙarewa Hansa’u kallo. Gani ta ke  kaman idon matar na mata kama da wacce ta sani amma ta rasa gano ko wacece.

Bayan Hansa’u ta bar wajen Madam Bintu ta tambayi Bilkisu yadda taron matan Gwamnoni ya kasance dan lokacin da aka yi taron ba ta ƙasar.

“Ba abunda zan ce miki Bintu sai dai in ce kawai taro yayi kyau. Kuma za a sake wani taron nan ba da daɗewa ba”

Madam Bintu ta kalli Hajiya Bilkisu cikin rashin fahimta, maimakon ta mata ƙarin bayani sai kawai ta fashe da wata ƙasaitacciyar dariya.

**

A chan gidan Yallaɓai kuwa Chief of Staff (COS) ɗin Gwamna ne a gaban Yallaɓai yana ma sa bayani mai mahimmanci wanda ya sa Yallaɓai nitsuwa na ban mamaki. Har ya gama bayanin Yallaɓai bai ce komai ba sai ma  murza gemunsa da ya fara yi a hankali.

Ba kasafai ya ke samun ma su taurin zuciya irin ta KACHALLAH ba. Shekaru da dama an taɓa yunƙurin aikata irin wannan abu sai dai kuma komai ya zo ya chanja a ƙurarren lokaci.

“Ka haɗa meeting da Kachallah cikin satin nan”  Yallaɓai ya faɗa bayan yayi dogon nazari.

COS yai murmushin gefen baki dan ya san yanzu liyafa za ta cigaba. Ya ƙwallafa rai sosai akan Gwamna Saminu Bacchi sai dai cikin shekaru uku da yai a kan mulki sun samu saɓani sosai domin lokacin da idon Gwamna Saminu ya buɗe da kuɗi sai ya zamana yana ƙoƙarin take duk wata hanya da su suke  yagan rabon su, yanata wawure komai shi kaɗai da iyalin sa ba dan Yallaɓai ya tsayar ma sa ba wasu abubuwan haka za su dinga wuce shi.

Saifuddeen Sa’ad Kachallah daban ya ke da Gwamna Saminu, kuɗi ba za su ruɗe shi ba. SSK ya gaji arziƙi irin arziƙin da ko da ba zai yi wani aiki ba zai isheshi ci da iyalen sa har iya karshen rayuwar su ba tareda sun yi talauci ba.

SSK shine mafita a gareshi da shi da KACHALLAH.

***

“Wallahi an cuceni Ya Ubayd. MD mugu ne wallahi”

Ubayd yai murmushi ya ce ” ni kam ya min dai-dai, dama daurewa kawai na ke yi amma kullum aka nunaki a TV sai na ji kamar zuciyata za ta fashe”

“To ta Allah ba taka ba. Sai an maidani reporting unit”

“Ina kishin ki Asiya na haƙura ne kawai saboda babu yadda zan yi amma Allah idan ki ka shigo gidana ba za ki sake bayyana a TV ba, ko dai ki tsaya aiki a bayan fage ko kuma ki haƙura da aikin”

“Ya Ubayd you are joking right”

“I’m not Asiya. Gara ma ki saba da inda aka kai ki yanzu”

Sati ɗaya da suspension ɗin ta aka kirata akan ta dawo. Yau ta fara fita aiki amma duk ta ji ba daɗi ba ta son ɓangaren da aka kaita ko kaɗan.

“Ya Ubayd ba haka mu ka yi da kai ba baka ce za ka rabani da aikina ba”

“Ba rabaki zanyi da aikin ki ba na dai ce bayan munyi aure ba ƙaton da zai sake ganin ki a TV yana ƙare miki kallo especially with irin shigan da ki ke yi” yai maganar da ɗan ƙarfi

Asiya ta miƙe daga kujeran da ta ke zaune ta ce “ba ka isa ba kuwa”

Ta wuce ta barshi a wajen baki buɗe.

Washegari ko jiran sa ba ta tsaya yi ba ta  hau keke ta wuce office…

***

” na gaya miki babu kuɗi a ƙasa, duk wani abu da zamuyi yanzu mutane za su yi magana. We need this year to work on something saboda campaign da za a fara nan da watanni huɗu ma su zuwa”

Gwamna Saminu Bacchi kenan yana ƙoƙarin lallashin matar sa. 

“Kana so ka ce min ba ka da kuɗin da zamu celebrating 8years anniversary na mu?”

“Ba wai ba kuɗin bane amma kuɗin campaign ne”

“Kar ka gaya min magana dan Allah. Uban me Saifuddeen Kachallah ke da shi da zai iya celebrating 15yrs anniversary na su a tsakiyar teku  shekaru biyu da suka wuce. Na je party ɗin fa. Sati biyu aka yi a cikin jirgin ruwa wanda komai da komai da mutanen ciki su ka yi yana wuyan sa”

“Sha’awanatu. Saifuddeen Kachallah  millionaire ne tun kafin mu hau gwamnati ko mi zai yi ba wanda zai zargeshi amma ni…”

“Ba zan yadda ba fa. Dole ne ayi anniversary party namu a Italy. Wallahi kai ka ke sawa ma Bilkisu Kachallah tana raina ni. Ina matar Gwamna amma  ko motan da ta ke hawa tafi tawa”

“Yanzu kinsan ya za ayi ne? Za mu yi party amma a nan Nigeria. Bamu jima da dawowa daga ƙasar waje ba idan muka sake fita mutane za su yi magana…”

“Wai ina ruwanka da mutane ne. Kai fa Gwamna ne. Gwamnar jahar CONGO wancan tafiyar Asibiti ka je wannan tafiyar kuma yana cikin yiwa iyalinka hidima ne”

” Amma Sha’awa…”

Daga haka Gwamna Saminu Bacchi ya haɗiye sauran maganar sa saboda haɗe bakin su da Sha’awanatu ta yi.

Washegari da safe Gwamna ya tashi da wani irin ciwon kai da ciwon ƙirji, ciwon ne ma ya tashe shi daga bacci tun ƙusan ƙarfe huɗun Asuba.

Wasa-wasa har ƙarfe shida jikin ba sauƙi duk da kuwa ya sha magungunan sa. 

“Za mu wuce Asibiti ne ko a kira maka likita?” First lady ta tambaya cike da fargaba.

“Ki kira Likita”  ya faɗa da ƙyar saboda yadda ƙirjinsa ke takure.

Bai kai awa ɗaya ba saiga likitan sa ya iso koda ya duba shi cewa yai jinin sa ne ya hau sosai idan akwai wata damuwa da ke ransa to yai ƙoƙarin kauda ita dan   abunda ya sa a ransa ka iya jawo ma sa bugawar zuciya.

Shi dai ya sani bai sa komai a ransa ba. Ba a fara campaign ba balle ya ce shine ke ɗaga ma sa hankali. To kodai Barasar daya kwankwaɗa jiya da dare ne? Duk da likitan sa na chan Germany ya hana shi shan barasa. Duk da kuwa ya san ba zai iya dena sha ba, sai dai ya rage sha ba kamar da ba.

 Allura da Likitan ya ma sa ya taimaka ma sa sosai dan har ya samu yayi  bacci. Lokacin da ya farka kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe. 

Sha’awanatu ta taimaka ma sa yai wanka ta kawo ma sa abinci har kan gado amma bai iya ci ba sai shayi kawai ya sha.

Ƙishirwar giya ce ta dameshi dan duk da yana jin jiki yayi amanna idan ya ɗan kurɓi kaɗan zai samu sauƙi. Fita yai  daga ɗakin Sha’awanatu ya wuce na sa ɗakin a nan ya fito da kwalbar giya ya kwankwaɗa ya girgiza kai ya sake kurɓan kaɗan sannan ya mayar da sauran ma’ajiyar sa.

Shiryawa yai ya fita saboda akwai meeting da zai yi da wasu contractors ƙarfe biyu na rana.

“Yanzu yadda baka da lafiya haka za ka fita?” 

“To ya za ayi dole ne mu yiwa talakawa aiki” 

“To. Amma ka dai yi tunani akan abinda na ce”

Dariya Gwamna ya fara yi sai kuma ya dafe ƙirjinsa saboda yadda ya ji ƙirjinsa na suya kaman an saka masa wuta.

“Your excellency jikin ne?”

Kafin ta ƙarisa maganar Excellency ya kai ƙasa.

“Your excellency, miya faru? Ƙirjin ka ne?”

“Waye a nan? a kira likita. Excellency… Saminu…Saminu ka tashi”

Lokacin da aka garzaya da Gwamna Asibiti ya riga ya cika likita ya ce zuciyar sa ce ta buga (cardiac arrest)…

***

Mataimakin Gwamna na zaune a  office Chief security officer ya kira shi, kiran da ya ɗaga ma sa hankali  sosai dan kuwa a kiɗime ya fice daga office ɗinsa ya wuce Asibiti.

Mummunan labarin da aka gaya ma sa a waya shi ya tarar a wajen domin kuwa  Allah yayiwa Gwamna Saminu Bacchi rasuwa.

A chan Kachallah House kuwa Alhaji Sani Kachallah ne ke waya da mijin ‘yar sa wato Saifuddeen wanda ya jaddada ma sa mutuwar Saminu Bacchi.

“Mi aka ce ya kashe shi?”

“Baba ba zan iya cewa komai ba yanzu”

Alhaji Sani Kachallah ya ce “ba komai zan kiraka anjima”. Yana kashe wayar ya shiga kiran numbar Yallaɓai.

A chan gidan mataimakin Gwamna kuwa Bilkisu Kachallah ce zaune a falo tana cin gasashshiyar kifi da soyayyen dankalin turawa haɗe da lemo mai sanyi.

“Hansa’u, Hansa’u ” Hansa’u ta fito da gudu.

Miƙo min remote ina son kallon news.

Hansa’u ta miƙa ma ta remote ɗin Bilkisu ta chanja channel daga Zee world zuwa Congo news…

***

Asiya Shahidah na zaune a sabon office ɗinta tana aiki akan computer abokin aikinta Ɗahiru ya shigo office ɗin da sauri.

“Shahidah kin san labarin dana ji kuwa daga fitata a office ɗin nan?”

“Miya faru?”

“Yanzu Abigail ta ke kawo rahoto cewa Gwamna ya rasu”

“Wani Gwamnan?”

“Gwamnan Congo mana”

“Innalillahi! Dan Allah?”

“Allah kuwa”

Asiya Shahidah ta miƙe ta bar office ɗin da sauri…

Kusan awa ɗaya da rasuwan sannan Mataimakin Gwamna kuma acting Gwamna ya bada sanarwan mutuwar Gwamna Saminu Bacchi.

*”Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’oun. Haƙiƙa dukkan mai rai mamaci ne. Muna yiwa Jahar Congo ta’aziya bisa rasuwan Mai girma Gwamna Alhaji Saminu Bacchi wanda Allah yai wa rasuwa yau shabakwai ga watan Nowamba. Haƙiƙa wannan jaha ta yi babban Rashi”* hawayen da ya zubo ma sa yai saurin sa hankerchief ya goge sannan ya cigaba da bayani

*” Insha Allahu za ayi jana’izar sa a gidan gwamnati da ƙarfe biyar na yamma”*

Asiya Shahidah da ke kallon news ɗin a talabijin da ke office ɗin su CY ta ce “Ikon Allah har da kukan munafurci kaman bai ji daɗin abinda ya faru ba, Shege. Ai yanzu kam jahar nan ta shiga uku a hannun wannan Wawan”

A ɓangaren Yallaɓai kuwa yana gama kallon bayanan da SSK yai ya danna remote ya kashe T V sannan ya kai duban sa ga Kachallah ya ce

“To kyan alƙawari dai cikawa. Ina fata Saifuddeen zai bamu haɗin kai”

“An gama Yallaɓai”

Yayinda wasu ke cikin baƙin ciki da rasuwan Saminu Bacchi wasu kuma na nan suna planning yadda za a juya Gwamnati.

Duniyar kenan. Tunma kafin a sa shi cikin ƙasa har an riga an cire shi daga lissafi.

Da ‘yan siyasa za su dinga tunawa da cewa akwai ranar da dukiya ko matsayi ba zai amfanesu ba ƙila da za su tausayawa talakawan su.THE GOVERNOR’S WIFE*

“Rayuwa kenan. Yau kam Saminu Bacchi sai kwanciyar kabari”

Abba da ya kashe rediyon sa ya faɗa.

Ubayd ya ƙara da cewa “Ya tafi ba abunda ya ɗauka kuwa” 

“Muna addu’ar Allah ya taya Saifuddeen  riƙo Amin”

Ubayd ya ce Amin. Shiru ne ya biyo bayan haka na ɗan mintuna kafin Abba ya ɗaga kai ya ce ” ‘yata ta dawo kuwa?”

“Ƙila aiki ne ya tsaida ita”

“Ka je ka dubo min ita”

Bai musa ba ya miƙe yana karkaɗa key ɗin mota.

Lokacin da motar sa ta sako kai farfajiyar ma’aikatar su Asiya ya hangota tana shirin hawa babur ɗin CY. Yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya ke ƙin aikinta irin yadda ba ta damuwa da irin mutanen da ta ke mu’amala da su. Ya sha hanata mu’amala da wannan camera man ɗin amma kaman ma duk cikin Kamfanin su tafi jituwa da shi.

Sarai ta hango shi amma ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba. Sai da CY ya tada machine su ka fara tafiya ya kula da motar Ubayd.

“Aseey ba motar fiancee ɗin ki ba ne wannan”

“To sai me”

CY yai saurin taka birki har sai da Asiya ta bugu da bayanshi.

“Ya ka tsaya?”

“Bebz i no wan trouble, plz ki sauka”

“CY ka wuce mu tafi”

Lokacin da ya tada machine ɗin a hankali ya ja su har wajen da Ubayd yai parking  motar sa Asiya na ta ma sa faɗa akan ya wuce su tafi amma bai saurareta ba.

“CY za ka haɗu da ni gobe ai. I will deal with you”

Bai kulata ba sai ɗagawa Ubayd hannu da yai yana faɗin “weldone Sir”

Ubayd ya sauke glass ƙasa ya ce “Sannu da ƙoƙari fa”

“Sannu Sir, a yiwa Amarya haƙuri yau ta gaji dayawa ne”

“Nagode”

Asiya ta watsawa CY harara kafin ta zaga ta je ta shiga motar Ubayd.

Sai da ya ga ta shige motar kafin ya ja machine ɗin sa yai gaba.

Ubayd bai ce mata komai ba ya tada motar su ka fara tafiya. Itama ba ta kula shi ba sai ma kwantar da kujera da ta yi ta rufe idonta kamar mai bacci.

Traffic ne ya riƙesu saboda ma su dawowa daga maƙabarta.

Ƙaran siren ne ya tada Asiya daga baccin daya sace ta. Ta rintse ido ta buɗe da kyau ganin har yanzu suna round about na GRA kenan ko kusa da gida ba su yi ba.

Sai da motocin Gwamna su ka wuce kafin aka basu hanya suma suka fara wucewa hakan ya sa Asiya ta ja tsaki.

“Asiya” ya dakatar da ita lokacin da ta ke shirin fita daga mota.

Ta juyo ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba.

“Zan kiraki bayan sallar Isha”

“Ok” ta faɗa sannan ta fita.

Data shiga gida tana jin shewar Abida ƙawar Hindatu mai murya kaman na maza. Ta dawo kenan ta faɗa a ranta sannan ta wuce ɗakin Umma.

Bayan ta yi sallar isha tana kwance akan sallaya tana danna waya kiran Ubayd ya shigo. Ta san dalilin kiran shiyasa ba ta ma ɗauka ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.

“Yau kuma shigar ta malamai ne”

Ubayd ya faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin zama akan kujerar roba da ke gefen sa.

“Idan ma gatse ne ka san dai daga gidan Malaman na fito”

“Shiyasa na ke alfahari da cewa jikar Gwani Baba zan aura. Allah ya jiƙan rai”

“Ka huce kenan?”

“My Aseeya kenan. Kin riga kin sani bana iya fushi da ke ai. Ki yi haƙuri”

Asiya ta ɗan haɗe rai tana tura baki.

“Kwantar da hankalinki ba haka nan na zo biko ba, na zo da kayan sulhu”

Yana maganar ya jawo ledar da ke gefensa ya ɗaura akan cinyarta.

“Whoa! Pringles, chocolates. Ba dan halin ka ba dai kaima ka yi haƙuri” tana maganar tana buɗe robar pringles ɗin.

“Ya Ubayd gaskiya yau ka yi abin kirki” tana maganar bakinta yana ƙurmus-ƙurmus.

“Ba za a sammini ba?”

“In your dreams. Ka san yanzu a zaune sai na cinye wannan bai isheni ba”

Ganin ya sakata farin ciki ya sa shi yi mata hiran shirye-shiryen bikin su da tsarin yadda komai zai kasance. Yau baya so ayi maganar kowa sai ta su. Ana taɗi ya tuno mata da ranan da ya fara ganinta a gidan su hakan ya sa Asiya mingirewa da dariya tanayi tana “kai Ya Ubayd”

Farkon haɗuwar su tana shekara shaɗaya a duniya ta zo yiwa ummanta hutu. Lokacin ‘yar mitsila da ita amma wai tana JSS 2.

Ya shigo gidan ya ga tsumma a kan igiyar shanya, bai kawo komai a ransa ba ya cire ya tsoma cikin ruwan Omo ya fara wanke machine ɗin Abba da shi.

Kamar daga sama ya ji wata siririwar murya tana salati a bayansa ya juyo a ɗan firgice dan ya ɗauka ba kowa a gidan na su, biki ake a gidan su Addaye ƙanwar Abba, duk ‘yan gidan suna chan.

“Lahaula… Sallalahu Alaihi wa Sallam. Tsumman abuna!”  sai kuma ta riƙe baki tana zaro ido.

Ubaydullah yana riƙe da tsumman ya kalleta da mamaki ya ce “tsumman miye? Tukunna ke daga ina?” Bai yi aune ba Siririyar yarinya mai wushirya ta yi wuf ta karɓe tsumman daga hannunsa ta shige ɗakin Umma da gudu, bai ƙare mamaki ba sai daya ji ta bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi.

Shi kam bai gane mi ya ke faruwa ba. Ya dai ƙarasa wanke machine ɗin hakanan.

Har ya gama abunda zai yi ya fita yarinyar ba ta fito ba. Sai bayan magariba daya dawo gidan ya tambayi ƙanwar sa Ummi wace baƙuwa su ka yi a gidan. Ummi ta sanar da shi ‘yar Umma Kurma ce itace Asiya Shahidan ta da Abba ya basu labari.

Tun daga lokacin kuwa Asiya ke gudunsa har ranan da ya titsiye ta yana tambayarta miye dalilin ta na ƙwace tsumman ranan. Yadda ta dinga inda-inda ne ya sa ya fahimci tsumman miye.

Ƙannensa sun wuce nan ai dan tun lokacin da ya taɓa kama ƙanwarsa Ummi tana ɓoye tsumma cikin zani ya ɗaurawa kansa siyawa ƙannensa audugar mata tun ma yana shekaru shabakwai kenan balle yanzu daya ke shatara shigar sa Jami’a ya sake wayewa.

A ranan ya je ya siyowa Asiya auduga ya bawa Ummi ya ce ta nunawa Asiya yadda za ta yi amfani da shi.

A hankali-A hankali kafin ta ƙare hutun ta dena jin kunyar sa tana ɗan sakewa da shi. Tun tana zuwa hutu gidan har ya zamo lokacin da za ta shiga Jami’a ta dawo gidan su da zama gaba ɗaya.

Har yau idan yana son ya tsokali Asiya to kalmomi biyu kacal zai faɗa ya tunzurata *”tsumman abuna”*

Bai bar gidan ba sai ƙarfe goma saura minti biyar nan ma dan baya son tsallake dokar Abba ne wato baya son hiran ƙarfe goma.

Asiya na komawa ɗaki da ta duba wayarta ta ga saƙon KaSaSa a email ɗinta wanda waƙar da ta rubuta yau akan mutuwa ne, wanda tai wa Marigayi Gwamna Saminu Bacchi. 

Bayan ta karanta kuwa sai da ta tuno mutuwa biyu da su ka fi girgizata a rayuwarta. Mutuwar Kakanta Gwani da kuma mutuwar ƙaninta ɗan shekaru biyu wanda ya rasu a bayanta. 

Auri sakin mahaifinsu ne ya je ya auro wata mai juju. Dan idan abu ya haɗata da sauran matansa duka ta ke musu, shima kuwa da ƙyar ya sha a wajenta ranan da ya mareta ta kamashi da kokawa sai da ƙyar aka raba su. Ba dan an raba da wuri bama alamu sun nuna Ale Faruƙ ne zai sha kashi a wajen Indo, dan Indo irin matan nan ne ma su ƙarfi, ga jiki ga tsawo. Ale Faruƙ na sane da dukan miji da akace tanayi wanda ya rabata da sauran mazaje uku da ta aura a baya amma  ya rufe ido ya ce Indo-ƙarfi zai aura.

 Bayan faɗan ne kuwa Ale Faruƙ ya saketa ashe tanada ciki. Da ke ba ta da hankali yaron ko suna ba ayi ba ta zo ta ajiye shi gaban Tabawa mahaifiyar Ale Faruƙ wai ga tsiyar su nan.

 Haka yaro ya taso ba gata. Tabawa ma da ƙyar ta ke kula da shi dan Ale Faruƙ baya kawo kuɗin madara sai ta tsiya-tsiya.

Da yaron ya fara wayo ba shi da wata gata a gidan sai ta Asiya. A haka ya taso a yarjale har Allah ya ɗau ransa lokacin yayi wani zazzaɓi mai zafi Asiya ta goya shi tana jijjigashi a bayanta saboda kuka dayake ta tsalawa har Allah ya karɓi ran sa. Shekarunta tara a lokacin amma har yau ba ta taɓa manta yadda abun ya faru ba. Ya jima da rasuwa a bayanta ba ta sani ba har sai da ta zo kwantar da shi lokacin za ta yi wanki dan ta ɗauka bacci yai sai ta ga idonsa a kafe ta fara jijjigashi amma inaa babu alamun motsi nan ta saka ihu ta fita tana ƙwalawa Tabawa kira…

***

“Seriously Justice ina tsoro. Kwana biyun nan bana iya bacci fa. This is so sudden for me”

Bayan Justice Yunus ya gama yi ma sa nasiha ta jan hankali ne ya ce “Shikenan na gode. Ka gaida Maman ‘yan biyu”…

“Kai da waye a waya?”

Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajensa tana zuba ƙanshi.

“Justice”

“Oh Galadima. Hope zai zo rantsarwar ka”

” i dont think so dan ya ce suna Las Vegas”

“Ayya! Allah ya dawo da su lafiya. Muma gashi babu halin tafiya tunda ga yadda lamarin Ubangiji ya kasance. Just like a dream”

“Just like a dream kam. Har yanzu ina jimamin mutuwar Gwamna”

“Haka Allah ya ke lamarinsa. Idan lokaci yayi babu makawa sai an tafi”

“Hakane. Muma duk lokaci mu ke jira”

Kallonta yai da kyau sannan ya ɗaga gira sama ya ce ” sai ina?”

“Zamu je shopping ni da yara. Duk cikin kayan su babu na zuwa swearing in naka a ciki. I think dole a chanja mu su wardrobe kwanan nan”

“Hmmm. I trust you Bilkisu” ya faɗa yana ɗan jijjiga kai

“Miye?”

“Allah ya kiyaye hanya”

Kiss ta manna ma sa a baki kafin ta fice daga ɗakin ya bi bayanta da kallo. “Mata kenan, wai duk cikin kayan da ta ke dasu babu na zuwa wajen rantsarwar sa da za ayi ranan Monday”.

“Seriously Mommy i cant believe yanzu mune first family of the state” Nana ta faɗa tana dariya

“Well get used to it, dan yanzu aka fara governor’s daughter” 

Bilkisu ta faɗa tana murmushi.

Nana ta saka ihu. 

Har su ka isa Kachallah House hiran yadda rayuwar su za ta kasance yanzu su ke yi.

Sai da su ka fara isa ɓangaren Hajiya Aisha wato mahaifiyar Bilkisu kafin su ka wuce gaida Dadda mahaifiyar Alhaji Sani Kachallah.

Ko da su ka gaisa Bilkisu ta tambayi ina Mahira ta ke, Dadda ta ce ta wuce Islamiyya.

“Yanzu yarinyar nan abinda za ta min kenan bayan na ce ma ta zamu zo”

“Inaga ta manta ne” Dadda ta faɗa tana tauna goro.

Ba su jima  a gidan ba su ka wuce bayan sun barwa Dadda saƙo akan idan Mahira ta dawo ta je gida Bilkisun na nemanta.

***

Farar Shadda ya saka ɗinkin babbar riga haɗe da baƙin hula zanna, ya saka baƙin shoe ƙirar Loius Vitton. Ya duba kan sa a madubi ba ƙarya ya fito sosai. Sai dai a ƙarƙashin wannan kayan zuciyar sa ce ke bugawa da ƙarfi kaman za ta ɓula ƙirjinsa ta fito.

Lokacin da aka rantsar da shi a matsayin mataimakin Gwamna bai tsinci kan sa cikin fargaba da tsoro kaman na yau ba kodan yanzu matsayinsa ya chanja ne?

Ya fesa turarukan sa ma su ƙanshi guda uku sannan ya fito daga ɗakinsa ya wuce ɗakin Bilkisu. A tunanin sa ta gama shiryawa amma har lokacin ana kan yi mata kwalliya. Tamkar biki za a yi haka Hajiya Bilkisu ta nemo professional make up artist da za ta gyara ma ta fiska yau.

“Your excellency” mai kwalliyar ta faɗa tana wani ƙamewa.

Bilkisu ta ɗago ido ta ce ” Darling ka gama shiryawa, yi haƙuri yanzu zan gama nima”

Tun kafin ta ƙarisa maganar ya riga ya fice inda ya wuce ɗakin yaran sa. An gamawa Nana da Airah kwalliya Mahira ake yiwa lokacin daya shigo. Fiskarta tamau alamun ba ta so a dole ake mata. Ya sani ta ɓangaren son ƙyale-ƙyale kam Nana ce ta ɗauko komai na Bilkisu amma Mahira bai dameta ba.

“Daddy Governor” Nana ta faɗa tana ƙarasowa wajen sa.

“Yi a hankali N Luv kar ki ɓata ma sa farin kaya” Airah ta faɗa daga inda ta ke zaune tana danna waya.

” Daddy selfie ɗaya kafin ka tafi please”

Bai so ba amma dole haka ya tsaya Nana ta mu su selfie kafin ya wuce ɗakin Junior inda tuni Hansa’u ta shirya shi dan lokacin da ya shiga ɗakin ma yana buga game ne. Ya kama hannunsa su ka fice daga ɗakin…

Kotu ya cika maƙil da mutane da kuma ‘yan jarida. Bayan Alƙali ya shigo ya tsaya sannan Gwamna Saifuddeen Sa’ad Kachallah ya shigo biye da bodyguard ɗin sa. Bilkisu kaman ta narke saboda farinciki ganin Mijinta a gaban Alkali wai za a rantsar da shi a matsayin Gwamna.

Lokacin da SSK ya dafa alƙur’ani ya maimaita kalmar da Alƙali ya faɗa wato*I…Saifuddeen Sa’ad Kachallah. Do solemly swear…*  lumshe ido Bilkisu ta yi sannan ta kai dubanta ga ɓangarenta na dama inda Alhaji Sani Kachallah ke zaune ɗauke da Junior a cinyarsa. Irin yadda fiskarsa ke washe da farin ciki da annashuwa ko ita da ta ke Matar Saifuddeen albarka. Mahaifinta shine musabbabin saka Saifuddeen a harkar siyasa and yanzu ne zai ga alfanun sadaukarwar da yai a rayuwar Saifuddeen domin yanzu shi ɗin Gwamnan Jahar Congo ne….

***

Asiya ba ta yi tsammanin kira daga MD ɗin su ba dan rabonta da shi tun ranan da aka bata suspension letter.

Sai da ta  ƙarisa aikin da ta ke yi kafin ta wuce office ɗinsa.

“Sannu da aiki Sir”

“Yawwa Asiya. Ya aikin?”

“Alhamdulillah”

“Inada assignment da za ki yi. Idan kin carrying out na shi da kyau za ki dawo aikin ki na da”

Washe fiska Asiya ta yi ta ce “Sir wani assignment ne?”

Wata takarda ya tura gabanta ya ce “muna so ki yiwa Gwamna Interview”

Murmushin fiskar Asiya ya ɓace ɓat. Wata na biyu kenan da SSK ya zama Gwamna kuma har yanzu ya ƙi yin interview da kowani gidan jarida. Sau ɗaya yai press conference sati ɗaya bayan an rantsar da shi a matsayin Gwamna.

“Sir i think Hill TV ta nemi hira da shi kwanakin baya kuma ya ƙi”

“Shiyasa na ce assignment ne. Ko dai yanzu akwai aikin daya gagari Asiya-Shahidah ne?”

Asiya ta ƙunshe baki tareda sauke ajiyar zuciya.

“Ba komai Sir zan nemi permission daga gidan Gwamnati kafin satin nan ya ƙare Insha Allah”

Ko da ta bar ofishin sa office ɗin su CY ta wuce ta sameshi yana editing wani video da za a ɗaura anjima.

“Babez ya na ga kin haɗe rai?”

“za ka rakani Government office gobe”

“Government office? Why?”

“Kai dai ka shirya kawai”.

“Okey dokey”

***

Ƙarfe takwas saura suna bakin Gidan Gwamnati. Ba su samu matsalar shiga ba suna nuna ID card ɗin su aka ce su wuce.

Wani security ne ya mu su rakiya har ofishin Sakataren Gwamna.

Asiya ta yiwa Mr Baffayo Sakataren Gwamna bayanin abinda ke tafe da su. Bayan ta gama ya ce ” Malama Asiya na ji daɗin zuwan ku gaskiya sai dai Mai Girma Gwamna ya ce ba zai yi zama da kowani ɗan jarida ba yanzu, sai dai ko gaba”

“Ranka shi daɗe, Hill TV zata yi hira da shi ne gameda tarihin rayuwar sa babu maganar siyasa a ciki”

“Malama Asiya kenan. Zai fi dai ku haƙura zuwa lokacin da Gwamna zai so yin hiran da kan shi”

“Sir da dai ka miƙawa Gwamna letter ɗin mu ƙila a dace” ta faɗa a marairaice

Sakatare ya karɓi wasiƙar ya ce zai miƙawa Gwamna.

Su ka ma sa godiya su ka tafi.

Koda Gwamna ya dawo Sakatare bai ba shi wasiƙar ba, bai ma gaya masa su Asiya sun zo ba.

Asiya na nan tana jiran kiran Sakatare amma shiru. Washegari ƙarfe goma ta sake komawa ofishin Gwamna.

“Kin ga abinda na faɗa miki ɗin ne dai, Gwamna ya ce ba zai karɓi gayyatar ku ba”

“Dan Allah Malam ka sa baki. I really need to take his interview”

“Ki yi haƙuri. Zan dai sake yi ma sa magana ince kin sake zuwa. Kin san matsalar ne. Akwai wanda su ka fi ki naci sunyita zuwa Kwanakin baya, ƙarshe Gwamna ya ce kar a sake bari ɗan jarida ya zo ofishin sa amma…”

“Oh haka ko?” Asiya ta faɗa a hasale

Sakatare ya zuba ido yana kallonta da mamaki.

Asiya ta ciro wasiƙar da su ka ajiye ma sa jiya a ƙasan laptop da ya ke aiki da shi.

“Zan iya rantsewa wannan bai je hannun Gwamna ba”

Sakatare ya fara kame-kame. Allah na gani girman shekarunsa da Asiya ta gani ya sa ta iya controlling kanta ba ta ma sa rashin mutunci ba.

“Zan dawo gobe, zan jira ko ƙarfe nawane sai na ga Gwamna da kaina na bashi wasiƙar. Zan haƙura ne kawai idan shi da bakinsa ya ce ba zai yi hira da ni ba”

Daga haka ta fice daga office ɗin ta bar Sakatare  baki buɗe.

Bayan tafiyar Asiya da Sakatare ya shiga  wajen Gwamna kai ma sa wasu takardu sai ya haɗa da wasiƙar Asiya.

“Wannan fa?” Gwamna ya tambaya yana ɗaga envelope ɗin da wasiƙar ke ciki.

“Your excellency gidan talibijin na Hill TV ke son hira da kai”

“Malam Baffayo hira da ‘yan jarida sai gaba, we have better things to do with our time now”

“Yes excellency”

Daga haka ya fita bai sake ɗago maganar ba.

Washegari kuwa kamar yadda Asiya tayi alƙawari sai gata a ofishin Gwamnati sai dai wannan karan ko ƙarasawa ofishin Sakataren Gwamna ba ta yi ba aka dakatar da ita.

“Ban gane in tafi ba. Ina son ganin Gwamna ko akwai dokar da ta hana hakan?” Asiya ta faɗa wa security guard ɗin daya tsareta cikin tsawa.

“Gwamna baya office ki je ki dawo wani lokaci”

“Ba inda zan je. Gwamna yana nan. I need to have audience with him”

” idan ba ki fita ta lallami ba, za a fita da ke ta ƙarfi. So please leave”

“Ba inda zan je fa” Asiya ta faɗa tana gyara tsayuwarta.

A ofishin Sakatare kuwa Gwamna ne ya zo wucewa zuwa wani exco meeting ya jiyo hayaniyar da ake yi hakan ya sa shi ya ɗan tsaya.

COS da ke bayan sa ya kalli Sakatare cikin tsawa yace “wai wacece a wajen nan ne?”

“Wata ‘yar jarida ce ta dage sai ta ga Gwamna”.

“Kul ka taɓa ni, wallahi yatsata ka taɓa sai ka san wacece Asiya-Shahida a garin nan. Na san ‘yanci na dan haka kar ka kuskura ka min barazana”

Wannan karan tana maganar ta zauna a  kan kujera da ke Lobby ɗin tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana huci.

“Malam Baffayo ka ce ta dawo ranan Monday”

Ba da ƙarfi yai maganar ba amma duk sun ji shi. Bai jira mai Sakataren zai ce ba ya wuce abinsa.

Asiya ta zauna na kusan minti shabiyar kafin Sakatare ya fito.

“Malama Asiya ya da haɗe rai haka”

“Ba fa inda zan je”  ta faɗa tana girgiza kai

Sakatare ya miƙa ma ta wani envelop. Tana gama karanta takardar da ke cikin envelope ɗin ta saka ihu. Sai kuma ta yi saurin rufe bakinta da hannunta.

Sakatare yai dariya ya ce ” gaskiya kin taki sa’a. Gwamna ya amince ya ganki ranan Monday, best of luck”

Fiska a washe Asiya ta ma sa godiya ta tafi. Shi kan sa Sakatare yayi mamaki da amincewar Gwamna cikin sauƙi haka.

***

A chan ɗakin da ake taro kuwa dukkan wanda ya ke da alaƙa  da wannan taro ya riga ya hallara dama Gwamnan kawai ake jira.

COS ne ya ja masa kujera ya zauna yana kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Kusan minti guda ya ɗauka sannan ya ja dogon numfashi sannan ya ce “gentlemen ina buƙatar report na wannan wata”

“Kwamishina Isiaka” Gwamna ya kira yana duban wani ƙaton baƙin mutum sanye da babbar riga kalar light blue. Kwamishinan ilimi yai gyaran murya sannan ya fara bada bayani wanda ya ɗaukeshi tsawon minti huɗu da rabi.

“Not impressive Kwamishina Isiaka. Ban ji ka yi maganar Albashin Malaman firamare da za a ƙara ba”

“Your excellency mun submitting budget farkon watan nan amma abunda ya iso mana daga hannun Kwamishina of Finance shi mu ka yi amfani da shi”

Gwamna SSK ya juya ya zubawa  Mr Paul idanunsa ma su kaifi hakan ya sa shi fara wiki-wiki da ido.

“Mr Paul!” Gwamna ya faɗa da ɗan ƙarfi.

“Excellency saboda akwai basusuka dayawa da tsohon Gwamna ya bari muna so a fara rage wannan kafin a fara maganan ƙara albashi”

“Abinda aka fara tunkarana da shi lokacin dana ƙarfi wannan kujera shine maganan ƙarancin albashin Malaman Firamare. If i can remember clearly. Sai da na ce Kwamishina Isiaka ya drafting budget ya nuna maka, kana tunanin da wasa na yi maganar?”

“No your excellency” Mr Paul ya faɗa yana sunne kai ƙasa.

“Ina Kwamishinan raya karkara”

“Your excellency” wani mutum fari dogo ƙyamusashshe ya faɗa yana ɗaga hannu.

“Banga report dana buƙata ba tun farkon watan nan”

Cikin turancin sa da take nuna asalin harshen bahaushe ya fara bayani.

“Na tura memo wa Kwamishina Paul  ya kai sau huɗu amma babu wanda ya reply aciki”

Wannan karan ma Gwamna ƙurawa Mr Paul ido yai.

“Your excellency budget da aka yi da tsohon Gwamna babu buƙatun Kwamishina Ɗanladi a ciki shiyasa babu yadda za ayi yanzu a ƙirƙiro kuɗi a bashi sai yai haƙuri sai wata shekarar”

“Oh hakane ko?. Ina buƙatar budget da aka drafting na wannan shekarar da kuma abubuwan da akayi da su haɗe da receipts na komai. Kwamishina Paul zan saurari report ɗinka gobe da safe a office ɗina”

Mr Paul ya taƙune fiska kamar wanda ya tauna flagyl yayinda sauran excos da ke wajen kowa ya sha jinin jikinsa.

 Lokacin da SSK ya ke mataimakin Gwamna bai taɓa ɗaga murya ba, infact idan za ayi meeting sau dubu to zaka iya irga iya maganan da yai a meeting ɗin amma wai yanzu roughly wata biyu daga rantsar da shi ya rikiɗe musu ya koma wani Zaki.

Magana ta ƙarshe da aka yi shine maganar naɗa sabon mataimakin Gwamna wanda Gwamna ya tabbatar mu su da cewa ranan talatin ga wata za’a rantsar da mataimakin Gwamna wanda har yanzu basusan ko wanene ba.

“Babu mamaki idan kuka cigaba da irin wannan sakacin a office ɗin ku zan sake sabon cabinet”

Gwamna na gama faɗin haka ya miƙe tsaye yana ɗaukan wayoyinsa guda biyu da ipad yayinda sauran excos ɗin ma suka miƙe tsaye suna faɗin “Excellency”…

A ɓangaren Asiya kuwa tana fita daga gidan Gwamnati ta wuce ma’aikatar su. Tun a hanya ta kira CY ta ma sa albishir.

Tana isa kuwa Office ɗin MD ta fara wucewa. Tana shiga ta ajiye ma sa takardar hannunta wanda tunda ta cirota daga cikin envelope ba ta iya maidashi ciki ba.

“Yaushe zan koma bakin aikina?” Ta faɗa tana kallon MD daya wangame baki saboda ganin seal ɗin Gwamna akan takardar.

“That’s fantabulous Asiya. Ya kika yi? Kai i’m happy. This means gidan talabijin ɗin mu ne za ta fara hira da Gwamna Saifuddeen. Whoaw!”

Asiya ta sa dariya. Farin cikinta ko kaɗan ba shi da alaƙa da kasancewarta ‘yar jarida ta farko za ta yi hira da Gwamna SSK tun da ya hau kujerar Gwamna. Farin cikin ta ya zo daga abu biyu ne. Na farko aikinta da za a dawo mata da shi (ta tsani aikin editting ɗin nan). Na biyu kuma cimma burinta da ta yi.

 Idan za ka lissafo halayen Asiya to dole ka sako cewa ita ɗin mace ce mai son cimma duk wani abu da ta sa a gaba.

A cikin dictionary ɗinta babu kalmar impossible. Akoda yaushe slogan ɗinta shine *it’s possible but…. HOW*

Kafin ta bar office ɗin MD sai da ya ce ta drafting tambayoyin da za ta yiwa Gwamna ta kawo mishi kafin a tashi…

Tunda Gwamna SSK ya zauna ya ke sauke numfashi akai-akai saboda maganganun Baffan na sa daya saka mishi rashin nitsuwa har ya ji ƙirjinsa ya cunkushe. Ƙarshe hannu ya sa a aljihu ya lalumo inhaler yai saurin jijjigata sannan ya kai bakinsa ya matsa.

 Alhaji Sani ya sassauta muryansa ya ce “sannu Saifu. Har yanzu yana damunka sosai ne?”

“Nagode Baba” abinda ya iya faɗa kenan

Alhaji Sani bai matsa da cigaba da maganar da su ke ba ganin SSK yana buƙatar hutu sai dai kafin su rabu ya jaddada ma sa cewa tabbas zai kai ma sa ziyara zuwa office ɗin sa gobe.

Bayan Gwamna ya bar Kachallah house kai tsaye gidansa ya wuce dan har yanzu ba su koma gidan Gwamnati ba saboda gyararraki da ake yi.

Bayan wannan dogon rana ba abunda ya ke buƙata irin bacci cikin kwanciyar rai amma yana isa falonsa ya iske Bilkisu tana zaman jiran sa.

“Excellency Darling” ta faɗa tana manna ma sa kiss a kumatu.

“You’re just here on time, yanzu na gama parking kayanka. May be mu je ka gani ko akwai abubuwan da za ka buƙata”

“Parking?”

“Dont tell me ka manta jibi Asabar za mu koma Government house”

“An gama gyaran ne?” Gwamna ya faɗa yana zama a kan kujera

“Darling yaushe ka fara mantuwa ne. Jiya fa na ke gaya maka an gama gyaran gidan za mu iya shiga yanzu”

“Bilkisu ki miƙo min ruwa mai sanyi please”

Sai da ta ɗan tsaya kaman mai shirin shawara da zuciyarta kafin ta miƙe. Ya sani da a falon ƙasa su ke sai dai ta kira ma sa Hansa’u ko ɗaya daga cikin ma su yi mu su aiki.

Ko da ta kawo ruwan ba ta barshi ya sha da daɗin rai ba ta cigaba da maganar komawar su gidan Gwamnati.

“Hansa’u da Uwaji za su bimu, sauran za su zauna a nan tunda dai ba za a bar gidan kango ba”

Kallon da ya ke mata kallon ki barni na huta ne amma ita Bilkisu sam ba ta karanci hakan ba. Sai ma cewa da ta yi “ko akwai wanda ka ke so a tafi da su bayan su Hansa’un?”

Bai amsa ma ta ba, sai ma  kauda zancen da yai da cewa “ina yarana?”

“Duk sun yi bacci. Mahira ma ta dawo yau da yamma”

Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin “sai da safe”…

***

“Ya Ubayd ina tsoro, mafarkin danayi jiya ya tsoratani sosai”

“Wani mafarki kenan?” 

“Na yi mafarki wai…” sai kuma ta yi shiru. Ta ina za ta fara ce ma sa ta yi mafarkin marigayi Kakanta Gwani yana ɗaura aurenta da Gwamna Saifudden Kachallah. This is absurd ai, ba abune da ya ke da daɗin faɗa ba. Balle ta san halin kayanta da shegen kishi.

“Ance ba kyau faɗin mummunan mafarki dan haka ka barshi kawai”

“Yau kuma?” Ya faɗa yana taɓe baki

“Mu bar zancen kawai. Ya maganan aikin kitchen ɗin nan an saka sink ɗin nan kuwa?”

“An gama Yallaɓiya. Kin matsu ko? Saura wata huɗu da kwana ɗaya tak”

Yana maganan ta ji ƙirjinta ya buga hakan ya sa ta yi saurin faɗin “Insha Allah” shima Ubayd ɗin ya maimaita kalmar.

Bayan sun gama hira da Ubayd ta shiga ɗaki ta iske Umma na duba wasu kulolin abinci. Umma na ganinta ta mata magana da hannu akan ta zo ta duba kulolin ko sun yi kyau. Asiya ta zauna tana dubasu tareda faɗin kulolin sun yi kalan ‘yan ƙyauye.

“Umma ni ban san miyasa kike siyan kaya a wajen Laraba dillaliya ba. Ga kayanta tsada gashi ba wani kyau ne da su ba. Indai ni kika siyawa gara ki mayar mata dan ba su min ba” ta ƙarisa maganar tana turo baki

Umma ta taɓe baki tana kallon Asiya.

“Allah Umma ko kin saka a kayana kyautar da shi zan yi, dan wannan kulan ba zai zauna a dining table ɗin gidana ba ehe”

Umma ta yi murmushi sannan ta mata bayani akan gudummawar da ta ke son bayarwa ‘yar maƙotan su da za a aurar ne nan da sati biyu.

“Yanzu na ji batu Umma na” ta yi maganar tana rungume Umman ta…

Yau ma dai mafarkin data yi ne ya tasheta daga bacci, abin mamaki irin mafarkin jiya ne sai dai wannan karan Gwani ya haɗa hannunta dana Gwamna yana ma ta nasiha akan mahimmancin haƙuri da kuma yarda da juna a rayuwar aure.

Ba ta cika yin mafarki ba hakan ya sa a mafiya lokuta idan ta yi mafarki za ka ga abun yanada nasaba da rayuwarta.

“Allah ka sa wannan mafarki ba gaskiya ba ne. Ubayd na ke so ya Allah” ta faɗa a hankali tareda sauke ajiyar zuciya sannan ta koma ta kwanta sai dai bacci ya gagareta…

***

Asiya ta fito daga kitchen a fusace saboda ruwan wankanta da aka juye.

“Wani marar imanin ne ya juye min ruwana?”

“Waye a banɗakin nan ne?” Ta faɗa tana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin kaman za ta ɓalla shi.

“Mutum ya tashi da Asuba ya saka ruwa azo a juye ma sa, a hakan ba za a saka masa wani ba. Koma waye yau sai ya biyani ruwana”

Kusan minti uku sannan Hindatu ta buɗe ƙofa ta fito ɗaure da zani.

“Miye ne kike ta buga ƙofa kamar wata sabuwar mahaukaciya”

“Ke ce mahaukaciyar ai. Na saka ruwa a heater kin zo kin juye min saboda tsabar iya shege”

“Dama akwai wanda ya kafa dokar idan kana gidan ubanka sai ka nemi izinin Agola kafin ka yi amfani da abun gidan ne?”

Asiya ta buɗe baki za ta yi magana amma ta fasa saboda ɓata lokaci ne biyewa Hindatu da sassafen nan. Ba ta san mi ta tsarewa wannan Hindatun ba. Ta rasa kishi ta ke da ita ko kuma haka kawai tsantsar ƙiyayya ce.

Banɗakin ta shige ba tareda ta tankawa Hindatun ba, ta fito da bokiti ta je ta ɗebo ruwa mai sanyi. Kafin ta ce za ta haɗa wuta ta ɗaura wani ruwan wankan lokaci zai tafi dan haka kawai ta daure ta zo ta yi wanka da ruwan sanyi. Tana fitowa kuwa da gudu ta je ta shige ɗakin su ta kullo ƙofar da ƙarfi

Umma ta kalleta ta ce lafiya? da hannu

“Sanyi Umma” ta amsa tana ƙarisawa wajen jakar kayan kwalliyarta.

Ƙarfe bakwai saura kwata Asiya ta fito daga gidansu sanye da wandon jeans blue, baƙin riga sai farin blazer jacket da ta saka sannan ta yane kanta da  light blue gyale. Keke ta nema ta wuce ma’aikatar su.

Tana zuwa office ta fara duba tambayoyin da ta tsara wanda jiya da daddare MD ya kirata ya ce ta ƙara da tambaya ɗaya wato miyasa Gwamna ya naɗa tsohon Kwamishinan ayyuka Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa.

Kusan komai ya tafi daidai. Zuwa ƙarfe tara Asiya da CY su ka kama hanya zuwa gidan Gwamnati.

Lokacin da su ka zo an ajiye su a waje na musamman kafin Gwamna ya fito.

A cikin ofishin Gwamna kuwa COS ne ya ke ganawa da Gwamna.

“Your excellency ina so ka dai sake tunani akan wannan lamari, yanke wannan allowance ɗin dai dai ya ke da fushin cabinet members ɗinka”

“Wani ɓangare ne cikin magana na baka gane ba?. Kana sauraron kanka kuwa?. For God’s sake bayan ɗimbin ayyukan da ke gaban mu har kuna da zuciyar da za ku tambayi wani allowance”

“Excellency wannan allowance ɗin tun kafin administration ɗinka ake bayarwa idan ka ce ba za ka cigaba da bayarwa ba za a samu matsala”

“Look Mr Damana. Ba zansa hannu a wannan ɗimbin kuɗin ba bayan munada abubuwa dayawa a gaban mu. Ka ƙara jaddadawa Mr Paul cewa bazan biya kuɗin nan ba. Now please leave my office”

COS ya miƙe jiki a sanyaye.

Bayan fitan COS Gwamna ya kira Sakatare

“Malam Baffayo ka haɗa meeting da Contractors ɗin nan ƙarfe goma”

Sakatare yai saurin cewa “Excellency akwai hiran da za ka yi da ‘yar jarida daga Hill TV ƙarfe goma, sun ma iso lokaci su ke jira”

Har zai ce a ce su dawo wani lokaci sai kuma ya fasa yace  ya maida meeting ɗin sa da Contractors ɗin ƙarfe goma da rabi saboda minti talatin kacal zai yi da su Asiya.

Asiya na tsaye tana yiwa CY magana Gwamna da tawagarsa su ka iso.

Ganin CY yayi saurin miƙewa ya sata juyawa ba shiri.

“Your excellency Sir” CY ya faɗa yana murmushi. SSK ya miƙa ma sa hannu CY yai saurin saka hannu biyu ya damƙi hannun SSK yana faɗin ” myself Clement Yohanna”

“Welcome Mr Yohanna” sannan ya miƙawa Sunusi hannu dreban daya kawo su Asiya.

“Allah ya ja zamanin Gwamna. Allah ya kare ka, Ubangiji ya maka jagora” Sunusi ya dinga sunbatu kamar zai haɗiye Gwamna saboda farin cikin sun yi musabaha da Gwamna SSK.

Tunda Asiya ta juya ta ganshi bakinta ya kafe. Yadda kasan an tura mata dunƙulen Auduga a maƙoƙoro haka magananta ya toshe ya ƙi fitowa. Sau ɗaya su ka haɗa ido amma gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. Kaifin idanunsa gareta sun karya ma ta duk wata laka da ke jikinta. Abin mamaki wai ita Asiya-Shahidah da ta ke iƙirarin ba mutumin da ba za ta iya magana a gabansa ba sai gashi kusan minti biyu da zuwan Gwamna wajen ta kasa ko da gyaran murya ne.  A baya duk lokacin da aka yi maganar ƙwarjinin SSK ƙaryatawa ta ke yi sai gashi yau ta gani a zahiri.

Bayan Gwamna ya gama darawa bisa surutun Sunusi da CY sannan ya maida hankalinsa ga Asiya.

*”Asya?”*  Ya kira sunanta da sigar tambaya

Ji tayi jiri yana shirin kwasarta a wajen saboda irin yadda taji wani abu ya ratsa jijiyoyin jikinta lokaci guda. Taya ma zai iya kiran sunanta da daɗi haka?

Ta yi kusan sakan goma kafin ta iya haɗiye koma minene daya toshe mata maƙoƙoro ta ɗan yi ƙaramar gyaran murya sannan ta ce ” your excellency, Asiya Shahida Faruƙ Baba”

“Of course. The famous Asya ta tashar Hill tv”

“Sit” ya faɗa yana nuna mu su kujera. Sai da ya zauna kafin suma su ka zauna 

“Wannan location yayi ko za a chanja wani?”

CY yai caraf ya amsa da cewa “yayi your excellency. Barin saita camera sai a fara ɗaukan hiran”

Da rawar jiki CY ya miƙe ya fara saita camera yayinda Asiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tanajin kamar idanun Gwamna yana yawo a duk ilahirin jikinta. Sai yanzu ta yi dana sani da hijabi ta saka ba gyale ba.

Kusan minti shida kafin CY ya gama saita komai ya ɗagawa Asiya hannu yana faɗin one, two…. “ina zuwa CY” ta faɗa sannan ta yi saurin ɗaukan ruwan da aka kawo mu su ta tsiyaya a kofi ta kafa kai sai da ta shanye. Ta sake tsiyaya wani ta shanye.

CY ya ɗaga gira sama yana faɗin “Aseey are you nervous?”

Asiya ta yi saurin girgiza kai tareda yin gyaran murya ta ce “muje, na shirya “

CY na ɗaga ma ta hannu ta tattaro duk ƙarfin halinta ta fara bayani kamar haka *”ma su kallon mu barkar mu da warhaka, barkan mu da sake saduwa da ku a cikin shirin nan mai suna ‘Siyasar mu a yau’. A yau dai za ku ga sauyin tsari, domin shirin namu kwacokam zai kawo muku hira ne da wani shahararren ɗan boko, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wato mai girma Gwamna Saifuddeen Sa’ad Kachallah inda zai bamu cikakken tarihin rayuwar sa da yadda aka yi har ya kawo wannan matsayi. Ni Asiya-Shahidah Faruƙ Baba zan gabatar da shirin a madadin abokin aikina wato Comrade Faisal Kamaye”*

Sakataren Gwamna ne ya ƙariso wajen da sauri ya ɗan rankwafa yai wa Gwamna magana a kunne. Hakan ya sa C Y ya dakatar da ɗaukan shirin.

Gwamna ya kalli Asiya ya ce “za’a dakatar da shirin zuwa ƙarfe shaɗaya Insha Allah”

Bayan Gwamna ya tafi sannan Asiya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda fara yiwa kanta fiffita da hannu dan duk iskar wajen ta mata kaɗan.

CY ya matso wajenta yana yi mata dariya tareda tsokanarta kan cika bakin da tayi kafin zuwansu sai gashi ganinta kusa da Gwamna ta ruɗe.

Tun suna jiran Gwamna zai dawo ƙarfe shaɗaya har su ka fara sarewa ganin har ƙarfe ɗaya saura.

“CY anya ba za mu tafi ba. It seems wannan Gwamnan ya manta da mu fa”

Kafin CY ya bata amsa  Sunusi driver yai saurin ɗaga murya da cewa ko ƙarfe nawa ne za su jira Gwamna tunda ya ce su jira shi.

“Bar Aseey, tana mana baƙin cikin kyautan da Gwamna zai mana ne” CY ya sa baki.

“Wannan maƙon ne zai baku kyauta?. Keep dreaming Clement”.

“Allah idan aka bamu banda ke aciki tunda naga adawa ki ke da Gwamna”  Sunusi ya faɗa yana ƙarisa sauran maltinan da Asiya ta rage.

Bayan Gwamna ya bar wajen su Asiya kai tsaye office ɗinsa ya wuce inda Alhaji Sani Kachallah ke jiransa. Idan ba shi ɗin bama waye zai shiga office ɗin Gwamna kai tsaye haka bayan Gwamna baya zaune a kujera.

“Baba sannu da zuwa” SSK ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa. Bayan sun yi musabaha sannan ya je ya zauna a kujerarsa yana kallon Alhaji Sani. Sun gama maganar naɗa mataimakin Gwamna tunda ya naɗa wanda su ke so bai san kuma mi ya kawo sirikin nasa office ɗinsa ba wannan safiya.

Bai yi mamaki ba da Alhaji Sani ya kawo maganar allowance na cabinet members daya riƙe. Sai dai duk da kunyan Alhajin daya ke ji hakan ba zai sa ya aiwatar da wannan baɗala ba.

“Baba tunda na hau kujeran nan na ke tsoron haƙƙin mutane da ke kaina. Idan na basu kuɗin nan tamkar na ci amanar wannan Jaha ce. Bayan ɗimbin albashi da sauran allowance da doka ta tanadar a basu miyasa zan sake ɗaukan maƙudan kuɗi na basu bayan akwai tarin ayyuka a gabana”

Gwamna yayi maganar ne a sanyaye saboda darajar Alhaji amma idan da zai fidda tiriri da zuciyar sa ke yi to ba ƙaramin amon wuta zai yi ba.

“Saifu kenan. Kaga siyasa lamari ne daya ke buƙatan hankali da takatsantsan. Kwata-kwata abun da za ka yi a wannan kujera kafin a sake wani  zaɓe bai kai shekara ɗaya ba. Idan kuwa hakane dole ne ka tafi da mutanen nan yadda aka riga aka ɗaura su akai. Idan muna da rai kaci zaɓe sai ka fara naka sabon tsarin”

Gwamna yai shiru yana kallon Alhaji Sani. Yadda yai maganar cin zaɓe ya bashi mamaki. Domin zaɓe dai ba ayi ba balle a san ko zai koma kan kujerarsa ko ba ze koma ba.

“Baba da kamar wuya. Kuɗin sun yi yawa”

“Ka biya kaso 70% na kuɗin”

Gwamna ya tauna leɓensa na ƙasa tareda sauke ajiyar zuciya. Yadda Alhaji Sani ya shawo kansa akan maganar naɗa Bala Yamai a matsayin Mataimakin Gwamna baya tunanin wannan karanma zai bar ofishinsa har sai ya samu abinda ya ke nema.

“Zan biya su kaso 40%”

Alhaji Sani ya ɗan ɗaga ido sama na ɗan daƙiƙu kafin ya sauke akan Gwamna Saifuddeen ya ce “mu rufe shi kaso 50% Saifu”.

Bayan fitan Alhaji Sani daga office ɗin Sakatare ya shigo ya sanar da shi Contractors da za ayi meeting da su sun iso. Gwamna ya miƙe ya fita.

A chan wajen meeting ɗin ma wani ɓacin ran ya tarar domin kusan kaso saba’in da biyar na ayyukan da marigayi Gwamna Saminu Bacchi ya fara duk akan bashi ne. ‘Yan Kwangila suna son a biyasu kuɗaɗen su idan ba haka ba sun dakatar da duk wasu ayyuka har sai baba ta gani.

Gwamna ya duba COS ɗinsa sannan ya maida dubansa ga Mr Paul. Waɗannan biyun sun fi kowa ɗaga jijiyar wuya akan maganar allowance amma yanzu ana maganar ayyukan cigaba na Jaha amma kowannen su yayi tsit.

Kuɗin allowance ɗin nan da su ke buƙata idan da za a haɗa na wata huɗu zai biya gaba ɗaya basussukan da contractors ɗin nan su ke bin Gwamnati.

Haƙuri Gwamna ya basu tareda mu su alƙawarin zai biyasu dukkan kuɗaɗen su zuwa wani watan sai dai wannan wata za su fara ne da kaso 25% na kuɗin da zai biya su. Basu ɗau lokaci ba suka amince da maganar Gwamna.

A take a lokacin Mr Paul ya miƙa masa wasu takardu tareda check Gwamna ya saka hannu sannan aka miƙawa jagoran contractors ɗin wato Mr Azad Sahib Khan.

Gwamna na komawa kan kujerarsa Mr Paul da COS suka biyo bayansa da takardar da suke son ya saka hannu. Gwamna ya duba takardan a walaƙance sannan ya kalli fiskar Mr Paul wanda ƙarara ta nuna bai ji daɗin kaso 50% ɗin da za a basu ba ya ce ” Mr Paul ina fata baka manta maganan ƙarin albashin malaman makaratan firamare ba”

“Your excellency na sani”

“Good”.

Kusan ƙarfe biyu saura kwata da Gwamna zai fita sallar Azahar Sakatare ya tuna masa da su Asiya da ke jiransa tun ƙarfe goma.

Gwamna ya girgiza kai ya ce su dawo gobe dan akwai inda zai je idan yayi sallah.

Idon Asiya ɗar akan wayarta lokacin da wani security ya iso ya ce musu Gwamna ya ce su dawo gobe ƙarfe goma.

“Kan Uba…”

“Mungode zamu dawo gobe ɗin” CY ya faɗa yana hararan Asiya.

Har suka isa ma’aikatarsu Asiya bata bar zagin Gwamna ba kan walaƙantasu da yai. Har iƙirari ta yi akan gobe ba za ta koma ba sai dai Comrade Faisal ya je yai tunda dama asali shirinsa ne. Sai dai MD bai bata damar hakan ba dan cewa yai ita ɗin dai yakeso tayi hiran da Gwamna goben.

Da dare da Ubayd ya zo hira kaman ta shaƙeshi dan yadda ta ke masifa tamkar shine Gwamnan.

“Mine, sunana Ubaydullah ni Likitan Ido ne ba Gwamnan Jahar Congo ba. Ki ajiye fushinki a gefe please”

“Dan shi Gwamna ne sai akace ya maidamu Awakai. He treat us like goats fa. Ya shanya mu for good 4 hours munata jiransa”

“My Asiya Gwamna fa akace. The first citizen of the state”

“And so bloody what!”

“Shikenan. Yayi haka a chanja hiran”

“Da wani shegen idonsa a wajen…” ta ƙarisa ƙarshen jimlar a hankali saboda wani abu da ya zo ya dabaibayeta. Idon da ta ke zagi shi dai ta gani yau ta birkice, ta rasa nitsuwarta. Idon ne dai da ya ke sukanta kamar kibiya lokacin da ta ke zaune daura da shi kafin CY ya gama haɗa camera.

Ba ta gayawa Ubayd wannan ba ƙila shiyasa ta dage kawai akan cin mutuncin da Gwamna ya mu su. Sai da Ubayd ya sako zancen kayan lefenta da yake haɗawa kafin ta ture maganan Gwamna a gefe ta koma ta rayuwar da su ke shirin farawa tare nan da watanni kaɗan.

***

Taron gaggawa Mr Paul ya kira a gidan Yallaɓai tunda suka haɗu kuwa aketa cacar baki sai da Yallaɓai ya tsawatar kafin sukayi shiru.

“Mr Paul ina sauraronka”

Mr Paul ya ɗaga takardar da Gwamna SSK ya sa hannu yace “Yallaɓai tunda Saminu Bacchi ya hau kujera bai taɓa chanja tsarinmu ba amma gashi nan wata biyu da hawan Saifuddeen ya hanamu allowance lokacin da ya ga daman bamu kuwa kaso hamsin ya bayar. Ka gaya min ta ina zamu yarda da wannan cin mutunci. Idan har ba zai iya ba to kuwa yai resigning a ɗaura Bala Yamai”

“Ka ci gidanku Eugene Paul. A gabana kake cewa Saifu yai resigning saboda baka da hankali”

“Alhaji Kachallah ka kama girmanka, ka san bana yarda da cin mutunci a gidan nan”

“Ayi haƙuri Yallaɓai amma Paul ya sani cewa an ɗaura Bala Yamai ne ba dan shi ba sai dan kawai lokacin saka mutumin Agun ne a matsayin mataimakin Gwamna. Ya kamata kuma ya sani cewa ba zan lamunta a ci mutuncin ɗana ba”

Bayan duka ɓangare biyu sun gama gabatar da ƙorafinsu sannan Yallaɓai yai magana.

“Kowani Gwamna muna bashi wata shida dan ya aiwatar da abinda ya ga dama a farkon tenure da kuma ƙarshen tenure ɗinsa. Lokacin Saifuddeen ne yanzu, Mr Paul ka barshi yai abinda yake so”

“Amma…” Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu hakan ya sa shi datse maganarsa.

Back to top button