Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 22 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

*_Typing📲_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

 

_Shafi na ashirin da biyu_

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

____________

……..Tsaf ya gama bincike wayar, cikin Sa’a kuwa ya samu abubuwa da yawa fiye ma da waɗanda yake neman. Hakan bai ishesa ba sai da ya saita wayar tata da tashi ta yanda duk sanda aka kirata ko ita ta kira shima kiran zai shiga wayarsa. Kuɗaɗen bankinta biyu dake kan wayar suma ya gama haddace pin nata batare data sani ba, a yanzu ya zauna ya kwashesu tsaf ya maida a nasa account ɗin ya bar mata kaso ɗaya bisa huɗu. Bai tsaya anan ba, ya kwashi wani numbers na abokan huɗɗarta masu muhimmanci harda na Abaan. Ya kammala yana ƙoƙarin miƙewa ya maida mata wayar duk da yasan yanada sauran lokaci saboda maganin daya zuba mata a yogout kira ya shigo. Nadwa ce, dan haka ya ɗaga ya kai kunne batare da yace komai ba. Cike da zumuɗi Nadwa dake tunanin Kainaat ce ta ɗaga ta fara magana kai tsaye, “Matar nan tun ɗazun nake tsumayen kiranki amma shiru kake ji. Ai ɗan Alhaji ya sanar min mutuminki ya dawo gida. ALLAH dai yasa kin aiwatar da duk abinda malam ya baki dai-dai dan mu samu a wuce wajen zuwa gobe. Yanzu ma inada albishir amma sai gobe zan baki idan komai ya kammala” sai kuma tai shiru jin ita kaɗai ke tsiyaya surutunta. Wayar ta cire a kunne cikin mamaki, sai kuma tai tunanin ko Kainaat ɗin na tare da Dafeeq ne shiyyasa taƙi magana. Da sauri ta yanke kiran tana dariya da faɗin, “Haka kawai kin ɗaukama kanki alaƙaƙai”.
Ya jima tsaye yana cuɗawa da cakuɗa zantukan Nadwa a ransa. Kafin ya ce, “Hummm” kawai ya fita ya maida mata wayar dan ya fahimci komai. Wato gidan malam aka kai sunansa, wannan shine dalilin da yasa yaga magani a ruwan wankansa. Ya saki murmushi mai faɗi yana wani cije lips. Da ace ya samu dukan takardu da abubuwan da yake buƙata na Company babu shakka zai iya sakinta yau ma sai dai ta tashi taga doguwar wasiƙa da rubutu. Sai dai an samu akasi. Ba duka takardun Companyn ya samu ba akwai wasu masu muhimmanci da bai gani ba, dan haka sai ya amshesu sannan. Asiri kuma ta cigaba da nema itace a wahale.

Matuƙar mamaki da ruɗani Kainaat ta shiga a washe gari, dan bata farka ba sai washe gari. Ta dinga kallon Dafeeq da yay fuska abinsa, sai dai ta gagara cewa komai. Ko salla batayi ba sai da tai kiran Nadwa. Sai dai ta yi shuka a idon makwarwa batare da ta sani ba. Dan duk abinda ta tattauna da Nadwa shima ya jisa. Dan haka tana gama wayar ya fara borin kumya sakamakon yin wani tunani. Exactly yanda yaji sun tattauna akan halin da malamin yace zai tsinta kansa a ciki ya fara gwadawa. Kafin wani dogon lokaci faɗa ya harƙe tsakaninsu. Ranta fes da farin cikin tunanin aiki yaci. Dan haka itama ta fuske ta biye masa kamar yanda malam ya bata shawarar kunnashi. Al’amarin kamar wasa sai ya zama gaske sakamakon fahimtar da tai babu wasu muhimman abubuwanta data adana a ɗakin a washe garin cikarsa kwana biyu da dawowa gidan. Dan faɗa sosai sukeyi ta buƙaci ya bata abubuwanta. Shi ko bai musa shine ya ɗauka ba dan kai tsaye ma har takai shi da tabbatar mata idan tana son saki sai ta bashi sauran takardun Companyn ta. Idan kuma tai tunanin sanarma wani shima zai sanarma Abaan ɗin da take harin komawa komai, ya ɗan balgata mata wani sirrinta daya ɗauka a cikin waya daya shafi Abaan ɗin.
Matuƙar tashin hankali Kainaat ta shiga. Gaba ɗaya ma ta rikice. A take ta shiga bincike sosai a ɗakinta. Tako samu ya yashe komai harda kuɗin dake a cikin bank nata duka biyu. A takaice dai bata da wani ƙarfi ma da take tunani na dukiya da zaisa ta iya masa rashin mutunci ko gayyato hukuma cikin al’amarin nasu. Sannan maganar zai kaima Abaan wani yankin sirrinta ma wani tashin hankali ne gareta da bazata taɓa fatan ya kasance ba. A cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja a gidan. Ta fahimci hatta wayarta idan tai kira ko aka kirata shima tana zuwa cikin tashi wayar. Sai ma tarasa ina zata kama taji daɗi. Gashi ƙiri-ƙiri ya kulle ƙofar gate yama sallami Dauri maigadi da kuɗi masu yawa wai yaje ya huta zai nemesa. Yayi magana da Manager na Companynta da wayarta cewar a cigaba da al’amura shi da Madam sunyi tafiya zuwa Lagos honeymoon. A haka suka kwashe sati ɗaya a gida babu wani cigaba sai na tafka rikici da masifa. Kowa kuma yaƙi zuwa gidan sakamakon bin duk wanda yasan zai iya nemanta a waya ya tura masa text message cewar sun tafi honeymoon sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya. Tayi masifar tayi zagin tayi kurarin amma yaƙi bata wayar. Ta nema iya nema amma ta kasa gano a inda ya ɓoye. Shi kuma wayar hannunsa babu ma wanda yasan layin sai iyayensa kawai balle wani ya kirashi yasan suna gari. Tun Kainaat na ɗaukar al’amarin wasa harta fahimci yafi ƙarfin wasan fa yaron nan da gaske yake shirin mata ɗibar albarka yake da gaske. A yau suna cikin rikici ta maresa ya rama. A take dambe ya nema harƙumewa a tsakaninsu. Sai dai ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba, ya bubbugeta dan Dafeeq dai akwai zuciyar banza. Sannan duk da ƙananun shekarun nan nashi baya ƙaunar raini kowa ya sani tunma bai kai haka ba. Itama dai ta samu nasarar ƙwala masa plate a goshi harta jimasa ciwo. Hakan yasa shi nufar bayi domin wanke jini batare da ya lura da wayarsa data faɗi ƙasa ba. Yana shiga kira na shigowa, dan haka Kainaat ta ɗauki wayar da sauri, a mamakinta sai taga mamansa ce. A take zuciyarta ta bata shawarar ɗagawa, dan ta fara zargin lallai uwar tasa tasan komai dake faruwa tunda ita kaɗai ke kiransa a layin nan sai babansa. Ɗakin da Khadijah ta zauna ta shiga, ta maida ta kulle ƙofar sannan ta ɗaga wayar tana gab da tsinkewa. Tana kaita kunne Maman Dafeeq na kwaɗa sallama…….

____________★

Abubuwa sun rincaɓe sosai a gidan su Khadijah yau ɗin nan. Dan har dare an hanasu ko ganin Baba. Sai da Zuhrah da taga basu da wata mafita tai kiran saurayinta da zata aura. Hankali tashe ya zo station ɗin. Abinka da mai kuɗi a hannu, cikin ƙanƙanin lokaci da ya ga d.p.o aka basu Baba. Sai dai zuwa safe zasu koma da shi wai za’a turasu kotu dan laifin bin mutum da makami ba abune na wasa ba tunda mutane da yawa sun shaida hakan a cikin anguwa shima kuma baba bai musa ba.
Kusan ƙarfe sha biyu da rabi na dare suka dawo gidan. Idan kaga Khadijah a wannan lokacin dolene ka tausaya mata. Idanunta sunyi masifar kumbura saboda kuka. Gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta fiye da kowa na gidan. Tunda suka shigo ta zube a gaban Baba kawai tana kuka da roƙon dan ALLAH su yafe mata. Ba su Baban kaɗai ba, hatta da ƴan uwanta roƙonsu ta dingayi akan su yafe mata duk laifinta ne, duk a dalilinta ne komai ke faruwa. Babu wanda dai ya iya cemata komai, sai maƙwafcinsu da aketa kai kawo da shi ya ce, “Suje su kwanta da safe koma minene ayi yanzu dare yayi Baba na buƙatar hutu. Dole duk suka shige ɗaki, sai dai sam Khadijah ta kasa barci, daga ƙarshe ta fito ta ɗaura alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta anan baranda ita kaɗai a tsakar gida ta fuskanci UBANGIJI mai share kukan masu kuka. Mai jin roƙon bayi da rahamarsa da jin ƙansa. Yanda take jero addu’oi da magiyar nan gafara a gun UBANGIJI cikin harshen larabci a cikin sujuda ɗinta ya jawo hankalin Baba da ya kasa barcin shima. Tsaye yay a jikin ƙofa kawai yana kallonta. Shi shaida ne duk cikin yaransa Khadijah dabance a fagen ilimi da ƙarancin kwaramniyar, tanada kaifin basira matuƙa, duk da suma sauran nada ƙoƙari amma tata basirar daban ce. Sai gashi ƙaddara da son zuciya ya ɗebeta aikata abinda ta aikata. Dan ALLAH shine shaidarsa yayi iya ƙoƙarinsa akan Khadijah hakama mahaifiyarsu. Sunbi duk hanyar data dace matsayinsu na iyaye domin dawo da ita hankalinta, nasiha, lallashi, kurari matsayinsu na iyaye duk sunyi amma duk da haka basuci nasara ba, ba kuma kowa zai fahimci ƙoƙarin su ba, wasu ma kallon sune masu kuskure sukeyi….
Khadijah da bata san da ana kallonta ba kuka take sosai bayan idar da sallar tana addu’a da roƙon ALLAH gafara da fatan ya ɗauki ranta a tsakanin nan, ya kuma saka iyayenta su yafe mata koda bayan ranta ne, ya wanketa da ga aibatantata da Dafeeq yayi a idon al’umma. Ta jima tana addu’ar anan ma kafin tai yunƙurin miƙewa tana layi dan ta gama yanke shawarar abinda zuciyarta ke ayyana mata. Daga baba har Mama dake bayansa tana hawayen tausayin ƴar tata binta da kallo sukai. Ganin ta nufi rijiyarsu gadan-gadan yasa Baba zabura cikin jan ƙafarsa da bai iya takawa. Tuni Mama ma ta rufa masa baya. Da ƙyar ya iya kaiwa dai-dai Khadijah ta tafi gaba ɗayanta zata afka kanta a rijiyar. Wani irin fisgota Baba yayi ya rungume a jikinsa dake rawa hawaye masu zafi na kufce masa. Mama ma ta haɗasu su duka biyun ta rungume itama tana mai fashewa da kuka. Sai ga Ni’ima da Zuhrah da ashe suma dai ba barcin suke ba a guje suma suka rungume iyayen nasu.
“Baba dan ALLAH ku barni na faɗa, ku yafe min kuma dan girman ALLAH. Nasan na cutar da ku, kuma bazan iya yafema kaina ba. Kun haifeni, kun raineni cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa da nagarta da bajinta irin ta jaruman iyaye da duk ɗa na gari zai so samu a duniya. Amma son zuciya da wata baƙar soyayya mara amfani da amfanarwa ta ruɗeni na bijire muku. Kaicona ni Khadijah, kaico da haihuwar ɗiya irina. Wlhy Mama naga illar saɓama iyaye, naga illar ƙuntata zuciyar Iyaye. Inama ace jiya zata iya dawowa a duniyata na goge da shafe abubuwan dana aikata a gareku. Sai dai kaicona, hakan bazai taɓa kasancewa ba. Na riga na ɓata sunana, na goga muku baƙin fentin da bazai taɓa gogewa a tarihin wannan gida ba. Dan ALLAH Baba, Mama, ƴan uwana ku yafe min ku barni na faɗa cikin rijiyarnan. Maybe idan na mutu ba’a gani na baza’a sake tuna muku da abinda na aikata ba balle a aibantaku da wanda ban aikata ba. Wlhy gara na mutu, gara ace mutuwarma nayi ko Baba?…”
“Muna son ganinki a raye Aunty Khadijah. Dan ALLAH ki daina faɗar zaki kashe kanki. Muna sonki muna sonki sosai”. Zuhrah ce ta faɗa cikin kuka da sake ƙanƙame hannun Khadijah data kamo. Ɗagowa tai da sauri tana girgiza ma Zuhrah kai, sai dai kafin tace wani abu baba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaura yatsarsa akan lips dinta ya ce, “Shiii!! Ya isa haka. Ku zaunar dani kun san yanzu babanku babu ƙafa.”
Da sauri suka kakkamashi zuwa baranda, Ni’ima ta kawo tabarma da sauri ta shimfiɗa masa. Duk zama sukai shiru sai Khadijah dake durƙushe gabansu ta kama kunnuwanta har yanzu tana hawaye. Kusan kallon mintina uku Baba ya mata kafin ya ce, “Bamu labarin miya faru kika iya barinmu Khadijah? Miya faru a inda kuka je? Ya akai Dafeeq ya dawo ga iyayensa bayan watanni da barinku gida amma ke mace kima kasa hakan? Da gaske ne Dafeeq ya jima da sakin ki kika tafi wani waje daban saboda tsoron kar ki dawo garemu ai miki dariya?”.
“Sam ba haka bane Baba. Wlhy ba haka bane ba. ALLAH kuma shine shaidata duk abinda zan faɗa muku shine gaskiya. Sannan inada shaidu akan abinda zan faɗa mukun tun daga wanda ya ɗaura auren mu har zuwa inda muka zauna da dalilin farkawata a barcin kuskuren bijire muku na dawo gida. Duk da wlhy tunda na barku ban taɓa jin salamar haka ba a raina. Kawai ina dannewa ne dan kar naima Dafeeq laifi a wautata da son zuciya. Amma kullum a cikin mafarkinku nake, nakanyi kuka a ɓoye da jin kamar na dawo na baku haƙuri, sai dai ina jin tsoro, ni burina da nawa hangen shine idan na haihu zan zo muku da yaƴan maybe kufi yafe min kuskurena. Sai kuma aka samu akasin hakan abinda nake burin ya zamar min jagoran zuwa gareku ya gagara samuwar…….”✍️

 

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 23 By Billyn Abdull

 

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button