Halysaah Page 220 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 220…*I dedicate this very chapter to one and only Meenah parrot😍 a big fan that turns sister, I don’t even want to start mentioning her huge contributions effortlessly from the beginning of Halysaah till now🥹, thank you so much for ur support Meenah, Allah ya bude maki hanyoyin samu fiye da zaton ki, Allah ya raya maki Aseeyah, ya sa ki gama da iyayenki lafiya*💖 Ana gobe naming ceremony din little Jawwad Khaleesat ta fito daga dakin Mami da daddare bayan Mami tace mata taje Ajay na jiranta tun daxu, throughout ranan bai shigo part din ba saboda mutane, hatta su Nenne da kishiyoyin ummanta har da Hajiya Zaliha da Baaba Gaje duk suna masarautar sun zo sunan little Jay, ga kareren dangin Ajay yan Ethiopia su ma part guda aka basu a masarautar su kwana, tawagar Kilishi na zazzaune parlor ana ta hira da raha Khaleesat ta wuce su ta nufi bedroom din da Ajay ke shiga duk sanda ya shigo part din Mami, tana shiga dakin ta samesa tsaye kusa da window yana danna wayarsa with full attention, ta dinga kallonsa don babu abinda ya zo mata a rai sai farkon rayuwarsu na Maryland tun daga sanda ta fara ganinsa, who could have thought Ajay will one day become her husband and the father of her child, ya daga kai ya kalleta, ta sauke idonta ta rufe kofar ta nufesa tana tafiya a hankali, kallonta kawai yake babu ko kiftawa har ta iso gabansa, red henna din hannunta yayi masa kyau sosai, ya sauke idonsa kan kirjinta da suka kara ciccikowa, jawota jikinsa yayi a hankali, murya can kasa yace “Jeeddah” Ta kwantar da kanta saman kirjinsa ta lumshe idonta tana sauraron bugun zuciyarsa cikin sanyin murya tace “Happy Birthday my man” Yana murmushi yace “You still remember?” Murmushi kawai tayi idonta a lumshe ta yaya zata iya mance birthday dinsa har karshen rayuwarta, ya zame dankwalin kanta yana kissing gashinta slowly memory din birthday gift din da ta basa 3 years ago na yawo a kansa, the day she gifted him that parcel was also among the days he will never forget in his life, the gift meant a lot to him that very day, yayi kasa da murya yace “I turned 37 today” Tana murmushi a hankali tace “And I knew you when you were just 34….” Yace “Just?” Dariya tayi, ya fara Kissing dinta yana tattaɓa kirjinta yace “Hope ba dayawa kike ba Baby Jay ba?” Er dariya tayi tace “To ai nasa ne yanxu” Ya hade rai yace “In ji wa?” Ta ɗan kallesa tace “Inji Mamarsa” Ajay yace “In dai takura min zai yi gwara kawai a mika ma takwaransa shi tun yanxu, idan ya so sai ya ba Mami ta tayasa rainonsa har ya girma, ko kuma ya ba matarsa ta hadasu da Eeman ta rene su, ni ya bar min matata” Ita dai kawai murmushi take bata ce komai ba, ya saka hannu a aljihunsa ya ciro abinda ke ciki ya saka mata a hannunta, a hankali yace “Thank you for making me a father Jeeddah, thank you for this expensive gift, I know what i am giving you is not enough, it’s just a little token….” Khaleesat ta daga hannunta tana kallon abinda ya saka mata cikin hannun bata ko kifta ido, ta daga idanuwanta ta kallesa a sanyaye, rungumesa tayi cikin sanyin murya tace “Thank you so much Mijina, Allah ya saka maka da alkhairi, Allah ya bar min kai….” Ya girgiza mata kai yace “It’s little Jeeddah, nothing can compensate the little being u brought to life…..” Shiru tayi tana kara jin son mijinta sosai a ranta, ya ɗago kanta yace “Mu je ki gani?” Girgiza masa kai tayi ta kamo hannunsa tace “I don’t want anyone to know about it plss dear, kawai ka bar shi kamar naka ne” Yace “Saboda me?” Shiru tayi, yace “Baki so ne?” Da sauri tace “A’a ba haka bane, me zai hanani son kyautar da ka min? Just that idan wasu suka taya ni farin ciki wasu baza su yi farin ciki ba, i don’t want to spoil any one’s mood, and most importantly bana son ya kasance kamar an fifita ni akan Hadiyah tunda ai ba ni kadai na haihu ba, kuma kafin in haihu ita ce ta haihu a gidan nan” Ajay ya zaunar da ita gefen gadon dakin ya zauna kusa da ita yana kallonta yace “Listen to me Jeeddah, to avoid all this duk ranan da kika yi 40 days we are leaving this palace to my own House, I am glad Mai martaba ya bani izinin in zauna duk inda zan zauna as far as it’s within Bauchi, i don’t want you to be feeling this way anytime i gift you anything….” Khaleesat dai shiru tayi tana kallonsa don har ranta bazata so abinda zai sa wani yaji haushi a gidan nan because of her, in dai za ayi mata abu zai fi a hada ayi masu ita da Hadiyah a nata tunanin, Ajay ya katse mata tunanin da take yace “If you mean Hadiyah, ai ita ma mijinta yayi mata kyauta da ta haihu, he gave her two complete set of Gold jewelries worth 17M or so, and babu wanda bai sani ba a gidan nan, ko bata nuna maki ba?” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa don ko da wasa Hadiyah bata nuna mata ba, bata kuma gaya mata ba, can ta langwabar da kai tana ɗan murmushi tace “Ta gaya min” Yace “So why are you worried saboda na siya maki mota?” Rungumesa tayi ta lumshe ido tana shakan daddaden kamshin turarensa cikin sanyin murya tace “Thank you so much Hubby, Allah ya kara daukaka min kai” Dagota yayi ya bata ɗankwalinta ta rufe gashinta suka fita daga bedroom din zai kai ta taga lafiyayyen ride din da ya siya mata, Khaleesat ta dinga kallon sabuwar mota dal that is worth over 40M, juyawa tayi ta bi inda suke da kallo kawai ta rungumesa hawaye cike idonta tace “Thank you so much the love of my life” He was so glad she loved it, yana murmushi yace “Anything for my wife” Khaleesat na komawa cikin gida ta kasa gaya ma Mami kyautar da Ajay yayi mata na sabuwar mota, Mami dai sai gasa ma takwaran only son dinta cibiya take a dakin, Khaleesat ta zauna gefen gado, sai ga Hajiya Habibah ta shigo dakin da sallama, Mami ta amsa mata, Hajiya Habibah ta zauna kusa da Mami tayi kasa da murya tace “Fulani Aseeyah kin san me ke faruwa kuwa?” Mami na kallonta don sai da gabanta ya fadi tace “A’a, me ya faru?” Hajiya Habibah ta taɓe baki tace “Yanxu labari ke iske mu wai za ayi amputating ƙafafuwan Walid duk biyu” Mami ta ci gaba da abinda take yi ma jaririn hannunta without much interest don ta tsani gulma, can dai tace “Mai martaba ya gaya min tun shekaranjiya ai, Allah ya sa mu dace” Hajiya Habibah ta gyara zama tace “Aiyoo ashe kin sani, mu sai yanxu mu ke ji a bakin Nafisah tunda er uwata ce ai, gaskiya ta kare ma Hafsat a rayuwa, ta gina ramin mugunta ta afka ciki, ki ga fa don ta cusguna ma Mai martaba bayan ya saketa haka nan ta kwashe ‘ya yan nan mata ta bar gidan nan, su ma suka nuna sun zabi uwarsu akan umarnin da Sarki yayi, sai nake ganin kamar asiri ta ma yaran nan wallahi banda haka ai umarnin Mai martaba za su bi ba nata ba, shi ma Walid din da ya kwance mata zani a kasuwa haka nan ta kinkimesa ta tafi tunda Allah ya dora mata sonsa a ranta kamar ta kashe kanta, kuma banda Hajja da tayi ta tausan sarki ai da ya sallama mata yaran gaba dayan su, amma kin ga duk da haka yana daukan responsibilities dinsu tunda Hajja ta masa umarnin yin haka, to wallahi ta haka Hafsah take kara samun uban kudaden bin Malamai, yanxu gashi ta kara ja ma Walid salalan tsiya za a yanke kafafuwa, tunda aka ce spinal cord dinsa ya tashi aiki ba sai su hakura daga ita har shi ba, amma bayan duk abinda ya sameta akan idon kowa a gidan nan saboda tana da wata mugun manufa na daukan revenge sai da ta kinkimi yaron nan ta kai sa can wani kauye a kasar Nijar wai ana warkar da irin wannan lalura, wato ya warke ya dawo ya karasa Junaid, in ba mu yi hankali ba mu ma duk ya bi ta kan mu, to gashi nan ta kai sa sun salwantar masa da sauran kafafuwan, an ce duk sun rube suna wari inji Nafisah, shikenan ya zama gurgun gaske yanxu….” Mami dai taki tanka Hajiya Habibah tayi concentrating akan little Jay dake hannunta, mikewa Hajiya Habibah tayi tunda Mami bata bada fuska ba tace “Allah dai yayi mana me kyau duniya da lahira, ya sa mu fi karfin zuciyar mu” fita tayi daga dakin ta kullo kofar, Mami ta ja tsaki, ita dai Khaleesat tayi shiru don tun shekaranjiya Mami ta gaya mata abinda ya samu Walid and she felt bad about it, after a while Khaleesat ta daure kawai ta nuna ma Mami makullin motar da Ajay ya bata, and Mami was very happy, tun a daren ta sanar ma su Kilishi duk suka tafi ganin mota a parking space, kan kace me gida ya dauka an siya ma Halysaah ride, zancen har kunnensu Nenne dake sashin da aka sauke su, dangin Ethiopia su ma labari ya isa har inda aka masu masauki suka yi ta farin ciki da murna amma banda Ruky Bjw da take ganin kamar Ajay ya tatike kansa ne wannan tsadadden mota haka da ya siya ma Khaleesat, ta ina zai fara tara wannan uban kudade da ya kashe yanxu, abun duk ya dameta. Duk wani expenses da aka kashe na sunan Eeeman exact dinsa Mai martaba ya bada for little Jay’s ceremony amma sai da su Kilishi suka yi exaggerating komai yanda na little Jay zai fi na Eeeman armashi don sai da suka karo raguna biyu bayan babban Cow da raguna uku da sarki ya bada a siya, sannan suka karo kaji, suka yi komai extra baja baja, Souvenirs ma sai da yayi tripling wanda aka yi ma Eeeman don har da su atamfofi a Souvenirs din da za a raba, ga uban gayyan da suka yi na jama’a kamar za ayi taron bikin aure, duk Ummi na kula da abinda suke yi, haka ma Hajja, Mami kuwa ko lura bata yi ba tana ta harkan gabanta. Ranan suna masarauta ya cika makil da jama’a, duk inda ka bi baƙi ne a gidan, anyi shagali iya shagali, dangin Ajay dama rumfar su daban a gidan, can na hango su Hajiya Safiyyah Usuman an sha gwaggwaro da baƙin glasses ga jakarta a hammata, Shanono dai na gefe ta sha jan lipstick tayi shiruu tana ta tunanin ran Monday zata tafi aiki fa gashi bata san kwana nawa za a dauka ana shagalin sunan ba don taga alama kamar ba shagalin rana daya bane wannan uban abubuwan ciye ciyen da aka yi a gidan, Hajiya Fati Nata’ala kuwa cikin su Kilishi ta shige suna ta cashewa da kidan kwarya, Coursemate Amina Mas’ud ta dungura ma parrot er ta, ita ma ta shige cikinsu Kilishi ana ta rawa, Nenne da tawagarta ma na zazzaune a tsakar gida, kai kace Nenne ta hada jini da sarauta tsabar yanda ta kame tana basarwa, juyawa Nenne tayi da sauri tana kallon Hajiya Zaliha jin ta ce “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…..” Nenne ta gwalo ido, su Mama Zubaida da Baaba Gaje ma duk suka maida hankali kan Hajiya Zaliha, bayan Hajiya Zaliha ta ajiye wayar Nenne na zare ido tace “Lafiya Zaliha? Me ya faru??” Cike da alhini Hajiya Zaliha tace “Haiydar ne ya kirani yake gaya min Allah yayi ma mahaifiyar Abdul rasuwa yanxu” Duk su Mama Shatu da Baaba Gaje da Aunty Murja suka hau salallami, Nenne tace “Don Allah ku rufa mana asiri ku yi a zuciyarku kar ayi zaton wani abu ne ya faru mu ɗaga hankalin jama’a suna tsaka da budiri su yi zaton wani a danginmu ne ya rasu, Allah ya ji ƙan musulmi kawai, idan mun koma gida sai ayi jimamin a nutse, amma ba a nan ba ana tsaka da farin ciki, don Allah ku rufa mana asiri kar mu lalata masu taro…..”


