Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 77 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Ranshi a matuƙar 6ace yace”hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ƙarƙashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!

Waro ido waje Sehrish tayi tana kallonshi,hankali atashe jikinta sai faman kerma yakeyi,ji take tamkar ta zura da gudu,saboda yadda taga Sgr ya fusata tsoranta kar ya ciro belt ɗin wandonsa ya rufe ta da bugu,tana cikin wannan zancen zucin muryar shi ta katseta da cewa”listen to me!”
Natsuwa tayi tana sauraronshi kamar yadda ya Umarta,
“Banaso na ƙara ganin Azmee tazo part ɗina da sunan za tayi mun aiki,ke nakeso ki kawo mun breakfast sannan ki gyaramun part ɗina,hope u understand?”
Muryarta har kerma takeyi wurin cewa”E zan..na..fahimta,’
Jinjina kanshi yayi tare da cewa”Okey,yanzu kizo kiyi serving ɗina,then idan kin kammala ki gyara mun bedroom,”babu wasa a fuskarshi yake yin maganar,wato yadda ya tsare Sehrish yadda kasan ƴar cikinshi,ta yi tsuru tsuru,Ni dai bansan ya Sehrish zata ƙare ba,ga umarnin mahaifinta gana kuma yayanta mai matukar tsauri,shin wa zatayi ma biyayya?a sanin mu dai Umarnin Mahaifi shine sama da komai,bayan na mahaifiya,bari mu gyara zama muga yadda wannan Al’amarin zai kaya,

Ja da baya yayi tare da juyawa ya koma saman sofa ya zauna sannan yace”Am waiting for u,”
Jiki asanyaye Sehrish ta ƙaraso inda yake,yatsun hannunta sae kerma sukeyi,a haka ta shiga serving ɗinshi,a plate ta zuba mashi chicken pepper soup ta tura mashi agabanshi,yana ci tana satar kallon fuskarshi,ba ƙaramin mamaki Sgr yake bata ba,ta jinjina ma ƙarfin halinsa na yau,batasan me zai faru gobe ba amma tabbas akwai badaƙala,

Bayan ya kammala cin dinner ɗin nashi,sai da ta gyara mashi bedroom ɗinshi,sannan ta samu ta fito daga part ɗinsa da kayan abincin,a hankali take taka stairs ɗin,ranta a jagule ba don komai ba sai don karya umarnin mahaifinta da tayi,wanda kuma ba komai ne yaja hakan ba face shegen tsoron Sgr da takeyi,da ba don haka ba,da ba abunda zai hana tayi mashi gardama,don a yadda yake da bad temper ɗin nan ta kuskura tace zatayi mashi jayayya,bugu zai kai mata,zuƙunnawa tayi asaman steps ɗin benen tana faman cizon la66anta,a hankali ta furta”sae yaushe ne zan fita daga wannan KURKUKUN ƘADDARAR da nake ciki?yaushe ne abubuwa zasu fara tafiya dai dai arayuwata?daga wannan sai wannan”? Idonta cike tab da hawaye tayi maganar,kafin ta yunƙura tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinsu bayan ta kai kayan kitchen,a hankali ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,bayan ta datse ƙopar ta juya,mamaki tayi ganin jahad ruƙe da wayarta a hannunta ta ƙura ma screen ɗin wayar ido,duk a tunaninta zata zo ta same ta tayi bacci,ashe bata koma bacci ba tun bayan da Azmee ta tashe ta,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon a gefenta ta zauna,cike da mamaki take kallon jahad,ganin ko motsi ba tayi,bama tasan ta shigo ɗakin ba,ko menene yaja hankalinta haka?
“Jahad!”Sehrish ce ta ambaci sunanta,a firgice ta juyo tana kallonta,ganin sehrish yasa ta sakin murmushi tare da cewa”Har kin dawo,ae nayi tunanin acan zaki kwana,”
dariya sehrish tayi tare da dungurin goshinta tace”Abun hada tsokana,Nima nayi tunanin zanzo na same ki,kina bacci ashe idonki biyu,me kike yi da wayar ne”?don naga gaba ɗaya yaja hankalinki,”
Ƙayataccen murmushi jahad ta saki tare da cewa”Hmmmm ba zaki gane bane,wani zazzafan hausa novel ne nake karantawa acikin wayarki,dama jira nakeyi kizo in tambayeki a ina zan samu cigaban littafin”?
Cike da mamaki Sehrish tace”Novel kuma?ae ni bana karatun littafin hausa,banma san ya akai kika samu littafin a wayata ba,don gaskiya bana ajiye su,”
Wani kallon rainin wayau jahad tayi mata tare da cewa”Kina nufin duk haɗuwar littafin nan baki ta6a karanta shi ba!hakanan kike ajiyar shi acikin wayarki?
Yatsina fuska Sehrish tayi tare da cewa”nifa bansan dashi ba,may be cikin friends ɗina na makaranta ne wata wurin tura ma wasu ta turamun shi batare da sani na ba,”
jinjina kai jahad tayi tace”gaskiya an barki a baya,tunda uwata ta haife ni ban ta6a karanta littafin me shegen daɗi irin wannan ba,tunda na fara karantashi bakina ke awashe,kamar anyi mun albishir da gidan aljanna,”ta karasa tana daria,
Ta6e baki sehrish tayi tare da cewa”Wai ya sunan Littafin ne?naji sai faman zuzuta shi kike yi,inaso inji sunanshi ne saboda tun daga kan sunan littafi ake tantance in mai daɗi ne ko mara daɗi,”
Ƙayataccen Murmushi jahad ta saki tare da Furta sunan Littafin*A SANADIN MAKWABTAKA*!
Maimaita sunan Sehrish tayi”A sanadin makwabtaka”
Jahad tace”kwarai kuwa,sunanshi kenan,”
Gyara zama sehrish tayi tare da cewa”kawo wayar mu gani,zan jaraba karanta one page naji ya daɗinsa shin yakai Abban sojoji da nake jin friends dina nata faman cewa ya hadu”?
Jahad tace”Ae ya zarce nan,”tayi maganar tare da miƙa mata wayar tace”one page kika ce zaki karanta,zan jira ki kammala don inci gaba daga inda na tsaya,”
Hannu sehrish tasa tare da kar6ar wayar,ta buɗe page ɗin littafin asanadin makwabtaka,a natse ta fara karantashi,”
Zuba mata ido jahad tayi tana jira taga reaction ɗinta,
a hankali murmushi ya fara bayyana akan fuskar Sehrish,daga ƙarshe ma ta fashe da dariya,tunda tafara karanta littafin sae faman zabga murmushi takeyi,ita da tace zata karanta one page sai gashi ta zarce page biyar,ganin abun ya wuce gona da iri yasa jahad sanya hannu ta kar6e wayar tana cewa”Ya isa haka,je ki kwanta,gobe akwai shirye shiryen waleema,”
ɗaure fuska sehrish tayi tare da cewa”wlh baki isa ba,sai da kika fara ɗanɗana mun zuma abakina na lasa daga baya kuma kizo kice zaki hana ni”?
itama jahad ɗin ta tamke fuskarta tace”ae ni na fara karantawa tun farko,ke da bakisan ma da zaman littafin acikin wayarki ba sai da na faɗa maki”
wurga mata harara sehrish tayi tare da miƙa mata hannu tace”Bani wayata,”
Jahad tace”wlh bazan bada ba,sai na kammala karanta littafin nan,”
Abu kamar wasa suka shiga cece kuce,ran sehrish yayi mugun 6aci,aikuwa ta cakumi wuyan rigar jahad,nan fa suka shiga kokowa asaman gadon kamar ƴan wrestling,wani bugu da Sehrish takai ma jahad a kumatunta ne yasa ran jahad ya 6aci,a fusace tayi wurgi da wayar Sehrish,kai tsaye ta faɗi saman tiles,ta daku sosai ji kake taratssss!screen ɗin wayar ya tarwatse,
Tashin hankali,
la66an sehrish har kerma sukeyi wurin cewa”kika fasa mun wayata”?
Girgiza kai jahad tayi hankalinta a matuƙar tashe tace”dan Allah sehrish kiyi haƙuri,wlh bada sanina nayi hakan ba,raina ne ya 6aci saboda naji zafin bugun da kikai man”
Hawaye ne suka cika idon Sehrish cikin murya kamar ta mai son yin kuka tace”Ni babban baƙin ciki na,ba wayar data fashe bane,nasan daddy zai iya canzamin wata,Amma littafin fa?a ina zan same shi,daga ji zai dauke ma mutum damuwa yasa shi nishadi”?
Jahad tace”Am so sorry sehrish,na maki alƙawarin cewa,zan nemo maki shi,nasan baza a rasa me shi ba,akwai wata class mate ɗina sunanta hafsat bature,ta kware wurin karanta littattafan hausa,insha Allah idan muka koma school zan tambayar maki ita,nasan bazata rasa littafin a wayarta ba,idan ma babu littafin to ina da tabbacin cewar tasan marubuciyar shi,sae ta bamu numbar wayarta,”
Jin haka yasa sehrish sakin murmushin jin daɗi,matsawa tayi tare da rungume jahad tace”yawwa jahad,kinyi tunani mai kyau,nagode sosai,yakamata mu kwanta yanzu,dare yayi fa sosai,”
tayi maganar ayayin da ta gyara kwanciyarta,itama jahad ta kwanta,atare su kayi addu’ar bacci cikin ƙanƙanin lokaci baccin ya ɗaukesu,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

“Nagode sosai da shawarwarin daka bani,kuma insha Allah ina da tabbacin cewar in muka biyo mashi ta wannan hanyar zamuci nasara akanshi,abun zai zama tamkar wasan kwaiwayo,” Acewar Abbansu junaid dake tsaye a bakin ƙopar fita daga ɗakin Uncle abusufyan,Uncle ɗin na a bayanshi fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,da alama sun kammala tattaunawar da sukeyi,

“Nike da godiya yaya Hossain,idan har wannan abun ya tabbata,zanfi kowa farin ciki,”

Juyowa Abba yayi cike da zolaya yace”kada ka manta,gobe ne fa sunan ƴan ukun da aka haifa maka,me zaka yanka masu”?
..sunnar dakai ƙasa Abusufyan yayi yana dariya,yace”Sa za’a yanka masu guda uku,raguna uku,ɗawisu guda uku,ƴan shila guda ɗari uku,kaji guda ɗari uku suma,”
Dariya Abba yayi yana bubbuga kafadarshi yace”Abun ya ƙayatar dani wato komai guda uku kenan za’a yanka masu,idan ma ba uku ba to ɗari uku,dole dae ukun ta fito kamar yadda suke ƴan uku,a ƙagare nake da goben nan tayi,bari na hanzarta zuwa na kwanta,”
“Allah ya nuna mana ita lafiya,”acewar abusufyan daga haka Abba ya bude kopar tare da fucewa yana faɗin”mu kwana lfy,”
Bayan fitarshi,Abusufyan ya koma tare da hayewa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke fuskantar ceiling,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face ABU,a kullum cikin tunanin wani hali take ciki yake,haƙiƙa ya damu da ita sosai,kusan kullum ne sai yayi mafarkinta,dama da yawa idan ka sanya abu aranka,zaiyi wuya bakayi mafarki akansa ba,babban abunda yafi damunshi duk in zai ganta a mafarkin cikin wani irin mawuyacin hali,
“Bakomai ne yasa na damu sosai akanta ba,face sanin cewa ita marainiya ce,bata da kowa a duniyar nan wanda zai damu da ita idan bani ba,da kuma ƴa’ƴan data haifa ba,Abu bata da kowa bata da wanda zai neme ta idan wani mummunan abu ya faru da ita,da ace ƙaddara bata haɗani da Abu ba harna aureta ba,a yau akace ta 6ace,nayi imanin cewa babu wanda zai damu akan hakan,mahaifinta ne kawai shi kuma Allah yayi mashi rasuwa,Allah yajiƙanka baba buzu,haka ya damƙa mun amanarta,duk da yasan halina bana jin magana ga ƙuruciya dake fusgata,yayi mun halaccin da bazan ta6a mantawa ba,kuma Insha Allah zan ruƙe mashi amanar daya bani,bazan ta6a mantawa dashi ba,saboda shine silar komai,gashi har nasamu ƙaruwar ƴan uku tare da ƴarsa,naso ace yana raye nasan zaifi kowa farin cikin ganin jikokinsa,’
Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwansa masu ɗumin gaske,murmushin takaici ya saki tare da gyara kwanciyarshi,ya runtse idanunshi daƙyar bacci ya ɗauke shi,

A 6angaren Abba kuwa,bayan sun rabu da Uncle abusufyan,yana shiga bedroom ɗinshi,ya tsaya turus ganin junaid kwance yana sharar bacci,ga mommynshi agefe tana bacci itama,girgiza kai yayi tare da cewa”bansan meyasa junaid keyi mun haka ba,ya raina ni wlh,”juyawa kawai yayi tare da fucewa daga bedroom ɗin ya koma upstairs bedroom ɗin junaid ya nufa ya kwanta,ya ƙyale shi ne saboda yana cikin farin cikin gobe walima,baison abunda zai 6ata ranshi,

Karanta>>> Abubuwa 8 da yin jima’i akai-akai ga mace mai ciki ke yi.

Wuraren ƙarfe 2 na dare junaid ya farka sakamakon zungurar shi dayaji anyi da sanda,a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare manyan idanunshi masu ɗauke da bacci,ƙasa ƙasa yaji ana ambatar sunanshi Junaid!junaid!aikuwa a tsorace ya sanya hannunshi tare da toshe kunnanshi ya fasa uwar ƙara,kai tsaye sautin ƙarar daya saki ta daki dodon kunnan Alexandra,a firgice ta farka,ganin junaid da tayi a zaune jikinsa sai kerma yake yi hakan yasa ta miƙe tare da janyoshi jikinta tana faɗin”junaid!romeo ɗina what’s wrong with u?baka lafiya ne,”duk tabi ta tsorata da halin da yake ciki,
..Muryarshi na kerma yace”Mommy,wani abu zai faru dani,dan Allah ki taimaka mun,banso in mutu yanzu,”
Jin wannan maganar ta junaid ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba,kankame shi ta ƙarayi muryarta na rawa tace”Junaid,kadaina faɗin haka banason ji,babu abunda zai faru dakai indai kana tare dani,nasan cewa mafarki kayi,pls calm down ur mind,mu koma mu kwanta,
ɗagowa yayi daga jikinta,cikin shessheƙar kuka yace”Mommy dan Allah,ki tashi muyi sallah,sai kiyimun addu’a,”
a ruɗe tace”Salla kuma junaid,am not a muslim bana sallah,zan daiyi maka addu’a,”
“A’a mommy nidai ki tashi muyi sallah,kiyimun addu’a,”Ashagwa6e yayi maganar,
“Junaid ka fahimce ni,bakasan cewa niba musulma bace!ko daddynku bai ta6a faɗa maka bane,Ni bana sallah,I don’t even know how to do it,”
Jin haka yasa junaid sake fashewa da wani sabon kukan mai sautin gaske yana cewa”Mommy ki tashi muyi sallah,ki tashi mommy!wlh idan baki tashi munyi sallah kinmun addu’a ba mutuwa zanyi,”
Tashin hankali,gaba daya junaid yabi ya rikice mata ya hanata sakat,duk yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita ba musulma bace,bata sallah amma abun ya faskara,junaid ya kurmance mata,
Babu arziƙi ta amince zatayi sallar,tasata gaba yayi ta shiga toilet ta dauro alwala,ko alwalar bata wani iyaba,ruwa kawai ta watsa a fuskarta,ta wanko hannayenta da kafafuwanta tafito,shi ma ya shiga cikin toilet ɗin,wucewa tayi wurin wurin closet ɗinsu,ta buɗe kayan Abbansu ne a jere sai kayan sawar ta,wanda tazo dasu,gaba daya babu hijabin da zata sanya,dakyar ta samu wani mayafin doguwar rigarta mai ɗan tsayi,ta ɗauko shi tare da sanyashi ajikinta,sae yayi mata tamkar hijabi,
tsayawa tayi tana jiran junaid ya fito suyi sallar,lamarin nashi ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ƙiri ƙiri junaid yasata za tayi sallah,ya rufe idonshi ya nuna tamkar baisan cewa ita ba musulma bace,aranta tace”Anya junaid bai samu ta6in hankali ba?in ba haka ma meyasa zai yi forcing ɗina akan inyi salla bayan yasan cewa ni ba musulma bace,Omg!ni bansan ma ya akeyin sallar ba,ko time ɗin baya dana ta6a musulunta ba don Allah nayi ba,ko sallah banyi a lokacin,”
tana cikin zancen zucin nata sai ga junaid ya fito daga cikin toilet yana faman yarfa hannunshi,ruwan alwalar da yayi yana ɗiɗɗigowa ƙasa,
Carpet ɗin salla ya dauko masu na abbansu sannan ya dawo ya shimfiɗa masu shi,

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Juyawa yayi tare da kallon Mommyn tasu wanda tayi sototo tana binshi da kallo,
“Ni zan shiga gaba saiki tsaya abaya,”
Dawowa bayanshi tayi ta tsaya,shi kuma ya tsaya agaba,tare da daidaita natsuwarshi,ya kabbara sallar,anatse suka shiga yin sallar atare,tunda suka kai raka’a dayan farko,bacci ya kwashe Alexandra,junaid bai sani ba yaci gaba da yin sallarshi,sai da yayi kusan raka’a takwas sannan ya sallame,
cikin bacci taji an ambaci sunanta da ƙarfi”Mommy”!!a firgice ta farka tare da buɗe idanunta tana kallonshi,muryarta adisashe irin ta mai bacci tace”junaid har mun kammala sallar,”zum6ura mata baki yayi rai a6ace yace”nadai kammala sallar mommy,kin barni ni kaɗae,kina ta bacci,”
cikin lallashi tace”kayi haƙuri romeo ɗina,saida na faɗa maka cewa banyin sallah,nifa ban iya ba,nadai samu nayi ɗaya,dakyar itama na samu nayi ta,don bacci nake ji,”
“Shikenan kiyimun addu’a yanxu,sai muje mu kwanta”
Yadda yayi maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,nan take taji kamar bata kyauta mashi ba,jiki asanyaye ta sanya hannunta tare da ruƙo hannunshi,ta shiga karanta mashi addu’oin,cikin harshen Faransanci,bai damu da yaren da takeyi mashi addu’ar ba,saboda yasan cewa Allah yana ji da kowani irin yare aka roƙesa,”
Ta jima tanayi mashi addu’a tana tottofa masa asaman sumar kanshi,kafin daga bisani suka koma saman gadon suka kwanta,ba ƙaramin kwanciyar hankali junaid ya samu ba,tunda ta tofa mashi addu’ar nan take yaji wani sanyi aranshi,tamkar an bashi ƙwarin guiwa,kuma tunda ya kwanta bacci ya ɗaukeshi bai ƙara jin an zungure shi ba,

DARE YAYI GARI YA WAYE,

Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara ɗaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za’a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za’a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,nan suka haɗu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wani irin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko’ina na kitchen ɗin,

Hatta main palour ɗin kamshi ya karaɗe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya ɗauketa,tana cikin bacci ta dinga jin ƙamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziƙi ta farka tana faɗin”wannan wani irin ƙamshi ne mai tashin mutun daga bacci”?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,

Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa”Ikon Allah,ƙamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daɗi,”
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
ƙarasawa tayi cikin kitchen ɗin suna haɗa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa”ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba ɗaya girkin nan bai ciyu ba,ƙarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faɗa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba ɗaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari’a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za’a kaita ƙara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daƙyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa….’
Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba ɗaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace”Kai gwaggo,”
gwaggo tace”ƙarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faɗi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za’a kai ƙarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za’ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku ƴan gayu da kuka ɗauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza’ayi dashi ba,”
Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba ƙaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,”
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya ɗaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta ɗaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce ɗakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga ɗakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaƙulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta ɗauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba ƙaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya ƙare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
“Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,”azmee ce tayi maganar,
Gwaggo tace”komi ma da kuka girka,a zuba mun in ɗanɗana inji yaya ɗanɗanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaɗan,”
murguɗa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faɗin”nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan ƙare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,”
Saude bata fito daga cikin store ɗin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a ƙaton tray ta fuce dashi tana cewa”idan na cinye wannan zan dawo a ƙara mun,”
dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace”sai kin dinga haƙuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu’a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka ɗaura mata,”
Saude tace”insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu’a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waɗanda ke shirya masu wannan maƙarƙashiyar,Allah ya kawo ƙarshensu,”
Azmee tace”ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,”
Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Sabulun Da Zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Da Kuma Maganin Kuraje

Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba’a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za’a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka’aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,

Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a ƙarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin ƴar aikinsa ba,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa”Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu,”
jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,ɗaure da towel a waist ɗinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruƙe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi,”
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa”Aiki ya same ki hosana,kowa na ɗokin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuɗin da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu,”
Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuɗi tace”dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuɗin da muka samu”?
Jinjina kai sehrish tayi tace”kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki,”
Cike da zumuɗi ta miƙe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet ɗin tana kwankwasa ma jahad,
“Ki fito nima in shiga,”
Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji ɗazu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau,
Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part ɗin Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast ɗinshi,kuma ta gyara mashi bedroom ɗinsa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata ɗauka,da anjima Azmee tace za’ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,

Karanta>>> Domin Dawo Da Martabar Nonuwanki Cikin Sauki.

Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buɗe tana ƙare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya,
“Da rana zan sanya shadda lace ɗita,da marece kuma zan ɗauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown ɗin,naga sai faman ƙyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba ƙaramin kyau zanyi ba,”ta ƙarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba ɗaya jikinta adon stones ne masu ƙyalli da ɗaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daƙyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba ɗaya tabi shape ɗin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist ɗinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki,
siririn mayafin ta ɗauko,ta sanyashi asaman kafaɗarta,wa’iyazubillah,ba ƙaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace”Nayi kyau,”
Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba ƙaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buɗe baki tace”Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar ƴar matan aljanna,”
Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga ɗakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baƙi tana kai masu,
Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta,
“Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,”.

Azmee tace”ae kin zarce duk yadda nake faɗi maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faɗi,”
murmushi kawai ta saki tare da cewa”Aunty azmee ina kayan breakfast ɗin babban yaya inaso nakai mashi,”
“Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki”?
“Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki ƙara aiki part ɗinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faɗa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki,
Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa”Tabɗijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daɗi idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki”?
Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta ƙasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla,
Gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa”Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast ɗin ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki,”
Amsa mata tayi da toh,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,’

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

Tunda sehrish ta fito daga kitchen ɗin gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa’a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba,
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data ƙarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinshi,taji muryar namiji a bayanta,
“Ji mana,”a firgice ta juyo don taga wanene,ɗan zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa”Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,’
muryar sehrish na kerma tace”Am…um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito,
“Okey,zan tsaya awaje,but pls don’t stay long,”
Ya faɗi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace”Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,”ya ƙarasa maganar tare da fucewa,
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace”Kowanene wannan jarababben,baisan nan part ɗin wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,’
kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,

Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,ƙiris ya rage ta saki tray ɗin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,

“Zoki wuce ciki,”yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom ɗin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya ɗauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi,
..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faɗi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruƙe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haɗashi da abokanan ƙannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya,
Fuskarshi a tamke yace”Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part ɗina!”?
Muryarshi na kerma yace”wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miƙo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso ƙafata nazo,”
Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi ƙarya bayan yaji duk abunda yake faɗa ma sehrish,
Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi,
Hannu Sgr yasa tare da ruƙo neck tie ɗinsa yace”menene sunanka”
Cikin sauri yace”Jazz,”
Sgr yace”Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,’yana kai ƙarshen maganarshi yace”just u can leave…..”ae tunkan sgr ya ƙarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs,
Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,

a ƙopar shiga bedroom ɗin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ƙoƙarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape ɗin hips ɗinta ya fito sosai,ba ƙaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya gane dalilin dayasa wannan saurayin ya biyota,tunda yaga babban kaya dole ya zauce,baisan cewa babban goro sai magogin ƙarfe,

gyaran muryar da yayi ne yasata yin saurin ɗagowa,tana ganinshi tasha jinin jikinta,ƴan kame kame tashiga yi kamar wata mara gaskiya,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samu wuri daga gefen gadon ya zauna,sannan anatse yace”Am hungry,”
cikin sauri ta dawo gaban table ɗin tashiga ƙoƙarin yin saving ɗinshi,coffee mai zafi ta fara miƙa mashi acikin cup,hannu yasa tare da kar6a,yana cikin kur6ar coffeen kamar ance mashi ya ɗago,idanunshi suka sauka akan Boobs ɗinta da suka fito sosai,tamkar zasu fasa gaban rigar,zukunnawar da tayi ne yasa suka yi hakan,
Nan take ya shaƙe,ba arziƙi ya ajiye cup ɗin dake hannunshi,gaba ɗaya duk yabi ya susuce ya shiga yin tari,tamkar maƙoshin shi zai 6allo,ganin haka yasa sehrish dakatawa daga yin saving ɗinshi da takeyi,tashiga yi mashi sannu,
daƙyar ya samu ya daidaita natsuwarshi,muryarshi ashake yace”Ke!ina scarf ɗinki yake”?
Muryarta na kerma tace”gashi nan agefenka,da zanyi gyara ne,na ajiye shi anan don karya takuramin,
Harara ya ɗan watsa mata tare da cewa”ɗaukarshi ki yafa,banason na ƙara ganinki haka kina yawo,”
“Toh,”ta amsa mashi,sannan ya kai hannunshi a gefenshi ya ɗauko mata mayafin ya miƙa mata,tana kokarin kar6a ta aza hannunta asaman nashi,ɗagowa yayi da idanunshi kai tsaye suka shiga cikin nata,agigice tayi saurin kawar da nata idanun,
Tunda yake arayuwarshi wata ƴa mace bata ta6a jan hankalinshi ba,da surar jikinta,harya shake irin haka ba,mata dayawa suna kawo mashi kansu,wasu har cire kayansu sukeyi don suja ra’ayinshi,amma basu ta6a cin nasara ba,donshi bashi da wannan Sha’awar ko kaɗan,akan sehrish ne kawai ya ta6a ganin wani sauyi,A ranar da suka faɗa saman gadon shi atare,har yau yana mamakin wannan abun,

*Aunty Babba*

Tuni sun kammala shirinsu na zuwa abuja,wankan shadda ta ɗauka,doguwar rigace ta kashe ɗaurin ɗan kwali abun sai wanda ya gani,Hafsat kuwa Code lace ta sanya ajikinta,riga da skirt milk colour,su aunty babba hada trolley na kayan sawa,ta sanya abayan boot ɗin motarsu,dama tace in taje sai tayi sati biyu,hafsat dae kallonta kawai takeyi,ita kadae tasan me zai biyo baya,hafsat ce take tuƙin motar yayin da aunty babba ke zaune agefenta,
kafin su fita daga garin Kaduna,Hafsat tace”Mommy,yakamata mu tsaya a kasuwa ki saya mana niqabi,”
aunty babba tace”Niqab kuma?daughter me zamuyi da niqabi sai kace wasu munafukai,”
murmushi hafsat ta saki tare da cewa”Mommy zaiyi mana amfani sosai,tunda nace maki mu sayi niqabi akwai dalilin dayasa nace maki haka,’
…..guntun tsoki aunty babba tasaki tana cewa”Ni ba wani niqabin da zan siya,kedai in kina buƙata ga hanya nan kije ki siya,”
Parking ɗin motar tayi,adai dai bakin wani shopping mall,
“Ni zanje in siya,kina bukatar wani abu”?
“A’a adawo lafiya,”
Fita hafsat tayi daga motar,kusan 15 mins sai gata tadawo hannunta ruƙe da sabon niqab,ta siyo,komawa tayi cikin motar,sannan ta tashi motar,suka miƙi hanya,

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

A 6angaren Amani kuwa tuni ta kammala shirinta,sun ɗau wankan lafaya itada Amal,Abbas da kanshi ya ɗaukosu acikin Motarshi,

Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,wasu matsiyatan motoci haɗaɗɗun gaske,suka shigo cikin layin gidan,irin motocin nan na jigunan masu kuɗi,masu rai da numfashi,su huɗu ne motocin tare da security guards suke,kowace mota soja ne ke driving ɗinta,har suka ƙetara gate ɗin gidan,
A jere motocin suka tsaya,da gudu wani soja,jiki na rawa yazo ya buɗe mata ƙopa,
Tunkafin ta fito daga cikin motar,hayaƙin tabar da take sha ya fara fesowa waje,tashin hankali da ba’a sama shi date !Ko wacece Wannan.

 

Back to top button