Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 19 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma sha tara_

_____________

METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da’ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1….12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za’abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al’umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah

Phone number 07038708382/09069163665

_________________

…….Wani irin jijjiga zuciyar Dafeeq tai a dalilin jin amsar da maigadi ya bashi cewar ai tunda safe wai Khadijah ta fita a gidan. Baki ya buɗe zai masa masifa sai kuma ya fasa tamkar wanda ya tuna wani abu. Ciki ya koma, babu jimawa sai gashi ya dawo da key ɗin mota a hannu. Dan zuciyarsa na sanar masa Khadijah na can tsohon gidansu ne. Sosai ya dinga gudu duk da babu nisa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso. Ji yay ya ɗan samu nutsuwa ganin gidan kamar ba’a kulle ba, dan haka ya afka ciki yana wani cika da batsewa shi a dole zaiyi hukunci. Sai dai me, tako ina babu alamar Khadijah a gidan, kai hasalima kamar babu wanda ya shigo gidan.
(Kodai gidan Baba Hakimi ta tafi) zuciyarsa ta ayyana masa cike da ƙarfafawa. “Tabbas hakanne ma, dan nasan ko giyar wake tasha bazatace zata tafi Kano ba kuwa. To inama taga kuɗin motar tafiyar ne. Aiko bazan je ba, ta gama guje-gujenta har sai nan da kamar wata ɗaya ma zan leƙa gidan baba Hakimin sannan ta gama galabaita. Barima na cire layin da duk ƴan gidan suka sanni da shi ta yanda zan ƙara dafata da gigita rayuwarta”. Ya ƙare faɗa yana wani murmushi da ciro wayarsa a aljihu ya cire layin da yasan su baba Hakimi zasu iya samunsa da shi. Fitowa yay ya kulle gidan, daga haka ya tattara batun Khadijah ya watsar gefe, dan daga nan gidan abinci ya nufa yaci ya ƙoshi sannan ya fito zuwa wani hotel ya kama ɗaki dan itama Kainaat ɗin yay alƙawarin sai ya mata yaji na kwana biyu, sannan ya tsara yanda zai fara aiwatar da shirinsa a kanta dan ya fahimci itama ƙwalluwar kanta ce dole sai ya tashi tsaye…

     🚴🚴🚴Hummm

___________

        Babu wanda ya iya ƙwaƙwƙwaran motsi a tsakanin Baba da su Mujee. Sun zubama JJ dake kuka ido kawai zukatansu na duka tamkar zasu ɓallo ƙirazansu su fito waje. Tsahon mintuna biyar sannan cikin ƙarfin hali mahaiyarsu da suke kira Inna ta share hawayenta muryarta na matuƙar rawa ta ce, “Jazool kai ne ka aika aka kashe su kenan?”.
“Wlhy Inna ni bance su kashesu ba.” JJ ya faɗa cikin shaƙewar murya da karkarwar harshe hawaye na kwaranya a idanunsa….
A fusace Yaya Inusa ya ce, “Munafuki ƙarya kake yi. In ba kai kasa su kashesu ba ya akai sunanka ya fito a bakinsu. Dolene dasa hannunka a mutuwar bayin ALLAHr nan Jazool. Ka zaluncemu ka ɓata mana sunan gida, ka zubar mana da mutuncinmu. Idan aure kake so miyyasa bazaka faɗa mu maka ba. Duk da mu bamasu ƙarfi bane na tabbatar bazamu gagara maka aure ba harda ginin muhallin zama. Miyasa ka aikata wannan zalincin Jazool? Miyasa kasa a kashe su? Mi suka maka innalillahi wa-inna ilaihiraji’un…” kuka ya sarƙeshi.
Yunƙurawa JJ yay zai tashi amma ya kasa sai jikinsa ne ke rawa. Dole ya koma ya kwanta yana jujjuya kai ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo. “Yaya wlhy bance su kashesu ba, na turasu ne kawai su amso min wayoyinsu su kuma kwaso min takardun gidan, nayi hakanne dan na ɓoye duk wani abinda Hajiya Lailah zata iya amfani da shi wajen tona min asiri. Takardun gidan kuwa zan mata barazana da shi ne bayan ta yarda bazata fidda maganar ba sai na maida mat…..”
Tauuuu!!!!. Ka ke jin saukar wani gigitaccen mari a kan fuskarsa. A take kowa ya gigice a ɗakin aka shiga waige-waige. Yayinda JJ ya dafe kunci ya fashe da wani irin marayan kuka tamkar zai shiɗe. Wani marin aka sake ɗauke fuskarsa da shi, sai gashi zaune dingan gan yana kwara ihu da waige-waige. Amma abun mamaki babu alamar wanda ke marinsa. Sake ƙwala gigitacciyar ƙara yayi yana zabura da mamuƙe cinyarsa. Dai-dai nan Alimah ta bayyana a cikin idanunsa da wuƙa jazurr alamar an sakata a cikin wuta ne. Dan gaba ɗaya inda ta ɗora masa wuƙar ma ya yaye. Sai azaba mai ratsa kwanya dake shiga har a tsakkiyar ƙwalwar kansa. Sauran ƴan ɗakin ba ganinta suke ba, dan haka duk sukayo kan JJ ɗin suna tambayarsa mike faruwa da ƙoƙarin ganin cinyarsa daya riƙe gam.
Bai iya basu amsa ba, sai kuma da yake yana faɗin, “Dan ALLAH kiyi haƙuri zan faɗi musu gaskiya, ki taimakeni ki bar ƙonani, dan ALLAH kada ki kasheni na tuba. Wlhy ni ne nace su sakama gidan wuta bayan sun ƙwace komai nasu, amma wlhy bance suma mahaifiyarta fyaɗe ba. Nayi tunanin kuma zasu gudu subar gidanne dan wlhy bance a saka musu wutar dan su mutu ba ne. Kuma koda sukazo suka sanar min abinda suka aikata na musu masifa har nace bazan biyasu sauran kuɗin aikin ba mukai faɗa da su, sukace zasu tona min asiri shine na haƙura na basu cikon kuɗin, ni kuma na cire kuɗin Hajiya Lailah dake account ɗinta dana Anoosh dan duk naga komai a cikin takardun gidan da alama ta rubuta ta ajiye ne saboda Anoosh ɗin. Sannan ko auren Anoosh dana yarda nayi batare da saninku ba nayi ne dan mutane karsu zargi komai a kaina, sai kuma sanadin hakan akaita kawo kuɗin gudunmawar kula da ita a asibiti daga ƴan anguwar da mutane, sai kuma Anoosh ɗin ta rasu kafin ayi aikin. Da kuɗinne na fara kasuwanci na kumayi gini na sai mota sannan na gyara gidan nan”.
Salati aka sake ɗauka a ɗakin matan na sake fashewa da kuka. Mamaki da al’ajabin JJ na sake kashesu. Dan bazaka taɓa zaton zai iya aikata hakan ba. Duk cikin gidan yafi yaran shiru-shiru, idan ma ka kallesa saika ɗauka shine ustazun gidan saboda ƙarancin yawan kwaramniyarsa a zahiri. Ashe a can cikin rai sheɗanin kansa ne ƙanin iblis….

     ★★★

  Sun iso Kano cikin ƙanƙanin lokacin da ya bama Khadijah mamaki, duk da dai ba’a cikin hayyacinta take ba ma dan hankalinta sam baya tare da ita. Tun a airport ɗin aka sakata a wata ƙyakykyawar farar mota tare da Awwal aka wuce da ita asibiti. Ba haka taso ba, taso ace gida suka wuce da ita ko suka barta ta tafi, sai dai bata iya tayi magana ba dan tana jin jiki sosai. Ga ƙarfinta ya gama ƙarewa saboda jigatar dukan da tasha wajen ƙaton banza Dafeeq, ga yunwa ga barazanar fashewa da zuciyarya ke neman yi na damuwa da tashin hankali abinda zata iya tararwa. An kaita wani clinic mai ƙyau da bata ko san a wace anguwa ne ba. Babu ɓata lokaci aka shiga bata kulawa ta musamman mai nuni da cewar ansan Awwal a wajen, kuma yana da faɗa aji, ko kuma wanda taji yana kira da yayansan ne mai faɗa ajin tunda shine ya turosu nan ɗin shi kuma ya wuce sabgarsa…

      Yini guda curr Khadijah na samun kulawa a asibitin nan dan har ƙarin ruwa suka saka mata. Duk yanda take magiya da roƙon su barta ta tafi gida babu wanda ya saurareta, ga Awwal shima tunda ta farka bama ta gansa ba. Wata Nurse aka sa take kula da ita, a bakinta take jin cewar Awwal ne ya kawo abinci kuma shike tsaye akan komai yanzu babu jimawa ya tafi dan an kirasa a waya. Bata iya tace komai ba sai gyaɗama Nurse ɗin kai datai kawai. Da taimkonta ta gyara jikinta, ta bata wata doguwar riga wai ta saka inji Awwal. Batai musu ba ta amsa, ita dai fatanta su barta ta wuce kawai, dan babban burinta kawai a yanzu danganewa da iyayenta koda ace zasuyi gunduwa-gunduwa ne da ita. Da ƙyar ta ɗan tsakiri abincin tace ta ƙoshi, Nurse ɗin tayita lallaɓata amma ta dage kan ta ƙoshi, dole ta barta ta bata magunguna ta sha. Jingina tai da gadon shiru tana tunani kawai, sai dai jinta take kamar ta rumtse ido taga bata a asibitin nan.
Bayan la’asar Doctor ya shigo dubata, matsawar da tai kan a sallameta yasa shi lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta zasu sallameta a yau ɗin anjima kaɗan. Taji daɗin hakan sosai duk da ranta fal fargabar yanda zata tunkari iyayenta kuma. Kusan misalin ƙarfe biyar Awwal ya shigo ɗakin bayan yay sallama Nurse ɗin dake kula da ita ta bashi izinin shigowa. Tana ƙoƙarin gaidashi kanta a ƙasa wani baƙon ƙamshin turare bayan na Awwal ɗin ya shige mata hanci. Duk yanda taso dauriyar karta ɗago hakan ya gagara. Dole ta ɗago a hankali. Wani kalar harbawa zuciyarta tayi sakamakon saukar idanunta akan kamilallen mutumin mai yanayin nutsuwa da rashin gaggawa. Ido suka haɗa ya kauda nashi a ɗan fisge. Hakan ya sakata maida nata kan ƙasa itama.
Awwal ne yace mata, “Ƴar uwa kin tashi ashe? Yaya jikin naki?”.
Kanta ta gyaɗa masa tare da faɗin, “Alhamdullah”.
Murmushi yay ganin yanda take ta faman noƙe kai, sai kuma ya kai dubansa ga mutumin nan tare da sake juyowa gareta ya ce, “Ga Yaya zai dubaki dan doctor ya sanar mana zai sallameki yau ne”.
Kanta ta jinjina a hankali, batare data ɗago ba ta samu kanta da faɗin, “Ina yini. Nagode sosai da ƙoƙarinku a kaina, ALLAH ya saka muku da alkairinsa. Kuyi haƙuri na saka ku ɓata lokaci a kaina.”
Awwal ɗin ne dai ya amsa da faɗin, “Babu damuwa ai yima kai ne. ALLAH dai ya baki lafiya. Yanzu sai ki faɗa mana address ɗin gidan naku dan mu kaiki ko”.
A ɗan razane ta ɗago ta kalli Awwal ɗin, sai dai karaf suka haɗa ido da mutumin nan da yake cema Yaya. Wanda tunda ya shigo waya ke a kunnensa da alama magana yake da wani, kuma wancan ne ke maganar tunda shi dai baice komai ba tunda ya shigo ɗakin. Kauda kanta tai da sauri gefe, sai kuma ta shiga kokawar haɗiye hawayen dake neman zubo mata. “Basai ma kun sake wahal da kanku ba ai, hakan ma Nagode da kulawarku. In sha ALLAHU zan iya kai kaina gida babu wata matsala”.
“Mune zamu kaiki”.
Dakakkiyar muryarsa ta daki kunnensu a bazata. Kusan a tare suka kallesa dan babu wanda yasan ya kammala wayar. Fuskarsa ba’a ɗaure take ba, amma kuma ba murmushi yake ba. Cikin nuna rashin damuwa da kallon da suke masan ya ƙara ɗan takowa gaban gadon sosai. Muryarsa a sauƙaƙe yanzu ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda muka ɗakkoki zamu kaiki ga iyayenki domin cika ladanmu. Ki kimtsa sai Nurse ɗin nan ta taimaka miki zuwa mota” daga haka ya juya ya dubi Awwal. “Ka tayasu kwashe kayan”.
Da girmamawa Awwal ya amsa masa da “To Yaya”.
Ficewa yay batare da ya sake cewa komai ba. Hakan yasa duk suka bishi da kallo ƙasa-ƙasa musamman ita da Nurse ɗin nan da tagama mutuwar zaune a kallonsa. Dan babu ƙarya guy ɗin ya haɗu kam. Gashi Suit ɗin dake sanye jikinsa sun sake haskaka shi tamkar wani baturen balarabe…

     Tafiya motar keyi amma tamkar tayoyinta na burgawa da bugun zuciyar Khadijah ne. Tunda take a rayuwa bata taɓa jin makamancin ruɗanin da take ciki a yanzu ba. Ji take kamar ta tsilga a motar tace ta fasa zuwa. Ko wata motar tabi takanta kawai a kai gawarta gidan nasu. To amma idan tayi haka ba lallai ta samu rahamar UBANGIJI ba, dan zata mutu iyayenta suna a masu fushi da ita. Bata taɓa tabbatar da ta cuci kanta ba sai yau. Lallai bata yiwa kanta adalci ba na barin iyayenta akan saurayi. Iyayenta jaruman nan masu jajircewa matuƙa da sadaukarwa akan farin cikinsu ita da ƴan uwanta. Duk da kasancewarsu ba masu ƙarfi ba, sun hidimta musu tamkar yanda masu arziƙi ke hidima ga ƴaƴansu. Sun basu ilimin addini dana zamani, sun suturtasu da sutura ta ƙawa koda su bazasu saka ba, sun ciyar dasu da abinci mai daɗi koda su bazasu ci ba. Sun hanasu barci a lokacin da suke buƙatar yin barcin. Amma ta rasa dame zata saka musu sai fifita saurayi a kansu. Ya ALLAH itako minene ya kaita wannan son zuciyar? (Soyayya) zuciyarta ta bata amsa. Jitai hawaye suna rige-rigen gangarowa a kumatunta. A karan kanta ta bama kanta amsa da (Ai babu soyayyar duniya sama data iyaye akan ƴaƴansu….)
“Inaga nan ne ko ƴar uwa?”.
Furucin Awwal ya dawo da ita hankalinta. Firgigit ta ɗago tamkar wadda ta farka a suma. Wani irin jijjiga ƙirjinta da zuciyarta da kanta sukai a lokaci guda sakamakon saukar idanunta akan ƙaninta autansu dake tsaye a ƙofar gidan sanye cikin uniform ɗin islamiyya alamar yanzu ya dawo dan abu yake amsa wajen wani yaro da zasuyi tsaho ɗaya shima dai sanye da uniform ɗin……..✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 20 Complete Novel

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

         _1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

           _2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

              _3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

        _4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

AKWAI BONANZA TA MUSAMMAN TA 24HRS
DAN SAMUN RANGWAMEN BIYAN 1K GA DUKA HUDUN💃💃💃💃💃💃💃
Daga yau 25 December zuwa gobe 26 December🔥🔥🔥🔥🔥

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_KUYI MAZA KAFIN BONANZA TA ƘARE MASOYA😘😘_*

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button