Zafafa 2023

Duniyata Complete Novel Document

Duniyata Complete Hausa Novel By Huguma

Description/Story:

Duniyata Complete Novel Document

Written By Safiya Huguma 

 

Description

“Maaaam…….don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama……idan kika tafi waye zai kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?” Muryar yaron da gaba daya bazai haura shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba’a gaya maka ba…..koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba…..koda baka kalli hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici.

 

Idanunshi qur bisa kanta yana fatan jin qididdigaggun kalmomin

 

“Na fasa tafiya” daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar gabanta.

 

“Don Allah mariya…….ba don ni ba……ko don yaran nan,kiyi haquri……ki zauna ki rungumesu,ni tawa me sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar……” Mutumin da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa.

 

Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa…..sai gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala’i da firgici da take shirin jefa rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo dasu a kansu.

 

Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu…..kodon kalmar mutuwa daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa. Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin

 

“Mariya……idan kika tafi waye zai kula dasu?” A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana rataya jakarta bisa kafadarta

 

“Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas” tana kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske fa take!

Ba zata rusuna ba!.

Da alama kuma ba abinda zai sanyata rusuna din!.

 

Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa.

 

Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar tana cewa

 

“Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da zama,dukkanmu ni daku za’a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba”.

 

Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan fitarta qofar dakin.

 

Wata gigitacciyar tsawar data girmi shekarunsa ya daka masa

 

“Dawo ka zauna!……zamu rayu…..zamu rayu da mahaifinmu!…….zamu rayu da wuya ko da dadi!…….zamu rayu da farinciki ko babu!…….mu din dolen junanmu ne yanzu!……bamu da kowa sai kawunanmu sai mahifinmu!” Ya qarashe maganar yana numfarfashi qirjinsa yana dagawa sama da qasa.

 

Cak ta tsaya,ta kuma waiwayo,idanunsu suka sarqafe guri guda. Ba sanin shekara daya ko biyu tayi masa……ba kuma sanin shanu tayi masa ba…….tasan dabi’unsa dake zubi da dabi’un mutumin daya dauki wani dogon xango xamani ko kuma qarni cikin sararin duniya…… dabi’un da sukan jefata duniyar mamaki a wasu lokutan….. Amma ko a shifcin qwaqwale bata taba tunanin fitar wadannan kalamai masu tsananin zafi daga harshensa ba. Kalaman da suka jeru da kyau!. Suka kuma isar da saqo tamkar dai ya jima yana ajiyarsu……kamar kuma rubuta masa su akayi ya dauki dogon lokaci yana gwajin yadda zai furtasu.

 

Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai. Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai ba.

 

Bashi da wani sauran FATA a kanta……amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo……fitar daya alaqantata da sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa.

Duniyata Complete Novel Document Txt

File Name  Duniyata … Hausa Novel Doc.
Title  Duniyata Complete Novel Document 
Author  Safiya Abdullahi Huguma
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    27/12/2024
File Size    45KB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No  09033181070
Download Duniyata Complete Novel Document By Safiya Huguma 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button