Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 1 Complete Novel

*ASM Bk 2

 

001*

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

Wani mugun bugu kirjin Fatuu ya fara yi tamkar ana mata luguden ta6are ganin abunda ke faruwa ta cikin glass d’in hannuwanta har wani kerma suke saboda tsabar rud’ewa da razana don abune wanda bata ta6a ganin Haisam d’in yayi ma wata Mace ba tunda take dashi, lokaci guda ta tambayi kanta wacece wannan? Kasa jurewa tayi ta bud’e Motar ta fita ta tsaya a jikin kopar tana k’are mata kallo can ta furta “AUNTY FANAN…..!” yadda ta furta da matukar razana, Ji tayi sam kafafunta suna niyyar kasa daukarta saboda kermar da suke yi ga wani irin bugu da kirjinta keyi mata saboda tsabar razana, tambayar dake ta faman kai kawo acikin zuciyarta itace, mike tsakanin Ya Handsome da Fanan da har yake mata hakan? Ko k’annanshi da suke uwa d’aya uba d’aya bata ga yana masu hakan ba sai ita da take Cousin d’inshi, to ko dae dama soyayya suke da ita ne? Damm! k’irjinta yay mata wani Mugun bugu yin wannan tunanin lokaci guda kuma taji fitsari ya d’aure mata mara yana niyyar zubo mata da sauri ta nufi gida ko kopar motar bata rufe ba ga wani duhu da take gani da kyar ta shiga gidan don har wani jiri jiri take gani tsabar rud’ewa da kuma fargaba, toilet ta shiga tayo fitsarin tana fitowa ta nufi d’akinta ko ta kan ta duba gwaggo bata bi ba tana shiga ta fad’a saman gadonta ta duk’unk’une wuri guda sai faman zare ido take……..

 

Nufar gaban Motar sukae hannunsu cikin na juna Fanan ta kalli wadda ke a mazaunin driver itama da gani hutu ya zauna mata duk da ba fara bace irin fatar jikinta za’a iya kiranta da chocolate fuskarta lumi tana da kyau ba laifi, da Murmushi Fanan tace “Khairat meet mah Babe” itama Murmushin take ta mik’o mashi hannu tace “Hi Haisam it’s nice meeting u” aikuwa da sauri Fanan ta ka6e hannun tace “he don’t do dat” dariya sosae khairat d’in tayi dama tsokanace kawae ba wani abu ba don tasan irin Mugun son da take ma Haisam dole ne tai kishinshi sosae, gaisawa sukai da haisam tace “so ga heartbeat d’inka na kawo maka sai a bani tukuici” fuskarshi da Murmushi yace ta fad’i abunda take so tace “bawani abu babba nike so ba just babynka zaka kawo man ta kwana gidanmu don nayi ta kwanan man but she refused” kallon Fanan d’in yay ta d’an yamutsa baki ta girgiza mashi kai alamar bazata je ba ta kwantar da kanta a shoulder d’inshi, khairat tace “so now da babe d’inki ke gefenki shine zaki gujeni ko, it’s owk zamu koma india inda zan rama ne” k’ayataccen murmushinta mai k’ara mata kyau sosae ta saki tace “kar ki damu Babe zai kawo ni in spending day” yar harara ta wurga mata tace bata so tana kokarin tashin Motar Fanan na d’aga mata hannu tace sai sunyi Magana daga haka taja ta tafi, wani kallo mai wuyar fassarawa yayi mata ta nok’e kai tana dariya har jerarrun hakoranta farare tass suka bayyana yace “Why baki sanar dani about your coming today?” cikin muryarta ta yan gayu tace “am so eager to see u babe shiyasa na baka huge suprise” ta k’arasa Maganar tana kashe mashi ido, hannu ya kai yaja dogon hancinta tayi yar k’ara yace su shiga ciki har zasu juya tace mashi Zarah fa Hajiya ta gaya mata sun fita outing tare sai lokacin ma ya tuna da Fatun na acikin Motar har ya juya ya hango kopar a bud’e ba tare daya kawo komae ba yace yana tunanin ta shiga gida ma, still hannunsu na cikin na juna suka nufi Motar tace ya zagaya d’ayan side d’in ita ta shiga side d’in driver tajasu suka idasa gidan bayan Officer CD ya bud’e masu gate, bayan sun shige ya rufe gate d’in ya dawo kan bencin daya tashi ya kalli d’ayan Officer yace “ita wanccan d’in wacece wai, ba itace naga dazun an kawo a jeep d’in nan ba?” yace mashi “eh itama jikar Hajiyarce baka ganin kalanta na zuwa”

“Itama ta wurin Hajiya Maryam d’ince kenan?” kai ya d’aga mashi alamar eh yace “Ma sha Allah amman duk tafi yan uwanta kyau gaskiya ni ban ta6a ganinta ba sai yau” Officer ya amsa mashi da eh ai bata cika zuwa ba kuma yanzu tana karatu a kasar waje ne,

 

tana ruke da hannun Haisam suka shiga falon Hajiya lokacin tana zaune kan kujera tana kallon tv, Fanan ce tayi sallama hajiya ta maido idonta kansu tana kallonsu da Murmushi suka nufi 2 seater suka zauna Hajiya tace “ina ta nemo ka” yana Murmushi yace “mun dawo ne”

“Ai ce man tayi in ta raka k’awarta bazata shigo ba har sai ta nemo ka wai,nace to Allah ya bada sa’a da yake ma akwae gidajen radio isassu maji cigiyarta in an tsinceta” d’an kallon fanan d’in yay still murmushi take kanta a saman kafad’arshi Hajiya taci gaba “sai kawae ganinta nayi kaman daga sama fa ni abun mamaki ma ya ban har saida na kira uwar tata nai mata korafin baza’a sanar mutum zai zo ba a shirya masa take ce man wai ita ta hana a sanar mana tana so ne ta bamu mamaki nace aikau ta bamu mamakin gashi tazo ma tak’i cin Abinci wai sai kazo zaka bata a baki nace ai sai taita jiranka tunda ita ba ranar da zata girma da hakan” shidae Murmushi kawae yake can ya mik’e ya d’agata ganin zasu nufi Dining area yasa tace mashi “but Babe u need to take bath ka dawo daga wani wuri nasan ka gaji” girgiza mata kai yay suna nufar dining table d’in yaja kujera ya zaunar da ita yace “eat first” yaja kujeran gabanta shima ya zauna k’in ci tayi wai sai dae ya bata a baki tayi missing hakan dole a bakin ya rink’a bata cike da kulawa, bata wani ci mai yawa ba tace ta koshi yace bai yarda ba tace ai ta d’an ci agidansu khairat tunda acan suka fara sauka sannan ya kyaleta, k’ara kama hannun juna sukai suka nufi cikin Falon zasu fita yace ma Hajiya zaije yay wanka tace to,ganin zasu fita tare tace ma Fanan bazata jirashi ya dawo ba ta mak’e mata kafad’a wai zata je ta za6ar mashi kaya ne, d’an ta6e baki Hajiyar tay tace adawo lafiya.

 

Jama’a ina Fatuu???

 

Tunda ta kwanta bata mik’e ba sai faman sak’e sak’e take aranta ga wata irin fargaba data mamayeta ,fitowa gwaggo tay daga dakinta idanunta suka sauka kan takalman Fatuu dake ajiye a bakin kopa da mamaki aranta tace wannan ai takalman da Fatuu ta fita dasu ne ta dawo ne, nufar d’akin tayi tana kwala mata kira tana jin muryar gwaggon ta rufe fuskarta da gyalenta dake yashe gefe yabar saman kanta, d’aga labulan tayi ta hangota a kwance har lokacin da mamaki akan fuskarta ta kira sunanta amman bata amsa ba har saida ta k’ara kiranta sannan ta amsa tace “yaushe kuka dawo ne?” daga yadda take tace “yanzu ba dad’ewa Kawu shi6ado na gaidaki sun bada sak’on dawon Fura da Nono ma akawo maki yana Mota” da kyar take Maganar hakan yasa gwaggon cewa “To lafiya kika wani dukunkune saman gado?” shiru ta d’anyi tana tunanin abunda zata ce mata can tace “banjin dad’i ne kaman zazza6i zai kamani nike ji shiyasa ma dana shigo ban maki Magana ba” shiru gwaggon tayi tana k’are mata kallo kafin tace “ina shi yayan naki yake?”

“Muna dawowa yaga sun yi bak’i ya tsaya wurinsu shine ni kuma na shigo” jinjina kai tayi tace “halan kinyi wasa da ruwa ne ko, nasan halinki sarai baki ganin ruwa ki k’yale” sai lokacin ta cire gyalen fuskarta ta bayyana ta kalli gwaggon tace “a’a wllh ai Ya Handsome bazai barni ba kawae dai banjin dadin jikinne”

 

“To Allah ya sawake ki tashi kici Abinci sai kisha Magani” tace “na k’oshi da Abincin bari dae insha maganin kaina ciwo yake man sosae” tana gama Maganar ta saukko daga gadon da k’yar ta tunkari kopa gwaggo ta saki labulan ta koma d’akinta ta d’aukko mata Maganin ta fito ta bata, ganin yamma tayi sosae yasa tace ta shiga Falo ta zauna Magriba ta kusa ba’ason kwanciya a irin wannan lokacin in tayi Salla sai ta kwanta tace mata to.

 

Bayan sun shiga Parlon Haisam sosae Fanan ta yaba da tsarin parlon, Haisam yace ta zauna bari yaje yay wanka ya juya zai nufi hanyar Bedroom kawae sai ji yay tace “should i come and help?” cak ya tsaya ya juyo yay mata wani kallo tasa dariya daga haka ya juya yana shiga Corridor ta d’an d’aga Murya tace “Soon i would be doing dat to u Babe” girgiza kai kawae yay ba tare daya juyo ba ya tura kopar Bedroom din ya shige, bayan wani lokaci ta mik’e ta nufi Bedroom d’in sanin yana toilet, bin d’akin tayi da kallo kafin ta nufi Closet d’inshi ta bud’e dan dudduba kayan tayi ta za6o mashi wanda zai sa ta d’aura su a gefen gado ta koma gaban Dressing mirror ta jawo drawer chest ta sama ta daukko kwalin agoguna data gani ta fiddo wadda zata hau da kayan ta daurata samansu kafin ta mayar da kwalin daga haka ta juya ta fito falo, bai dau wani dogon lokaci ba saboda Magrib tayi ya fito sanye da bathrobe yana ganin kayan data ajiye mashi yay wani kayataccen Murmushi, bai dau wani dogon lokaci ba ya gama shiryawa cikin kayan ya fita tana zaune kan L-shape idanunta akan tv tana kallo jin fitowarshi yasa ta mik’e ta nufeshi tana mashi Murmushi ya kama hannunta suka fita, saida ya rakata har bakin entrance d’in falon Hajiya sannan ya juya ya wuce Masallaci da aka fara kiran salla itama tana shiga d’akin Hajiya ta wuce don tace bata zama ko wane d’aki sai nan lokacin Hajiya ta kabbara salla ta wuce Toilet tayo wanka ta fito d’aure da farin towel, trolley d’in kayanta ta d’aura gefen gado ta bud’e ta fiddo riga da wando marasa nauyi rigar off shoulder ce blue sai wandon baki,bayan ta shirya ta d’aukko d’aya daga cikin hijjaban Hajiya dake cikin wardrobe tasa itama ta kabbara sallar, bayan an gama sallar isha gaba d’aya suna zaune a falon suna fira Fanan na manne jikin Haisam sai kace mage Hajiya tace “wai ni ina yar tafiya ne tunda kuka dawo banji d’uriyarta ba sun gaisa da Auntynta Fanan kuwa ma?” Fanan d’in tace “No ban ganta ba ta shiga gida ne bayan sun tsaya so bata zo wurina ba” Hajiya tace “aikuwa yakamata a aika masu da abubuwancen tunda kace d’aya ledar furar tasu ce ga kuma kifi shima a d’ibar mata Dije ta ga tsarabar Dam bari Saude ta je ta kai masu” tana rufe baki Fanan tace “ki kawo mu kai masu mana sai in gaisa da granny d’inta” Saude ta k’wala ma kira bayan ta fito ta gaisar dasu gaba d’aya Fanan na Murmushi ta amsa mata, umarnin ta d’ebo rabin kifin a leda sannan ta d’aukko leda d’aya ta fura da nono ta bata, ba 6ata lokaci ta kawo mata, mik’ewa Fanan tayi ta nufi Bedroom ta yafo d’an madaidaicin veil ta dawo hannunta ruk’e da wata yar babbar leda mai handle tace ma Haisam su je yace taje ita kad’ai cike da shagwa6a tace ita da bata san gidan ba Hajiya na dariya tace “ka rakata mana ita da ke bak’uwa” kafeta yay da idanu yana mata wani kallo ya d’an lumshe ido kafin ya yunkura ya mik’e yace suje ta d’auki ledojin ta bashi d’aya ya rike tace ma Hajiya sai sun dawo, lokacin da suka isa kopar gidan tsayawa yayi yace ta shiga zai jirata amman tak’i wai ita da ba’a sani ba bashi ne zai gabatar da ita ba yace to ta shiga tace zai shigo tace to, suna a Falo gwaggo na zaune kan kujera idonta akan tv Fatuu kuma na kwance kan darduma dake shimfide kan Carpet tun bayan data gama salla tai kwance wurin da k’yar gwaggo ta samu ta dan ci Abinci kad’an don duk jin bakinta take ba dad’i, da zazzak’ar muryarta ta kwad’a sallama har saida gaban Fatuu ya fad’i, amsawa gwaggo tayi ta tashi ta nufi hanyar fita ta tsaya bakin kopa tana kallonta har saida gabanta ya d’an fadi ganin wadda tay sallamar a d’arare tace “Maraba ki shigo” k’arasowa tayi gaban gwaggon ta aje ledojin hannunta tace,

“Ina tare da Ya Haisam zai shigo” ta fad’a da hausarta mai dad’i gwaggo na jin hakan da sauri tace “to to ba wani abu kice ya shigo” juyawa tayi da d’an d’aga murya tace “Babe Come in” da sallama ya shigo gwaggo ta idasa fitowa tana amsa mashi tay masu nuni da cikin Parlon tace su shiga,cire takalmanshi yay ya shiga Fanan ma ta daukki ledojin tabi bayanshi suka zauna tare saman 3 seater gwaggo ma ta zauna saman 1 seater, cikin cool voice d’inshi ya gaida gwaggon ta amsa tayi mashi ya gajiyar tafiya da godiyar ziyara Fanan ma ta gaidata da fara’a itama tana mata dariya ta amsa shiru ta d’an biyo baya sai Murmushi suke ma juna can gwaggon tace”ban wayeki ba ko bak’in da Fatuu tace an yi ne”

“Eh nine na zo daga Lagos” gwaggo tace “to yar wajen Hajiya Maryam ce kenan, to babbar ce ko k’aramar ni sunanku had’e man yake wllh” ta fad’a tana dariya Fanan d’in tace “Fanan ce babban”,

 

“Ah kice Amarya ce kenan” tana dariya tace “eh nine” tana rufe baki Haisam dake latsa waya ya d’an bugeta da hannunshi ta juya da sauri tace mashi “What?” shiru yay bai d’ago ba bai kuma ce mata komae ba gwaggo na dariya tace “ai kwanaki can muna fira da Hajiya take gaya man anyi baikon ku tuni amman sai kin gama karatu za’ai bikin, ko kin ma gama ne?”

“Yea but zan koma akwae wani exam da zamu yi shine final”,

“To ma sha Allah, Allah ya bada sa’a” tace Amin, kokarin mikewa gwaggon tayi tana Fad’in ta barsu ko ruwa Fanan din tace “ba wani abu granny yanzu munsha ruwa harda Abinci” gwaggo tace “amman dae yakamata kisha na zumunci ko” tana dariya tace to abata, bayan gwaggo ta kawo mata ruwan da lemu ta fara kokarin zuba mata a Cup tana ta barshi zata zuba tace a’a ai ita bak’uwa ce ba’a barta da aiki ba, bayan tasha ta aje cup tace ma Gwaggo ga kayan sis Zarah gwaggo na dariya tace tsarabar tafiya tace eh ta nuna nata tace wannan ita ta kawo mata gwaggon tayi mata godiya sosae tace Allah ya bar zumunci, kallon inda Fatuu ke kwance tayi tace “itane ke bacci” gwaggo tace “eh tun d’azun take ta faman kwanciya tunda ta dawo wai bata jin dad’in jikinta kuma kanta na yi mata ciwo” ta kai hannu tana kokarin tashin Fatun Fanan na ta kyaleta gobe sun gaisa, duk abunnan da suke kaf tana jinsu jikinta ya mutu murus a inda take ba kamar data ji Maganar aure dake tsakaninsu yanzu ta tabbatar da abunda zuciyarta ke zargi, kenan ita ba sonta yake ba? Wannan tambayar ita ta tsaya mata har wani tuk’arta take a k’irji kaman zata yi amai, tadata gwaggo ta shiga yi tana Fad’in bari dae ta tashi su gaisa bata tunanin baccin yayi wani nisa tana cikin tashin nata taji wani amai ya taho mata da sauri ta tashi tsaye hannunta dafe da bakinta tayi hanyar fita Falon da gudu,tana fita ta nufi hanyar Toilet saidae tana kaiwa saitin kitchen ya zubo mata da k’arfi ta durkushe anan tana kwara shi sai kace yan hanjin cikinta zasu fito, a rud’e Fanan da gwaggo suka bi bayanta suka nufeta da sauri Fanan ta duk’a ta dafata tana Fad’in “Sannu Sis Zarah” gwaggo ma sannun take ta mata duk Fanan tabi ta rud’e, da k’yar aman ya tsaya tasa hannu guda ta dafe gaban kanta tana nishi da karfi yayin da d’ayan hannun ke dafe da k’irjinta Fanan ta kalli gwaggo tace “granny pls ki bamu ruwa” da sauri tace to ta nufi kitchen ta d’aukko wata yar roba taje bakin fanfo ta taro ruwan, bayan ta kawo mata tallabo kan fatun tayi ta zuba mata a baki tace ta kuskure bakin kafin ta wanke mata fuskar, d’agata tayi ta nufi cikin parlon da ita gwaggo kuma ta fara gyara wurin, sauran ruwan roban data sha ta daukko ta bud’e murfin ta kafa mata abaki tace tasha, sosae tasha ruwan don kirjinta wani irin zafi yake mata,

 

“Sannu sis Zarah” kai ta d’aga mata tana kokarin kwanciya, bayan ta kwanta matsawa Fanan tayi gefenta ta zauna tana d’an tatta6a jikinta ta tambayeta ko cikinta ya lalace ne fatun ta girgiza mata kai alamar a’a, duk wannan abun Haisam na zaune yana kallonsu ko lokacin da take yin aman yana ji, dawowa gwaggo tayi ta zauna inda ta tashi Fanan ta tambayeta tasha Magani ne tace eh ta bata paracetamol d’azun da tace kanta na ciwon, ta6a jikinta ta sake yi jin da d’an zafi yasa ta kalli Haisam tace tana tunanin Malaria ce ke damunta abunda yafi ayi mata allura kawae, kai ya d’aga mata ya mik’e yace bari ya d’aukko mota suje su siyo tace ok, bayan ya d’aukko Motar horn yayi mata ta mik’e da sauri tace ma gwaggo bari suje su dawo tace to, komawa tayi kusa da Fatun bayan sun fita ta zauna tana mata sannu ita dae kai kawae take d’aga mata, bayan kaman minti 30 suka dawo Fanan ce kawae ta shigo shi Haisam yana waje cikin Mota duk ciwon da Fatun keyi ya dameshi ganin lafiya lau suka dawo da ita amman har yayi tsanani haka, Artemether da paracetamol injection suka siyo, had’a allurar ta shiga yi bayan ta gama tayi mata har saida gwaggon tayi mamakin yadda ta tsaya tayi mata allurar don ita in zata yi mata wani lokacin sai tayi fama da ita da can ma da bata girma ba haka wani lokacin sai tasa Amadu ya ruke mata ita, bayan ta gama ta tambayi inda dustbin yake gwaggo ta mik’e ta amsa taje ta yado su ta dawo Fanan tace ma gwaggo yakamata taje d’aki ta shiga Net saboda sauro tace to, mik’ar da ita tayi suka nufi hanyar fita gwaggo na biye dasu ta tambayi ina d’akin da zata kaita gwaggo ta nuna mata dakinta suna shiga ta nufi gado da ita ta taimaka mata ta kwanta sai faman sannu take ce mata kai kawae take d’aga mata ita kanta Fatun bata san mi take ji game da Fanan d’in ba ita kawae abunda ya dameta shine Ya Handsome bai sonta ba zai Aureta ba, a hankali kwalla suka fara ziraro mata daga kwancen ta juya masu baya yadda bazasu ga Fuskar tata ba,

“Granny ni zan tafi Ya Haisam na jirana gobe in sha Allah zanzo in yi mata second dose” godiya sosae gwaggo ta shiga yi mata tana cewa Allah yasaka da Alkhairi ya bar zumunci ta amsa da Amin juyawa tayi ta dafa jikin Fatuu tace “Sis Zarah Allah baki lpy kinji” kai ta d’aga mata kawae ta juya ta tafi gwaggo tayi mata rakiya har zaure saida ta lek’a ta k’ara yi ma Haisam godiya kafin ta komo daki wurin Fatuu, a gefen gadon ta zauna tana kallonta yayin da take ta sak’e sak’e aranta game da silar ciwon Fatun tsoronta kar ace abunda take tunani ne sanin inda suka je ciwon na iya tasar mata, yin wannan tunanin yasa da sauri ta girgiza kai a fili tace “in sha Allahu bama shi bane” dafata tayi tace mata sannu ta d’aga mata kai ta tambayeta ko tana son wani abu ta girgiza mata kai alamar a’a tace “to tashi ki rage kayan jikinki bari in je in d’aukko maki wanda zaki canza” bayan taje d’akinta ta d’aukko mata kayan bacci da taimakon gwaggon ta tashi ta canja kafin ta koma ta kwanta gwaggo ta lullube mata rabin jikinta tasa mata Net.

 

Bayan sunyi parking Motar a parking space suka fito sukai ma juna irin rukon nan na turawa wato a sak’ala hannu suka nufi part d’in Hajiya, lokacin da suka shiga ba kowa a falon hakan yasa suka wuce bedroom dinta lokacin har ta kwanta amman bata yi bacci ba wutar d’akin ma a kunne take da alama jiransu take, jin motsin shigowarsu yasa ta d’ago ta kallesu suka nufeta suna Murmushi suka zauna a bakin gadon,

“Ai nayi zaton Zarah ta rik’e ki acan zaki kwana don nasan dole zatayi farinciki da zuwanki” da sauri Fanan ta girgiza mata kai da yar damuwa tace “Sis zarah ba lpy dat’s why we stayed a bit long” yunkurawa Hajiya tayi ta tashi zaune da mamaki kan Fuskarta tace “Ba lpy kuma miya sameta” fad’i mata abunda ya faru Fanan din tayi harda uban aman da tayi Hajiya tasa salati ta kalli Haisam dake saurarensu tace “dama bata lpy kuka dawo” kai ya girgiza “No lafiyanta lou wai bayan ta shiga gida tace ma grandma d’inta tana jinta abnormal and kanta na mata ciwo sosae” jinjina kai Hajiya tayi da yar damuwa akan fuskarta tace “tohhh, Allah ya kyauta yasa ba mutanenta bane kuwa tunda anje wurin ruwa” cikin rashin fahimta duk suka kalleta Fanan ta tambayeta suwaye mutanenta,

“Jinn nike nufi” waro ida Fanan tayi a rud’e tace “Ajanu!” yadda tayi Maganar har saida Hajiya ta d’anyi dariya ta jinjina mata kai alamar eh,

“Dama tana dasu?” Haisam daya kasa hakuri ya tambaya, Hajiyar tace “Eh mana amman basu kada ita yanzu saidai su sata ciwo, tama dad’e gaskiya bata yi ciwon da take irin nasu ba” jinjina kai yay taci gaba da cewa “ai na Mahaifiyarta ne suka komo kan Fateemar amman basu cutar da ita gaskiya sai rashin ji da suka saka mata” wani d’an guntun Murmushi haisam d’in yay ya furta “the whole things make sense now”,

“but su dama basu son aje wurin ruwa?” Fanan da duk alamun tsoro ya bayyanar mata ta tambaya dariya hajiya tasa tace “ai kinsan su ko ina akwae su ba iya wurin ruwan ba saidae akwae inda zaki ga sunfi zama kaman toilet to wurin ruwan ma matattararsu ce, kai bamma tunanin su ne gaskiya k’ilan dai ta de6o sanyi ne kawae shine ya tado mata zazzabin” jinjina kai Fanan tayi tace Allah dai ya bata lafiya hajiya ta amsa mata da Amin, mik’ewa Haisam yay yace zaije ya kwanta Hajiya tace “Allah ya bamu Alkhairi” kokarin mikewa Fanan ta fara yi tace bari ta rakashi yace tay zamanta tace ko bakin kopa ne, suna fitowa yace ta koma sai kawae ta jingina bayanta da bango tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar kauna hannu ya kai ya d’an shafi cheek d’inta da wata irin Murya ya furta mata “I luv u Sweetheart” hannu tasa ta dafa hannun nashi tana Murmushi tace “dat’s my breath babe” yar dariya yayi ya fara kokarin wucewa ta kamo hannunshi ta baya ya juyo da narkakkun idanu tace “Gud nyt nd Dream of me” lumshe ido yay kafin yace “Always” d’ago hannun tay tayi mashi kiss a bayan hannun kafin ta saki ya tafi, saida ya kai bakin kopar fita ya juya ya kalleta yay mata alamar ta shiga cikin d’aki da kanshi,blowing kiss tai mashi kafin ta d’aga hannu tay mashi bye bye ta juya ta shige……….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button