Halysaah Page 130 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 130…Tun da Mami ta bar parlon Khaleesat ke zaune kan kujera lokaci lokaci take satan kallon Ajay da yaki kallon inda take, daga karshe tayi breaking silence din parlon a hankali tace “Dama fa warmer din da Mami ta baka zogale jiya naje in maida mata….” Mikewa yayi ya dakatar da ita without looking at her fuska daure yace “Ban tambaye ki ba” Daga haka yayi shigewarsa daki, ita dai ta bi sa da kallo, lokaci daya jikinta yayi sanyi, bayan kusan minti ashirin ta mike tana tafiya a hankali ta nufi cikin dakin, zaune ta samesa gefen gado ya dafe kansa, ta sauke idonta ta karasa cikin dakin ta tsaya kusa da gadon cikin sanyin murya tace “In kawo maka breakfast din nan?” Bai tanka ta ba, tana ta tsaye for almost 5 minutes, ganin yaki cewa komai ta juya walking slowly ta fita daga dakin, fita tayi daga parlonsa ta koma can babban parlon dake part din, ta karasa ta kulle kofar parlon don in aka zo wucewa ta corridor din dole sai an kallo cikin babban parlon in dai kofar a bude yake, ta tafi kan kujera ta zauna ta fara goge hawayen da ya taru idonta, sai yanxu ne ma ta fara jin zafin abinda Hadiyah tayi mata, hade kai tayi da jikin kujeran tana shesshekan kuka a hankali… Wajen karfe biyu sai ga Mami ta bude kofa ta shigo parlon Khaleesat dake zaune kan darduma tun da tayi sallah ta gaishe da ita cikin sanyin murya, Mami ta zauna kan kujera ta amsa gaisuwarta, bayan few seconds cikin karfin hali Mami tace “Halysaah ki gaya min gaskiya, kar ki boye min komai, kin tabbata duk abinda kika gaya min daxu da safe haka ya faru ko kin boye min wani abu?” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “Wallahi abinda ya faru kenan Mami ban maki karya ba” Mami bata sake cewa komai ba, can ta mike ta fita don akwai abinda take son dubawa ne kar kuma ta duba taga ba haka ba don hakan zai kara destabilizing dinta. Karfe hudu saura na yamma Ummi ta diro masarauta, direct bangaren Aunty ta fara nufa, nan ta tarar da ita da su Gimbiya Firdausi da Hajiya A’isha sai Kilishi, nan Hajiya A’isha da Kilishi suka rako Ummi har bangaren Mami, Mami na can bedroom dinta bakin ciki yasa ko zaman parlor ta kasa yau, ko breakfast bata yi ba ga lunch shi ma bata ji zata iya ci ba, tun da Jay ya bar part din Ajay da safe har zuwa yanxu bata gansa ba don bai zo part din nata ba, Ummi na tsaye tsakiyar parlon Mami ta dinga rafka sallama, Hajiya A’isha da Kilishi duk suka nemi kujera suka zauna, Mami na fitowa ta dinga kallonsu daya bayan daya a parlon, Ummi na huci tace “Wallahi kin ban mamaki Fulani, ban zaci haka daga gare ki ba, har wai zaki goyi bayan wata er iskar bare akan Hadiyah?? Me Hadiyah ta maki kika tsaneta haka ne? Kawai don tana auren ɗan ki kuma kina baƙin cikin soyayya da kulawan da yake nuna mata tunda ke ba haka kika so ba shi yasa kike tsangwamarta kike kyararta a gidan nan? ko dai kin mance matsayin Hadiyah ne a gidan nan?” Da mamaki Mami tace “Rashin kunya kika taso tun daga Lagos ki min Maimuna? Ni kike gaya ma maganganun nan?” Hajiya A’isha tace “A’a Fulani mu kan mu mun yi mamakin ki, kuma duk jikinmu yayi sanyi don bamu zaci haka daga gare ki ba, ta yaya kiri kiri zaki hau Hadiyah da zagi akan wata er iska can da bamu san ma cikakken asalinta ba? Meye hadinmu da ita da zaki goyi bayanta akan Hadiyah warce take jininmu? Har kina kallon Junaid ya ɗaga hannu ya gaggaura mata mari ki ki cewa komai, instead ki ja matsiyaciyar yarinyar ki fita da ita ki bar Hadiyah? To in kin mance wacece Hadiyah bari mu tuna maki Fulani, da uwar Hadiyah da Mahaifin Jawwad Allah yayi masa rahama, uwa daya uba daya suke” Cike da rashin mutunci Ummi tace “Ku kyaleta ai amanar marigayi Yaya Ahmad ta ci ba namu ba, dama tun ba yau ba nasan babu alkhairi a zuciyarta, to in haka ne me yasa bata saka ɗan nata a gaba tana kallo ba tunda bata son yayi aure ya nuna ma matarsa kulawa, ko kunya babu ki dinga kishi da matar ɗan ki, matar ma jinin marigayin mijin ki” A hankali Mami tace “Maimuna ni kike ma rashin kirki yau?” Cikin i don’t care attitude Ummi tace “koma yaya zaki sa shi ni bai shafeni ba wallahi, akan ‘ya ta babu abinda bazan yi ba sai dai ayi hakuri, kuma babu shegen da zai taɓa Hadiyah ya kwana lafiya a gidan nan, zan zuba ido in ga hukuncin da sarki zai dauka wallahi sai dai ayi abun kunya a masarautar nan in dai ba a bi ma ‘ya ta hakkin marin da aka yi mata ba” Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mami ta bi ta da kallo baki bude, su Hajiya A’isha duk suka mike suka bi bayan Ummi, bayan sun fita Kilishi tace “Ai baki san wani abu ba Maimuna kafin sarki ya dau wani mataki ya kamata Hadiyah ta rama marukan da ɗan iskan nan Junaid yayi mata akan matsiyaciyar yarinyar, bayan ta rama marin akan yarinyar sai kuma a jira hukuncin da sarki zai dauka….” Hajiya A’isha tace “Kwarai kuwa, gwara ta fara rama marin kan shegiyar yarinyar kafin ma a zauna da Mai martaba” Khaleesat na zaune babban parlor ita kadai abun duniya ya taru ya dameta, ko Lunch da Yakumbo suka kawo daxu suka ajiye a babban parlon bata ko bude ba balle ta san me aka kawo, bude kofar parlon aka yi ta daga kai duk tunaninta ko Mami ce ta sake dawowa, Ummi ta shigo fuska murtuke tana rike da hannun Hadiyah dake biye da ita, ga Hajiya A’isha da Kilishi na biye da su a baya su ma, ai ko gama shigowa parlon basu yi ba Khaleesat ta mike kan kace me sai gata a parlon Ajay a tsorace, ita kanta bata san ko gudu tayi ba ta dai ganta parlon jiki na rawa, fitowar Ajay daga bedroom dinsa kenan zai je Masallaci, da gudu ta tafi bayansa zuciyarta na bugawa ta fara masa kuka, sai ga su Ummi sun shigo parlon fuskarsu duk babu alamar rahama, Ummi ta sake hannun Hadiyah cikin tsawa tace “Ta fi ki rama marin da yayi maki akan ta” Hadiyah ta kalli Ajay dake kallonta, Kilishi ta mata wani tsawan tace “Baza ki tafi kiyi abinda aka sa ki ba, ko ubanki ne shi Junaid din da kike kallonsa?” Ita dai Hadiyah ta kasa karasawa ganin kallon da Ajay yake mata, Juyawa yayi ya kama hannun Khaleesat ya shige Bedroom dinsa ya bar su wajen a tsaye yayi banging kofar sa. Ajay bai fita zuwa masallacin da yayi niyya ba yayi sallan a dakinsa, ita dai Khaleesat na zaune gefen gado sai goge hawayen da yaki tsaya mata take tana shesshekan kuka, sosai ta kara tsorata da gidan, ji take kamar ta gudu ta bar gidan, banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, bayan Ajay ya idar da sallah ya mike ya nufi kofa don ma ya dena jin kukanta dake kara bata masa rai, tana ganin haka ta tashi da sauri ta nufesa muryarta na rawa tace “Don Allah kar ka tafi ka bar ni wallahi tsoro nake ji” Ya mata wani kallo yace “Na aike ki kije ki dauko ma kanki magana?” Ta fashe da kuka moving closer to him tana girgiza masa kai tace “Wallahi kawai naje kai ma Mami cooler ne sai in gaisheta daga nan….” Cikin tsawa yace “Did you know the Mami from anywhere??” Girgiza masa kai tayi tana goge hawayen dake zuba idonta ta rasa abinda zata ce, ya kara daure fuska yace “You went to her part with the intention of meeting with Jawwad, you went there purposely because of him, probably ma shi yace ki je can don haka bear the consequences now kar in gaggaura maki mari….” Kasa cewa komai Khaleesat tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, bata taɓa ganinsa cikin yanayin nan ba, ya bude kofar yayi ficewarsa daga dakin kamar zai tashi sama. Har kusan Magrib Khaleesat na zaune kasan carpet a dakinsa, tun da ya fita ko digon hawaye bai kara zuba idonta ba saboda abubuwan da ya gaya mata, she was just sitting like a statue in the room tana jin zuciyarta babu dadi kwata kwata, daga karshe jin ana kiraye kirayen magrib ta mike a hankali walking slowly ta fita daga dakin, bata gansa parlornsa ba ta bude kofa ta fita, daya daga dakunan dake part din ta bude kofa ta shiga ta kulle da makulli….. Ajay na zaune parlon Mai martaba kansa a kasa, Jay ma na zaune opposite to him sai dai babu wanda ya kalli wani cikinsu, Mukhtar was also in the parlor kusa da Jay, kusan gaba daya familyn masarautan ne zaune a parlon har da Gimbiya Firdausi da Hajiya Habibah, duk ana sauraron jawabin Sarki wanda ko minti biyar bai yi da fara magana ba cikin nutsuwa, duk an kagu yaje main point din da yasa duk aka tara su a parlon, Ummi dai fuskarta a daure yake ta ma fi kowa ƙaguwan sarki ya gama jawabinsa taji hukuncin da zai yanke akan marin Hadiyah da Ajay yayi, sannan kuma su ji makomar Khaleesat a gidan kamar yanda su Hajiya A’isha su ma duk suka baza kunne su ji hukuncin da sarki zai dauka akan abinda aka ce Khaleesat tayi, babu wanda ya wani damu da reputation din Jay a cikinsu su dai kawai a shafa ma Khaleesat baƙin penti da bazai taɓa gogewa ba yanda zamanta zai zo karshe a masarautan don cewa suka dinga yi abomination ta tafka, gashi ba karamin tsari Aunty tayi ma Mai martaba ba akan abinda ya faru and she made it look so bad wajen narrating ma Sarki, bayaninta yayi muni sosai, wanda har shi ma Mai martaba sai da jikinsa yayi sanyi daga sanda ya samu labarin nan ya dawo gashi nan gashi nan ne dai kawai amma bai nuna hakan a fuska ba cause he was very calm, but ko abinci ya kasa ci, Hadiyah dai na zaune kusa da uwarta tana jiran sarki ya tambayeta abinda ya faru dama su Hajiya A’isha sun kara yi mata tsarin abinda zata fada don zancen ya kara girgiza sarki, tun da abun ya faru da safe take bangaren Aunty sun ki barin ko Jay ya ganta don kar ma ya canza mata ra’ayin fadan abinda suka kitsa mata, Jay dai sai kallonta yake a parlon ita kuwa taki yarda ta kallesa cause she is ready to say all what she was instructed to say that will paint Khaleesat black, yayi mata kira yafi ashirin ranan da text messages amma duk su Kilishi suka hanata picking kiran balle tayi replying messages dinsa kawai jiran lkcn da za a zauna da sarki suke, Mami dai na zaune parlon kanta a kasa duk da sai da Mai martaba ya aika ayi kiranta sannan ta taho wajen zaman, Mai martaba na kallonta calmly yace “Fulani….” Mami bata ɗaga kai ba tace “Allah ya taimake ka” Mai martaba ya nisa yace “Me zaki ce game da wannan lamari da ya faru yau? Ina nufin menene ya faru yau a sashin ki Fulani?” Mami ta ɗan yi shiru, after some seconds tace “Ranka shi dade ni babban parlor na akwai Cctv Camera tun bayan abinda ya faru shekarun baya da aka kwashe min gwala-gwalai na” Walid dake parlon shima ya ɗan kalli Mami sai kuma ya dauke kai, Mami ta ci gaba da maganarta cikin nutsuwa tace “Ina jin babu wanda yasan da Cctv din sai yanxu da nake magana, don haka ina ga wannan kadai ya isa bada labarin abinda ya faru ba sai na tofa komai ba, don na sa Mukhtar ya taho da Cctv DVR ayi connecting da TV kowa ya gane ma idonsa, a nan kuma zaka san ba komai suka ma yarinyar nan ba illa kazafi da sharri wanda su masu zuga Hadiyar suna da yaran nan mata kuma basu san abinda gobe zai haifar ba, ba komai ya kawo yarinyar parlor na ba sai alkhairi amma suka mayar sharri” Tun da Mami ta fara magana Ummi da su Hajiya A’isha da Aunty suka daga kai suna kallonta babu ko kiftawa, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi shiru na wani lokaci don he felt relieved immediately, can yace “Amma ke kin kalli clip din Fulani?” Mami tace “Kwarai na kalla a laptop tare da Mukhtar ranka shi dade” Mai martaba ya kalli Mukhtar yayi instructing dinsa yayi playing dinsa a TV, ba komai yasa Sarki yace a kunna ma kowa clip din ba kawai yasan hakan ne kadai zai kashe zancen nan, sanin halinsu Kilishi yasan tsaf za su ce gyara zancen Mami tayi saboda reputation din ɗan ta, Mukhtar ya mike da hanzari yayi yanda Sarki yace yayi, aka jona Cctv din da TV, yana fara playing Hadiyah ta sunkuyar da kanta, Ajay dai ya ɗaga kai yana kallon TV din kamar yafi kowa son ganin clip din, kowa a parlon yaga exactly abinda ya faru a parlon Mami tun daga shigowar Jay da Khaleesat da ya tarar zaune a parlon, bayan yayi hanyar dakin Maminsa ya dawo ya zauna parlon and they were not close to each other ko kadan, yana kan kujera tana zaune kasa kuma ba kallonsa ma take ba, bai fi sau daya zuwa biyu ta daga kai ta kalli inda yake ba, sai kuma wayarsa da ya mika mata daga karshe sai shigowar Hadiyah parlon da yanda ta taho ta cakume Khaleesat sai ga yan gidan duk sun shigo parlon su ma, amma Aunty har da ce ma sarki rungume da juna Hadiyah ta kama su, Mai martaba ya ɗaga kai yana kallon Aunty da taki kallonsa, kowa na parlon sai cika yake yana batsewa irin ba haka aka so, daga karshe Mukhtar ya kashe TV din, shiru ne ya biyo baya na kusan minti uku a parlon, Sarki ya kalli Hadiyah da taki dago kanta yace “Ashe ke mutuniyar banza ce Hadiyah? Me yarinyar nan ta maki kike kokarin tarnishing Image dinta a gidan nan? Not only her, har reputation din mijin ki da na gidan nan as a whole kika so kiyi tarnishing, kin san ma’anar wannan abu da kika yi kuwa? To ina me umartar ki da ki tafi har bangaren matar Junaid ki bata hakuri akan abinda kika yi mata, umarni kuma nake baki, and I am highly disappointed in you” Duk aka daga kai ana kallon Sarki jin yace taje ta ba Khaleesat hakuri, Hadiyah dai taki ɗago kanta hawaye cike idonta, Ummi sai wani kumbura take a inda take zaune kamar zata fashe, Cikin kakkausan murya Mai martaba yace “Sannan daga wannan very moment din na kashe wannan maganar a gidan nan, bana son sake jin wani ya tadasa har abada, idan kuwa ba haka ba zan dau mummunan mataki akan koma waye….” Babu wanda ya iya daga kai balle yace wani abu a parlon, bayan minti daya kilishi ta kwantar da murya tace “Ina son er wata magana idan an bani dama ranka shi dade” Sarki yace “Go ahead” Cike da takaici tace “Allah ya taimake ka, sau biyu Junaid ya ɗaga hannu ya mari Hadiyah fa tana matar wan sa ko kunyan wan nasa bai ji ba, gashi nan har sai da fuskarta ya kumbura akan marin da yayi mata, yanxu haka cewa take hakoranta na ciwo sai an je wajen Dentist, shi mijinta bai ɗaga hannu ya mareta ba sai shi saboda yafi kowa son matarsa?? Yanxu da Jawwad bai kai zuciyarsa nesa ba ai batattciya za ayi a masarautar nan tunda shi ma yana son matarsa” Mai martaba ya juya ya kalli Ajay da ya sauke kansa kasa yace “Ahmad” Still Ajay kansa na kasa yace “Ur highness” Strictly Sarki yace “This should be the first and last time da zaka ɗaga hannu ka taɓa ko wani yaro a gidan nan da sunan duka, ina me tabbatar maka idan hakan ya sake faruwa zaka ga ɓacin raina Ahmad, a baya na sha maka warning akan hakan to wannan shi ne na karshe da zan maka” Mami ta daga kai tana kallon Mai martaba tace “Ranka shi dade ka mance matsayin Hadiyah ne a wajensa? Laifi ne don ya hukunta kanwarsa?” Tun shigowar Jay parlon sai a sannan ya daga kai ya kalli Maminsa jin abinda tace, Ummi ma wani tsinannen kallo take ma Mami haka Kilishi, Mai martaba yace “Babu wannan zancen Fulani, Hadiyah matar aure ce yanxu don haka ba shi da right din daga hannu ya mareta, ba ma ita ba idan ya kuskura ya sake daga hannu akan ko wani yaro cikin gidan nan zan dau mataki akan hakan tunda aikinsa kenan shi, na sallami kowa…” Mikewa Sarki yayi ya bar parlon ya shiga second parlor dinsa, Mami ta mike ta fita duk da tana da maganganun da take son yi da Sarki amma ta bari sai gobe da sassafe zata zo ta samesa. Ajay ya mike shi ma ya fice daga parlon su Kilishi da Ummi suka bi sa da wani irin kallo, yana komawa part dinsa yayi using makulli ya bude kofar babban parlon don sai da ya kulle before leaving, bai ga Khaleesat a parlonsa ba har ma a bedroom, and he began wondering inda ta tafi duk da yasan ya kulle kofar part din kafin ya fita, can ya fita ya bude all the 3 rooms in the part, yaji daya a kulle ya gane she is inside kenan, murda kofar yayi ya kwankwasa yace “Ke, bude kofar nan” Duk da Khaleesat na jin sa taki cewa komai tana kwance kan gado, daki ne babba that is well furnished babu abinda babu a ciki, sai bayan da ta shigo dakin taga ashe duk akwatunan ta ma suna dakin, sau uku yana knocking kofar taki tankawa, ya juya kawai ya tafi kitchen din dake part din ya ciro fruits a cikin fridge ya wanke su ya zuba a bowl ya koma parlornsa, yana ta zaune har lokacin isha’i yayi, yayi sallah sannan yayi wanka ya saka pajamas dinsa ya kunna TV a bedroom dinsa yana kallon football amma ya kasa concentrating duk sonsa da Ball, kawai ya kashe TVn wajen karfe goma da rabi ya kwanta kan gadonsa ya lumshe ido, ya dade abu bai dakesa ba kamar yau don ko abinci bai iya yaci ba yau, rabonsa da shiga irin wannan damuwan kilan tun bayan da Mai martaba ya sanar masa auren da ya daura masa da Khaleesat sai kuma incident din daxu da safe, but he felt relieved bayan clarification din da Mami tayi with evidence, mikewa yayi ya fita xuwa kitchen ya duba dinner din da aka kawo masu yaga Khaleesat bata taɓa komai ba a ciki, da rana ma yana lura bata ci abinci ba, ya juya ya fita :,daga kitchen din ya tafi kofar dakin da take ciki yayi knocking calmly yace “Jeeddah, open the door,…”
