Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 5 Complete Hausa Novel

    WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

 ~Unique Barakancy~

        FIVE📍

          Fatima Zainab tashi tayi da niyar dauro alwala kasancewar mutum me Ibada,a duk halin da take ciki bata yarda sallar farillan nan ya wuceta,kuma duk girman uzurinta barinshi take tayi sallah ta dawo…. Fitowa tayi daga toilet din parlourn duk suka bita da kallo…… Tsaki taja kamar batasan magana tace “sai nace abani abun sallah sannan za a bani in gaida ubangiji na?”……. Da sauri imaan da tafi kusa da ita tashiga daya daga cikin bedroom din dake parlourn,ta dauko abun sallah ta shimfida mata sannan “Bismillah anty”….. Bata kulata ba ta tashi ta tada sallah……… 

      Shigowar Dr Deen da alhaji ne ya razana mama,hankalinta ya tashi,budar bakinta keda wuya sai tace “Alhaji Ina Doctor din,ko be karaso bane”….. Hade rai yayi yace “bagashi a kusa dani kina gani ba”….. A kidime ta sake cewa “Toh ai ba wannan bane family Doctor dinmu ba”….. Ko kallonta alhaji be sakeyi ba,ya dago yana kallon deen da gabadaya ya zama absent minded…… Shiko Deen tinda ya shigo yakebin occupants din parlourn da kallo yana tinanin ta ina ze hangota,abinda yakeji a cikin ransa na kara basa assurance din cewa lallai tana parlourn nan,amma abin mamaki be ganta,kalle kalle ya cigaba dayi saiya hango wata a edge din parlourn ta juya baya tana sallah,hakanan kawai ya samu kanshi da bin bayanta da kallo ko kifta ido bayayi,shidai burinshi kawai ta jiyo yaga wacece ita?,ko ita din yake nema?….. Alhaji ne ya katseshi da cewa “son karaso mana,tinanin me kakeyi haka at this young age”……. Sai kuma yace”wai ina Fatima Zainab ne? Tinda nashigo banganta ba”……. Momma ta bashi amsa da”gata chan tana sallah”….. Murmushi yayi yace “Daughter case,ta dauko rigima kuma ko a jikinta ta barmu ta tafi tana gaida ubangijinta”…… 

Sauke Littafin : Dr. Bobby Complete Novel Document

“Son, sample din abincin nan nakeso ka dauka,ka duba if there’s any harmful abu a ciki pls”…… Murmushi Deen daya kara shiga rudanin jin wani suna waishi ‘Fatima Zainab’ yayi,toh tayaya zaace mutum yanada sunaye guda biyu masu asali?Kuma tabbas wacce ke sallahn nan ce me sunan tinda yaji ance tana sallah,sai hakan ya kara mishi curiosity akan wanda yake ciki,yaji lallai yana san ganin me sallahn nan,amma saiya daure ya dauki sample din kamar yanda alhaji ya umarce shi,sannan ya tafi domin tsayawa ta idar ba huruminshi bane…..…….. 

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Hausa Novel

      Fitarsa keda wuya ta sallame,ta karaso inda daddy yake tana cewa “Toh shi wannan wani irin shashashan Doctor ne,harya gama binciken?”……. Girgiza kai daddy yayi yace “Kai daughter haryanzu wannan gajan hakurin naki baki dena ba?,toh ya dauki sample din abincin ya tafi dashi lab domin ya bincika,sai mujira result din ko” Tabe baki tayi batace komai ba tasamu guri ta zauna…… Suko gabadaya mutanen parlourn sunyi jigum kamar shukar da akayi ruwa ya dauke kam,kada ma mama taji labari dan tafita hayyacinta kamar ace kyat ta zura da gudu,sai sake sake takeyi a ranta shikuma wannan doctor daga ina alhaji ya samoshi?. Karfa yazo ya tona mata asiri a banza,ya bata mata nomar data dade tanayi, gaskiya dole ma tayi wani abun…… Tashi tayi da sauri,ta manta cewa da mutane a parlourn saboda tsabar rudewar da tayi,ta rasa ina zata saka ranta taji dadi…. Daka mata tsawa daddy yayi yace “koma ki zauna” ganin yanda duk ta rikice….. Da sauri ta koma ta zauna tana rarraba ido kamar wata tababbiya…….. Kallon mama Fatima Zainab tayi tace “ko ni ko ke a gidannan yau” sannan ta kalli daddy tace “nifa yunwa nakeji, zanje part dina in nemi abinda zansa a cikina,dan ban yarda da mutanen gidannan ba”….. Gyada kai daddy yayi yana mata addu’ar shiriya aranshi……. Batako sauriri me zece ba ta ficewarta..….. 

Karanta Littafin : Abban Sojoji Hausa Novel

       Tinda Deen ya tafi yake Allah Allah ya dawo yaga me sallarnan,shiyasa yana zuwa nan da nan ya dibi portion na sample din yasa a microscope sannan yayi detecting duk wani abu da yake cikin sample din,ya fitar da result,ya fita daga asibitin da sauri,abokinshi safwan ya bishi da kallo ganin yanda ya mayar da hankali akan aikin dayazo dashi,a iya saninshi dashi yasan aikin lab ma saidai ya bayar ayi badai yayi da kanshi ba……. Shiko Deen bema san yanayi ba,abunda yake gabanshi ma ya ishe shi……… 

Da sallama ya shigo parlourn yana dube dube kamar me neman wani abu,burinshi kawai yaga me sallah,sai kuma yaga wayam ba kowa a wajan ga kuma abun sallahn na nan…. Alhaji ne ya hangoshi yace “karaso mana son, harka dawo?” Daga kai yayi yace “Eh dad” Yana mikoma alhaji result din….. Sai alhaji ya umarceshi daya bude ya sanar dashi menene result din…. Numfasawa yayi yace “Anyi injecting food din da botulinum toxin injection”… Kallonshi yayi yace “Expand Doctor”….. Dan shiru yayi sannan yace “Shi ake cewa ‘miracle poison’,wanda idan mutum yaci abincin da aka sakashi a ciki,ko five minutes bazai kara a duniya ba,it is so deadly”……  Jin hakan yasa gabadaya wa’yanda ke parlourn suka zaro ido suna kallon Doctor,shiko daddy dafe zuciyarsa yayi yace “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” sannan ya danne zuciyarsa yace”Thank you son,you can go”…… Ai ji yayi kamar ya cewa alhaji ze zauna,saidai bazai iyaba,shi in an tambayeshi me yake damunsa yanzu ma bayace gashi ba……. Sallama yayiwa alhaji ya fita yana tafiya kamar wanda beda laka………. 

Fitowarta kenan daga part dinta bayan tagama bawa cikinta hakkinsa,taga anja mota an nufi gate,bin motar tayi da kallo tanajin wani iri a ranta,chan kuma saita danyi tsaki ta nufi parlourn tana dan wani sake sake a rai……….. 

      Tana shigowa kowa ya zuba mata ido,banda daddy da yaketa girgiza kai yanata salati,gabadaya yaji ya zama speechless dukda tarin abubuwan dake ranshi…. Karasa inda daddy yake tayi,sai tace “wai haryanzu baa kawo result din ba”….. Kasa bata amsa daddy yayi saboda besan ta ina ze fara ba,tabbas saiya hukunta mama amma kuma zai so ace Fatima Zainab baza taji wannan magana ba…….. Itako ganin ya mata shiru yasa ta dakawa ameera tsawa tace “ke dan uwarki meyafaru akayi shiru haka kamar gidan mutuwa”………. “Ehm eh daman mmm mama ce,mama ta saka poison a abincin” Ameera ta fada a kidime,harji take kamar ta saki fitsari tsabar yanda tsawar ta daketa,gashi dai tsawar ba wani me sauti bane amma har cikin kwakwalwarta tajita………. Tsare ameera ta cigaba dayi da kallo alamun tana bukatar karin bayani,ameera ko bata san lokacin data zayyano mata duka abunda Doctor yace ba…… Sai a lokacin daddy ya fusata yace “kin bani mamaki hafsah,ashe har zaki iya kisan kai? Ashe da muguwa nake zaune tsawon wannan lokacin bansani ba?,meta tsare miki a duniyarnan? Kinsan ko WACECE ITA?,kinsan gangancin da kike neman tafkawa kuwa?,bazan taba yafemiki abunnan da kika so aikatawa ba,domin da kin kasheta daba karamin masifa zaki jawo min ba,Allah ya isa tsakanina dake hafsah,kije NA SAKEKi!!!”….. Alhaji na fadin haka mama ta fashe da kuka ta durkusa a gabansa,sai ihu take tana cewa “Alhaji dan Allah dan annabi kamin rai,na tuba,wlh kuskure ne da sharrin shedan,idan kace in bar gidanka bansan inda zani ba”…. Ko kollonta beyi ba ya fice daga dakin….. Sai a lokacin Fatima zainab ta fashe da wani mugun dariya tana tafa hannu tace “Wai da ni zaki kashe?,Ina miki kallon shashasha ashe kinada hankali har haka? Wow” Ta kuma fashewa da dariya sannan tace “Dadin abundai kika kasheni danku kika yiwa asara,dan na tabbata ina mutuwa ze hadiyi zuciya ya biyoni”…… Mama kam in banda kuka ba abunda takeyi,ya’yanta na tayata,ganin Fatima zainab ta nufi hanyar fita yasa ta bita da sauri ta riko kafarta ta fara rokonta tace “Dan Allah dan annabi fatima zainab kiyi hakuri,na tuba,wlh sharrin shedan ne,ki taimakeni kiyiwa alhaji magana ya mayar dani dakina ,nasan ke kadaice zakiyi masa magana yaji”……  Hankadeta tayi tace”mu zuba nida ke,bakiga komai ba”……….. Koma tayi ta zauna tana zaro wayarta daga cikin bag,call log dinta tashiga tayi dialing numbersa sannan tasa a hands free,mama ta bita da kallo cikin idon tausayi tana addu’ar Allah yasa alhaji zata kira ya maida ita dakinta……..

Karanta Littafin : Matar Makaho Complete Hausa Novel

   Zaune yake a office dinsa yana daddanna system cike da kwarewa,kallon wani hotonta dake bangon office dinsa yayi ya kama murmushi kamar wani wawa,hotone da yayi mata da hijab har kasa da kuma niqab harda hangloves kamar dai yadda ta saba shigarta,baya ganin komai na jikinta,dukda hakan ba karamin farinciki hoton yakesa masa ba,musamman inya tina irin masifar data masa akan hoton,wai dan me ze mata hoto?…………

Wayarshi ce tafara ringing da wani kida me dadin sauraro,a mamakance yabi wayar da kallo,dan yasan ita kadai yasawa wannan ringtone din,da mamaki da farinciki ya daga wayar yana bin wayar da kallo,baze iya tina when last ta kirashi ba?,kuma shima kafin ya sameta a waya sai yayi dagaske,har ze katse ya kirata back sai kuma ya fasa dan yasan tsap zata iya kin dauka,tace akan me ze katse ya kirata tinda ita taga daman kira,dauka yayi da sauri kar call din ya katse………..

   Daddadar muryartace ta daki dodon kunnensa tana cewa “Sai yanzu zaka daga wayata Khaleel?”…. Cikin murya me sanyi yace“Sorry wifey,nashiga kogin tinaninki ne har bansan wayar nata ringing ba,gashi farinciki ya lullubeni ganin sarauniyar zuciyata ta kirani yau”….. Wani abu ne ya daki zuciyar momma jin hakuri yake bata akan be dau waya da wuri…… Fatima zainab ce ta katse mata tinaninta da cewa”Ina gida,ina tsakona?” Murmushi yayi me sauti sannan yace “Haba sweetheart bazaki tsaya mugaisa bama?,sakonki kuma na gurin abdul,yace yanata kiran wayarki baya samunki”………. “Ok,ni badan gaisuwa na kira ba,bye”….. “I love you so much”… Ya fada batareda ya damu da abinda ta fada ba….. Tsaki taja ta kashe wayar……… Abdul jiki na rawa ya maza ya tashi ya tafi dauko sakon kafin ta juyo kansa….. Shigowa yayi dauke da wani katon box ya ajye a center table,ya russuna yace”Ga sakon anty”….. Kallon box din tayi tace”Bude”….. Budewa yayi wasu rose flowers masu shegen kyau suka zubo,saiga wasu cards anjera su daga gefe,sai wasu box guda biyu a ciki,da babba da karami,nuni ta mishi daya bude su suma…. Budewa ko abdul yayi saiga chocolates iri iri a cikin babban box din,dayan karamin box din ko waya ce kirar iPhone 14 pro max a ciki,tashi tayi ta zare wayar tasa a jaka,sannan ta dibi sauran kayan ta watsa musu a parlourn,ta dauki jakarta tayi hanyar waje……..             Abdul naganin ta fita ya bita da sauri,momma na kiranshi ko sauraranta beyiba…… Ajiyar zuciya momma tayi cikin kunan rai tace nida haihuwa,wata da juya min yara,khaleel dama yazama sallamamme akanta,shiko wannan da zarar ya ganta kamar an sashi a aljanna………..

             Tafe suke abdul na binta a baya yarasa ta ina ze fara fadamata abinda yakesan gayamata….. Saida suka shiga parlournta yana biye da ita sannan ta juyo tace “Lafiya abdul?”…… Numfasawa yayi sannan yace “anty dan Allah wani favor nakeso kimin,na dade ina nemanki na rasa yanda zan sameki gashi inna kira wayarki bana samunki,dana fadawa yaya kuma saiya fara zagina wai uban me zan miki da nake nemanki”………. “Ina jinka”… Ta fadi haka Tana kallonshi….. Sunkuyar dakai yayi yace “Dama motatace taketa bani matsala,inata gyarata,kullum ni kenan hanyar garage,shekaranjiya ma na sake kaita amma haryanzu bata gyaruba,nayiwa Ya khaleel magana akan ya taimaka ya siyamin wata ko ya bani daya daga cikin nasa,amma yaki,wai wallahi baze bawa unserious being irina ba saboda na sakeyin spill two a school,dana fadawa daddy sai ya goyi bayansa wai ai gsky ya fada,bawanda ze tsaya yana kashewa irina kudinsa a banza,dan Allah sis ki taimakamin nasan ke kadai ce zaki yiwa yaya magana yaji”…….. Ba yabo ba fallasa tace “Kawai saboda ka sake spill two sai a hanaka jin dadin rayuwarka?,ai ba akanka aka fara unseriousness ba da zaa takura maka haka”……. Wani dadi ne ya lullbeshi,shiyasa yaketaso tazo,saboda yasan indai tazo duka matsalolinshi sun warware…. 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Tashi tayi tashiga bedroom dinta,ta bude bedside drawer,ta shiga bin car keys din dake wajan da kallo,guda biyu ta zaro ta rufe wajan….. Fitowa tayi taga abdul yayi zuru yana jiran fitowarta,karasowa tayi tace mishi “muje”,jiki na rawa ko ya bita a baya……….. Fita sukayi ta nufi parking lot abdul na biye da ita,juyowa tayi ta kalleshi tace”abunda nakeso dakai shine,karka kara karatu in zaka shiga exam hall”…… Zaro ido yayi cikin tsoro yace “Kai anty nayi karatun ma ya aka kare bare banyi ba”…… Cilla masa daya daga cikin car keys din tayi sannan tace “Nidai nagaya maka,in kaga dama ka dauki shawarata”…. Wani farinciki ne ya lullubesa harda tsugunawa kasa yana mata  godiyar jindadi,yes yasan motar yayanshi ce amma muddin yace masa ita ta dauka ta bashi,yasan zance ya kare….. Bata saurareshi ba shige mota kirar Mercedes benz ta tafi……..

   Tafe take cikin sabuwar motar data dauka Tana jin music mai dadi,wani nishadi na kamata,ko banza ta haddasa fitina harda saki,ko tausayin mama bataji a ranta ba tinda mama muguwace,kawai sai traffic light ya tsayarda ita,gyara zama tayi tana lalubo niqab dinta a jakarta…..

    Tinda Dr ya baro gidan alhaji yayi parking a nearest cafe,yashiga yayi ordering coffee,yashiga sha yanajin kamar idan ya koma gidan alhaji yanzu ze ganta,domin zuciyarshi kwatakwata taki amince masa bata gidan……..  Ya dade a zaune,chan kuma ya hakura ya fito,ya nufi motarshi ya shiga yaja……. 

A daidai traffic light daya tsayar dashi,kawai yaji zuciyarshi na fuzgarshi daya kalli gefe………….. 

    Hmmm ku biyoni dan jin yanda zata kaya tsakani Dr Deen da fatima zainab,ko zasu hadu a traffic??!!😅

     ~Unique Barakancy~

Back to top button