Uncategorized

Macijine Shi Page 29-30 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 29/30

_________________Cikin wani irin salo da murya mai maka da yana jin barci,Adeeb yace “Hulwa” 

Ahankali fattu ta dago kanta tana mai kallon bayan Adeeb ɗan ganin ta ina hulwar zata fito.

Rarraba idanu take ,amma bataga kowa ba,ikon Allah ko ina hulwar take ?bisani Banga kowa abayansa ba ,kuma ba kowa cikin ɗakin nan, fattu ta faɗa tana mai waige bayanta ,dan ita dai bataga hulwa anan ba.

Duk abinda take Adeeb na kallonta,kuma ya gane me take nufi,wato suna daya faɗa shine bata ganeba,take neman mai sunan.

Juyowa fattu tayi ta kalli Adeeb ɗin cikin rashin fahimta tace “Hamma Ina hulwar take ?naga ba kowa cikin ɗakin nan ?

Kallonta yayi tare da ɗan zafi ido yace “yanzu ke bakuga hulwar tawa ba anan?” Ya faɗa yana mata kallon tuhuma.

Waigawa fattu ta sakeyi bayanta,amma wllh ita kam bataga kowa ba,juyowa tayi tace “alƙur’ani banga kowa ba” ta faɗa tana ɗan buɗe hannayenta dan tabbatar masa da cewar ba kowa aɗakin.

Yaɓe baki yayi yace “matata ce hulwa kuma gata nan akusa dani idan ke bakya ganinta toni ina ganin abata,ya faɗa yana ɗan kallon kusa da gadon da fattu ke tsaye.

Ai fattu najin haka wani irin tsoro ya kamata,da gudu ta watsar da kayan hannunta ta taho gareshi ,tana zuwa ta biye abayansa tana tsuma, ahankali take masa faɗa cikin kunnensa,”aradu Hamma aljanna kake gani ba matar ka ba,dan ba kowa acikin ɗakin nan,Ni dama tun dazu nakewa dakin kallon na aljanu,dan wannan ɗakin baiyi kama dana mutane ba ,kyanshi yayi yawa aradun Allah” fattu ta ƙare magannarta cikin kunne Adeeb da sunan tana masa raɗa dan kar Hulwa tajisu.

Tunda ta fara masa magana akunne ya wani lumshe idanunsa,har cikin ƙwaƙwalwar sa yake jin sautin maganarta, yayi da yake jin tana zaga dukkan ilahirin jikinsa, wani yuuuuum yakeji ajikinsa har kamar zai faɗi.ahankali ya buɗe idanunsa,jin ta kai aya akan maganar tata. Wacce shidai yaji farkon,amma sam bai fahimci me take fadi ba daga ƙarshen.

Yana shirin yin magana ne yajiyo ƙarar na’urar sanarda mutum yayi bako tana faɗin tareek na jikansa afalo.

Dan haka ya fasa yin maganar ,kawai saiya juyo yana kallon fattun da tunanin idanunsa,ahankali ya buɗe baki da gyara yace “wait for me here I will be back” ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kofar,ai carab fattu ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata gam!tana kallonsa.

Kallonta yayi shima da nuna alamun menene?

Turo baki tayi tace ” Ni ma zan bila Hamma,dan naji ka kira sunan wasu mutanen da yawa,bayan waccan hulwar Ni wllh tsoro nake ji” fattu ta faɗa tana mai kallon fuskarsa.

Hannunsa data rike cikin nashi,yabi  da  kallon,kafin ya ɗago yana kallonta,waima shi yaushe ya kira sunan wasu mutane kuma?ahankali ya sanya hannu ya zare nata hannun daga nashi kafin yace”bazaki bini ba, kuma Ni nace ne ki Kijirani kawai”ya faɗa yana harararta tare da bude ƙofar,yana sanya ƙafarsa waje fattu ma ta fito jikinta sai rawa yake,juyowa yayi yana kallonta fuska ba walwala yace ” koma”

Marairaicewa fattu tayi kafin tace ” wllh tsoro nakeji,dan Allah kaje dani,wannan hulwar fa tana ciki” harara ya Banka mata kafin yace “get  in I said ,hulwar ta cinyeki” ya faɗa yana turata ciki dakin yana ƙofar ya kulle.

Hauka yake yaje da ita gurin tareek cikin wannan shigar?ai wllh idan tareek ya ganta ahana,inaga saina kusan mutuwa dan baƙin ciki.cewar Adeeb kenan yana nufar madaidaicin falon daya gaji da hadewa,zama yayi yana kallon tareek  ɗin  cikin yanayinsa ya haɗe fuska.

“Yallaɓai me yake faruwa ne ?naga ka shigo cikin tashin hankali?”tareek ya faɗa cikin harshen larabci yana kallon Adeeb ɗin.

Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin ya jingina kansa jikin kujera ,kusan minti biyu kafin ya buɗe baki dagyar yace ” ta tsoratane ,shine ta suma” shima cikin harshen larabci yayi maganar.

“Ya Salam, yallaɓai koka sanar da ita wanann maganar ne?”

“No ban faɗa mata ba” cewar Adeeb .

Shiru suka ɗanyi na wani lokaci, kafin  tareek yace “yallaɓai abie baisan da dawowarsa,bansanar da kowa ba kamar yadda ka buƙata” 

Ɗagowa Adeeb yayi daga kwanciyar da yayi jikin kujera,kafin yace ” Yes,bana son ya sani yanzu,sai dare yayi zamuje gurinsa, ka shirya komai da komai,yanzu zanje na  rage suman nan ne” Adeeb ya faɗa yana mai shafa  dogon lallausan gashin kansa zuwa  gefen fuskarsa da gemunsa.

“Ok me kake ɓukata yanzu yallaɓai ” tareek ya faɗa cikin ladabi.

“Kaje ka kawo mata kayan buƙata duka, sannan ka tahomin da wayoyi ayi duk abinda ya kamata” yana faɗin haka bai jira me Tareek zaiceba ya miƙe tare da nufar wani ɗakin da ban.

Fattu kuwa Adeeb yana kulle ƙofar taji wani mugun tsoro da fargaba, wayyo Allah,yanzu ya zanyi idan hulwar nan mai shan jini ce ? Kuma gashi bana ganinta ?

Zama tayi agurin tare da ƙanƙame jikinta tana kuka sosai harda shashsheka,Allah Sarki baffanta ,ko wane hali yake ciki yanzu?ko wane hukunci mai gari ya ɗauka akansa? Allah dai ya kare mata baffanta Aduk yanayin daya tsinci kansa.

Tana nan zaune sai waige waige take ,ta gaji sosai ga yunwa ,ga barci,gashi tana sonyin salla dan rabonta da abinci tun wanann jakwalkwalon da Hamma ya bata awanann gidan.tana zaune shiru kawai taga wasu labulaye masu  suna saukowa ahankali daga kowane bango na ɗakin.wata zabura da tayi cikin tsoro ta kwallah ihu tana mai komawa tsakiyar dakin ,banda rawa ba abinda jikinta keyi”wayyo Allah ma hulwa dan Allah kiyi haƙuri,karki cinyeni ,wllh ba abinda nayi miki,Hamma ne ya kawoni gidanki”abinda fattu ke fadi kenan tana rawar jiki da karkarwa,tana juye juye atsakiyar dakin,ta kalli wannan bangon ta kalli wancan..

Sukuwa labulaye ,sai sauka suke kasa,kuma basu tsayaba ,saida suka dire har  aƙasa.

Sai kuma taga hasken ɗakin ya sauya kala ,daga farin haske zuwa dim light,kuma daga can gefe wata bishi sai walwali take .

Kuka sosai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin abinyi,yaukan yasan kwananta kawai ya kare kamar wacce akace kalli can ,tana juyowa wajen da sif ɗin nan take ,kawai taga abubuwa kamar malam bude mana littafi, suna ta yawonsu ajikin sif ɗin.

Wata irin numfashi fattu ta jaa da ƙarfi,kafin kuma tayi ƙasa sululu ta faɗa kan gadon asume.

Shikuwa Adeeb yana shiga wannan dakin kwanciya ya ɗanyi akan lafiyayyen gadon dake ɗakin,so yake ya ɗan huta,dan gaba ɗaya yarinyar nan ta gama gajiyar dashi ,yana kwanciya sai yayi tunanin ai baiyi Sallah ba,dan haka tashi yayi tare da sake wanka sannan yayi Sallah,ya koma toilet ɗin ya gabata fuskarsa,sosai naga kyansa ya ƙara fitowa ,ashema kyanshi ya wuce yadda nake tunani,dan kallo daya idan kayi masa ,kuma kuka haɗa idanu ,bazaka iya ƙara yarda ku haɗa ido ba,dan yana da wani irin kwarjini da haiba.

Wannan karon ƙananan kaya ya sanya,riga da wando ne na jins, rigar light blue ce ,yayinda wando kuma ya kasance blue ne sosai.kansa ya taje, sannan ya fashe jikinsa da tauraruwa masu masifar ƙamshi, danaga ya buɗe wata loka guda ,duka turarukane acikin lokar tunda ga sama har ƙasanta.

Wata lokar ya buɗe naga agoguna ,masu azabar kyau da tsada,wani agogon kwal ya dauko ya daura ahanannunsa, sannan ,sannan ya buɗe bangaren takalma,nidai gefe na koma na zama yar kallo.dan abun yafi karfina, daki guda duka na kayan Amfanin mutum ɗaya?wani aikin sai amasar.

Yana gama shiryawa ,dakin ya dauki wani ƙamshi mai rikitarwa da sanya nutsuwa,kanshi ya taje sannan ya shafa mayuka kusan kala biyar akan nashi,tuni kan ya dauki walwali da sheƙi,

Fitowa yayi daga ɗakin ya nufi kitchen,masu karatu kuzo kuga kitchen ,aini kodaga nam aka barni ,tabbas na more,dan iya tsaruwa kitchen ɗin nan ya tsaru.

Wani irin tea naga ya haɗa ,sannan ya siya kwai tare da imdomie,shikam arayuwarsa baida wani abinci daga tea  sai imdomie  saiko nama, 

Yana gama  haɗawa ya tsaya yana kallon abincin daya haɗa ɗin cikin wani kayataccen faranti, mamakin kansa yake ,wai yau shine da haɗawa wata  abinci,kuma shi zai kai mata da kansa.koda yake ai itaɗin amanar sa ce,kuma dole ya kula da ita.

Ɗaukar tiren yayi ya nufi dakin da Fattun ke ciki,

Kwankwasawa yayi kafin ya dannan wani guri sai ga kofar tana komawa gefe guda,harya buɗe gaba ɗaya ɗaya .

Kansa ya kunna cikin dakin yana mai kallon yadda komai ya canza,wannan alamun e na lokacin barcinsa yayi ,dama haka dakunan aka shiryasu suke sauya komai da kansu,idan lokacin barcin rana ne kona dare ,kokuma safiya .

Ajiye tiren yayi yana mai kallon ta ina zai hangi fattu,can ya hangota kwance akan gado ,saidai da’alama kwanciyar bata daɗi bace, dan haka da sauri ya nufeta, kamar yadda yayi tsammani kuwa suma tayi,cike da fargaba ya ɗagota yana mai kiran sunanta ,”Hulwa !hulwa!!amma bata ko motsaba,ajiye ta yayi tare da bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi yana yayyafa mata.amma bata ko motsaba ,wai wannan suman na menene haka?duka duka yaushema ta dawo hayyacinta ne ?gashi yanzu ta ƙara suka.

Huci kawai yake yana kallon fuskarta,zuciyarsa kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito,sam baya ƙaunar ganin fattu cikin wani mugun yanayi,waima menene yayi silar wannan suman nata ne?kallon dakin yayi yana mai jinjina kai ,ba shakka tayi arba da yadda dakin nan ke sauyawa ne,wani irin runtse idanunsa yayi tare da dafe kansa,duk laifinane dana fita da ita da duk haka bata faru ba.bude idanunsa yayi wanda suka juye zuwa na macizai sak, ahankali jikinsa ya kama wata irin girgiza yana hayaƙi,kan kace me saiga ɗakin ya turnuƙe da hayaƙi, kusan minti biyar dakin yana wanann yanayi hayaƙi da wata irin ƙara,kafin hayaƙi ya  baje, saiga wani murtukeken maciji mai girman gaske ya fasa kai yana huci.

Cikin tafiyar macizai macijin nan ya fara sauƙa daga kan gadon ,bangon dakin ya kama tare da fara lauye jikin wanan haɗaɗdun labulayen yana nannadesu tare da fesa musu wani irin ruwa daga bakinsa,da zaran ya fesa ruwan sai kaga labulen yana hayaƙi tare da murmushewa, haka yayi tayi saida  ya bata gaba dayan labulayenan sannan ya fara bugun kwayayen dakin dake bada hasken nan mai ban sha’awa  da jelarsa.tas saida ya gama fashesu, sannan ya nufi kan gadon,yana zuwa ya hau kan cikin fattu dake kwance ,cikin halin suma,zagayeta ya farayi tare da shigewa ciki rigarta  sosai,yana goga  mata sanyin dake jikinsa. 

Aikuwa sanyin yana fara ratsa fattu ,ta fara bude idanunta ahankali,tana mai dafe kanta tare da yamutse fuska.

Abu taji yana fitowa sululu daga cikin rigarta,da sauri ta tashi zaune tana mai daga rigarta sama,daidai lokacin shikuwa macijin ya gama fitowa daga jikin nata.

Saƙare fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki,shima macijin kallonta yake ido cikin ido.

Masu karatu meke faruwa ne?

Wannan macijin kuma waye?

Shin Adeeb dama bai daina zama macijin ba?

Muje zuwa takuce anty mammy 

Mrs babi💘💘💘

Share and comment

Fisabilillah.

More comments

More typing.

Back to top button