Labarai

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 37 By Hafsat Bature

 

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E37

Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji

Sun É—auki tsawon lokaci rungume da juna suna ta kuka, Sai da suka yi mai isar su tukunna kowa Ya yi shiru, ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba, Muryar deeja a disashe tace”Na gaji da irin wannan rayuwar angel, bazan iya jure ganin Æ´an uwana suna shan wahala ba, tun da ba yanzu suka fara ba, zasu ci gaba da zuwa suna É—aukar mu ne É—aya bayan É—aya har sai sun Æ™arar damu, nayi tunanin cewa gata ne ake nuna mana acikin kurkukun nan ashe ba haka bane, tsohuwa ta yi mana Æ™arya da tace mana gidan marayu ne, za’a gatanta rayuwarmu, ta yaudare mu ta cuce mu, ba zamu ta6a yafe ma duk wanda yayi silar sadaukar damu zuwa cikin kurkukun nan ba…….”

katse maganar ta yi, batare da ta kaiga Æ™arasa ta ba, saboda wani irin Æ™ululun baÆ™in ciki da ya tokare mata maÆ™oshinta, Sai lokacin angel ta iya buÉ—e baki tace”Dama ni nasani tun farkon zuwana kurkukun nan na gane cewa Ba orphanage home bane, Tun daga kan sunanshi, shiyasa nayi ta Æ™oÆ™arin in fahimtar daku, saboda ni nayi rayuwar Æ´anci da hankalina da wayau na, sihirin tsohuwa tamira bai yi tasiri a Jikina ba, shiyasa Tunina bai gushe ba, dama taya za’ae Gidan marayu ya kasance Kurkuku? Kuma ba shige ba fuce, Abinci sau É—aya arana! Uniform kala É—aya, sai dai idan munyi wanka mu cire mu wanke mu maida a jikin mu? Ga shi babu wani mai kula damu, Rayuwa muke yi kara zube, wlh ko dabbobin dake garari acikin daji sun fi mu Æ´an ci, koba komai zasu yawata inda suke so, Kai ni da irin rayuwar nan ma Æ™wara mutuwa, saboda É—aci ne da ita, rayuwar kulle, babu wanda zaiso ya kasance cikin irin wannan makauniyar rayuwar, Ai ko maÆ™iyi na bazan yi ma fatan shigarta ba…..” Sai lokacin angel ta raba jikinta daga na deeja, Idanuwan kowannan su ya yi jawur saboda tsabar kukan da suka sha, Cikin karyayyiyar murya deeja tace”Ni bana Jin ma zanyi tsawaicin kwana, Gani nake kamar nice gawar fari acikin mu….” kafin ta karasa maganar angel ta yi saurin sanya tafin hannunta ta toshe mata baki, tana girgira kai, Hawaye na bin fuskarta tace”in sha Allah ba ke bace gawar fari, wlh bana Yi mana fatan mu rasa rayuwar mu acikin kurkukun nan, ina matuÆ™ar so inga kuma kunyi rayuwa kamar kowa, Idan ma mutuwar ce na Æ™wammace ni in fara yinta, saboda bazan Juri rashin wani acikin ku ba, bakisan yarda nake jinku ba, akan ku bana jin tausayin kaina, saboda ku ne abun tausayi” DaÆ™yar takai Æ™arshen maganarta, hawayen deeja duk sun wanke hannunta data rufe mata baki dashi,

“Kowani É—an adam da irin tashi Æ™addarar rayuwar, kowani bawa da irin Æ™alubalan da yake fuskanta acikin rayuwarshi, Allah yana jarabtar bayin shi ba dan baya sonsu ba, face don ya jaraba imaninsu, babu wanda zaice maka 100% yana rayuwa Cikin jin daÉ—i, dole akwai ranakun farin ciki da kuma na baÆ™in Ciki, wani farkon rayuwarshi Jin daÉ—i ne, tsakiyar rayuwarshi wahala ce har zuwa Æ™arshenta, wani kuma da farko zai ci baÆ™ar wahala amma daga Æ™arshe sai kaga Ya samu farin Ciki, Akwai wanda kuma Kaf rayuwar shi tun daga zuwanshi duniya Allah zai fara jarabtar shi, har zuwa Æ™arshen rayuwar shi bazai ta6a jin daÉ—in duniya ba, zai fuskanci Æ™alubale iri iri wanda idan Baida Æ™arfin imani da tawakkali zai fidda rai da rahamar ubangiji ne, Zaiyi tunanin cewa ko Allah baiso na ne? At end har yakai ga tunanin salwantar da rayuwarshi don ya huta, wanda yin hakan kuma zai Æ™ara Jefa kanshi Cikin matsala ne, Kazo duniya a wahalce kuma ka koma a matsayin zero duka kayi asara, Amma idan kayi haÆ™uri ka miÆ™a lamurranka ga Allah subhana’hu wata’ala Koda baka ji daÉ—i anan ba, acan ana kyautata zaton zaka dace, akwai wanda kuma bai ta6a shan wahalar duniya ba, gatanci ta ko’ina, wahalarta kaÉ—an ya sani, in kaga 6acin ranshi to wani Ya rasa na kusa dashi, aduk halin da bawa ya tsinci kanshi Ya kasance mai godiyar Allah, Kafi wani, wani yafi ka, yanzu kamar rayuwar waÉ—annan bayin Allah, tunda suka zo duniya A garÆ™ame suke kamar dabbobi, An tauye musu duk wani haƙƙinsu na rayuwa, basu son komai game da jin daÉ—in duniya ba, sun yi rayuwa acikin duhun jahilci, Basu son iyayensu ba, Basu son danginsu ba, su kansu basu Su wanene su ba, Haba jama’a, wannan rashin imanin har ina? A haka ake so su mutu su fuskanci mahaliccinsu, ai Æ™wara wanda ke rayuwa acikin mutane yana fuskantar jarabawar rayuwa, Amma akwai imani azuciyarshi, Atlease Ya tsira da wannan idan yayi tawakkali, amma waÉ—annan bayin Allahn fa? Ba don zuwan angel acikin rayuwarsu ba da shikenan An kashe su da ransu an gama dasu, yakamata mu Æ™ara jin tsoron Allah acikin zukatanmu, mu kasance masu tawakkali, kuma mu kasance masu godiya ga Allah aduk halin da muka tsinci kanmu, tun da bamu rasa komai na rayuwa ba, ka kwana ka tashi da ranka da lafiyarka, ka je inda kake so, Ka ci mai kyau kasha mai kyau, ka sanya sutura mai kyau, kana a tare da iyayen ka ko babu su akwai danginka, kai idan ma babu dangin naka Allah Yana atare dakai, Zaka Iya rayuwa ko babu su, da daÉ—i da ba daÉ—i, Allah ya baka rai da lafiya, Amma sai kaga bawa yana Ƙorafi don ya rasa wani abu Æ™alilan, ko angaza biya mashi buÆ™atarshi, dayawa gajan haÆ™uri kesa wasu harsu fara neman duniya ido rufe, Allah dai yasa mu dace, Shiyasa ake so mutun ya dinga ziyarta asibitoci da wuraren da faÆ™iran talakawa suke yin rayuwa, Kodan ya Æ™ara imani, Allah dai ya tsare mu ya kare mu daga faÉ—awa tarkon halaka, kada amanta adunga taya Æ´an uwan mu addu’a waÉ—anda ke a hannun kidnappers da kuma Æ´an boko haram, da matsafa, muna roÆ™on Allah ya kawo mana Æ™arshen wannan masifar da muke fama da ita a Æ™asarmu badan halin mu ba, Alfarmar Annabi muhammad (SAW) addu’a takobin mumini ce da ita ne kaÉ—ai zamu Iya yaÆ™ar su, tun da mu bamu da yadda zamuyi, waÉ—anda keda ikon Yin sun gaza, saboda rayuwar mu bata da mahimmanci awurinsu, takansu suke yi, wanda nayi imanin da ace yau hada Æ´a’Æ´ansu aka É—auka da anga tashin hankali, cikin Æ´an awanni sai sun san yadda zasuyi an dawo musu dasu, Akwai dai ranar Æ™in dillaci, ranar da dukiya ko ya’ya ko wani muÆ™ami na duniya bazai amfane su da komai ba, A ranar zasu shaida cewa ALLAH ÆŠAYA NE.

A hankali angel ta zame hannunta daga saman bakin deeja,

“Deeja kodai in taimaka maki ki yi wanka? Naji jikin ki wani iri, daga gani baki jin daÉ—in shi” girgiza kai deeja tayi”a’a, bazan Iya yin wanka da ruwan sanyi ba, Jikina zai Æ™ara tsauri, ki barni kawai ahaka, ” tsananin tausayinta ne ya Æ™ara kama angel.

“To Mu je mu kwanta, ko kin samu ki yi bacci ki huta” shiru deeja ta É—an yi batare data amsa mata ba, har sai da angel ta Æ™ara maimaita mata, tukunna ta buÉ—e baki tace”bazan iya tashi ba, ki kije ki tada su daga bacci, ki faÉ—a musu cewa an dawo dani, su zo mu gaisa,” maganar deeja ta yi matuÆ™ar girgiza angel sai taga kamar bankwana ne take so ta yi dasu, muryarta na kerma tace”amma meyasa? Idan baki iya tafiya ne, ni sai in É—auke ki abayana in kai ki cikin É—akin ki kwanta, In yaso gobe da safe sai ku gaisa da su” idanuwan deeja a marairaice take kallon fuskar angel, da wata irin raunatacciyar murya tace”dan Allah ki kira mini su in gansu, kada na mutu batare da nayi tozali da Æ´an uwana ba,” girgiza kai angel tayi cikin shessheÆ™ar kuka tace”In..sha.. Allah ba zaki mutu ba, har sai mun fita daga cikin kurkukun nan, Na roÆ™e ki ki daina Yi mini maganar mutuwa, kina karya mini zuciyata, Kinsa Jikina duk ya yi sanyi” hawaye ne masu É—umi suka wanke fuskar deeja, idanuwanta sunyi jawur sosai, la66anta na kerma tace”dan Allah ki kira mini su mu gaisa, inaso inga Æ´an uwana.”

Juya mata baya angel ta yi tare da cewa”Ki hau in kai ki cikin É—akin, Sai in tada maki su ku yi magana” fashewa deeja tayi da kuka tana faÉ—in”bana ce maki bazan Iya miÆ™ewa ba, Kije ki kira mini su ko so kike saina mutu ne batare da nayi bankwana dasu ba”? Yanayin da tayi maganar yayi matuÆ™ar girgiza angel, Hatta muryar deeja ta canza sosai, a Æ™arshe ta sassauta muryarta tana yi mata magiya akan ta kira mata su, Muryar angel na rawa tace”shikenan ki jira dan Allah, yanzu zanje in tada su daga bacci kinji,” AruÉ—e ta yi maganar, ta miÆ™e da sauri tana tafiya tana waiwayon deeja, fargabarta kada ta mutu kafin ta dawo daga kiran nasu, bayan ta cire jamlock É—in Æ™opar da gudun gaske ta faÉ—o Cikin É—akin har kusan tuntu6e ta yi, tun kafin ta Æ™arasa cikin É—akin ta dinga kwala musu kira, Haris danish, naufal hanna hibba batool yasmin ku tashi an dawo da deeja, da alama sunyi nauyin bacci babu wanda ya motsa, gaban gadajensu taje tana bubbuga Æ™afafuwansu tare da cire musu bargunan da suka lullu6a dasu, Wannan karan muryarta da sauti mai Æ™arfi take kwala musu kira, a matuÆ™ar firgice kowannansu ya farka Yana faman Yin hama, Ba ta bari sun wartsake ba, tace musu”ku tashi muje toilet, deeja tana aciki, An dawo da ita, amma bata da Æ™oshin lafiya, ita ce tace in kira mata ku, tana son ganinku” Jiki na rawa suka sauko daga saman gadajensu, Haris yafi kowa zumuÉ—i, shine agaba sai naufal da mubeen da danish, tare da javed, Matan kuma batool ce agaba sai su hanna hibba eve da su Parveen, Mutun É—aya ce bata sauko daga saman gadonta ba, Azeeza amma ta farka tana ta kuka tana faÉ—in ita ba wanda zai kai ta wurin deeja, saboda anga bata da ido, har angel ta juya zata bi bayansu Batool sai kuma ta fasa jin muryar azeeza da sauri taje bakin gadonta ta ruÆ™o hannunta, tare da taimaka mata ta sauko daga saman gadonta, suka nufi toilet section É—insu, lokacin da kowannansu ya hallara acikin toilet É—in da deeja take, hankalinsu Yayi matuÆ™ar tashi, Ganin yadda jikinta ke ta kerma, wata irin zufa ce ke tsastsafo mata a jikinta, gaba É—aya ta jiÆ™e sharkaf, a sukwane suka zuÆ™unna gabanta suka kewayeta, suna ambaton sunanta, hannu biyu haris ya sanya tare da tallabo fuskarta, daÆ™yar take iya buÉ—e idanuwanta da suka rune tana kallonsu, ita kaÉ—ai tasan irin raÉ—aÉ—in azabar da take ji ajikinta, muryar haris a ruÉ—e ya ambaci sunanta”deeja! ke ce kika koma haka? me ke damunki? kina iya ganinmu”? jinjina ma shi kai ta yi alamar eh, Azeeza dake ta kuka tana faÉ—in su nuna mata deeja, angel ta zuÆ™unnar da ita agaban deeja, Ta haÉ—a hannun azeeza dana deeja, Sosai deeja ta Æ™anÆ™ame hannun azeeza dake acikin nata, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanta”Azeeza”! Amsa mata tayi”na’am, deeja ashe an dawo mana dake muna ta bacci bamu sani ba, Mun yi missing É—inki sosai, ” shafa fuskar azeeza ta yi da hannunta, nan take azeeza ta É—an zabura tana faÉ—in”Zafi hannunki deeja, baki da lafiya ko”? Bata amsa mata ba, sai dai binsu da take yi da kallo, matsawa batool ta yi daga gefenta ta É—aura hannunta saman wuyan deeja, da sauri ta zame shi, jin wani irin zafi na fitar hayyaci, hankalin ta ya yi matukar tashi tace”Yakamata mu kira tsohuwa ta duba jikinta, kwata kwata babu alamun lafiya atattare da ita” haris yace”me tsohuwa zata Iya yi mata? Ai kawai ku taimaka mata ta watsa ruwa ajikinta, zata ji sauÆ™i,” girgiza kai batool ta yi tare da cewa”bazaka gane ba, kwara a kira ta, tun da ita tafi mu sanin meke damunta” Angel ta lura dasu kowa yana tofa albarkacin bakin shi, amma banda Danish tunda suka shigo ya zuÆ™unna na É—an wani lokaci sai kuma taga ya miÆ™e ya jingina bayanshi jikin bangon da deeja take a zukunne, ya goya hannayen shi saman Æ™irjinshi, ya É—aga kanshi sama idanuwanshi na fuskantar ceilling, tsabar haushin shi ne ya kamata, shi da yake amatsayin babba acikinsu yaÆ™i buÉ—e baki ya yi magana, Koda lallashin deeja ne yayi duba da irin halin da take aciki,’

“Ko da ace kun kira tsohuwa, ba abunda zata Iya yi mini, nidai tunda na gan ku Alhamdulillah hakan ma ya wadatar” Deeja ce ta yi maganar, Hanna tace”pls ki tashi mu koma É—aki ki kwanta,” kallon hanna deeja ta yi, Æ™arfin hali kawai take yi wurin yi musu magana”Ae bazan iya miÆ™ewa ba, Æ™afafuwana sun ruÆ™e,” Juya mata baya haris yai tare da cewa”ki hau in goya ki, mu shiga” nan ma tace mishi bazata Iya motsawa ba,’ lamarin yayi matuÆ™ar girgiza su, jikinsu yayi mugun yin sanyi, Rubina tace”nidai zanje na kira tsohuwa ne” tana kai karshen maganarta, da sauri ta juya ta buÉ—e kopar toilet É—in ta fuce, gudu gudu sauri sauri ta Æ™arasa bakin Æ™opar É—akin tsohuwa, Tasa hannu ta kwankwasa Æ™opar, kusan sau uku tana yin knocking, kafin ta samu tsohuwa ta buÉ—e mata Æ™opar É—akin, fitowa daga Ciki tayi hannunta ruÆ™e da sanda, ta É—ago da ido tana kallon rubina, Muryarta na rawa tace”dan Allah kizo ki taimaka mana an dawo da deeja amma jikinta babu sauÆ™i, ko iya miÆ™ewa bata Yi,” duÆ™ar dakai Æ™asa tsohuwa ta É—anyi batare da tace komai ba, “dan Allah ki taimaka badan halinmu ba, kada mu rasa Æ´ar uwarmu,” kafin tsohuwa ta É—ago da kanta sai ga su Javed da hibba hada yasmin sun fito daga Cikin sashen toilet dinsu, Hankalinsu duk atashe, É—aya bayan É—aya tsohuwa take binsu da kallo, Gaba É—aya suka haÉ—a baki wurin yi mata magiya akan tazo ta duba jikin deeja bata da lafiya, duk sun ruÉ—e bayin Allah, Girgiza kai tsohuwa ta É—anyi fuskarta babu yabo ba fallasa tace”Ni da bani da amfani awurin ku?me kuma zan Iya yi maku? Ita uwar ta ku bata iya duba mata jikin nata ne”? Duk sun gane akan wa take magana wato angel, hibba tace”pls ki taimaka mana mu dai, ki manta da komai kizo ki duba Jikinta, mun gane kuskuren mu, bazamu Æ™ara ba” suna kai karshen maganarsu gaba É—aya suka zube saman gwiwowinsu, suna roÆ™onta, Da buÉ—ar bakinta sai cewa ta yi”zan iya taimakon ku, bisa sharaÉ—i É—aya”! A Æ™agare suka tambayeta menene tace”Su je su kira babarsu angel, tazo ta durÆ™usa agabanta ta roÆ™e ta, idan har ta yi hakan ita kuma zata duba lafiyar deejan su,” da sauri suka miÆ™e da gudu suka nufi cikin toilet É—in, a lokacin Deeja tana kwance saman Æ™irjin haris, ya Æ™anÆ™ameta da hannayenshi, su angel duk suna a kewaye da ita, banda Maji daÉ—in gado daya ke atsaye kamar gunki, Yadda suka banko Æ™opar toilet É—inne yaja hankalinsu angel zuwa ga kallonsu, a fujajen suka faÉ—o, kusan atare suka haÉ—a murya wurin cewa”Ki zo angel, tsohuwa tace zata duba jikin deejan mu, amma dole sai kin durÆ™usa agabanta kin roÆ™e ta,” Waro ido waje angel ta yi bakinta asake galala take kallonsu, lallai wannan tsohuwar ta É—auko ta da zafi, taya zata ce saita durÆ™usa mata sannan zata duba lafiyar deeja? Mamaki ya hana ta motsa, magiya su javed suka dinga yi mata akan tazo suje ta duÆ™ama tsohuwa, ko sun samu ta duba Jikin deeja” kasa tanka musu ta yi, Har saida batool tace”Angel ki taimaka ma rayuwar deeja, dan Allah badan halin mu ba, Kije ki roÆ™eta, wannan ce kaÉ—ai damar da muke da ita, idan ba haka ba, deeja zata Iya mutuwa ki kalli yadda jikinta keta kerma yana zufa, duk ta fita hayyacinta” Batool na rufe baki azeeza ta fashe da kuka tana faÉ—in”Dan Allah angel kije kada mu rasa deejan mu, muna son Æ´ar uwar mu,” É—aya bayan É—aya angel take kallonsu, a karshen ta tsayar da idanuwanta kan fuskar deeja dake kwance saman kirjin haris, la66anta sai kerma suke Yi, ” ganin zata 6ata musu lokaci yasa suka nannaÉ—e hannuwan rigunansu, batayi wani aune ba, taji sun sunkuceta gaba É—aya suka cuccu6ota suka juya da ita zuwa cikin É—akin, tana ta kiciniyar Æ™wace kanta amma sunÆ™i bari ta kubce musu, a haka suka shigo da ita cikin É—akin, Tsohuwa na ganinsu ta saki wani irin bazawarin murmushi, dama tasan taurin kan angel da kafiyarta baza su ta6a bari ta tako da Æ™afafunta zuwa gabanta ba, su javed na Æ™arasowa inda tsohuwa take a tsaye suka saki angel ta faÉ—i Æ™asa, Idon tsohuwa na akanta, É—agowa ta yi fuskarta a hargitse, saboda tsabar masifa ta rufe idanuwanta tana zazzaga masu masifa tana faÉ—in don me zasu je su É—auko ta? Ita fa bazata ta6a duÆ™ama wannan tsohuwar najadun ba, mai kafirar zuciya wadda batasan Allah ba, ‘ta inda take shiga bata nan take fita ba, Hankalinsu Rubina ya Æ™ara tashi ganin tana Æ™oÆ™arin 6ata musu lokaci, ga deeja can tana jin jiki ita kuma da suka É—auko donta taimaka masu gashi tazo tana Æ™ara Kwafsa musu, ZuÆ™unnawa su ka yi gaba É—ayansu saman gwiwowinsu suna roÆ™on angel akan ta taimake su badan su zata yi ba, ta dubi girman Allah ta roÆ™i tsohuwa taje ta duba lafiyar deejansu, ” tsananin tausayinsu ne ya kama angel ganin hada hawaye akan fuskokinsu, saboda tsabar jaraba da jin takaici ta fashe da kuka tana faÉ—in”wayyo Allah na na shiga uku, yau zan aikata babban zunubi arayuwata, wlh na tsane ki kamar mutuwa ta, bansan ganinki, muguwa azzaluma, mai zuciya irinta kafiran farko, ke daga ganinki kin hada iri da jinsin fir’auna, saboda rashin imani taimakon ne bazaki iya yi mana ba, dole saina roÆ™e ki…..” Bata Æ™arasa maganar ba, yasmin ta sanya hannu biyu ta toshe mata baki, Cikin shessheÆ™ar kuka tace”dan Allah angel kidaina, idan baxaki Iya ceton ran Æ´ar uwarmu ba, bai kamata kina Æ™ara fusata tsohuwa ba, so kike ta fasa taimakon mu” A tsiyace angel ta buge hannun yasmin data toshe mata baki dashi, idanuwanta sun yi jawur tamkar garwashin wuta, kallon kallon suka shiga yi ita da tsohuwa,

“Lokaci Yana Æ™ure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin É—akina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaÉ—ai damar da kuke da ita” tsohuwace tayi maganar, fuskarta É—auke da shu’umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaÉ—i ba irin na yau, a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuÆ™unne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaÉ—a kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace”zan roÆ™e ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin Æ™asÆ™antar dani ne, zanyi ne saboda waÉ—annan bayin Allahn, da kuma Æ´ar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata’ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana” daÆ™yar takai karshen maganar ganin tsohuwa na Æ™oÆ™arin juyawa ta koma Cikin É—akinta, aikuwa da sauri angel ta É—ago ta zuÆ™unna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace”Na roÆ™e ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja” Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin Æ™ululun baÆ™in Cikine ya TurniÆ™e zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace”hakan ya yi mini, haÆ™iÆ™a yau na shaida irin Æ™aunar da kike yi musu, ke É—in uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba Æ™aramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roÆ™o na akan lafiyar Æ´arki deeja, Naji daÉ—i sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuÆ™unna saman gwiwowinta domin ta roÆ™e ni……”Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace”Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni” cike da shaÆ™iyanci tsohuwa tace”To gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi” Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faÉ—o kasa,

Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin É—akinta, muryar javed ta katse ta”deeja fa? Naga zaki koma Cikin É—aki” batare da ta juyo ta kalle shi ba tace”Ku jira ni yanzu zan fito,” Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta É—aya ruÆ™e da gorar ruwa ta gargajiya, miÆ™a ma javed tayi”RuÆ™e mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita” da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan Æ™asa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durÆ™usawa tsohuwa,

Lokacin da suka shiga Cikin toilet É—in, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya Æ™yaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, É—aya bayan É—aya suka fuce daga Cikin toilet É—in, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin É—akinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet É—in suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuÆ™ar tashi, gaba É—aya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin Æ™opar toilet É—in a datse suka same shi, A dole suka zauna Æ™asa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin É—akinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a Æ™asa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,’ wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari,

Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaÉ—ai take gyangyaÉ—in bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta É—an É—aura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi, Naufal ne ya lura da ita, ruÆ™o hannunta yayi acikin nashi yace”azeeza tashi muje in raka ki cikin É—aki ki kwanta, kada ki yi bacci anan” maÆ™e mashi kafaÉ—a tayi muryarta adisashe tace”ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja” Haris dake sauraronsu yace”naufal, Kada ka biye mata, pls ka É—auke ta, ka kaita cikin É—aki,” rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja” Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata Æ´ar baby haka ya ruÆ™ota ya nufi Cikin É—akin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaÉ—e ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara É—agowa ya kalli danish dake kishingiÉ—e saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a Æ™asa, Ya É—an girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet É—in, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buÉ—e Æ™opar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miÆ™ewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruÆ™e da sanda, Ta É—ago ta kallesu tace”Ina babar taku take Ne”? Suka haÉ—a baki wurin cewa”Tana acikin É—aki” tsohuwa tace”Ku je kuce mata ta É—auko bargo tazo, ta É—auki diyarta, ” amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin É—akin ta isar da saÆ™on zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruÆ™e da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa,

Matsa mata Hanya tsohuwa tayi”Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, ” batare da ta amsa mata ba ta nufi Æ™opar toilet É—in ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa”idan sun fito ka É—auko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita” ya amsa mata da toh,’. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace”Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya Æ™ure garin ya waye” bata rufe baki ba, sai ga hasken É—akin su Ya gauraye ko’ina, sun yi matuÆ™ar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haÉ—a baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi”bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan,” Fuskarta É—auke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet É—in ta nufi dakinta,

Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta É—aya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne,” wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin Æ´ar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na É—an kerma tace”Sanyi nake ji, ku Æ™ara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi É—umi,” Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka É—auko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin Æ™anÆ™anin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duÆ™awa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu’o’i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta É—ago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu’a suma, kowa ya É—an zuÆ™unno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taÉ—an koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage saura haris dake a tsaye sai angel dake zuÆ™unne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna, ba laifi yanzu hankalin shi ya É—an kwanta, kallon angel yae tare da cewa”Ke fa? Baki jin bacci”? daÆ™yar ta iya É—ago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faÉ—a mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta,

(Akwai Sauran free pages amma yakamata ku fara yin payment, nayi kokari dai na baku book one kyauta, nima sai ayaba mini, Masu son shiga paid group na Facebook sun tuntu6i 08169856268, for whatsapp 08103884440) 500 ne, ta bank ake turawa koda pos, in mutun baida account, idan Æ™aramar wayace in ka tura kuÉ—in zaka fadi sunan me banki ko mai pos din za’a duba. alert,*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers É—in (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button