Uncategorized

Auren Fansa Hausa Novel Complete Document

Wannan labari na AUREN FANSA kagaggen labari ne da na kirkira don Ilimantarwa,Nishadantarwa, gami da Fadakarwa.

Labarin ya kunshi Cin Amana, Son Duniya, Burin arziki da sarauta kota halin  ƙaƙa, Son Zuciya, Da kuma soyayya mai tsanani.

Sunayen mutane, garuruwa, sarauta, da kuma masana’antu da aka ambata a cikin labarin duk FICTION ne. Idan labarin yayi kamanceceniya da rayuwar ki/ka to arashi ne kar mu manta, its a fictiuos story.

NOTE:  mai karatu zai iya cin karo da abunda ya sani a cikin labarin, yana da daman tofa albarkacin bakinsa, amma banda wuce gona da iri da fatan zamu girmama juna. Littafin zai zo maku a book 1 da kuma book 2

Ina taya daukacin al’ummar musulmi barka da sallah da fatan Allah ya karbi ibadunmu ameen.

Kauyen (goruba) dake cikin garin fufore lokal gwammen a jihar Adamawa, kauye ne da Allah ya albarkaci al’ummarta da albarkar noma da kiwo, domin kab jama’ar wannan yanki manoma ne da makiyaya da ake ji dasu a fadin jihar ta Adamawa da ma kewayenta, domin a wannan kauye a ke fitar da kaso goma cikin dari na abinci  dangin masara, shinkafa, wake, dawa, alkama da dangoginsu, wanda ake amfani dasu a fadin kasar.Hakama bangaren madara,nono kindirmo,da kuma nama sunyi fice a kai. Sannan suna samar da kayan lambu dangin yayan itatuwa da kayan miya rani da damuna, Domin yana da ga cikin albarkar da Allah yaiwa wannan yanki shine ruwa da kuma damshin kasa.

 garin goruba kewaye yake da ruwa mai bada mamaki suna da tabkeken kogi wanda baya kafewa rani ko damuna, kogin ya taso ne daga kasurgumin koginnan dake kasar kamaru wanda a ke kira LODDO ya shigo ta wannan yanki ya wuce zuwa kogin jimeta sannan ya zagaya yayi connecting da wasu manya manyan kogunan Nigeria.

Alhaji Sama’ila Nomau, shine sarkin noman garin goruba, Allah yamishi arziki mai tarin yawa domin kap yankin goruba anyi ittifaqin ba wanda yakaishi arziki, ba wanda ya kaishi samun amfanin gona na rani da damuna, ba wanda dabbobinshi suke hayayyafa da habaka tamkar wutar daji kamar nashi.  Saidai kash dukiyar takasa masa rana,dukiyar takasa bashi farin ciki, dukiyar ta kasa auro masa matar daza ta haifa masa ɗa,magajinsa a cewarsa..

Shin ta ina yasamo wannan dukiya.?

Menene ginshikin wannan arziki nashi.?

Muje zuwa dan jin wannan amsa.

Yarinya ce yar kimanin shekaru uku kacal a duniya ke zaune a wani tabkeken tsakar gida tana wasa cikin farin ciki da annashuwa, jin alamun tsayuwar mota a waje yasa ta dagowa a mugun tsorace, kafun ta yi wani yunkuri taji an banko koramar kofar shigowa gidan, ba tare da ta kalli mai shigowa ba ta kwasa a 360 tayi ainahin cikin gidan sanin da ta yi cewa mutum daya ne mai irin wannan buga kofar, duk da karancin shekarunta tasan cewa baya sonta, in akwai abunda yafi tsana a duniya a zahiri to ita ce karonsu baya mata dadi domin ba karamin azaba yake gana mata ba.

 A rikice ta afka cikin gida jikinta na tsuma yayinda fitsari  ya manta wanka gajab tsabar tsoratar datayi.

” Ke ke kalau kike kam  don uwarki zaki shigowa mutane a guje haka kamar karya.”? 

KARANTA ZAFAFA 2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

Cewar tabawa da ke zaune kofar dakinta, bata kula da maganar da ake mata ba ta afka cikin kitchen inda take jiyo muryar mamanta da alama tana girkin abincin darene, da gudu ta fa da jikinta tana sauke numfashi da fadin “ammi ki boye ni ya….na… zu…wa, ta karishe harshenta na sarke wa.

Da sauri Ammin ta rikota ta na fadin ke FAREEDA waki ka tsokana ya biyoki ban hanaki  tsokanan yaran anguwa baa? sai sunji maki ciwo koh? ”  Fareeda dake takure jikin mahaifiyarta tace “ammi  ba…baaa..baaa ” tun bata karisa ba suka ji amon muryar shi yana fadin “ina take shegiya mai kama da maiyar uwarta.” ?

Dum dum dum,  haka kirjin uwar da yar yake bugawa tamkar zuciyar su zai fito waje.

“Ba magana nakeyi bane an maidani  kamar mahaukaci marar abun yi?” cewar Alaji sama’ila sarkin noma. Tabawa dake zaune kofar dakinta ta tabe baki hadi da masa inkiya da hanyar kitchen da hannuta kana tace  ” suna  ciki”. 

Fuuu ya nufi hanyar kitchen din kamar zai tashi sama, kusan karo sukayi da Fareeda da Amminta da sukuma suke kokarin fitowa,a zabure yakoma baya yana mai karewa matar tasa kallo ko kiftawa ba yayi tamkar yau ya fara ganinta. A karo na ba adadi ya kuma kallon kyakyawar fuskar  ta da suke cike da alamun fargaba karara, kana ya gangaro da idanunsa kan shirgegen cikin da ke gabanta wanda girman shi yabashi matukar mamaki.

Take zuciyar shi ta hau bugun tara tara cikin tsananin tashin hankali da birkicewa ya shiga kwala kiran sunan “tabawa tabawa” tabawa dake amsa kiran a ranta tace “andawo kuma ae sai yanda Allah yayi damu”  ta iso wurin da fadin,

“Gani alaji mai kuma ya faru? daga dawowa zaka daga mana hankali ko ruwa baka sha ba ba balle aje ga batun gaisuwa, bayan watannin uku cur daka shafe baka nan.”

Alaji sama’ila yace “wani ruwa ko gaisuwa kuma tabawa, me wannan nake gani a jikin Adama.?” ya fada yana nuna tirtsetsen cikin dake gaban Ammi wacce ke tsaye kirjinta nata luguden bugu.

“Me kuwa Alaji face abunda idanunka suka gane maka, shukar da kayiwa ban ruwa ce ta fidda yabanya” cewar tabawa tana mai yatsine fuska.

“Amma ke dai munafuka ce tabawa menene ya rage wanda baki sani ba a gidannan? meyasa baki fada min cewa adama tana da juna biyu ba koda a waya ne aida nabar duk abunda nake yi nadawo don aiwatar da abunda yadace, yanzu dubi yadda cik…

WRITTEN BY:   ASMA’U MAI UNGUWA

NOVEL NAME:   AUREN FANSA 1&2

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         530KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    15- OCTOBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Auren Fansa Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button