Uncategorized

Hira Da Matattu Part 1 (True Life Story) By Jamila Umar Tanko

 HIRA DA MATATTU …..1 (True life story)

Mun yi shekaru ba mu hadu ba sai rannan mu ka hadu a babban kotun koli ta garinmu. Da kyar na gane ta dan ni ban yi zaton zanga Sharifa a wannan qasar ba kuma a wannan waje ba, a iya sanina ma Sharifa bata zama a kasar nan, tana zama a  qasar Turai ne. 

Mace mai kyau, fara tas ‘yar gayun gaske, dirarriya , ga aji. Da farko da ta yi min magana ban yarda ita ba ce, sai da ta tabbatar min da sunanta sannan na yarda. Saboda gaba daya ta juye ta lalace, a 100% babu  80% din kamanninta, da martabarta.

“Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya busa min numfashi kuma Ya busawa Sharifa. Kawata me yake faruwa” Tambayar da na yi mata kenan. Na riqe ta ina karkarwa. 

A tunanina zata fashe da kuka sannan ta bani labari saboda duk wanda ya santa a baya ya ganta yanzu ya san bala’in da ta shiga ba dan kadan ba ne. Amma sai na ganta a daskare cikin murya mai cike da jarumta. 

Amsar da ta bani ita ta fi gigita ni,  ta ce  “Hmmm  Sharifa daga sama ta fado, ita kadai ce tal a duniyar da bata da iyaye, bata da dangi, sai Ubangijinta kuma Shi kadai Ya isar mata.”

Sai na kalle ta kallo na tuhuma, babu tantama ta hadu da cutar tabin hankali, saboda na san iyayenta, da ‘yan uwanta da suke ciki daya sun kai su ashirin da doriya, da sauran danginta na wajen uwa da na wajen Uba bila’adadin. 

Kafin in sake yin wata magana wani dattijo ya leqo ya ce “Sharifa Nasir ki shigo”

Ko sallama bata da niyyar yi min, ta zabura za ta shiga. Sai na damqi hannunta na ce “zan iya raka ki ciki?”

 Dan idan ban shiga na ga abinda zata yi ba zan iya kasa bacci saboda tunani. Sannan ko zan taimake ta yadda take juya Hausar nan wacce bana fahimta, na san bata da niyyar bani labarinta.

Bata bani amsa ba sai ta jawo hannuna da sauri muka afka cikin ofis din. Wani tsohon alqali ne wanda daga ganinsa babu wasa ya dube mu. Ya tambaya “tare ku ke ne?”

 Gabana ya fadi dan kada ace in fita. Ta bashi amsa ” Eh ranka Ya dade tare muke.”

 Nan da nan na duqa na kwashi gaisuwa sannan na sami kujera a gefe na zauna cike da ladabi da fargaba.

Ta zauna a kujerar gaban teburinsa bayan sun gaisa ya dinga miqa mata takardu yana yi mata bayanin yadda zata cike tana cikewa.  

Abinda na fahimta a ciki Sharifa tana karar wani alqalin da bai yi mata adalci a sharia ba. 

Turqashi alkali gaba daya ta maka a kotun qoli. …..

Ya tura ta wasu ofisoshi a sama inda zaa saka hannu sannan kuma zaa yi photocopy, sannan ya umarce ta da ta dawo da su. 

Mu ka fito sai dai kash nima wanda na zo gani ya iso kuma sauri yake zai fita, ya sanar da ni a waya har yana min fada akan na bata masa lokaci. 

Na dube ta na ce “fada min abinda yake faruwa a takaice..”

Tafiya take kawai tana sauri da alama bata da lokacina.

 Sai na sake zabura na ce “bani number wayarki ta Nigeria zan kira ki.”

Amsar da ta bani ita ce ” Kin taba ganin matacce ya amsa waya?”  

Na ji kaina ya sara zuciyata ta harba na waiwaye da sauri na kalli ofishin da muka fito yanzu, wannan karon qofar ofishin ma rufe da kwado babu alamar an bude shi a yau, alhali yanzu muka fito. 

Na juyo a gigice zan yi mata tambaya sai na ga wayam ta bace, na daina ganinta. Sama ta hau? A qasa  ta nutse? oho. …

“Innalilahi wa inna ilaihi rajuun” Na fada a bayyane yayin da na dafe kirjin da zuciyar take bugawa kamar zata ballo waje saboda fargaba. Zazzabi ya rufe ni, jikina zafi qau. 

Na cika da tsoro hade da da-na-sa-nin meye ma ya kawo ni cikin kotun nan a yau? 

Mutumin da na zo gani ne yake kirana a waya. Qarar wayar ma ta firgita ni, na dauka fatale ce ta dawo. …..

To be continue…

Hira Da Matattu Part 2 (True Life Story)  By Jamila Umar Tanko

Madalla da ALQALAMIN JUT

Back to top button