Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 3 Complete Novel

    WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE‼️)

           ~Unique Barakancy~      

                THREE📍

A guje yake jan motar dan ya santa sarai jinta take kamar ta tashi sama,da kyar ta yarda ta dena driving ma,saboda yanda take driving recklessly,in anyi magana kuma tace ‘who cares?’… Ta riga ta kudurta aranta cewa third encounter dinsu bazaiyi kyau ba,dan sam bata yarda da kallon dayake binta dashi ba,taso tayi taking action tin a second encounter dinnan nasu,kawai sai taga takasa komai,shiyasa ta maza ta ware batare da ta ankarar dashi ba…….

Download>>> Babban Yaya Complete Document

       Gunjin kuka taji yana tashi da dan shidewa daga cikin room din,sallama tayi a zuciya tashiga ciki,kwance ta hango wata a dukunkune kuma da alamu daga gurinta kukan ke tashi,tabe baki tayi ta karasa kan bed dinta ta shige ganin sauran yan room din sai bacci suke kamar matattu,kilama basuyi sallah ba,sai a lokacin ta kula ashe bata bar jakar a mota ba,fitowa tayi tana tinanin ta mishi text yazo ta mayar kota bar jakar kawai a gurinta? Karar shigowar kiran wayace ta katseta,taja karamin tsaki tana duba mai kiran,wani tsakin ta karaja ganin me kiran aranta tace “oh Allah wannan anacin ne Allah ya taimake shi be turo kudin ba yaga rashin mutunci”,tayi kwafa sannan ta bude message box,ai kuwa taci karo da alert din 5m din,ta wurga wayar ciki tana ce mishi dan wahala a ranta….. Katseta eesha dake kudindine tanata murkususu tayi da cewa “Dan Allah ki taimakeni ki dauko min magani na a cikin bag dinchan” ta fada da kyar tana nuna wurin da akayi hanging bags daga chan gefen dakin……

Yi tayi kamar bataji ba kuma sarai taji ta,amma ita sam ba ruwanta da abinda ya shafi wani,matsalar tace ba tata ba……  “Dan Allah,dan annabi ki taimakamin” ta sakejin eesha ta fada tana fashewa da kuka da muryarta daya dishe lokaci daya,tana kara dafe mararta dake ciwo………. Tsayuwa ta cigaba dayi,ita bata motsa ba,kuma bata juyoba,a hankali kuma ta fara takawa ta karasa gurin bags din,tashiga binsu da kallo ba tare data tambayeta wanne daga cikin bags din maganin ke ciki ba,a hankali ta gyara zaman hand gloves dinta sannan tasa hannu a wata ash bag,ta dauko maganin tana jujjuyashi a hannunta,ta gama karanta content din tsap sannan ta tabe baki tana ayyana yanda mata suke fama da ciwon mara,ita abunda bata tabayi kenan a rayuwarta,ita da girmanta ma bazata tina yaushe ta taba ciwo ba………… 

A hankali ta karaso inda eesha take kwance,gabadaya ta gama fita hayyacin ta,for once,at that moment data tabajin wani ya bata tausayi a rayuwa,girgiza kai kawai tayi ta dauko ruwa,ta zuba a cup,ta hada da drugs din tana mika mata,sai kuma hannun eesha ya fara rawa ta kasa karba…….. Zare hand glove din right hand dinta tayi ta ballo drugs din ta tallafo ta,eesha ko najinta a jikinta sai jikinta ya fara rawa,ta fara kidimewa,chan kuma sai taga jikinta ya dawo normal………

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

Bata rai tayi sosai kamar wacce ake gani,yanzu yanzu wlh saita chanjawa yarinyarnan dan ta fara mata abinda bataso a rayuwa….. Itako eesha neman ciwon maran ma tayi ta rasa gabadaya,ta tsaya tana kallon ikon Allah,tinda take a rayuwarta bata taba ganin kyawawan yatsu haka ba,ga wani design din bakin lalle me shegen kyau da aka kawata hannun dashi,ita bama wannan ba haryanzu ta kasa gane a jikin mutum take ko kuwa? Cuz laushin fatarta is on another level,wai a hakama da hijab,Kai anya kuwa?,wait if she can recall ma bata fadamata wanne daga cikin bags dinba,kuma ta ballo mata mgnin with confidence kamar tace mata eh shine”it doesn’t seem alright” eesha ta fada a ranta tana kara bin hannunta da kallo,sai kuma kawai taji an hankadata,haka ruwan da maganin duk suka bita suka zube………….

       Smiling ya cigaba dayi yana imagining how furious she would be right now?“’d’aga wayar yayi yace KHAL what’s up?”…. Abokinshi sameer ya fada yana kara dawo dashi daga duniyar tunanin daya sake tafiya bayan ya daga wayar….. “Cool SAM,ka shigo kenan” ya fada yana smirking….. “Hmmm ba dole ba,babban harka ne yashigo dani ina gayamaka guy”…. “lallai kam yayi kyau ai,ya ka barosu chan?”

“Kalau wlh mimi na gaisheka tacedai ka kita?”

“ Hhhhh ba kinta nayiba,kaima kanka kasan mace daya kawai idanuna ke ganin a duniyarnan,sauran ko wlh kallon maza duk nake musu,I’m telling you man!”……… “Uhm hakane kam,wai ina mar’atussalihar taka?….. Murmishin daya kawata kyawun fuskarshi yayi yace “Hmmm wifey ko? Yanzu ma da ita nagama waya,gabadaya zazzakar muryartace kemin yawo a kwakwalwata”…… “Hmmm ai dagani babban kaice da kake bobboyeta haka,haryanzu mamakin yanda ka mutu akanta nake,kaida ke yiwa babes yeye a school,kace kai baa haifi tsararkaba”…. Sam ya fada yana kwashewa da dariya….. “Uhm kaidai in ana sallah kawai baa magana,sai gashi Allah ya hadani da wacce nakejin zan iya sadaukar da komai nawa akanta” Ya fada da fuskar tausayi….. “Dadin abundai itama naga kamar tana yinka,tinda tana tayaka kishin kanta,kwanaki kacemin zatazo ma?,ni wlh so nake naga wacce ta susuta abokina haka”…… “Kai kai kai wannan tafi karfin idonka yaro,kai zan iya hadiyar zuciya ma in wani ya kalleta,balle ma ni kadai nake ganin abata”….. “Hhhh ashe ko zaka hadiyi zuciya very soon,dan gsky inaso naganta,kai harfa mutumina DEEN nabawa labarinka,wai in ciwo ne Allah ya yaye maka” ……. ‘Kit’ sameer yaji ya kashe wayar,kuma yasan haushi yaji dan yace yanaso ya ganta,shidai wannan so na bashi mamaki…….

         A nitse yake sakkowa daga matattakalar jirgin,haryanzu yana jinshi wani iri,sam beso tawowa ba amma bashi da yanda ya iya,mutum ne shi da besan wani abu wai shi damuwa a rayuwa ba,sannan duk girman abu baya saka shi a rai,shidai gashi nan kamar mutunmutumi,bazaka ganshi yana farin ciki ba kuma bazaka ganshi yana bacin rai ba,neutral kawai haka yake,sosai kuma yake jida kanshi da san a bashi girma,sannan ba ruwanshi da damuwar kowa as the psychopath some people think he is………. 

KARANTA LITTAFIN: “MACIJINE SHI PAGE 1-2”

Janyo hular hoodie dinshi yayi ya dan rufe fuskarshi ya cigaba da takawa grandiosely,mutane nata bin giant stature dinshi da kallo da yanayin takunshi saboda a tafiyarshi kawai zaka gane mutum ne shi kakkarfa,sai kallonshi ake duk da baa ganin fuskarsa sosai saboda shades din dayasa….. Wani special spot a parking lot din ya nufa,wani security ya taso da sauri ya miko mishi car key,nufar gurin motoci guda biyu dake gurin yayi,ya shiga black Bugatti La Voiture Noire din,yayi relaxing a driver seat  yana warming motar,shi yafi ganewa ya bar mota a parking lot din kowani airport dayake zuwa frequently,yanda duk sanda yashigo garin basai ya jira an daukeshi ba,sbd duk kudin mahaifin shi dashi karan kanshi ma bayaso a tuka shi……….

Kara gyara zama yayi yana shirin jan motar wayarshi dake hannunshi ta fara ringing,duba sunan me kiran yayi yaga ‘this woman’ kamar yanda ya mata saving,kashe wayar gabadaya yayi kawai yaja motar ya tafi………… 

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Da sallama ya shiga part din mahaifinshi kanshi a kasa,fuskarsa a hade……… “Lale lale yaron hajiya,ashe kana tafe shine ba labari?” Ta fada tana mishi murmushi me kyau……. “Yes ina tafe dama,munsame ku lfy?” Ya fada yana dago kanshi….. “Alhamdulillah,wlh munyi missing dinka sosai, kamar wanda aka yiwa abu sai ka tafi kayi zamanka a abuja,haba Deen din hajiya?”…… “Zaa gyara Insha Allah” ya fada yana zama a kan kujera….. “Toh Allah yasa,Allah ya maka albarka son”ta fada tana fita daga parlourn,binta yayi da kallo harta fice,sai gata ta dawo da masu aikin gidan,aka ko cikamishi gabanshi da kayan ciye ciye da abinci….. Be taba komai ba a abubuwan da aka jera har tadawo tace mishi dad na kiranshi…… Tashi yayi yashiga main parlor din dad da sallama a bakinsa,ya hangoshi zaune yana karanta newspaper,sai ya karasa gabanshi ya zauna a kasa…………. 

Download>>> Yar Harka Complete Document

“Daka sani a gaba baka iya gaisuwa ba bayan sallama? Ai na dauka yau dinma bazaka zoba,you would have seen the very bad side of me tinda baka da mutunci,shashasha kawai wanda besan ciwon kansa ba”…. Shidai bece komai ba yaci gaba da sauraron mahaifin nashi….. “Da izininwa kuma kayi accepting invitation din university din chan?,meya hadaka da lecturing?,so kake kawai ka kaskantar dani kamar wanda ya rasa abunyi? Abunda ya kamata ka maida hankali kayi handling sai kamai dashi kamar wasan yara,ka tsaya kana shashancin da bai kamata ba ko?Toh wlh duk wanda ya mutu saboda gangancinka kaida Allah,kuma I’ll deal with you personally idan naji wani abunda bemin ba,stupid kawai!”………. “Bawai inata magana kamin shiru ba,ina maganarmu ta kwanaki da kullum kake cemin kana nazari kamar wani sa’an ka?”…… “Na amince!” Sai a lokacin Deen ya magantu….. “Good for you,lastly kar in karajin kaje university dinchan,out my friend!” Ya fada a tsawace…….. Tashi yayi yadaga kafada irin be damuba dinnan,ya fice daga parlourn,part dinshi ya nufa straightly,Mom na mishi magana ko kulata beyiba……… 

Yana shiga ya watsa ruwa sharp sharp kamar wanda ake jira,haka kawai yaji kamar akwai wani abu da yake ce mishi yayi sauri,gabadaya kuma sai yaji hankalinshi ya koma abuja duk da yanzu aka gama bashi warning,kunna data yayi yana duba available flight to abuja na ranar,luckily ko ya samu wani nan da 30mins,ai da sauri ya dau abunda ze dauka ya kuma fita……….. 

Download>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Document

        Tin dazu yake gaban hotel din a parking space,yana zaune a cikin mota kamar me jiran wani,kamar ance ya dago kawai ya hangota a tsaye jikin irin motar jiya cikin ire Iren shigarta,shi be mayi tinanin ita dince ko a’a ba,kawai gabadaya yaji zuciyarshi ta bushe yau,yaji dole sai ya tunkareta,ya kuma fincike niqab din munafurcin nan datake sawa dan bega amfanin lullubin ba in mutum yana zuwa hotel, toh meye na rufe rufe?, sannan yanaso ya tambayeta wacece ita a yau dinnan ? Sau biyu kawai ya taba haduwa da ita,amma shi kadai yasan irin tambayoyin da yake dashi a kanta,daga shekaranjiya zuwa yau har mamakin kanshi yake yanda ya damu da sanin wani mahaluki a duniya bayan shi be damu da ko kanshi ba bare wani……. Bude murfin motar yayi ya fito,kawai sai yaga wayam kuma,gadai motar nan amma bata a tsaye,kalle kalle ya farayi yana neman inda ze hangota,amma ko giftawar mutum be gani ba……. Dafe kirjinshi yayi yace”Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha,ya Allah idan ba mutum bace karka kara nunamin ita,idan kuma mutum ce ka taimakeni ka sanar dani WACECE ITA!”……….

      

Karanta>>> Wace Ce Chapter 4 Complete Novel

~Unique Barakancy~

Back to top button