Sirrin Rike Miji

Muhimman Abubuwa 3 Da Ya Zama Tilas Namiji Yai Da Zarar Ya Kammala Jima’i

Shin bayan kun kammala yin jimai wane Matakai kuke dauka don kare Kanku daga kamuwa da cututtuka irin na infection?

Lokacin gudanar da Jima’i, akwai abubuwa da yawa dake faruwa da ba kowa ya sani ba. Duk da yin Jima’i na kara sa jindadi da nustuwa, amma akwai wasu abubuwa da ake bukatar maza su dinga yi Jim kadan bayan sun kammala Jima’i da matansu don tabbatar da lafiyar jikin su.

Wannan rubutun na yau za mu kawo muku wasu daga cikin canje-canje da maza ya dace su kula dasu bayan yin saduwa don samun lafiyar jikin su kamar yadda binciken WebMed ya gano. Ga abubuwan kamar haka;

1) Fitsari, wannan na daga cikin abinda ya kamata duk wani namiji yai Jim kadan bayan kammala jima’i. Yana da kyau mace da namiji su yi fitsari idan sun sadu da juna. A cewar binciken akwai yiwuwar samun kwayoyin halitta irin na bacteria da kan iya shiga jiki. Wanda kan iya haifar da cutuka. Don haka yin fitsari zai taimaka wajen fitar da wadannan kwayoyin cutukan infection na bacteria. Kodayaushe ya zama na kun yi fitsari da zarar kun kammala jima’i don taimakawa wajen fitar da dukkan wasu kwayoyin cuta.

2) Wanke Hannu, maza da yawa na yin Kuskure wajen wanke jikinsu da zarar sun kammala Jima’i. Yana da muhimmanci ku wanke hannayen ku da al’aurar ku Idan kun yi jima’i. Kuma ana so ita ma mace ta wanke hannayenta don hakan zai taimaka wajen wanke dukkan wasu kwayoyin cuta kamar irin wanda mukai bayani a sama.

3) Shan Ruwa, yana da muhimmanci shan ruwa Kofi daya bayan kammala Jima’i. Wannan zai taimaka muku yin fitsari da sauri wanda hakan zai sa ku yi saurin fitar da dukkan wasu kwayoyin cuta na infection da kan iya zama barazana ga lafiyar ku. Shan ruwa yana da muhimmanci sosai don yana kara Kuzarin jikin dan adam.

Wasu za su dauki wannan bayanin a matsayin mara mahimmanci, amma kuma da zarar kun saba yiwa kan ku hakan za ku yi rigakafin kamuwa da dukkan wasu kwayoyin cuta na bacteria. Da fatan za a kula sosai.

Back to top button