Hausa novels

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 91-95 By Asma Baffa

Yar Aikin Karuwai Book 2 Complete Document

🌼’YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA

BOOK 2


91-95

 

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na ‘Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace ‘yar gayu ce mace ‘yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki ‘Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da ‘boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau’in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata ‘Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni’ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai ‘Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K’ARIN BAYANI
Use*08089965176*
*07084653262*

Page naku ne
Maman Afrah
Mmn Zee
Maman Queen
Nafee
Nafisat
Fiddausi A Nagwaggo
Fancy collection $ Graphi
Dan Mai goro
Oum Ibrahim
Oum Zahra

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

 

Mun gama jin dadinmu da Nawwar munyi bacci ma wai su Gaji sun zo gari,Nawwar na tasa nace Baby na jijjiga shi ya bude idonsa nace ka tashi wai su Dagaci suna tasha yace da Daren nan bari a Kira Auta,nace Auta ana takura masa da yawa gaskiya,yace to driver baya nan,ya Kira Auta a waya Kiran duniya yana kallo yaki dagawa ya sake shigewa jikin Salma,har tace ka dauka mana yace ko mutuwa akayi wlh naji da safe ba inda zanje kawai Dan kazo a karami shike nan,Nawwar yace bari na taso shi,ya fito ya nufo part din Auta dukan kofar duniya Auta yaki tashi da Kansa ya hakura ya tafi dakko su har can,suka zo har Dagaci a Daren na fito muka gaisa na kaisu masauki nasa aka basu abincin su dama nasa anyi musu da dare,nace kuci ku huta da safe sai muyi hira,Gaji tana mamaki tace oh ji gida wai Rabi kece kika yi baki kike surutu haka wai,Mairo dai bata ce kala ba sai Kallona takeyi ita Kam yanda na mata mugun kyau kamar bata sanni ba,sai daga karshe tace Rabi Idan ana Neman kudi to a Kalli jikinki,naga wata me kama dake muka dinga haduwa a Kaduna amma masifaffiya wlh sannan na ganta a Makkah,Nace Cele ce yar uwatace Yan biyu nace,Mairo tace haba Babu banbanci fa kamar tayi yawa,nace wlh dai sunanta Rufaida, Dagaci yace Masha Allah ya tafi dakinsa da Abincinsa Gwaggo ta mike ta bishi yaran Kuma dakinsu daban.

Anci sa’a Ahsan ya kyale Cele yau ta huta bacci suka yi kawai da safe da wuri ya kawo ta sabo da ta fada masa me nace Ina korafi, Cele tana zuwa ta samu su Mairo dukkanmu a Palo har Mami,ta shigo muka gaisa ta gane Mairo ta gaishe su,nace gasu nan Cele sune na gabatar dasu a wajenta su,Omaira tana zaune Mami tace Omaira kuyi girki yau masu aiki zasu je hutu kwana biyu zasu dawo,da sauri Cele tace ni zanyi,Mami tace Dan Allah ki bar Omaira tayi ita Mami tsoron cin kayan Cele take yi,Cele ta dage ita zata yi, Mami tace to karku dafa Dani nikam zanyi nawa a bangarenta
Sabo da me Mami me Dadi fa zanyi Mami tace a’a ni nake wa Baffa girki da kaina ku dai kuyi kuci naku,Cele tace to ko lemo fa zan hada me Dadi wlh na kawo muku da sauri Mami tace dazu nayi wani yana fridge Dina kar kiyi dani,Cele bata gane Mami tsoron cin kayanta take ba ita tsakani da Allah take fada mata amma tace Sam kar a sake a dafa da ita.
Iyamami ce ta shugo wai tazo daukan jariri amma ganin su Mairo nan da nan ta hade rai tana jin haushi su an dame su sai hararsu take yi,da suka gaishe ta ma da kyar ta amsa,Cele ta kalleta kawai tace lallai matar nan bata ji warning Dina ba kenan,taje tayi girkinta ita da Omaira suka gama lemo ya dau sanyi ta ta ebi cup biyu a juck ta zuba maganin a ciki ta tona,ta shirya abinci a tire ta Kai bangaren Iyamami,Iyamami gani take isarta ce ta sa aka kawo mata ta Kira Sabreen tace suzo su ci suka farwa abinci suka ci suka shanye lemo tas
Cele ta ebi wani lemon Shima ta sa maganin tare da zubawa Gwaggo da Dagaci tace yawwa gwara ke da Mijinki ku ajiye tarihi a Anambra,Tunda na sha wahala duk Wanda naga dama sai na zuba masa.
Nasu ne kawai bata sawa ba Salma tana can tayi girkinta na musamman tare da Auta suka yi abinsu.

Also Download Banana Island Book 2 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Iyamami tayi Sallar azahar ta kwanta zata yi baccin rana tace oh yau Kuma tunanin Malam nake Allah sarki Malam ana kabari Kashi yayi fari,sai na tuna sanda Ina budurwa,Sabreen ta kwalawa Kira ta shigo tace zauna in baki labarin Aure na tun Ina budurwa,Sabreen tace ni bacci zanyi ki bari sai gobe,Iyamami tace bafa ku kadai ne Yan soyayya ba soyayyar nan ba wacce bamu yita ba,Sanda muka hadu da Malam a gona ranar ban iya kallonsa ba sai wajen Babana yaje kin san sunansa Tanko shi da ya tasa Umaimatu,Malam ya dage shi fa nan duniya ni yake so,Sabreen tace uhm sai aka bashi ke ko? a’a ai sai da ya sha fama tun karfe takwas aka Saka aurena har goma na dare ba a daura ba ana artabu,Iyamami ta daga duwawu sama ta Maida abinta,bayan an daura a Daren aka kaini dakin mijina kuka na Shashi inda kisan ana yankar naman jikina,to mazan da ba wayo Malam ba abinda ya min sai da muka kwashe shekara ko shimfida bama hadawa Ina ma yanzu ne Sabreen ai da anga soyayya,sai yau Idan na tuna asarar shekara guda Malam yayi ba tare da ya rike ko hannu na ba Ina takaicinta da zan iya dawo da shekarata yau da na dawo da ita an rama min shekarata guda da aka min asara,Sabreen tayi dariya kamar me tace Wai duk gigin tsufan ne haka ko kuwa abinda nake ji kike ji,Iyamami tace me nake ji Dan ubanki da tsufa na da komai me zan ji daga Ina baki labari karfina ai ya kare, Sabreen tace Ina da wani Bazawari Kamal matarsa daya da yaransa uku yace Idan zan aure shi zai min gidana daban Iyamami yau dai na gaji da zaman gida Namiji nake bukata yau ji nake kamar zan haukace akan Namiji inshallah yau zance ya turo iyayensa su kawo kudi duk da ba wani damuwa nayi da shi ba amma Ina so tubana ya dore gwara nayi auren Nima indai akan Antena duk ake wannan tsiyar to zan aure shi tunda yana da ita kowa Allah yayi masa tasa,Iyamami tace kiyi abinki nima da zan samu me so na auren zan Kuma,Sabreen ta Bude baki,Iyamami tace to illar babu Wanda zan samu ya Soni fata duk tayi yaushi a haka ma wai da hutu,tace Maida tsohuwa yarinya zan samu ko zan Dan murje,Sabreen tace to da matsala wlh da walakin abincin nan da mukaci tabbas badan Allah Cele ta kawo shi ba magani ta sa mana,tunda naga ta kawo mana yarinyar da bata da mutunci ai nayi mamaki,Iyamami tace karki mata sharri yarinya tayi hankali yanzu kawai abincin ne tayi shi da sinadarai masu Kara lafiya shi yasa ya tashi garkuwar jikinmu data Daina aiki yanzu duk sun gyaru sun mike,yaushe Rabon da naji irin wannan yanayin tun Ina matashiya yanzu kuwa sinadiran da suka suma a jikina sun Farka dole nayi aure a gidan nan ki tashi ki Kira min yarana.

Sabreen dariya itadai kamar me tana jin sha’awar itama a haka ta Kira Papa, yana zuwa Iyamami ta zauna tace dama Allah ne ya nufa zanyi aure,Papa ya bude baki yace wanne tsinannen tsoho ne Bazawari yake zuwa zance bamu sani ba har kuka dai daita wlh ba Dan Iskan da zai aurar mana Uwa,haba Iyamami ace aure kamarki me Zaki da shi? kaddara ta ce Allah ya kaddara cewar Iyamami,Yace to wai wanne Dan iska ne wannan? Iyamami tace talla na zaku dora a yanar gizo ko zan samu,Papa yace wlh Babu lafiya sambatun tsufa kike yi,tsufan naki ta haka ya faro Allah ya kyauta ya tashi ya fita,shi Baffa ma kin zuwa yayi Sam tasa a kirashi Papa ya fada masa yace ku Rabu da ita Idan abin yayi yawa ma kaita dawanau,Papa yace wato Kam duk duniya ba abinda ya dace da sunansa irin Dawanau,asibitin mahaukata Kai daga jin sunan tun a sunan Dawanau kasan ba hankali a cikinsa,dariya suka yi,Sabreen kuwa ita sha’awar tasa saurayinta ta Kira tace ya turo manya,ya dinga murna kamar ba gobe yace a shirye nake gobe za a kawo kudi,tace a sa bikin sati biyu nima a shirye muke,yace amma abin ya min dadi wlh dama na gama gina gidan,suna ta murna.

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Iyamami tana kwance sai Kiran Malam take Malam….Malam
Cele ce ta zago tazo ta gani ta samu Iyamami tana Kiran Malam,dariya Cele harda rike ciki,tazo ta zauna tace Iyamami zazzabi kike ne? tace Kewar mijina nake yi Idan da dama Yar nan kiyi min hotuna ki sani a yanar gizo ko zan samu me so na,Cele tace to tashi ki shirya.
Iyamami ta mike harda dakko sabuwar atamfarta ta Saka ta wani kifa uban gogoro ta tsaya kyam kamar Soja ta zazzaro Ido Cele ta dinga daukanta da waya tana cewa Kaiiiiii sai kace Yar shekara 30 kin ganki kuwa,Iyamami tace bana bukatar yabonki kawai na samu dattijo me Dan Kwari ,Sabreen tana ta murna za a kawo kudinta itama.

Dagaci dai tunda suka ci suka koshi suka koma dakinsu,Gwaggo tace a gajiye muke yau wallahi tafiyar nan ba kadan ba bacci zanyi,nace to ai ya kamata ku huta,su Gaji su dake kalau hira muke kawai da su Gwaggo suna daki,Dagaci a hankali ya Saka key yana wani sanda yanda ba me ji,ya dawo saman gadon yace kina jin abinda nake ji kuwa Babar Mairo ?Gwaggo tace yanzu nake Shirin tambayarka dama, su gwaggo sun Saba fetsararsu a gida,Dagaci yace nan a gidan mutane muke kar naji kince uhum ranki zai baci,tace to dagaci suka dinga Abu daya an zaci bacci suke yi har wurin magriba Basu fito ba Babu Wanda ya Kuma neme su sai magriba ya fito cikin shirinsa na yadi me kyau zai tafi masallaci Shima ala dole ne Dan a gidan wasu yake shi yasa,Gwaggo ce ta fito itama ansha Atamfa ta zauna,Cele tana kallon su tana dariya a ranta tace wlh da ace Abba ma tare da Umma suke sai na saka musu,Ni dai ban yarda da Cele ba Sam idonta na faka na bude Jakarta na dauke maganin gaba daya na boye.
Auta ne ya Kira Cele ta fita suna compound yace Cele tamu,tace kaga ka fadi abinda yasa ka kirani Kai ya Sosa yace Salma taki yarda Dani ko first night har yanzu ta Hana,Cele ta sha mamaki tace wai da gaske take dama? Yace ae da gaske take mana cewar Auta,Cele tace Ina zuwa ta koma ta duba Jakarta ba magani tace wai Ina maganina ne? Nace wanne? Karki Raina min hankali Rabi ki bani abina babu me bude min jaka sai ke,Nace ni ban yarda dake ba Cele baki da tsoro muguwa kowa Zaki iya sa masa,Dariya tayi tace Dan Allah ki bani Auta yace wlh baiyi first night ba Salma taki yarda,Nace gaskiya tana zaluntarsa yarinyar nan a basu su sha su biyun,aka Dan zuba a cikin cock,Na dauke ragowar na boye fafur na hana Cele maganinta sai hakura tayi ta kyaleni ta kaiwa Auta,Auta yace na gode,tace Kai jeka ka jefa kwallo a raga,Auta yace daga yau sunana Maradona, nine maradona ma yau kwallo sai ta shiga raga,Auta ya tafi Yana zuwa Salma tana Shirin bacci yana shan abinsa a hankali yasan dole ne ta karba halin Salma ya sani,ai kuwa tace bani na sha Nima,ba musu yace gashi ta zauna a gefensa tana danna laptop dinsa tana Shan abinta har ta shanye,15mnt Auta ya birkice itama tana ji amma tsoro ya hanata,Auta ya daure bai kulata ba,Salma kanta ta Sosa ta dan doki kafadar Auta tare da girgizawa tace Auta babban yaro,Auta me abin mamaki,ta sake gigirza Auta tace Auta babbar harka,uhmm su Auta masu Antena Aunty zokala inyeeee,dariya ta kwacewa Auta sosai ya shiga kyakyatawa,Salma itama dariyar tayi tare da furta your are always on my mind,Auta ya shiga sarrafata sabo da tsoro har gardama tayi taki yarda,sai da taji Sako iya Sako bata San sanda ta bada Kai ba,yau ma an sha kuka ba a cewa komai amma ba irin na farko ba.

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

Dagaci yau ya ebi harka,Iyamami da Sabreen kuwa kwana suka yi rawar Banjo a daki ba Miji.
Kwanan su Dagaci uku suka je gidan Rabi suka gani sannan suka tafi da sha tara ta arziki.
Bayan tafiyarsu da kwana biyu Cele da Ahsan suka tafi Kaduna,ita Kuma Salma mahaukacin gidansu da ya warke Yazo tare da Baso da Yan uwansa.
Suna zuwa aka sauke su na fito gaida su ni da Nawwar sai naga Alhaji Kutama tsohon Wanda aka taba daura mana aure tun da ya tafi kasar waje bai dawo ba sai takadar saki ya Aiko min da shi,suna kama da mahaukacin da ya warke da Alama Kaninsa ne,Nawwar ya kalleni yace kin sansu ne nace ae nazo na zauna,Shima Alhaji Kutama mamaki ya kamashi yace Rabi ko ba Rabi bace? Nace ita ce mana Ina yininku muka gaisa yace me kike a nan? Nace aure na haihu ne nazo gidan iyayen mijina wanka,yace wow masha Allah,Nawwar na kalla nace shine Wanda aka taba daura mana aure baya kasar ya Aiko min da takarda,Nawwar sai kishi ya tashi ya wani canja fuska yayi kicin kicin,Alhaji Mukhtar mahaukacin da ya warke yace dama itace baiwar Allah kiyi hakuri,nace ba komai ni da mijina yanzu ai ya wuce,Salma tazo suka gaisa Alhaji Mukhtar yace ga Yar Albarka itace ance me bani abinci Salma tayi murmushi tace gaskiya naji Dadi daka warke bari na Kira mijina ta mike ta Kira Auta Yazo,suka dinga kallon Auta Dan matashi an masa aure su Kam abin ya birge su,Alhaji Mukhtar yace shike nan kunga sai ku girma tare da yaranku,irinku ne za a ga danku kamar kaninku,muka yi dariya mukullum mota ya mikawa Salma yace yata ga kyautarki,Salma ta karba jiki na rawa tace mukullin mene? Kar dai kace mota? Yace itace na siya Miki,Salma murna da godiya dai ba a magana,tace Aunty ku tayani godiya,dukkan mu muka masa godiya,Auta harda rungume Salma yana mata murna,muka fito ganin mota galleliyar gaske fara sol cikin motar komai pink kalar ta mata,zata Kai ta million uku,Salma ta dinga Murna ta mikawa Auta key din tace boye min,muka kwashe da dariya Sabun shiga motar ma baza ta iya ajiye key din ba da kanta.
Baso ne ya ja Nawwar gefe yace ya maganar tamu? Nawwar yace tana nan tasan da zuwanka Karka damu.

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Bayan mun dawo Palo mun zauna dukkanmu Alhji Mukhtar yace Salma Ina matukar godiya ke da Baso Allah shine zai biya ku bani da bakin gode muku domin a zamanin Kaci nama Kuma ka bawa mahaukaci Shima yaci naman,duk abinda Kaci Mahaukaci sai yaci ba ma Almajiri ko wani ba mahaukaci fa ai sai dai Allah ya Saka muku bani da abin biyanku,yau Nima zan baku labarina kuji a takaice Wanda ko Baso ban fadawa ba,Baffa da Mami muna zaune da su, ya fara kamar haka
Mun kasance mu takwas Babar mu ta Haifa mata shida mazan biyu amma dukkan mata tun suna Yara suke mutuwa sai iya mu biyun maza Allah ya bar mata ni da Kaninsa gashi nan Alhaji Kutama,bayan Babanmu ya rasu Mama itace gatan mu muna Yara lokacin baza mu iya yiwa kanmu komai ba,gashi bata da karfi

Ganin zamu sha wahala baza mu samu ilimi ba ta fara sana’ar wanki da guga,tana yin Kuma kosai a bakin Tasha da wannan sana’ar ta dauki nauyinmu muka yi ilimin boko tun daga primary har degree ni da Dan uwana,Muna dawowa daga bautar kasa ta tattara gadonmu da muka gada ta siyar ta bawa kowa kudinsa ya fara sana’a cikin ikon Allah dukkan mu sana’ar kasuwancin ya karbe mu kudi kawai muke samu.

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Alhaji Mukhtar ya fashe da kuka da kyar ya saurara yaci gaba da labarin yace Mama tana kallo muna samun kudin bata taba cewa mu bata sisinmu ba Kuma bata fasa sana’arta da ta Saba yi ba,maimakon mu hutar da ita amma bamu yi Hakan ba,muna kallo tana wahala dai amma sai Gini ma muka yi muka yi aure tana can gidan gado Wanda aka mutu aka barmu a ciki gidane rubabbe kamar zai rufto.
Har muka Kara bunkasa tana sana’arta kyautar duniya Idan mun mata mu bata dubu biyu,Amma bata taba complain ba sai dai tayi ta sa mana Albarka tana mana nasiha akan mu dinga yin sadaka muna taimakon talakawa tana nuna mana halaye na kwarai amma kwandalar mu ba Wanda yake ci to ita kanta bata ci bare Yan uwa bare Kuma a Kai ga talaka daga mu sai matan mu sai yayanmu Sai Kuma dangin matan mu,har arziki na yasa na Gina gida a Abuja katafaren gida haka uwata tana lalataccen gidan nan ga karfinta ya kare amma tana sana’arta bamu dauke mata komai ba, Kuma Babar Matata a gidana dake Abuja take zaune har Yan uwanta uwata Kuma tana nan tana fama.

Shi Kuma Alhaji Kutama Kano yayi gida sabo da sana’arsa gwara shi ma yana Dan Kai mata shinkafa da galon din Mai watarana Kuma ya fini yawan zuwa ganinta sannan yace Idan zata sha shayi taje wajen me shayi ta karba a ajiye masa list Idan Yazo zai biya kudin,amma Idan Yazo gari me shayin ya fada masa ya dinga bala’i kenan yana cewa shi ana Tara masa bashi da yawa,sai da ya zama Mama ta Daina karba ma gaba daya,duk layin nan zaginmu ake ana tsine mana Albarka mun bar uwarmu wacce ta sha wahala da mu.

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Tun Ina zuwa ganinta bayan watanni sai na dawo ma sai na shekara bata ganni ba,shi Kuma Alhaji Kutama yakan kwashe wata shida kafin taga wani,Idan muka je tace ko baza ku bani komai ba ku dinga zuwa Ina ganinku Dan Allah ai naji dadi amma bamu canja ba.
Yace haka muka kwashe shekaru masu yawa ba kasar da bama zuwa amma ita ko aikin hajji bamu kaita ba Wanda nayi imanin da mata ta Haifa da taga gata duk da cewa mazan ma da yawa akwai masu Albarka amma imanin mata na daban ne,kwallarsa ya goge yace ana haka watarana gidan da take ciki ya rushe Allah yasa ta dan fito amma duk da haka Gini ya zubo mata a kafa har bata iya tafiya sai Jan gindi,a haka Yan unguwa suka nemi number ta,kasan mu Hausawa ko ya mutum yake da kudi to baya daga waya sai yaga dama,Kiran duniya ban daga ba,haka ma Kutama bai daga ba,har wani makwafciya tana da Hali maaikaciya ce itace ta bata daki a gidanta take zaune ita take dawainiya da ita kafar taki warkewa,gashi mu bamu je ko ganinta ba bamu San ma a wanne hali take ba,daga mu sai matanmu,tana can tana Jinya tana Shan wahala amma wlh matar nan itace take mata komai inda kasan itace ta haifeta,Mijin matar Ashiru Kuma yana bakin kokarinsa Shima,a haka kafarta har ta rube aka ce sai dai a Yanke,Mijin matar har Abuja Yazo da Kansa ya sameni ya sanar min Halin da ake ciki amma ban je ba sai dubu ashirin na bashi nace ka Kai mata aiki ya min yawa zanzo ne,Mutumin ya tsaya yana kallona yace Alhaji Mukht baza ku gama da duniya lafiya ba,tun kuna Yara ba abinda uwarku bata muku ba amma wallahi baku da Imani Kuma tun a duniya sai kunga abinda zai same ku baza ku gama da duniya lafiya,wallahi duk me wulakanta iyayensa baya kyautata musu to ya shiga uku bazai ga dai dai a rayuwarsa ba,Uwa guda wasu ma nema suke Allah ya Basu su kyautata musu su nemi lahira amma ku itace Abar wulakanta uwarku guda,tayi wanki da guga a kanku,tayi kosai har ta Kare rayuwarta a tasha ta Kare sabo da rayuwarku ta inganta amma ita kadai gidan zama ya gagari uwarku,dakin kwana ya gagareta,ga matarka ga danginta ga uwar matarka a gidanka suna abinda suka ga dama,ku hau motar da kuka ga dama kuje kasar da kuke so uwarku gini ya fado mata sabo da rashin kula gashi nan kafarta za a Yanke mata an fada muku likita ya bada option za a iya kaita Germany ba sai an Yanke ba zata warke amma Kana bani wani dubu ashirin ya watsar min da kudin ya juya ya tafi abinsa,nasan gaskiya ya fada ban iya cewa komai ba.

Sai bayan sati daya naje na iske wai makwafcin da matarsa sun siyar da wata kadararsu sun hada kudin sun kaita Germany suna can,Alhaji Kutama shi Nan take ya shiga jirgi ya bisu can ni kuwa gida na koma naci gaba da aikina.
Alhaji Kutama yana can aka mata aiki bai dawo ba sai da ta warke ras amma tace da makfacin kar ya sake ya karbi ficikar Alhaji Kutama,Alhaji Kutama ya dinga kuka yana Neman afwarta da kyar tace ta yafe masa ta hakura ba komai,suna dawowa yace zai dauketa ta koma gidansa Kano tace bata so ta gode gwara ko aikatau tayi ta ci da kanta,tace Itakam Alhaji Ashiru da matarsa Fa’iza sune yayanta yanzu gidansu taci gaba da zama,Alhaji Kutama duk sati sai yaje da shatara ta arziki yana ta bata hakuri ko yaushe yana hanya yace ya tuba ya gane gaskiya wallahi matarsa tayi masa nasiha ya gane gaskiya,haka da matar tasa suke zuwa ko yaushe har suka samu ta hakura ta sauke tace zata bisu amma ita Alhaji Ashiru da matarsa sun Fi a wajenta a hakan ma sai da Ashirun ya sa baki sannan ta bisu ta hakura suka koma part dinta daban.

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Novel

Alhaji Kutama yayi dacen mata itace ta maye gurbin bata barin Mama tayi komai jin dadin duniya ta samu,Kuma kayan sawa komai tsadarsa haka za’a siyo da ita ko me ta Saka sai an siyawa Mama na dai dai kudin,Aikin Hajji ma tare suka je itace ta kula da ita,kasa kasa Alhaji Kutama yake samun lokaci su tafi da Mama ta ga duniya,Katsam yace zaiyi aure lokacin da ya ganki kenan Rabi.

Mama tace wallahi Bai Isa yayiwa matarsa kishiya ba matukar tana Raye,yaje ya taho da dangin Babanmu aka daura aure ba sanin Mama tace wallahi ba shi ba ita sanda taji labari yana wata kasar ma tunda yaji haka shine ya rubuta takarda ya bayar aka kawo miki,Mama ce ta samu suruka ta gari bata so a mata kishiya a bata ran matar Alhaji Kutama kinji dalili,Alhaji Kutama shi matarsa Allah ya bashi ta gari.

Ni kuwa Matata kawai danginta ta sani,bayan Mama ta koma Kano Alhaji Kutama Yazo da Kansa ya dinga min fada ya kawo min babban Malami yayi wa’azi sosai a wajen na dinga kuka na daga waya na Kira Mama tana dagawa da taji nine tace waye? Nace Danki ne Mukhtar Dan Allah kiyi hakuri,tsaki ta ja tace nayi da nasanin haihuwarka Mukhtar da haifar da irinka gwara Babu,irinka dai da na haife shi gwara na zauna bani da yaro ko daya,mahaukaci ya fika amfani a wajena,Hankalina ya tashi muka tafi can Kano Amma bata saurareni ba,a takaice naje yafi sau talatin taki ta yafe min,Matata Kuma ko a jikinta,wataranar asabar na sake tafiya a Kano domin Neman gafararta shine nayi hatsari na haukace na bazama duniya,Babu Wanda ya sake ganina,ni nasan hakkin mama ne ya bini duk da cewa kaddara ko ba komai takan fadawa Dan Adam amma ni nasan hakkin Mama ne,Jama’a muyi kokari mubi iyayen mu mu kyautata musu.

Alhaji Kutama yace bayan an neme shi an rasa Mama Kuma tafi kowa damuwa tayi kuka kamar zata mutu ta dinga cewa na yafe masa duniya da lahira,Allah ka yafewa Dana Mukhtar tana kuka kullum tana masa Addua ba dare ba rana har ya warke ya bayyana tafi kowa murna,ni naci gaba da kula da dukiyarsa har ya bayyana.
Bayan ya dawo Kuma matarsa bata so taji yayi zancen mama sai dai iyayenta da Yan uwanta so take ya sake juyawa Mama baya shine ya saketa kawai ya karbe yaransa hudu maza biyu mata biyu suna gida ne sabo da Babu amfanin zama da mace irin wannan face ta kaika ga halaka, babbar ribar Namiji a rayuwa yayi dacen mata mata ta gari,kuyi kokari ku dinga nusar da mazajen ku Idan zasu kauce hanya.
Labarin ya bamu tausayi matuka haka muna ta tattaunawa Baso ya silale ya ja Nawwar, Nawwar yaje ya Kira Omaira yace tazo Baso ya a Kiranta a palon Mami,taci kwalliya cikin doguwar rigar material golden tasha kyau tayi Sallama ta shigo.

Cele kuwa gidan Kaka ta fara Kai,Kaka ya ishi Ahsan da tambaya Yaya Shari mansir? Ahsan yace lafiya,Shari sittin fa ka bi ta can? ya ka baro shi?Ahsan ya sheke da dariya yace lafiya,Yace ya kuwa kantin Yabalash?yace an tashe su,yace Allah sarki,to Darul tauhid hotel fa ana nan ana ta hada hadar dana sani? Ya aka baro dakin Allah? Bakiyya tana can da bayin Allah kwance ciki? Ahsan da ni muna ta yiwa Kaka dariya na rungume kaka nace I miss you Kaka,Ahsan harda rada min Haram,yasan halin Kaka Idan yaji shi sai yaci ubansa sol ba kyale shi yake ba shi yasa sai rada yake min,amma duk da haka Sai da Kaka yace uban me kake rada mata? Ahsan sun dade a can sannan sai gidan Umma,Umma ta dawo daga Unguwa taga motoci harda securities sun tsaya a kofar gidanta,Cele ce ta fara fitowa tace Umma sannu da zuwa muna ta jiranki, Cele ke da waye haka? tace Umma Ahsan fa,Baki ta bude tace har ya Kai haka dama,Ahsan ne ya bude ya fito,Umma ta saki baki tana Shan kallo tace yo aini wannan sai naji tsoron haskensa ke Cele bakya jin tsoro,Cele tayi dariya tace Umma tare ma muke kwana a can ta fada direct,Umma tace to fitsarriya,dariya Cele tayi tace ai gaskiya ce a ranta Kuma tace wayyo Umma Dan baki ga Jan Antena bane ni nake ganin me nake gani,a fili Kuma ta rike Hannun Ahsan tace zo muje Alhaji Ahsan me komai dozin.

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Su Raheemah sai murna suke suna kus kus akan haduwar Ahsan, Rahma tace za a ga yanga a Makarantar mu Yayar na auren balarabe wallahi na Daina kula su Iklima,Umma tace to me zai ci? Cele tace har tuwo yana ci Auta ya min maganinsa, Ahsan dariya yayi Cele ta mike ta tashi ta kawo masa lemuka da ruwan roba dake Miracle komai available baya yankewa a gidan,Ga Umma tana ta koyar motarta ita da su,Ahsan ya Kalli Umma har da zuwa ya durkusa a gabanta ya dora Kansa a cinyar Umma wai Yazo Neman Albarka,Umma kunya ta kamata tace mu bama haka,Cele ce Kuma ta zuga shi wai yaje a sa masa Albarka tun a mota ta fada masa wai haka suke yi,Umma ta mata tace baza ki fada masa mu muna da kunya bama haka,Cele tace to ai kin zama Ummansa kema,Ahsan dai ko a jikinsa ya dawo ya zauna,Umma sai kunya take ji tace kuje Wajen Abba.
Suka tashi suka je can mamaki ya kama Cele ganin ana ta ginawa Abba sabon gida me kyan gaske,Suka yi parking Abba yana wajen ginin ya bude baki ganin Cele ta fito daga shirgegiyar mota ga wasu da securities,Ahsan yana fitowa Abba yace ta tabbata ta tabbata Allahu Akbar ya daga hannu sama yana kabbara yace Allah na tuba Allah na tuba ka yafen nayi butulci gashi tun a duniya Ina gani tun kafin Cele ta karaso gabansa ya fashe da kuka,Cele tana zuwa ta rike Abba tace Abbakati namu lafiya? Wai Abbakati bai San ma yayi dariya ba jin tace masa Abbakati,tace Abbatitiya yane gini naga ana yi waye? Yace Yar Albarka Miracle washe garin ranar da kuka tafi aka kawo kayan aiki,zanen gidan ma sai da na zaba tace ana gamawa zata siya min mota Kuma ta bani jari million biyu,Cele tace taci ubanta baza ta karasa ba duk ta kwashe mana ladan komai sai dai naji tayi wlh bata Isa ba sai dai na karasa maka gidan nan Kuma motar ni zan siya maka na kaiku Makkah da su Umma haka naji har su Bilkisu ta canja musu kayan daki,wai shi Nawwar komai bata yake ne Yar iskar yarinyar nan uban mene a local government dinta Wanda mu Babu sai wadaka take yi,Abba yace ai Rabi har local government ce da ita a gidan ubanwa zata mallaki local government,Cele a ranta tace wlh na gane me yasa Nawwar yake mata komai Yar bariki ce Rabi sun gama sanin kan tsiya,Nima zan dage bari na Saba na samu Ahsan na Maida shi cikakken Sallamammen Sullutu,Cele bata San shi Nawwar dama can yana da saki hannunsa a bude yake wasu banza ma taimaka musu yake bare iyayen Rabi,Su Star duk shine ya musu komai.

Abba Bai San mene local government ba,yana ta murna yana ji a Kan farin cikinsa har kokawa ake yi, na gane gaskiya mutum kawai yace Allah ya bashi masu Albarka na gari ko mace ko Namiji,Shiga muka yi ciki Uwa tana zaune tana gyara tabarmarta data ganmu sai murna nace lallai su Uwa an saduda an San darajar Kai,to kin San darajar kanki mana tunda kema macece bazan ce kin San darajar mata ba tunda harda ke kina cikin matan,mace bata son a haifo mata kinji kunya Uwa kin dinga cin arzikin mu kenan,Har da jefar da Rabi to gashi tana muku gini tana saki cikin suturar da ku kuka kasa kuka jefar da ita,Cele ta dafa kirjinta tace Wai Uwa ni Zaki ce Zaki jefar an haife ni sai Kaka aka bawa ni ya rikeni rukon da ko Wanda ya haife ni bazai min ba,Uwa wallahi gori sai in bamu hadu ba,Uwa tayi mukus tace Dan Allah kuyi hakuri ku yafe mana gashi yanzu Rabi har abinci tasa an kawo mana ba abinda bata kawo ba,Cele tace a’a duk dai Rabi muna tare Amma bata fada min ba uhmm to nima zanyi nawa bari komai yayi settling,Ahsan ya gaida su,suka amsa da fara’a suna jansa a jiki,mun Dade a gidan sannan nace zamu koma gidan Umma tayi mana girki Abba da Uwa har bakin mota suka rako mu suna ta kallo,Ina fadawa Ahsan Rabi ce du tayi ni banyi komai ba ta kwashe ladan,dariya yayi yace karki damu zamuyi musu namu na daban ai abin alkhairi baya karewa a duniya ni San me za muyi sai lokacin Cele hankalinta ya kwanta,Yace ga Kaka ma,Cele tace wannan kafata kafarsa rayuwa sai da Kaka,bazan iya barin Kaka na tafi wata Uwa duniya ba,Ahsan yace duk yanda kike so,amma fa bazan zauna a kasar nan ba sai dai kasar mu,na yarda dai zamu na zuwa hutu mu Dade amma ni bazan siya Miki gida a Nan arewa ba bai min ba can garin su Miracle yafi min weather tayi ga ba mutane da yawa in munzo zamu zauna can,Cele tace dole dai ka siyawa kaka gida a Nan Kaduna ko ka rushe nasa ka gina masa sabo Idan yana so yayi aure ban sani ba kar na shiga hakkinsa,Ahsan dariya yayi yace ya samu me dafa masa me ma kuke cewa abinda tsoho ke sha?nace kunu,yace na’am me dafa masa kunu,nace damawa ake cewa ba dafawa ba.

Download>>> Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Baso ne a zaune ya hakimce sanye cikin Shadda milk yayi kyau matuka hancin nan dodar ka rantse bai taba Shaye Shaye ba, Omaira ce ta shigo dauke da Sallama a bakinta Baso ya kalleta da mamaki dama itace shi kyawunta ya masa yawa,Harara ya balla mata ya mata Kiran kare cwa cwa cwa da Dan bakinsa,Omaira ta bata rai ta zauna itama tace Cwa cwa cwa ta Kara da fito fiii fiit…,Baso ya kalleta da sauri tare da furta ke yane? tace Yane Kuwa,bana son yawaa tashi na ganki kinyi ko baki min ba,Omaira ta kalle shi duk kyawunta ya Rainata mata wayo ta mike a fusace ta juya tace San kowa kin Wanda ya rasa ka kiyayeni nima Yar kwaya ce,Baso yace Allah? Wacce kike sha a ciki? ai ni irinki nake nema dama yana wani karkada kafafu kamar Dan sarki dama haka yake shi gadarar masifa kamar Dan wani,magana ma Dalla Dalla yake yinta da raini yana bin mutum da wani kallon baka Isa ba sabo da bashi da kunya shi Shaye Shaye ya gama kangarar da shi,Omaira wayarta taci gaba da latsawa tana chating da saurayinta na WhatsApp,Baso ma wayarsa ya jawo ya amsa Kira sannan yaci gaba da latsawa,sunfi minti talatin a haka,Wise ce ta shigo tace ah Bason Salma dare dare wlh, amsawa Wise yayi yace sai barawo ta gidana shike nan wai sun gaisa ta wuce,Omaira ta dinga mamaki a haka gaisuwa ce,mikewa yayi ya fito da kudi sababbi dubu ashirin ya zubewa Omaira a cinyarta yace Kya sha ko Ermo ce tunda Yar kwaya ce,Omaira tace ni nace ka bani kudink…..kafin ta karasa ma yayi nisa ya fice,dama shi suke Jira zasu tafi,Nawwar yace yaya to? Baso yace yayi dai dai take Dani babban Kai ce nafi son wacce zata yi maganina,Nawwar ya kama dariya ba a gane Ina Baso ya nufa Sam,yace kyau ya masa yawa yanzu yace yafi son wacce zata gara shi,Yace Anya kuwa Baso ya Daina Shan kwayar nan ko dai har yanzu bata sake shi bane.

 

 

Masu sharhi ku dinga sharhi na gode aci gaba tam🤣

 

Click Here To Read Book 2 Page 96-100

 

AsmaBaffa

Back to top button