Uncategorized

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 48 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                           FORTY-EIGHT📍

         “Ban amince ba! Afterall babu aure a tsakaninsu!!”…..

Umm ta katse abby da deen dake shirin magana…..

     “Bangane babu aure a tsakaninsu ba?”….

Abby ya tambaya mamaki dauke akan fuskarsa…..

Deen ne ya karba da fadin;

     “Eh babu! Bayan sunyi aure a dubai, yanzu kuma ya saketa saki uku! I have the paper with me!”……

Ya fada yana zaro papern da yaba khaleel ya saketa a cikin jirgi…. 

Da sauri khaleel yace; 

         “Wallahi ba’a daura mana aure ba, abby ka manta we followed you here saboda a daura mana aure?”…..

Abby zeyi magana kenan Deen ya riga sa;

      “Karya kakeyi wallahi! Abby karka yarda dashi! Da bakinshi ya fadamin an daura auren sannan hand to hand ya bani takardar sakin!”..

Ya fada yana mikawa abby papern yana wani cin magani yana kuma bin khaleel da wani mugun kallo……

Karba abby yayi ya bude paper, karanta content din ciki yayi a fili kamar haka;

     “Ni Ibrahim khaleel Ibrahim na saki matata Fatima zainab saki uku!!”…….

Da mamaki abby ya kalli khaleel ya mika masa takardar yace;

     “Is this not your handwriting?”…..

Saboda ya taba bawa khaleel wani takarda ya cike masa a asibiti, kuma be manta handwriting dinsa ba, sak irin wannan….

A daburce khaleel yace;

    “Yes amma wallahi bansan sanda na rubuta ba abby, banma aureta ba bare in saketa, ya zaayi in auri kamar wifey in saketa?”…….

Fizge takardar Deen yayi a hannun khaleel cikin kunan rai yace;

      “A gidan ubanwa ta zama wifey din? Matarka ce zakana ce mata wani wifey? Wallahi na sake jin ka kirata da wannan sunan saina aikaka inda aka kai ubanka! Nonsense!”..

 Ruko hannun Deen abby yayi yace;

      “Ya isa haka, khaleel fadamin gaskiya an daura muku auren?”……

Girgiza kai yayi kamar zeyi kuka yace;

      “Wallahi ba’a daura ba abby, trust me da an daura bazance ka zama waliyin mu ba, ka tambayi wifey Allah baa daura ba”….

Deen ya bude baki zeyi magana mami ta daga masa hannu tace;

      “Shikenan abar zancen haka, khaleel ka dawo gobe, Insha Allah kafin nan ta warware sai a tambayeta aji”……

Godiya sosai khaleel ya musu abun tausayi sannan ya nufi kofa yana taku a hankali saboda kafarsa dake masa ciwo…..

Juyawa mami tayi ta haura sama, ganin haka yasa daddy barin parlourn shima dan yasan she needs time kafin ta bashi dama suyi magana…….

Juyawa Deen yayi shima zebi bayan mami ganin Abby a durkushe a gaban Umm da baby tee dake bacci har lokacin, Umm tayi saurin yafitoshi da hannu, komawa yayi ya tsuguna a kusa da abby suka hadu duka su ukun suna kallon baby tee that is sleeping peacefully tana sauke numfashi a hankali…..

Hannun deen Umm ta ruko tana kallon baby tee tace;

     “She became part of me tin ranar dana fara ganinta! Bansan ya’ta bace but what I was feeling for her was a motherly love har naji ina son adopting dinta ta zama ya’ta despite everything going on then, duk wannan abun ya faru ne a sanadinka saif! I just can’t thank you enough! Badan kai ba da rana irin wannan bazata taba zuwa ba! I can’t count how many times kake ce mana ka fita sabgarta but you still never give up on her! Ashe kamar kasan jininka ce? Ni ko me zan saka maka dashi ne a duniyarnan saif?”……

Murmushi Deen yayi me kayatarwa yana kallon baby tee yace;

     “I have always feel like she’s part of us that’s why I couldn’t give up on her, ashe she’s my blood! Alhamdulillah words alone can’t express my happiness! Ba sai kin sakamin da komai ba umm addu’arki kawai ta ishe ni kamar koda yaushe!”…… 

     “A’a saif just mention anything, ba lallai materialistic abu ba kawai ka fadi koma menene kakeso ni kuma zan maka”……..

       “Haba kamar ba umm dina ba! Gaskiya you should stop saying this, ni babu abinda nakeso, I have always wanted to help her fisabilillahi!”……..

Dafa kansa abby yayi yace;

     “Masha Allah! Allah ya maka albarka son! May you continue to be the apple of our eyes, mungode mungode! Allah ya saka maka da gidan aljanna Saifuddeen”….

     “Ameen dan alfarmar annabi, bari nima in kara Allah ya bashi mata tagari mar’atussaliha”……

Umm ta kara tana murmushi….

Kallonta abby yayi yace;

      “Kamar ke ko ameen”….

Shiru tayi batace komai ba, ganin haka yasa deen saurin chanja topic din yace;

     “Kallonka kawai nake Abby kai bazaka bani offer din ba, dan kar ince wani mad private jet nakeso ko?”….

Dariya Abby yayi yace;

     “Kwantar da hankalinka a sirrince naso muyi amma tinda ka fadi abinda kakeso sai ka nemo port insa a sauke maka jirgi…..

Shafa gemunsa yayi yace;

     “Ni wasa ma nake”…..

     “Ai baka isa ba because your wish has been granted!”…..

     “Talaka dani bani da gurin ajye jirgi, ni kunga tafiyata ma”…..

    “Hhhh in dan wannan ne karka damu zamu rushe daya daga cikin mansion din Umm dinka kasa a ciki”……

Dariya yayi kawai ya haura sama…..

Dawo da kallonsa kan Umm abby yayi bayan Deen ya bar parlourn, maida idonsa kan baby tee yayi sai kuma ya sake dawo dashi kan Umm, gyada kai yayi yace;

     “She’s so beautiful just like you boddina! Amma kamar hancinnan nawa ne ko?”…..

Ya fada yana jan hancin baby tee….

Gyara zamansa yayi a kasa jin taki cewa komai yace;

      “I don’t know how to explain myself boddi amma wallahi ba laifina bane! Nasan dai kinyi forcing dina inje gidan huraira on that faithful day which is the very first day I started eating her food, at times idan kikayi forcing dina inje gidan huraira wallahi bana zuwa a hotel nake kwana, saida ta kai karata sannan nake zuwa kuma shima in naje bana kulata, but that day tin daga kamshin gidan naji komai ya chanzamin, and it got worse bayan naci abincinta, it was more like I lose my memory dan bansan na sakeki ba wallahi….. I know you must have gone through a lot knowing ba abinda kikamin na sakeki amma dan Allah kiyi hakuri and I’m really sorry for all that you must have gone through…Inaso mu dau hakan a matsayin kaddararmu but I don’t know if you can find a spot in your heart to forgive me, dan Allah ki janye Allah ya isan da kika min!”……

     “It’s okay!”…

Umm ta fada a sanyaye dan tasan dagaske ba laifinsa bane aikin asiri ne kawai, and waye asiri baze iya cinsa ba tinda yaci annabinmu ma?……

       “Kice kin yafe min dan Allah boddi!”…..

     “Na yafe”…..

Cikin farin ciki Abby yace;

    “Thank you so much my one and only boddi!”…..

Yi tayi kamar bataji ba ta cigaba da caressing gashin baby tee da mayafin abayar ya zame….

       “How about we fixing our marriage dan Allah?”…..

Abby ya tambaya a hankali kamar da wani a parlourn…..

      “I am not interested!”….

Ta bashi amsa har cikin zuciyarta dan dagaske tanajin kamar bazata iya sake aure ba saboda yanda ta zama so dedicated and occupied yanzu, sometimes ko time din kanta batada shi musamman in akwai interns da take training, yanzu ma annual break tayi taking, she owns her hospital but she’s an attending physician you can expect her not to be always busy…… 

      “Why pls?”…. 

Abby ya tambaya yanajin wani iri a ransa….

      “You don’t have the right to question my opinion! Ko bappa nasan baze yimin maganar aure yanzu ba bare kai so karka kara!”…..

     “Angama ranki shi dade”….

Shiru ne ya biyo baya sai suka koma zaman kurame, shi be tashi daga inda yake ba ita kuma bata motsa ba…..

Suna a haka har baby tee ta fara motsi alamun ta tashi, abinda basu sani ba kuma tinda suka fara maganganunsu ta farka ta dai lafe ne tana jin komai, bude ido tayi tana bin parlourn da kallo, umm ce ta dagota da sauri ta zaunar da ita a kusada ita, murmushi dauke akan fuskarta tace;

     “Hey beautiful! Kin tashi? How’re you feeling now?”….

Murmushin ta maida mata tace;

      “Na tashi, I’m okay umm”…..

    “Ni ba za’a kulani ba daughter?”….

Abby ya fada yana kallonsu lovingly…..

Da sauri baby tee ta juyo jin muryar da bata kaunar ji years back….

Tinda ta tashi take jinta kamar wacce aka dawowa da lost brain, duk wata azaba da ammy ta gana mata harda abby da yayi acikin rashin sani taji komai ya dawo mata sabo fil, a hargitse ta rungume umm tana fadin;

    “Kice mishi ya tafi! Bana san ganinsa! Duka na yakeyi shida ammy! Kice ya tafi banasoooo”…..

Cikin karyewar murya kamar zeyi kuka yace;

     “Ki yafemin daughter I know I was never a good father, but wallahi it wasn’t my fault, dan Allah ki yafemin”…..

    “You’re not my father! Kace in nemi wani uba bakai ba, ka kuma koreni daga gidanka, nima banasan ganinka yanzu, umm karki sake tafiya ki barni kinga a dakin me gadi nake kwana”….

Zaro ido Umm tayi ta kalli Abby tace;

      “Whaaat? A dakin me gadi kuma? It’s that true? Muhammad kana me ya’ta take kwana a dakin me gadi?!”…..

Hawaye masu zafi ne suka shiga zubowa abby, wato shi abu irin wannan ko ba’a cikin hayyacinka kayi ba you still have to pay for it?, a raunane yace;

     “Bansani ba boddi and the day I found out har sakin huraira saida nayi”…..

Ihun da baby tee tayi ne ya katsesa….

      “Ka tafiiiiiiii, I don’t like youuu”….

     “Just excuse us!”….

Umm ta fada tana nuna masa kofa, ze sake magana kenan ta kuma tace;

         “Ka fita kawai mallam!”…..

Fita yayi hawaye na zuba a idonsa yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya ya goge huraira daga tarihin rayuwarsu, tabbas ta cucesu irin cutar da har su mutu bazasu taba mantawa ba, sannan kome zasu mata bazasu huce ba…….

Yana fita Umm ta kara rungume baby tee hawaye na sauka akan kuncinta itama, tabbas tayi farinciki mara misaltuwa da Allah ya sadata da yarta amma kuma dole taji ba dadi duba da irin wahalar da baby tee tashiga suna duniya kuma, da gatanta da komai amma tashiga gararin rayuwa haka saboda mugunta irin na dan adam, babu abinda yake daga mata hankali irin abinda ammy tace wai tayi degree a karuwanci, tsoro take kar Allah yasa hakan ya faru dan she’ll be completely shattered, budurcin dasu daddy keta hauka akai waya sani ko ya riga ya watse a titi?, bazata taba dena cewa an cuceta ba har abada, right now tana bukatar charje baby tee tsap inba hakaba hankalinta baze kwanta ba, from all indications tasan ba’a daura aurenta da khaleel ba probably Deen ne yayi provoking dinsa har yayi sakin auren da babu shi, amma zata tambayeta taji gaskiyar lamarin, indai  ba’a daura auren ba toh babu abinda ze hanata yi mata allurar bacci ta duba ta tsap ko zata samu nitsuwar zuciya……

Dagota tayi ta kamo hannunta suka haura sama…….

      “Wai dama baki bar maganarnan ba mami?”…..

Deen ya fada yana hade rai….

Ba karamin danasanin hawa saman yayi ba dan tinda ya hawo mami ke masa fada akan abinda yayiwa khaleel, be gama kwasar haushin wannan ba ta wani sako masa maganar eesha…

     “Eh ban bari tinda ka kasa fito da wacce kakeso!”….

      “Mami dan Allah ki bani time, wallahi zan kawo miki wacce nakeso har gida”….

     “It’s too late ai dan har daddy yaje ya maka tambaya a gidansu kuma an baka!”…..

Bece komai ba ya tashi yayi slamming door din ya fita rai a bace sai magana yake shi kadai, kamar shi za’a ce anyiwa tambaya without his consent? Toh wallahi yanda suka tambayo haka zasu koma su bada amsar sun fasa! Ba dai tambaya akaje akayi ba, zeyi maganinsu…..

       “Lafiyarka kake tafiya kai kadai kana surutu?”…..

Ya juyo murya umm da suka hayo da baby tee…

Kamar jira yake yace;

      “Yauwa umm dama ke nake nema, ni wallahi ba’a kyautamin a gidan nan saboda anga inada hakuri!”……

Dariya umm tayi tace;

     “A rashin marasa hakuri ba? Me akayi kuma?”……

     “Zan fadamiki privately ba a gaban kowa nake san magana ba saboda gudun raini”….

Ya fada yana hararar baby tee kamar ta mishi wani abu…..

Dariya umm ta sakeyi tace;

      “Angama bappa, idan ka shirya magana sai kazo”….

Ta fada tana jan hannun yarta suka shige bedroom dinta……

Sauka yayi yana jin haushin kin kulasa da baby tee tayi bayan yana shirin sauke haushinsa akanta, so yake ya tambayeta maganar khaleel kafin kowa, yanda ko ba’a daura ba ze zare mata ido tace an daura kuma ya saketa shikenan babu aure a tsakaninsu kuma……

Suna shiga ta zaunar da ita a bakin gado, shiga toilet tayi ta dauro alwala ta fito sannan ta cewa baby tee itama taje tayi, tashi tayi ta shiga tayi alwala itama ta fito…..

Bayan sun idar da sallah umm ta dafa kanta ta fara mata addu’a, ta dade tana mata addu’a kafin ta janye hannunta, kallonta tayi kamar ta share abinda ke ranta sai kuma taji ta kasa, dago habarta tayi tace;

      “I hope babu inda yake miki ciwo baby?”….

Girgiza mata kai tayi alamun babu…..

      “Kanki fa?”….

    “Shima bayayi”….

   “Ta bata amsa”…

   “Da gaske an daura muku aure da khaleel?!”…

Ta tambaya abinda ke ranta kai tsaye…..

Dan jimm tayi sannan tace;

      “Ba’a daura ba”…..

     “Sakaninki da wa?”…..

Umm ta sake tambaya to be assured…..

     “Allah! Wallahi ba’a daura ba sunce saida waliyyi shine khaleel ya samo wanchan mutum, shi kuma yace idan mukazo Nigeria zesa a daura mana auren”…..

Kallon cikin idonta Umm tayi ba wasa a fuskarta tace;

      “Waye wanchan mutumin?”…..

      “Abby!”….

Ta bata amsa a sanyayye…..

     “He’s your father not wanchan mutumin okay?”……

Gyada mata kai tayi alamar taji….

Shiru ne ya biyo baya chan kuma sai Umm tace;

      “Bani labarin abinda ya faru, su waye sukace saida waliyyi kuma?”…..

Bata labarin duka abinda ya faru a dubai tayi, bata boye mata komai ba har rashin lafiyar da tayi da yanda khaleel yasan abby a asibitin….

Gyada kai kawai umm take, saida ta gama tsap sannan tace;

      “A apartment daya kuka zauna keda khaleel din?”……

Shiru tayi tana jin wani iri aranta, bata taba ganin aibun zama da wanda ba muharraminka a muhalli daya koda ba’a daki daya sai yau da Umm ke tambayarta, wani irin kunya abun ya bata harta rasa me zatace……

      “Answer me!”….

Umm ta fada with a serious face….

 A hankali tace;

     “Eh but different rooms”…..

Umm batace komai ba ta tsareta da ido, daburcewa tayi tace;

      “Wallahi we stayed in different rooms and nothing happened”…..

        “Ni ban tambayeki ba!”…

Umm ta fada tana mikewa daga kan sallaya, yayinda guilty conscience ya kama baby tee, ita tasan ba abinda ya faru amma she feels like umm bata yarda ba, ita kuma so take ta yarda, kasa hakuri tayi tace;

      “Wallahi I’m not lying umm”…..

Shafa fuskarta tayi tace;

      “I know dear! But do you love khaleel?!”….

Shiru tayi tana tinanin abinda zatace, idan tace batasan khaleel tabbas tayi karya amma kunyar fada takeyi, ita fa ta rasa meyasa takejin nauyin Umm tin bayan tagano itace mahaifiyarta, kodan ta dauka maman deen ce ita?……

      “It’s okay taso muje kici abinci”….

Ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala aranta sannan ta tashi tabi bayan umm…..

      Misalin karfe goma na dare, umm ce tsaye a bakin kofar bedroom din mami, knocking tayi mami tace a shigo, shiga tayi ta tarar da mami zaune a gaban wasu takardu tana harhadasu, zama tayi a gefenta tace;

     “Ashe bakiyi bacci ba yaya”….

    “Wallahi banyi bacci ba jam, report nake hadawa akan wani case”……

     “Oh I see, Allah ya taimaka”…

     “Ameen sis, ya akayi ne? You look disturbed!”…..

     “I am wallahi and it’s about baby tee!”…..

      “What about her? Banasan yanda kike daga hankalinki akan abu”……

      “Dole in daga hankalina yaya, ni kadai nasan abubuwan dake yawo a raina”…..

    “Menene? Share with me, Insha Allah zamu samu solution”….

Numfasawa umm tayi tace;

      “Zuciyata ta kasa nitsuwa akan abinda huraira tayi, the prostitution aspect!”……

      “Insha Allah ba abinda ya faru, ni banga alamun haka ba gaskiya”…..

Mami ta fada with full hope….

      “Can you prove that?”…

Umm ta jewo mata tambayar….

Dan shiru mami tayi tace;

      “Actually I can’t! Amma haka kawai zuciyata bata je nan ba”…..

Ajiyar zuciya umm ta sauke tace;

       “Well I think I have a way to go about it!”….

     “Okay? What way?”…..

    “I don’t mind her being deflowered already maybe hakan yana cikin kaddararta, so nake kawai in sani if it’s frequent saboda gudin cututtukan zamani, ina tinanin in mata allurar bacci in binciketa!”…..

Gyada kai mami tayi cikin gamsuwa tace;

     “Ke mahaifiyarta ce ko baki mata allurar bacci ba zaki iya dubata amma hakan ma is alright”….

     “Yeah naga alamar tana jin kunyata shiyasa nakeso in dubata batareda ta sani ba”….

      “Okay toh shikenan, amma karki daga hankalinki Insha Allah it’s not what you’re thinking”….

      “Allah yasa!, bari inje, duk yanda ake ciki zan sanar dake!”….

Sallama sukayi sannan umm ta fita, tana shiga dakin ta tarar da baby tee harta fara bacci abinta, tabata kadan tayi taji jikinta da dumi, bude ido baby tee tayi taga Umm tsaye akanta..

Dora hannunta umm tayi akan goshinta tace;

    “Are you okay dear? Naji jikinki da zafi?”….

          “Kaina ke ciwo umm”….

    “Perfect!”… 

Umm ta fada aranta ganin ta samu hanya me sauki da zata mata allura, a zahiri kuma sai tace;

      “Sorry love, bari in miki allura zaki fi jindadin jikin”….

Batasan allura amma saita kasa musa mata, tana kallonta har ta hada allurar tagama, hawa kan gadan umm tayi tana fadin;

     “Just stay still hannuna bashida zafi”….

Sannan ta tsikara mata allurar a hannu, rintse ido baby tee tayi tana jiran taji azabar data sabaji in zaa mata allura, saidai tsit taji kamar an dan soka mata pin an zare, sam babu zafi, lumshe ido tayi tana ayyana rashin zafin hannun umm, bata kara 5 minutes ba wani nannauyen bacci ya dauketa……

Kallonta umm tayi taga tayi bacci, barinta tayi saida baccin ya danyi nisa atleast ta bada tazarar 20minutes sannan ta tashi ta rufe kofa……

Dawowa tayi ta zauna a gefen gadon idonta akan baby tee, sai a lokacin taji gabanta na mugun faduwa, tambayar kanta ta farayi can you really do this? What if kika tarar da abinda ze daga miki hankali?.. wata zuciyar ce tace mata you’re her mother duk abinda kika tarar you deserve to know sai ki dau kaddara…..

Rufa ido tayi tayi undressing dinta completely, bata bawa zuciyarta space na bijiro da wani tinanin ba ta hau inspecting din ko ina na jikin baby tee kamar wacce keyin biopsy, ta dade tana lalubeta kafin ta sauke wani nannauyen ajiyar zuciya hawaye ta zuba akan fuskarta ta mike, fita tayi da sauri tana jan kofar gabadaya ta manta ta maida mata da kayanta tsabar yanda ta kagu ta isa ga mami……

    Mami na zaune taji anbude kofa ba sallama, mikewa tsaye mami tayi kirjinta na buguwa ganin Umm, rungumeta mami Umm tayi tana fashewa da kuka……..

    Ya dade a kwance yana karyata zuciyarsa akan abinda take raya masa, kiri kiri yasan hakanne amma yaketa forcing kansa yayi baccin dole, har wayarsa ya dauko ya hau danne danne but still abinda yake damunsa be raguba, kasa  jurewa yayi kawai ya mike, fita yayi daga part din ya nufi part dinsu mami yana addu’ar Allah yasa basu rufe kofa ba dan ko sun rufe sai ya bubbuga tinda ya riga yazo, haka kawai yakejin baze iya bacci idan bega baby tee ba, muryarta kawai yake san ji yaji if she’s okay, da tasan yanda rashin kulashi da batayi ba dazun ya damesa data daure ko zaginsa ne tayi yaji muryarta, murda kofar yayi luckily yaji ta a bude, wani ajiyar zuciya ya sauke tare da hamdala aransa, sama ya haura direct be tsaya ko ina ba sai kofar dakin umm, ko sallama beyi ba ya murda kofar ya shiga…….

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button