Uncategorized

Wata Sabuwa: Ummi Rahab ta mallaki wayar Iphone 13

 

 A wanna satin da muka yi bankwana da shi ne kamfanin Apple suka fitar da sabuwar waya samfarin iphone 13 wadda ta karaɗe manyan kasuwannin wayoyi da shafukan sada zumunta. Ita dai wayar ta zo a nau’ika iri uku, yayin da farashin nata ya fara daga 460k zuwa 930k ya danganta da wadda zaka siya da kuma kasuwa.

Tuni dai Manyan yara yar birni suka fara rububin siyan wayar duk kuwa da dan karen tsadar da wayar ke da ita, duk da ba a fi shekara da cin kasuwar wayar kirar iphone 12 ba wacce a yanzu ta zama tsohon yayi.

Ummi Rahab jarumar masana’antar Kannywood na daya daga cikin wadanda suka mallaki wannan tsaleliyar wayar, inda ta wallafa bidiyonta riƙe da wayar kirar iphone 13 tana murnar samun wayar, sai dai hakan da ta yi ya raba hankalin mabiyanta inda wasu ke fatan alheri yayin da wasu suke maganganu marasa daɗi ga jarumar.

Idan baku manta ba a yan kwanakin da suka gaba jarumar ta samu matsala tsakaninta da mai gidanta kuma ubanta a masana’antar kuma duk a dalilin karɓar manyan kyaututtuka da ita Ummi Rahab din ta ke yi wadanda suka haɗar da; kuɗi, mota da dai sauransu.

Inda bayan wasu yan shekaru da ɓacewar Ummi Rahab din a masana’antar sai ga Adam A Zango ya dawo da ita cikin harkar, inda ya saka ta a wani fim nasa mai suna farin wata shakallo.

Sai dai daga bisani anyi rabuwa baram-baram, wadda sam babu wanda ya ji dadin hakan, duk da dai Ummi ta ce har yanzu tana ma shi kallon tamkar mahaifi yake a wajen ta. 

To anan za mu ce da Ummi Rahab abi duniya a hankali yanzu ina Maryam Yahaya, nasan kila duk tashenki ba lallai ki kaita tashe ba.

Back to top button