Sirrin Rike Miji

Amfanin Hulba Ga Mata

Daga Malama Jummai Ibrahim

 

Assalamu alaikum ‘yan uwana mata da fatan kowa tana cikin koshin lafiya Allah yasa haka amin. Yau inaso in yi wa mata ‘yan uwanan karin haske akan hulba, mata dayawa na barnata da kudi wajen gyaran fatarsu, Karin ni’imar su, gyaran gashinsu da kuma gyaran cikowar kirji.

To yanzu zan kawo muku yanda hulba ke gyara fatar jiki.

 

GYARAN FUSKA

Zaki samu garin hulbar ki dama da madara da zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki zata yi sheki zai kashe miki pinplesya gyara miki fuska kuma yana maida tsohuwa yarinya.

 

GYARAN GASHI

Wato shi gashi wani abu ne wanda ke matukar karawa mace kyau da kima shi yasa yake da kyau mu dinga gyara gashin kanmu akai akai wato kuma aduk abun gyara gashi ba kamar hulba, ga masu son gashin su ya yi tsawo da sheki zaki hada garin hulba coconut oil kigauraya sosai sai ki shafa akanki ki barshi yadadi akalla kamar, awa daya ko ma fiye da hakan, kuma zaki ringa yin hakan kama sau biyu a sati guda, sannan zaki kiyi na mako uku, yana kara tsawon gashi, kuma gashin kanki zaiyi kyau da sheki, kuma yana hana karyewar gashi. Ga masu amosani, wato dandruff, zaki hada hulba da apple cider ko ruwan khalki shafa a kanki, da san dare ki barshi har gari ya waye, gabaki daya amosari zasu mutu kuma gashin ki zai yi kyau. Gyaran CIKOWAR KIRJI

Hotunan Gaban Mace Da Namiji

Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna zuba garin hulba ciki abinci kullum sunaci don gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da cuttutuka da dama a jiki.

Ku Karanta Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Dan-adam

 

Haka kuma iya samun kindirmo mai kyau sai ku hada da hulba kuma shay ana aiki biyu ne farko gyaran kirji na biyu kuma sa ni’ima.

Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin sa da kundirmo, sannan su sami mansa suna shan spoon daya da safe daya da rana daya da marce, bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa tsuma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su hsafa wa kirjin man sa.

Magana ta karshe anan kuma abin fahimta, ba’aso mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo nakuda da gaggawa. Na biyu mata masu shayarwa suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana kara nagartaccen ruwan mama, kuma zai sa jinjiri ya kasance cikin koshin lafiya.

Fassarar Mafarkin Ruwan Sama

Back to top button