Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 73 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E73

Wanda Basu samu damar karantawa ba Jiya saboda bai buÉ—e masu ba, xan raba page É—in biyu, Sannan zan sanya Sauran pages din Na yau

Prisoners

Cike da Æ™warin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na É—an wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace”Kamar fa akwai Æ™amshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikima don ta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin Æ™opar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai

Zama Angel ta yi dirshan a saman floor, ta jingina bayanta jikin bango, Hannayenta Biyu Dafe da kanta, Ganin ta zauna yasa itama batul ɗin ta zauna, Ya kasance suna fuskantar Juna ita da Angel, Kowa Da abunda Ya ke nazari a cikim kanshi duk a ƙoƙarinsu na su gano fassarar kalaman tsohuwa Tamira,

Sun Æ™urawa Juna ido Kamar Malaman Duba, tsawon mintuna kafin Angel ta soma Æ™oÆ™arin motsa bakinta wurin furta”idan ya kasance Æ™opa ce, to kuwa mun rasa Makullin da zasu Iya buÉ—e ta ko da ace mun gano ta, saboda adadin makullin da zasu iya buÉ—e ta basu Cika ba, Babban makullin ma baya a cikin mu, idan mu ka gano Æ™opar tayaya zamu iya tattara makullan da basa atare damu”? ta jefa ma batul tambayar, numfasawa batul ta yi kafin tace”Shi ne Abunda nima nake tunani amma anya kina ganin kalaman tsohuwa tamira suna nufin Æ™ofa ce ke akwai? Kodai kawai tana nufin mu zamu haÉ—a hannu don mu ku6utar da kan mu”? Fuskarta da alamun ruÉ—u ta yi maganar, Angel tace”Abin da zaki lura anan shine, Cewa ta yi mu ne makullan buÉ—e Æ™ofar, that mean Æ™ofar daban ta ke bamu bane Æ™ofar, sai dai mu zama makullan buÉ—e ta, ni dai a hasashe na kenan” kowa kanshi ya É—auki zafi, Girgiza kai batul ta yi”A’a ni nafi hasashen Mu ne zamu sama ma kanmu Æ™opar fita idan muka haÉ—a hannu, Ba wai tana nufin Akwai Æ™opa a cikin É—akin mu ba, kaina ya fara rikicewa, Ko dai inje in yi ma su Hannah magana Su zo mu haÉ—u Kowa ya faÉ—i nashi ra’ayin? Kinsan abokin shawara nada daÉ—i, wata’Æ™il acikin su asamu wanda zai faÉ—i ainihin me ma’anar ta ke nufi tunda mu kan mu ya kulle, Amma idan aka kira su wanda su ka fi raja’a akan cewa Æ™opa ce kin ga sai mu fara binciken inda zamu ganta, Idan Allah yasa muka gano ta sai mu yi Æ™oÆ™arin tattara makullan da muka rasa!”

Angel ta gamsu da bayanin da batul ta yi mata.

“Kina ganin mu tayar da su daga bacci yanzu ko mu bari sai gobe da safe”? Batul ce ta jefa mata tambayar.

“Wani irin gobe? ai yanzun nan zamu farkar da su, Babu zancen 6ata lokaci, zuciyoyin mu da fargaba su ke buga wa, duk daÆ™iÆ™a É—aya na rayuwar mu a tsorace mu ke yin shi don haka bamu da lokacin 6ata lokaci, wannan dama ce agare mu, ba zamu yi wasa da ita ba, dama tsohuwa tamira ta faÉ—a mana cewa Ba zamu fahimci me ta ke nufi ba sai nan da wani lokaci da muka fita hayyacin mu, wasu ma su ka rasa ransu, A yanzu mun rasa mutun biyu, bamu da tabbacin ma Ƴan uwan mu maza da aka É—auka zasu dawo mana da su dukkan su ba tare da an samu wanda ya rasa ran shi ba acikin su, fita hayyaci kuma mun yi sau ba adadi, Yanzu ne yakamata mu nema wa kan mu mafita tun kafin su Æ™arar da mu don inaji araina Bamu ga komai ba, domin kuwa har yanzu muna a TAKUN FARKO na kurkukun Æ™addara, Idan har muka kai TAKUN TSAKIYA a cikin Kurkukun nan ba tare da mun ku6uta ba, bana tunanin za’a samu rai É—aya da zai rayu acikin mu In ba wani iko na Allah,’ muryarta asanyaye ta Æ™arasa maganar, Batul da ke sauraronta ganin ta Æ™are maganarta yasa ta yunÆ™ura ta miÆ™e tare da cewa”Ki taso muje mu tashe su daga baccin”! MiÆ™ewa Angel tayi tare da kallonta.

“Batul duk wani motsi namu akan idon su! Dole sai mun yi takatsantsan idan ba haka ba Garin neman gira zamu rasa ido.

“Ya zamu Yi kenan”? Acewar batul
Angel tace”Ni aganina, mu kashe hasken É—akin mu wata’Æ™il idan mu ka yi hakan ba zasu Iya ganin mu ba, Sannan Ba kowa zamu tayar daga bacci ba, Mu za6i kamar mutun uku sun isa, Kinga mun cika mu biyar kenan, Sai mu ji ra’ayoyinsu.”

“Ni nafi tunanin atada su duka saboda kowa da irin baiwar da Allah ya yi mashi, musamman Azeeza da Deeja ga kuma Parveen sannan Hannah bayan ita sai sarah zata taimaka mana Tunda tana da tsawo sosai wani abun da ba zamu Iya hangowa ba zata iya hango shi.

Girgiza kai Angel ta É—anyi”Gaskiya baza a tada azeeza ba, kinmanta bata gani idan dare yayi? Ita kuma Jamimah tayi Æ™aranta ba abunda ta sani”

“Shikenan, Zan je na kashe hasken É—akin, Kafin mu dawo tare dasu Ki BuÉ—e Æ™ofofin kowani toilets saboda mu samu hasken Fitilun da ke a cikin su Ya haskaka sashen,’
Angel ta amsa mata da toh, Juyawa batul ta yi tare da fuce wa daga Cikin sashen.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da kifa kanta Jigin bango tana jiran dawowarsu, ÆŠuff Taji hasken É—akin su Ya É—auke duhu ya gauraye ko’ina, A hanzarce ta lalubi Æ™ofofin Toilets É—in ta buÉ—e su duka, Hasken Fitilun cikinsu Ya haskaka Sashen Duk da bai wadata sosai ba”

Jin motsin shigowar su Yasa ta yi saurin fuskantar su, sai faman murza idanuwansu su ke da yatsun hannayensu, Parveen sai hamma ta ke Yi bakinta hada miyan bacci.

“Sai da nace maki ban da Azeeza meyasa kika tado ta”? rai a6ace ta yi maganar idonta akan Azeeza, da Batul ta ruÆ™o hannunta

“Bani na tada ta ba, Ina cikin tada su Deeja ta farka tana Jin fitsari shi ne na ruÆ™o hannunta muka shigo atare” mayar da idanuwanta tayi akansu, Kusan su dukane banda Jamimah ita kaÉ—aice basu Tada ta ba, tana can Æ™udundune Cikin bargo saman shimfiÉ—ar su.

“Wai lafiya aka tayar da mu daga bacci? Ko an kawo abinci ne”? Parveen ce ta yi tambayar fuskarta a yamutse,

Harara Angel ta watsa mata”Halan mafarkin shi ki ke cikin Yi aka tada ki, shiyasa kike tambayar ko an kawo abinci” Kwa6e fuska ta yi ba tare da tace komai ba, Sai faman murza ido su ke yi, fuskokin su a tur6une.

“Hakanan muna yin baccin mu mai daÉ—i an tada mu,” hannah ce ta yi maganar tana murgaÉ—a Æ™aramin bakinta.

Jan hannun Azeeza Batul ta yi zuwa cikin toilet su ka shige.

“Ganin Yadda su ke ta kwa6a magana ransu a6ace saboda an katse masu bacci, har suna cewa ta tsare su da ido, idan ba abunda zata gaya masu zasu koma É—aki su kwanta ne” Har sun yunÆ™ura zasu Juya muryar batul ta katse masu hanzarinsu da cewa”AN SAMU ƘOPAR DA ZAMU GUDU” A ruÉ—e Suka dakata da yin tafiyar suna kallonta, tamkar saukar aradu Haka maganar ta dirar masu acikin kunnuwan su, wani irin kallon rainin wayau su ke binta da shi, Æ™arasa fitowa ta yi daga Cikin toilet É—in hannunta ruÆ™e dana Azeeza.

“Idan ku ka natsu zamu Yi maku bayanin komai” ga dukkan alamu sun shiga ruÉ—ani duba da irin kallon da su ke yi mata.

“Wannan maganar daga jinta a cikin mafarki ake yinta ba’a gaske ba” Hibba ce ta yi maganar, idanuwanta kamar na mashayin giya.

Sarah tace”Nima nafi tunanin mafarki ne mu ke yi, idan har ta tabbata dagaske mu ke ganin batul da ta yi maganar to kuwa tabbas Ganyen da muke ci ya fara zautar da ita, shiyasa ta fara mana sambatu”
Sarah na rufe baki Hannah tace”ni bazan tsaya sauraron wannan shirmen ba, Kun ga tafiyata”

ta yi magnar tare da nufar ƙopa zata fuce da sauri batul ta saki hannun azeeza tai wuff ta ruƙo wuyan rigar Hannah ta janyo ta tare da dawo da ita ta jinginar jikin bango.

Angel ta kasa kunne tana sauraron su, gani ta ke kamar ba za su iya fahimtar su ba koda ace sun faÉ—a masu, saboda basu É—auki abun serious ba.

“Kun tasa mu agaba kuna kallo kamar kun samu madubi, idan ba za ku buÉ—e baki ku yi magana ba, Ni zan koma É—aki” acewar Rubina.

“Ki yi masu bayani mana ko ni zan yi masu”? Batul ce ta yi ma Angel magana.

Gyaran murya tayi Kafin ta sassauta muryarta ta yadda sautin ba zai fita sosai ba, kamar maiyin gulma, ta soma fayyace masu komai dangane da hasashen da su ke yi akan Kalaman tsohuwa tamira.

Sun natsu suna sauraronta, Yadda suka tattara hankulan su akanta sai ta yi tsammanin ko sun Fahimci inda zancen nata ya dosa ne, sai da ta kai ƙarshen Maganar, kusan atare suka haɗa baki wurin jan tsoki.

“Kawai don ta yi kalami sai asamu Æ™ofa, sai ka ce ba ku san wacece tsohuwa tamira ba, In banda ma rainin wayau taya za’ace mune makullan buÉ—e Æ™opa? Ƙanzon kure ge ne wannan” Parveen ce ta yi maganar tana hura hanci ita ala dole an 6ata mata rai.

“Da nasan abunda zaku gaya mana kenan Allah da ban farka ba lokacin da batul taje tada ni daga bacci” acewar Eve

“Ni dama kwanakin nan ban yarda da ku ba, Ku biyun nan Batul da Angel, damuwa tasa kun fara zaucewa,” Yasmince ta yi maganar , kamar zasu rufe su da duka Kowa Da abunda ya ke furtawa, Mutun Biyu ne a cikin su basu yi magana ba, Deeja da ta jingina kanta Jikin bango ta lumshe idanuwanta sai Azeeza da ke a tsaye bakin Æ™ofar toilet, Ta kasa kunne tana sauraronsu duk bata ganin su.

“Koda ace baku yarda da maganar mu ba, Inaso ku bamu dama, Mu fara neman Æ™ofar da ke a cikin É—akin mu. Idan ba’a ganta ba ni na yarda Ku yi min duk abunda ya dace dani,” cikin sanyin murya Angel tayi masu maganar.

“Deeja! Banji kince komai ba? Ke baki faÉ—i naki ra’ayin ba, dangane da kalaman tsohuwa Tamira,”

DaÆ™yar deeja ta iya buÉ—e idanuwanta masu É—auke da bacci ta É—aura su kan fuskar Batul da ke Yi mata magana, da buÉ—ar bakin ta sai cewa ta yi”Oh wai da ba mafarki bane? Baki asake Take kallon su, Dafe kai batul tayi da hannu É—aya”Wai meye haka? Idan har ba ku É—auki maganar nan serious ba kun bamu haÉ—in kai tayaya zamu Iya ganin Æ™ofar….”

Tun kan ta Æ™arasa maganar Rubina tace”Ae ba za ku ta6a ganin Æ™ofa ba, hasashen ku akan kalaman tsohuwa tamira WasiÆ™ar jaki ce wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, in banda wahalar da kai ta ya tsohuwa Tamira zata Taimake mu? Ku yi amfani da kwakwalwarku mana, koda yake dama ba cikakken hankaline damu ba, ” Murmushin takaici Angel tasaki Jin abunda Rubina tace, wato dama basu da cikakken hankali.

Muryar azeeza ce ta janyo hankalin su ga kallonta.

“Ni ina goyan bayan maganarsu Angel, tsohuwa tamira tana son taimakon mu, kafin tabar cikin mu, Ta yi mana abubuwan da zata faranta mana rai wanda ke nuni da za ta yi kewar mu sanna ta faÉ—a mana cewa tana so wata rana mu tuna da ita acikin rayuwar mu, duk mutumin da ya furta maka wannan kalami dole asamu Æ™aunarka da tausayinka acikin zuciyarshi, yakamata muyi nazari sosai, Koda ace bazamu yarda da maganar su Angel ba dangane da hasashen su akan kalaman tsohuwa, Kada muÆ™i bin maganarsu Mu jaraba duba ko’ina na cikin É—akin, kafin mu yanke hukunci, Sannan inaso na tuna mana wani abu, kamar yadda Angel ta faÉ—a mana ba’a ganin wanda ya halicce mu, That mean idan zamu samu taimako daga wurin shi ba kai tsaye zai bayyana ba don ya taimake mu, sai dai Ya haÉ—a mu da wanda zai taimaka mana, ko ya fahimtar damu ta wata hanyar Kamar dai yadda Angel tayi mafarki da kalaman tsohuwa tamira……….” tun da Azeeza ta soma Yin magana Hankalinsu ya dawo kanta, Ko Æ™yafta idanuwan su basa yi, Sun natsu suna sauraronta, Musamman Angel tsabar mamaki yasa ta saki baki tana kallonta, Yarinyar Allah ya yi mata baiwa, Ita takasa fahimtar dasu yadda zasu gane sai gashi kalaman Azeeza sun yi ta’asiri acikin zukatan su.

Nauyayyiyar ajiyar Zuciya kowan nan su ya sauke, sarah tace”yanzu abunda za’ae mu fara neman Æ™ofar! idan Allah yasa aka same ta sai mu fara tunanin ta yadda zamu tattara makullan buÉ—eta,”

Atare suka haÉ—a baki wurin cewa”Haka Ya dace, ”
“ita fa azeeza da bata gani? Ko dai in kai ta É—aki ta kwanta”? Deeja ce ta yi maganar.

Tun kafin Wani ya bata amsa Azeeza ta bubbuga Æ™afafuwanta Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”wlh ba in da zan je, dani za’ayi komai kawai don anga bana Iya gani shine za’a ware ni” ganin zata ja masu hayaniya yasa Angel yin saurin kai hannu ta janyota zuwa jikinta, ta rungumeta tana faÉ—in”Its okey azeezata, Ai dole ma ayi tafiyar nan da ke, kwantar da hankalin ki” ajiyar zuciya azeeza ta sauke tare da sanya hannayenta Biyu ta Æ™anÆ™ame Angel.

“Kafin Mu fara bincike, Yakamata Mu fara Yin addu’a akan Allah ya bamu Ikon ganota Cikin sauÆ™i,” Angel ce ta basu shawarar Yin hakan, atare suka É—aga hannayen su Sama ta dinga jera masu addu’o’i suna amsa mata da ameen, bayan sun kammala Hibba tace”Bafa lallai yakasance Æ™ofa ta ke nufi ba, A kalamanta, ” Batul tace”ae shiyasa zamu fara dubawa, Kunga idan ba’a samu Æ™ofar ba, sai muyi wani tunanin na daban”

Gyaran Murya Angel ta yi Hankali ya dawo kanta.

“Zamu Raba kan mu wasu zasu shiga toilets, wasu É—aki, Amma na É—aki dole su É—aga gadajen mu, don ina hasashen Æ™ofar ta sirri ce, ta in da bamu tsammani zamu Iya ganinta, don haka mu sanyawa ran mu cewa har cikin Tukunyar fulawa zamu Iya samunta, kota jikin bango, kota Æ™arÆ™ashin gado, kai harma ta inda ruwa ke bi ya wuce, amma fa Wanda zasu duba ƘarÆ™ashin gadajen mu dole su yi taka tsantsan saboda ana ganin duk wani motsin mu, don haka Na É—aki mu bari sai gobe zan shirya mana wasan Ƴar 6uya, zamu dinga shigewa da sunan mun 6oye kunga zasu yi tsammanin wasa muke Yi, ba wani abu muke nema ba”

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

(Mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button