Sirrin Rike Miji

Shawara Ga Amaryar Gobe A Gidan Mijinta

SHAWARA GA AMARYA GOBE A GIDAN MIJINTA


☖ SIRRIN RIKE MIJI ☖

AMARYA KI SANI; kamar yadda mutane suke Kai mamaci cikin kabari su tafi su barshi cikin kabarinsa haka iyaye suke Mai amarya su tafi su barta cikin dakin aurenta.
Amarya ki natsu, gabanki ya daina faduwa saboda mijinki ba Mai cutarwa bane, farin ciki yazo miki dashi, Wanda yake maida budurwa ta koma uwa bayan lokacin kadan.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

➽ KADA KI FIRGITA DA YANA DA MATA KI ZAMA…
◦WAYAYYAR MACE GIDAN MIJINKI ◦

Wayayyun Mata kanana ko manya, kishi dasu yana da wahala. Idan mace ita ba wayya bace ko in ce idan bata dage ba, domin kwace Mata miji ba wuya zai yi ba, saboda wayayyar mace ba ta jij kunya ko girman kan yiwa mijinta duk Abu na farantawa saboda haka amarya ki zama wayayyar mace.

IDAN AKA SAMU WAYAYYAR YARINYA TUNI ZATA DANNE MANYA MATA A GURIN MIJI.

Haka ma babbar mace wayayya kishi da ita yana da wahala, Domin tana gyara jikinta tana kuma tattalin mijinta, abinda zai sawa abokiyar zamanta tunanin wai me wance takewa oga ne yake irin sannan rawar jikin ?
Ko wata kasar zashi da ita yake tafiya, don Allah kema zama wayayya a gurin mijinki.

Karanta>>> Yadda Zaki Kara Girman Kugu Cikin Sauki

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓
KALAMAN SOYAYYA NA MALLAKE MIJI CIKIN SAUKI.


ANGONA, ZAMU JE KA KWANTA NA SHIRYA.
Makwancina da Kai, babu abinda nake jira sai dai ka rike min hannayena mu tafi mu kwanta, kwanciya irin jaruman maza da matayensu….. I love you…..wane.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.


ℳijina barka da shigowa, da fatan ka shigo lafiya.
▣ KE DA ℳIJINKI AMARYA ▣

➽ ki girmama shi.
➽ ki bashi muhimmanci.
➽ ki San damuwarsa da farin cikinsa.
➽ ki sa shi dariya da nishadi.
➽ ki yawaita maimaita masa Kalmar nan ta I LOVE YOU.
➽ ki dinga yawan rumgume shi.
➽ ki dinga kokarin kasancewa tare da shi matukar yana Gida.
➽ ki dinga aika masa da kalaman sirrinku na ma’aurata ta hanyar sakon waya.
➽ ki tambaye shi gamsuwar sa bayan kun kamala saduwa.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
MATATA BATA DA NI’IMA, INA SHAN WAHALA DUK SANDA ZAN SADU DA ITA BAYAN BA BUDURWA BACE

Babbar magana ance da makasau bawa, domin dai duk matar dake da wannan matsakar lallai auranta yana cikin lilo domin ni’imar mace itace ke baiwa maigida nishadin kusantarta amma in dai jiki baki da ni’ima to kuwa idan ya dosoki da bukata ki tabbatar matsuwa ce, irin haka ne ke sanyawa kina ji kina
gani namiji ya dinga miki satar kwana, mai tsananin kaunar ki ne zai furta miki wanda yaga kuwa ba zai iya ba yayi ta kyara da hantararki karshe ma ki ga ya sake ki babu laifin tsaye babu na zaune.

Karanta>>> Ga Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

YA KAMATA MA’AURATA INDA KUNA DA MATSALA SAI KU NEMA SHAWARA GA MASANA RASHIN NI’IMA

Shike sanya mace duk sanda mijinta zai kusance ta sai ya sha wahala kafin mazakutarsa ta shiga farjinta ba wai matsuwa ba ce, a’a akwai masu irin wannan halittar ta matsuwar amman kuma ai da ni’ima ba a shan wahala duk sanda za’a kusance su, don haka yar’uwa da kin jiki kandas sai ki sani da akwai damuwa ga maigida.

Amman akwai wacce zaki ji tana cewa, ai ni idan ina tafiya ma ruwa har bi na
yake yi, to ki tambaye ta wane irin ne ruwan, don wasu fa ruwan karancin
wasu sindarai ne a jikinsu wanda fa ruwan karancin wasu sinadarai ne a jikinsu wanda bature ke kira da minerals kamar vitamin C, vitamin E, zine arginene, fotic acid, vitamin B1, 2, 3 and B3 da dai sauransu ne, wasu kuma ruwa mai wari na ciwon sanyi gonorrhea- sai ace wai ni’ima akwai cikakken bayaninsu a shafin mata don haka ga macen dake da wannan matsalar ga abubuwan da zata dinga yi domin samun wadatuwar ni’ima a jikinta kamar haka.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒

❀ HADIN NI’IMA ❀

Aya
Dabino
Mazarkwaila
Hakin daka
_madara ko nono mai kyau_

*YANDA AKE YI ZAKI*

Back to top button