Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 64 By Ayshercool

Cikin hanzari Viper ya tashi ya tsaye, yana cewa “Kina ina ne? Meyake faruwa?” Sai dai still shiru ba ta ce komai ba.Su Walid ma duk suka miƙe tsaye, suna kallonsa.Walid ya ce “Yaya meyafaru Viper?””Ki yi mini magana, kina ina meyake faruwa ne?”Liti ya ce “Mai zamani menene wai?””Yarinyar nan tana cikin matsala””Subhanallah, to tana ina ne yanzu?” liti yayi maganar yana kallon sa.”Safiya ce yanzu, ko tana gida, ko hanya ko wurin aiki. Babu yadda za a yi ace a gida ne wani abu ya same ta ta kira ni, da hanya ne kuma da tuni an kai mata ɗauki, ko dai an ɗauketa ne ko kuma tana wurin aiki, wuta na ji ta ce”Hanyar fita Viper ya nufa, Walid ya riƙe shi ya ce “Ina zaka fita ka je? Ba kai yakamata ka fita ba, liti ko ɗan mama, ɗan maman ma dai, ka san wurin aikinta ai in da kuka ɗaukkota?”Ya ce “Eh oga Walid””Je ka gano mana menene yake faruwa”Ya ce “To bari na canza kaya” Viper ya cigaba da bin layin Nabila yana kira, amma shiru ba ta ɗagawa.Nabila kuwa tuni ta fice daga hayyacinta, ba ta sake sanin in da kanta yake ba.Masinja ne da shigowarsa kenan, ya ga wurin ya turnuƙe da hayaƙi, ya shiga dudduba daga ina hayaƙin yake fitowa. Cikin tsananin tashin hankali, ya nufi ƙofar office ɗin Nabila, ya din ga bubbuga ƙofar, amma ya ji ta a rufe gam, ya girgiza ya girgiza amma a rufe, ya fito ya nufi wurin masu gadi, ya na sanar da su wuta.Suka tashi gaba ɗaya suka rankaya a guje, ɗaya daga cikin su ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Nabila fa ta shigo aiki, tana ciki jama’a ku taimaka”.Nan da nan wuri ya cika da mutane, ana ta ƙoƙarin a ɓalle ƙofar a cirota, a daidai lokacin barrister Habib ya ƙaraso cikin tashin hankali, kasancewar an kira shi a waya an sanar masa.Da kyar aka ɓalle ƙofar, wani irin huci mai ɗauke da hayaƙi ya buso waje suka ja da baya, wani matashi ne ya kutsa kai, ya na nemanta, ya hangota a yashe a cikin office ɗin ga jakarta da system ɗin ta, da wayarta a wurin.Wutar ta mutu ba ta cigaba da ci ba, iya wadda ta kama ce ta haddasa hayaƙi, da huci mai zafi.A kafaɗarsa ya saɓo Nabila, yana fitowa barrister Habib ya karɓi wayar da system ɗin, yayi waje da ita. A motar barrister Habib aka saka ta, suka nufi asibiti.Barrister Kabir ma hankalin sa yayi mummunan tashi, ya din ga kiran waya, Habib ya ce masa sun tafi da ita Asibiti.Gaba ɗaya hankalin ma’aikatan wurin ya tashi, dan duk jin kan Nabila da gayunta akwai girmama mutane, ga yawan kyauta da take yi musu.Viper ya kasa zaune ya kasa tsaye, Liti da Walid ne suke ta rarrashin sa, amma ya kasa nutsuwa, sai cewa yake tafiya zai yi ya gano halin da take ciki, suka din ga kiran wayar ɗan mama, amma bai ɗaga ba.Viper ya ce “Walid, ba zan lamunci a wannan karon wannan ita ma ta rasa ranta ba, dole fa na gano halin da take ciki”Walid ya ce “Mun sani, amma ka fara bari mu ji daga bakin ɗan mama”Suna tsaka da maganar ya kira waya, Viper ya fizge wayar daga hannun liti, ya ɗaga ya ce “Kai ana ta kiranka ka ƙi ɗagawa, yaya aka yi ka sameta?””Wuta ce ta kama fa a ofishin ta, lokacin da na je an buɗe ƙofar an fito da ita, za a tafi asibiti””Dalla ba wannan na tambayeka ba, tana ina yanzu a wane hali take ciki?””Eh, sun tafi kaita Asibiti, na bi bayansu a adaidaita sahu, an kaita wani ɗaki an hana kowa shiga, haryanzu dai ina asibitin, likitocin dai ba su ce komai ba, amma dai kamar fa ba ta da rai”Ashar Viper yayi masa, ya ce “Yaya aka yi ma wuta ta kama a iya  ofishin ta kawai? Me hakan yake nufi? Likitoci sun ce ta mutun ne?”Ɗan mama ya ce “A’a ni nake tunanin hakan, bata motsi ko numfashi a yadda naga an sakata a mota wallahi da ƙyar idan ba mutuwa za ta yi ba”Liti ya ce “Ɗan mama ko ɗan shegiya, gaba ɗaya yaron nan gaɓo ne, ya za ayi ka gaya masa wannan maganar?”Walid ya karɓi wayar daga hannun Viper, ya saka a kunnensa ya ce “Ɗan mama kana ji na?””Eh oga Walid””Duk abun da ka ke ciki, ka din ga sanar da mu””To oga walid in sha Allah””Jikinta wutar ta taɓa ta ne?””A’a, ba ta ƙone ba, hayaƙi ne ya yi mata illa, wutar ma ba ta kama sosai ba””To shikenan, muna saurarenka”Walid ya kalli idon Viper, yadda ya bayyanar da matsanancin tashin hankali.”Viper, ka kwantar da hankalinka dan Allah komai zai zo da sauƙi, in sha Allah ba zata mutu ba, sai ta cika maka burinka”Jiki a sanyaye ya ce “Walid yanzu shikenan duk wanda ya raɓe ni, rayuwarsa sai ta shiga hatsari, idan ita ma ta rasa ranta fa, jikina yana bani set up ne abun nan”Liti ya ce “Kar ka zargi kanka, dama can wannan ba ta ji, kuma haryanzu ai bata fara shari’ar ka ba, balle ace saboda kai ne”Walid ya ce “Ya isa haka liti, kai abu ba ya wucewa a wurinka””Yaushe zai wuce, tun da ta munafurce ni, ta saka aka kamani”***Abba kuwa Allah ne ya tsare bai yanke jiki ya faɗi na, bayan sanar masa da cewar, gobara ta kama a ofishin Nabila tana Asibiti.Haka Nasir ma, cikin gigita da tashin hankali, ya nufi Asibitin da aka ce an kai Nabila.Likitoci sun hana kowa ya shiga, an cire mata kaya an saka mata wata gown, ana duba jikinta ko da in da ta ƙone, amma babu, sai dai ga zuciyarta na bugawa, amma babu numfashi, idan tayi kamar zata yi numfashi, sai tayi ta tari, hayaƙi na fita ta hancinta da bakinta, sai tayi ɗif.Gaba ɗaya Abba a rikice ya ƙaraso asibitin, cikin matsanancin tashin hankali Abba ya ƙarasa asibitin, zuwansa babu daɗewa Nasir ma ya ƙaraso, Abba ya nemi a bar shi ya ganta, amma aka ce ba a shiga likitoci na aiki tukuna.Abba ya ce ” ‘ya ta ce, ko me za ayi mata ayi a gabana, idan ma ta mutu ne a bari na ganta, ai ni musulmi ne na kuma yadda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau” suna ƙoƙarin lallaɓa shi ya haƙura kar ya shiga, ya burkice musu, babu shiri aka bashi damar shiga wurinta.A kwance ya tarar da ita, ana ta allurai, ya ƙarasa gaban gadon ta ya zuba mata ido, dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka, an sha wahalar ciwonta na asma sosai da sosai, sai da ta girma ta ɗan samu sassauci, tayi gado mai wahala, dan mahaifiyarta ce mai ɗauke da ciwon ta gada.Ya kalleta a kan gado, sai ya ga ta koma masa kamannin mahaifiyarta sosai da sosai, lokacin da take gadon asibiti ta riƙe hannunsa a halin rashin lafiya.Ya riƙe hannun Nabila, ya ga alamar akwai rai a jikinta, amma a galabaice take, ya daɗe yana yi mata addu’a, sannan ya tashi ya fita waje.Barrister Kabir kuwa tuni suka yi reporting wurin Jami’an tsaro, aka zo aka fara bincike a kan musababbin tashin wutar, abun bai tsaya iya nan ba, sai da aka tattare masu gadin wurin, aka tafi da su wurin ‘yan sanda domin fuskantar tuhuma.Sumayya ma tun kan ta ƙaraso asibitin take uban kuka, saboda yadda aka gaya mata faruwar abun, ta riga ta fitar da rai Nabila tana raye.Sai da Nabila ta shafe awa biyu, likitoci na procedure daban-daban a kanta, aka samu numfashinta ya dawo, sai dai a wahale take yin sa, aka fito da ita daga emergency, aka mayar da ita wani ɗakin.****Bunkure ta daki tebur ta ce “Tana raye kenan?”Mutumin gabanta ya ce “Eh ranki ya daɗe, an samu nasarar fitar da ita daga wurin, amma na samu tabbacin tana raye, bata mutu ba sai dai tana cikin mawuyacin hali””Babu ruwana da mawuyacin hali, wannan wane irin aiki ne? Yaya za ayi ni ga yadda muka yi da ku, amma abun da ku ka yi daban?””Ba daga mu bane ba ranki ya daɗe, wallahi aiki an yi shi yadda yakamata, agajin gaggawa aka kai mata shiyasa”Ta numfasa ta ce “Shikenan, zaka iya tafiya, a asibitin zan saka a ƙarasata”.***Hankalin Viper bai dawo jikinsa ba, sai da ɗan mama ya dawo, ya tabattar masa da a kan idonsa aka fito da ita, tana raye, kuma ba ta ƙone ba, ko ƙwarzane babu a jikinta.Nannauyar ajiyar zuciya Viper ya sauke, yana fatan Allah ya sa hakan, ya kuma bata lafiya.Hatta ‘yan gidan su Nabila, sai da suka tausayawa halin da take ciki, duk da ba shiri suke yi da ita ba, baba magajiya kuwa kuka ta ɗora hannu a ka ta din ga yi, ba ta san iya tashin hankalin da zata shiga ba, idan aka ce ba Nabila.Sumayya na gefen Nabilan, ta riƙe hannunta tana ta matsar hawaye, tari ne ya kuma turnuƙe ta, kawai ta yinƙura zata tashi zaune, duk suka nufo kanta, Sumayya ta riƙeta tana kiran sunanta.”Viper wuta, wani ya kulle ni ta waje, ku taimaka mini, Viper wuta” gaba ɗaya sai suka yi sak, suka zuba mata ido.Abba ya ce “Waye kuma Viper?”Cikin matsananciyar tuhuma Nasir yake bin ta da kallo, da yake ta surutai cikin fita hayyaci.Barrister Habib ma sak yayi, Sumayya ta ce “Abba sunan wani ɗan daba ne, da take bincike a kan sa, maybe tana ƙadamin aiki a kansa ne abun ya faru”Abba ya ce “Na rasa irin Arfa, wataƙila ma a dalilin wannan kwashe-kwashen nata, aka yi yinƙurin cutar da ita.Barrister Habib ya ce “Bana tunanin haka sir, maybe ƙaddara ce kawai, ai tana yawan zancen ɗan daban nan ne, ta ce Yayanta shi ne incharge na nemansa tana fatan ta taimaka masa”Nasir duk da ido yake bin su da kallo, yanayin yadda take surutan, kamar akwai sabo da kuma shaƙuwa a tsakanin su.A hankali sumayya ta ce “Masoyiyya””Na’am sumy””Na’am””Wuta aka saka mini a office ɗina, da ta tashi, na tafi da gudu na buɗe ƙofa na ji an rufe ni ta waje”Abba ya ce “A’a Arfa, Allah ne dai ya ƙaddara tashin wutar, kar ki zargi kowa”Nabila ta ce “Abba, ni fa na buɗe office ɗin da kaina, na bar key a jiki ta waje na shiga, da wutar ta tashi na je na buɗe, na ji an murɗa key ɗin sau biyu”Abba ya ce “Ki na cikin hayyacinki, kin farka gaba ɗaya?” Ta jinjina masa kai.Ya ce “Alhamdilillah” nan aka din ga jera mata sannu, duk da tana ta haki a hakan ma.***Ramma ce a tsaye, ta shirya cikin doguwar rigar abaya, ta ɗora mayafin a kanta, Abdul ya bata facemask ya ce “Saka wannan” ta karɓa ta saka, ya ce “Wow, kin yi kyau sosai beb” ta yi murmushi tare da gyara mayafinta.Ya riƙe hannunta, har cikin motarsa, da hannu ɗaya yake tuƙi, hannunsa ɗaya kuma ya riƙe nata, loka-lokaci sai ya sumbaci hannunta, yana jin wani irin so da shauƙinta yana ratsa ilahirin jikinsa.”Ni ka daina shafa mini yawu a hannu””Haba Rahama, yawun ƙauna ne fa” yayi maganar yana satar kallonta.Ta jingina da seat ɗin motar, ta numfasa ta ce “Yaushe ne bikinka, ko an yi ne?”Ya ce “A’a, ya za ai, ayi ba ki sani ba? Wai bata ƙarasa karatu ba, da an so ayi ne idan ta dawo shikenan ta tare, babanta ya ce a bari ta gama, saura 2months”Ramma ta ce “Allah sarki, ni nawa karatun ko oho, na zama karuwa””Haba rahama, dan Allah ki daina wannan maganar, ina da kyakykyawan tanadi a kan rayuwar ki da iliminki, na san na cutar da ke, amma zan gyara laifina in sha Allah” tayi masa shiru tana kallon titi.Dare ne sosai, duk sahu ya ɗauke.Ya zuba mata ido, a lokacin da take shan ice cream ɗin gabanta, ya tuna yadda yake ta fama da mahaifinsa, ya tsunduma tunanin ya zai yi ya sanar da shi batun ramma? Dan sai dai ayi wadda za ayi a kan ramma, amma bai ji duk iya bala’in da za ayi zai rabu da ita ba, ta kalleshi ta ce “Ka sha mana” yayi murmushi ya jinjina mata kai, mama ya cigaba da jujjuya cokalin.Hakan ya sanya ta fuskanci a cikin damuwa yake, ta ɗebo icecream ɗin ta kai bakinsa, ya ɗaga ido ya kalleta, ya buɗe bakinsa ya karɓa.Ya ce “Kin yafe mini dukan da nayi miki, kin daina fushi da ni?” Ta jinjina masa kai alamar eh.”To ɗaya laifin fa?””Ban yafe wannan ba” ta bashi amsa kai tsaye.”Tun da ki ka yafe wannan, wancan ma zaki yafe mini in sha Allah” ta yi shiru tana kallonsa.Sai da ta gama ciye-ciyenta son ranta, sannan ya ce ta raka shi asibitin abokinsa, zai duba wasu marasa lafiya.A zuciyarsa yake zargin kamar wani cikin ne da ramma, amma bai tabattar ba, kuma bai ambata ba, balle ta tashi hankalinta, muddin kuma ya ce zai gwada za ta gane, kuma ta daina yarda da shi, dan ce mata yai, yayi mata allurar planing, ba zata sake ɗaukar ciki ba sai allurar ta sake ta.Waɗanda ya yi wa tiyata a asibitin ya duba, sun fito take tambayarsa “Nan ne asibitinka?”Ya ce “A’a, Asibitina na can wajen gari, na kan je wasu asibitocin da aka buƙace ni, na gabatar da aiki, zan kai ki namun ma ki gani”Ramma ta ce “Naka dai””A’a namu dai, idan komai ya daidaita, ai bikinmu za ayi, na nuna wa duniya ke, komai ya wuce”Ta ce “Taɓ kwaɗo”Babu tsammani yayi karo da wata matashiyar budurwa, hannunta riƙe da ledar Pharmacy.”Ke ba kya gani ne?””Ban gane bana gani ba, kawai ka zo ka tsaya a hanya, kana rangwaɗa, da alama kai jin daɗi ne ya kawo ka asibitin ba mara lafiya ne da kai ba” Ramma ji tayi kamar ta san muryar.A fusace ya yinƙura zai yi masifa, ramma ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri, mun tsare hanya kam, Allah ya ƙara afuwa ga mara lafiyan”Sumayya ta amsa da “Amin” ta harare shi ta wuce.”Dan Allah ka din ga rage faɗa, har marasa lafiyar ma, faɗa ka ke yi musu, haba kai kuwa” ƙwafa yayi suka tafi.***Sosai Viper yake son kiran wayar Nabila, amma babu hali, dan ɗan mama ya tabattar masa da ya ga an fito da wayarta, da jakarta da system ɗin ta, wani mutum ya karɓa, amma alamu sun nuna a wurin yake aiki shi ma.Viper bai san waye ya karɓi wayar da system ɗin ba, akwai ayyukansa a cikin system ɗin ta, da suke buƙatar sirri sosai da sosai.Nasir ya karɓi system ɗin Nabila da wayoyinta a hannun barrister Habib, sai dai ya kasa buɗewa, dan bai san menene password ɗin ta ba, har su walida ya tambaya ko sun sani, suka ce ba su sani ba.Ƙaramar wayarta kawai ya iya buɗewa, sunan confidential ya fara nema, yayi sa’a ya samo lambar, sai dai ya duba lambar da aka yi saving a kan sunan, ya tarar da suna babu lamba, ya duba ya duba, amma ya rasa samun lambar, ya din ga kwafar lambobin wayar, yana dubawa a Truecaller ɗin sa, amma babu wani suspicious abu da ya samu.Yanzu tantamar da yake yi a kan Nabila, ya wuce zargi, akwai abun da take aikatawa na rashin gaskiya, ya ƙallafa ransa sai ya gano, waye wannan mutumin da ya gansu tare sau biyu.A kunne ya bar wayoyin, sai dai yadda aka din ga kira babu ƙaƙƙautawa, tun yana ɗagawa yana saka ran, zai samu wani abu na information, harya haƙura ya daina ɗagawa.Nabila ta farga da rashin wayoyinta, ta tambayi a bata wayoyinta, aka ce mata suna wurin Nasir, ta jira ya zo Asibitin ta ce ya kawo mata wayoyinta ya ce ba zai bayar ba.Cikin mamaki ta ce “Amma meysa na san za a neme ni a wayar?”Ya ce “Kina fama da kanki, uban me zaki yi da wata waya?”Sumayya ta ce “Ke ma dai arfa, uban meye a wayar ne, ki hutawa kanki ki gama farfaɗowa” kallon Nasir take yi, tana nazarin irin kallon da yake yi mata, ta fara fatan Allah ya sa ba wani abun ya gano a wayar ba.Abba ne ya shigo, suka gaggaisa, ya din ga tsokanar Sumayya tare da Nabila, ko wurin aiki Sumayya ba ta zuwa, tana liƙe a asibiti da Arfa, Sai da Nabila ta magantu a kan wurin aikin sumayya amma ta basar da ita.Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, sannan aka buɗe.Jmau’an tsaro ne da bindigogi suka fara shigowa, gaba ɗaya suka yi ƙuri da ido, suna kallonsu.Alhaji wada m karofi ne ya shigo, suka gaisa da Abba, Nasir ma ya gaishe shi.Nabila ta ce masa “Lafiya, wannan kama ni za su yi?”Yayi murmushi ya ce “Saboda ke ce Sarkin laifi ba, yaya jiki ashe haka wannan iftila’in ya faru?””To ai na ganka da yan sanda me na yi?”Yayi mata shiru, suka ƙarasa gaisawa da Abba suka gaisa, Sumayya ta ce “Ina kwana?””Lafiya ƙalau T ladan, ya gidan radio?””Yana nan sir”Nabila ta ce “Dama kin san shi?”Sumayya ta girgiza kai.Ya ce “Eh ba lallai ta sanni, amma ita muryarta sananniya ce ai, kuma kina bani labarinta ai, ko ba sumayya T ladan ba ce?”Sumayya ta jinjina kai tana murmushi.Nan yake gaya wa Abba, ai a law firm ɗin Barrister Kabir yake ganin Nabila suke gaisawa, shi yake sanar masa tsautsayin da ya faru.Nasir dai ya din ga mamakin yadda karakainar Nabila, ta kai ga ta ga sanin manyan mutane har haka, bayan ya gama duba ta, yayi musu sallama ya tafi, Nasir ma da Abba tafiyar suka yi, aka bar sauda da Sumayya, suna tafiya Saudan ma ta shura takalmanta ta fice, dama ba son zaman take yi ba.Sumayya ta kalli Nabila ta ce “Nabila na ajiye aikina fa”Nabila ta waro ido ta ce “What? Saboda me?”Sumayya ta numfasa ta ce “Hakan shi ne yafi dacewa ne””Sumayya wannan ai wauta ce, meyasa zaki ajiye aikin?””Na gaji da barazanar da ake yi mini, da tashin hankalin da ake yi mini, Allah ya taimake ni an shiga tsakanina da indabo, ya rabu da ni, amma support ɗin da muke baki, da ni da yaya murtala baki ga rashin mutuncin da ake yi mana ba, ga hantara da tsangwama. Da barazanar kora babu yau babu gobe, na ajiye musu bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abun da zai ci”Cikin matsanancin damuwa Nabila ta ce “Sumayya baki kyauta mini ba, da ki ka ɓoye mini wannan babban al’amari haka, ki rasa aikinki a dalilina, haba sumayya”.Sumayya ta yi dariya ta ce “Kar ki damu, umma ma ta sani, kuma ta bani ƙwarin gwiwa yaya murtala yana yi mana processing ɗin wani sabon gidan radio, za su bani aiki da ni da shi, shi ma baro can zai yi, su ci kansu”Cikin damuwa ta ce “Sumayya duk da haka ban ji daɗi ba, idan kuma ba a samu aikin ba fa?””Zafa a samu in sha Allah, na bawa yaya murtala cv na, ya ce mini sun yi murna sosai da jin zan koma wurinsu, sabon gidan radio ne, za a buɗe dama lawisa a ƙule take da ni, ta ƙara takura mini, saboda mutane suna yi na, sai su kwaɗa gidan radion su cinye”Nabila ta numfasa ta ce “Sai mu duƙufa addu’a masoyiyya, Allah ya sa ki samu ya tabattar da dukkanin alkhairansa””Amin, amma Nabila wannan wutar kuwa ba set up bane ba, ana sane aka sakata ba?”Nabila ta ce “Set up ne mana, sai da na shiga na zauna sannan ta kama, na taho na fita kuma, aka sakawa ƙofar key””Wa ki ke zargi?”Ta girgiza kai ta ce “Bana zargin kowa, abun da nake yi ne dai ba zan bari ba””Nabila””Na’am sumayya T ladan””Haryanzu kina zuwa in da Viper yake kuna haɗuwa?”Nabila ta kalleta ta ce “Wace irin tambaya ce wannan?””Amsa zaki bani, ba ki tambaye ni ba””Ban ga gurbin yin tambayar a nan ba, ko dai haryanzu yaudarata ki ke yi, aiki ki ke yi wa Indabo a kaina?””Ko kaɗan, indabo ma Allah ya yi mini maganinsa, ya rabani da shi, amma alamu sun nuna kina haɗuwa da Viper, da sunansa ki ka farfaɗo a bakinki””Tuhumata ki ke ko zargi?””Babu ɗaya””To idan har ba aiki ki ke yi wa wani a kaina haryanzu ba, to ki bar maganar nan”Sumayya ta ce “Shikenan, an bar ta”Likita ne ya shigo, ya kalli Nabila ya ce “Barrister jiki yayi kyau, jiya doctor yasar ya shigo, ai da na sani nayi masa magana ya duba jikin naki, idan da wani abu da zai ƙara miki””Doctor ni dai dan Allah ka sallame ni, na gaji wallahi””Ki yi haƙuri, zai sake shigowa yanzu, mun yi waya da shi, zai ga masu hawan jini kan ya wuce, kin san shi abun ne ya haɗar masa, ga siyasa ga kuma aikin likita””Ashe kuwa zaka neme ni ka rasa a asibitin nan, tafiya ta zan yi na gaji””No ba za ayi hakan ba, bari na rubuta miki sallama, Alhamdilillah ai jiki yayi kyau sosai”.Sumayya ta ce “Mun gode sosai doctor”Tashin hankalin da Indabo yake ciki a yan kwanakin nan, duk sai tsufansa ya fito, ko bacci baya iya yi sai ya sha ƙwayoyi, saboda damuwa da tashin hankali.Cikin dare ya ga kiran Wada karofi, ransa ya ɓaci kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya ɗaga ya ce “Karofi wani irin wulaƙanci ne ya sanya kake kirana ƙarfe ɗaya na dare?””Kashedi, da kuma gargaɗi, Nabila ta tsallake wannan tarkon da kuka yi mata, kamar yadda na taka maka burki a kan ƙawarta, ina mai ja maka kunne a kanta, wallahi wani abu ya samu yarinyar nan, zan yi abun da baka so””Wacece hakan?””Ka fi ni sanin wa nake magana a kai indabo, mukiyaye abun da zai zubar mana da mutunci a idon duniya a matsayin mu na ‘yan siyasa kuma sirikai da ni da kai, ba zan lamunci wani mummunan abu ya same ta ba, mu cigaba da yaƙar juna ta ƙarƙashin ƙasa kar duniya ta ji wannan labarin ka kiyaye”***Madaki ne ya lallaɓo ya fito daga cikin ɗakin da yake, yana ta kiran wayar lakwari, amma taƙi shiga.Walid ya gani a tsaye, yana kallonsa, ya tsaya cak, suna kallon kallo.Walid ya yi murmushi ya ce “Duk ƙoƙarin da ka yi, ka gaza ɓoye mamakinka na ganina madaki, wannan da uban gayyar ka gani sai yaya kenan?”.”Meya kawo ka wurina?””Ahh ai ba abun faɗa bane ba, zuwa na yi na duba ya yanayin jikinka yake? Ni na hana mai zamani zuwa wurinka, da yazo nan da wani zancen ake yi ba wannan ba.Zuwa yanzu na san kana mamakin ina lakwari, kuma ya aka yi muka san in da kake? Lakwari dai Macijin nan mai ban tsoro viper, ya saya shi a cikin raminsa, sannan indabo yanzu ba ta taka yake yi ba, dan haka yanzu zaɓi ya rage gareka kafin mai zamani ya waiwayo gareka, ko dai ka fita ka nemi madafa, waɗanda ka zalunta su ƙarasa ka, ko kuma yunwa da wannan ruɓaɓiyar ƙafar taka su ƙarasaka a wurin nan.Ba zaka yi wa mai zamani wani amfani ba, saboda ya riga ya gama da kai, iya hakan nan da ya barka azaba ce mai zaman kanta, sannan ka sani, duk in da ka motsa ka tafi, yana sane da in da ka ke, ɗaukar fansa cikin ruwan sanyi” ya ƙarasa maganar yana ciro wata zabgegiyar wuƙa daga ƙugunsa.Madaki ya zaro ido ya ce “Kar ka matso in da nake, kar ka zo in da nake” yayi maganar yana dakatar da walid, dan idan yayi kyakykyawan yinƙuri, ji yake kamar naman cinyarsa zai zaftare ya faɗi.Babu tausayi, Walida ya kwarfe shi, ya danne shi a ƙasa, ya zana masa V a gadon bayansa da wuƙar hannunsa.Ya ce “Ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaceka, to kai kuma har ka ƙarƙare rayuwarka kana dakonsa da alhakinsa a kanka da gadon bayanka. Ka shirya a kowane lokaci zamu iya yi wa waɗanda ka zalunta cunenka. Kuma ina yi maka Albishir da hukuma ta kama tabar wiwinka da ƙwayoyi, baka ga tsuntsu ba ka ga tarko madaki”***Nabila ce tsaye a falo, tana yi wa Nasir magiya.”Dan Allah Dsp ka bani wayoyina, ina buƙatar cigaba da amfani da su, ga ayyukana a ciki, amma ka riƙe mini waya da system ka hana ni”Ya kalle ta ya ce “Ba dai da wayoyin ki ke janyo wa kanki matsala ba, kin yi sallama da su, ba zaki sake riƙe waya a gidan nan ba, and beside gaba ɗaya ni ban yarda da ke ba, akwai abun da ki ke aikatawa wanda ki ke ɓoyewa”.”Dan Allah ni ka bani wayoyina, ya za ayi ka karɓe mini kayan aikina, yaya wai meyasa ka ke yi mini haka ne?””Ni ki ke ɗagawa murya haka?””To ka bani mana”Abba ne ya shigo falo ya ce “Haba arfa, daga farfaɗowarki daga ciwon ki ke ta ɗaga murya har haka, sai numfashin ya sake samun matsala””Abba kayan aikina ya ɗauke mini, ka ce ya bani wayata da system ɗina”Mama a ƙule ta ce “Dan ubanka ka bata kayanta, ƙannanka babu wanda ya isa yayi maka abun da take yi maka, da sun motsa sai hantara da zagi, amma kalli abun da take yi maka”Abba ya ce “Tsaya, Nasir meyasa zaka kaeɓe mata kaya ka hanata?””Abba nayi seizing wayoyinta ne for a while, da su take amfani take janyo mana magana, haryanzu ba a tabattar da musababbin tashin wutar nan ba, amma zai iya yiwuwa saboda abubuwan da take yi ake neman sabauta rayuwarta”.Abba ya ce “Haka ne, kana da gaskiya, amma ka yi haƙuri ka bata, ke kuma ki kiyaye da abubuwan da zaki din ga aikatawa da wayar nan, idan ba haka da kaina zan ƙwace su aikin ma ki daina yin sa. Bi shi ya baki kayanki”Nasir ya numfasa, yayi gaba ta bi bayansa, ya ɗaukko ya miƙa mata yana kallon idonta cike da tuhuma.”Wuƙa garin tone-tone take tono wuƙar yanka kanta, yaya, ina martabaka da martaba zumuncin da yake tsakanina da kai. Bana son harkar aiki ta zama tangarɗa ga wannan alaƙa da na lissafa maka, bayani ne nake yi maka da manyan baƙaƙe a kan farar takarda, sai dai ba zaka gane nufina a yanzu ba, ko dai ka bari a haka, ko kuma lokaci ya zo da fassarar da ba ita kake buƙata ba, ina fatan idan lokacin ya zo, zaka tuna wannan bayanin nawa, kuma ba zaka ga abun a bazata ba”.

Ayshercool 08081012143

Back to top button