Hausa novels

Ruwan Zuma Page 8 Hausa Novel

(08) “Mas’ud bazan yi aure ba kuma bana buk’atar yi kwata-kwata. Ya zanyi Baba ya amince da wannan niyya tawa?”  Tsayawa yayi da cin abincinsa yana kallonta cikin tausayawa, dawowanshi kenan daga University in da yake aji biyu dalilin bai samu shiga da wuri ba. Shiru yayi domin bai san wace shawara zai bata ba a wannan karon, duk wata hanya ta zillewa Baba ya tosheta domin ya nuna cewa kawai aure yake son Laila tayi. Me zasu yi? “Kawai ki koresu kamar yanda kike koran samarinki a daa, idan yaga babu masu zuwa ai ba zai ce ki fitar da miji ba. Tun shekarun baya nace miki mu gudu amma kika k’i, Wallahi a yau kika ce kin yarda zan zubar da karatuna in kaiki in da zaki yi rayuwar da babu takura ke da yaranki cikin kwanciyar hankali.” Shiru ta yi itama tana jin hayaniyar Abul da Sabrin a tsakar gida, dawowarsu daga makaranta kenan inda Abul mai kusan shekara takwas yake Primary 3, Sabrin mai shekara biyar ke Nursery 2.  Sabrin ce ta fara shigowa d’akin a guje kamar yanda ta saba, Laila ta fara mata fad’a kan ta hanata shigowa babu sallama. A nan Abul shima ya shigo bakinsa d’auke da sallama wacce Laila ta amsa bakinta d’auke da murmushi. “Baban Babanshi, har kun dawo?” Tace dashi tana mai k’ara ganin tsantsar kamannin da yake yi da mahaifinsa. “Mun dawo kuma yunwa nake ji sosai. Bari in je d’akin Ummii in d’auko mana abincinmu.” Ya fita ba tare da ya jira me uwar zata ce ba. Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e ta fara taya Sabrin cire kayan makarantarta sannan ta saka mata na gida, tana gamawa yarinyar ta k’ara fita da gudu tamkar ba yanzu aka mata magana akan hakan ba. “Yanzu Idan nayi aure wa zai rik’e yaran nan? Irin zuciya da kuma miskilancin Abul har tsoro yake bani, ga Sabrin da sam bata da nitsuwa irinta d’iya mata, Ina zan kai su? Gidan Umma zan mayar dasu ko kuma a nan gidan zan barsu alhali nasan Umma baza ta ta6a yarda da hakan ba? Tukunna ma wa zan aura cikin manemana? Duk cikinsu babu wanda zan ji dad’in zaman aurensa. Ina tsoron tashin hankali Mas’ud, bana buk’atar k’arin hakan a rayuwata, wanda nake ciki ma ya isheni.”  Bayan rasuwan Marigayi Aliyu maza suka fara kawo tayin soyayyarsu ga Laila wacce take ganinsu a matsayin mak’iyanta na ajin farko.      Yaushe mijinta ya rasu da har zasu zo suna neman aurenta? Shin zata ma iya soyayya bayan wacce suka yi da Aliyu uban ‘yayanta? Sannan Ina zata kai ‘yayanta wanda halinsu in ba ita uwarsu ba babu wanda zai iya zama dasu ba tare da anji kansu ba?  Ana haka sai ga Nazifi ya zo wanda a tunaninta ya zo ganin yara ne kamar yanda ya saba, amma bayan ya gaisa da yaran ya aikesu su kira mamansu. Bayan ta zo yake fad’a mata sirrin zuciyarsa na cewa yana sonta kuma zai rik’e su Abul tamkar ‘yayan cikinsa da yake har lokacin Muna bata haihu ba.  Abun haushi ya bata matuk’a, lokaci d’aya kuma taji wata muguwar tsanarsa a ranta, wai yayan Aliyu ne yake cewa zai aureta? Yayan Aliyu? Bata furta masa a baki ba amma daga ganin fuskarta ya gane cewa bai samu kar6uwa a gunta ba. “Nasan da wuya Iyayenki su barki zaune a haka babu aure. Ki k’arawa kanki shekara biyu zuwa uku nan gaba, nasan a nan kam ko auren dole za’a iya miki don a kawar dake daga zaman zawarci. Sai dai ki sani, kamar yanda Umma ta fad’a miki ‘yayan Aliyu baza suyi agolanci ba haka nima zan k’ara jaddada miki, wallahi bazan bari kije gidan wani da yaran nan ba. Kinga kenan nine dai wanda zai cika miki burinki wato na rayuwa tare da ‘yayanki ba tare da kin kai ruwa rana ba. Ina nan ina jiranki Laila har zuwa lokacin da zaki gane gaskiyar al’amari.”  Da haka ya barta tsaye tana jin wani tuk’uk’i a zuciyarta tamkar zata fashe tsabar bakin ciki. Wato zai yi amfani da son da take yiwa su Abul domin ta yarda ta aureshi? Saboda sun ga tana son ‘yayanta? Ina zata k’ara rayuwa da Umma a matsayin suruka da kuma Muna a matsayin kishiya bayan duk abunda ya faru tsakaninsu a baya? Sannan uwa uba, bata jin ko d’igon sonshi a zuciyarta sai ma tsanarshi da take yi daya iya zuwa mata da kalmar soyayya bayan mijinta ya rasu.   Ana haka sai ga Dr Zubair wanda har yau gurinshi take kai ‘yayanta idan basu da lafiya. Kai tsaye ta fad’a masa cewa babu aure a gabanta, amma ya nuna shi yaji ya gani zai jira har lokacin da taji tana son auren. Da yake ta sayi waya, ta nan yake kiranta lokaci-lokaci suna gaisawa ba tare da ya k’ara mata maganar soyayyar ba, amma dashi da ita sun san kiran na tuni ne a akan maganarsa. Abdul ma yana dirowa Nigeria kai tsaye ya sauk’a a gidansu Laila. Ko da ta fito tsoro ne ya kamata har ta juya da niyyar gudu amma ta tsaya da yace mata ta’aziyya yazo yi mata.  Jiki ba kwari ta dawo suka gaisa sannan ya mata ta’aziyya tare da mik’a mata tsaraba yace a bawa ‘yayansa, kuma da zarar ya huta zai dawo ya gansu.  Tun a lokacin zuciyarta ta bata cewa shima zuwa yayi kamar sauran masu zawarcinta, don haka ta k’ulla aniyar rabuwa dashi cikin sauk’i ba tare da an samu matsala kamar na wancan lokacin ba.  Sai dai duk magana da magiyar da Laila ta mishi Abdul bai daina zuwa gurinta ba, wani irin bak’in naci yake dashi kamar na hauka. Akwai ranar da yake fad’a mata cewa,  “Saboda ke har yanzu nak’i yin aure Laila, Ina ji a jikina komin daren dad’ewa zaki zama matata, kiyi hak’uri ki k’ar6i tayin soyayyta a karo na biyu.”  Maimakon hakan yasa Laila taji sonshi ko kuma ta fara kulashi, sai ya kasance haushinsa taji sosai kenan ya saka a ranshi akwai ranar da Aliyu zai saketa ko kuma ya mutu domin shi ya dawo ya aureta? Wannan soyayya ce ko k’iyayya?  Daga ranar ta daina fita gabad’aya ko da Dr Zubair ne ya zo, dalilin bata son ta yaudareshi tunda ba auren ne a gabanta ba. Sannan yawan tsayawa dasu hiran ma zai wargaza mata tsarinta na kaucewa duk wata k’ofa na aure. Sati biyu ya cika, ita da kanta ta je d’akin Baba tun kafin yayi kiranta. “Da alama kin yi za6in ko?” Shine abunda ya fara tambayarta bayan ta gaisheshi. Girgiza kai tayi sannan ta fara magana, “Baba duk cikin masu zuwa gurina har yau babu wanda ya kwanta mini a rai har nake jin zan iya zaman aure dashi, Ina so a bani dama in cigaba da karatu har Allah ya kawo wanda zuciyata ta amince dashi, wallahi Baba na maka alk’awarin zan yi auren kamar yanda kuke so. Yanzu Idan na auri wanda bana so ya zaman auren namu zai kasance? Baba kaine kake fad’a mana cewa baza ka mana auren dole ba saboda shi zaman aure an auri wanda ake so ma ana hayaniya, Ina ga kuma in an auri wanda ba’a so? Idan na auri Nazifi, Umma da matarsa kad’ai zasu hanani zaman lafiya a gidan tunda tun farko ba sona suke yi ba. Abdul kuma tun farko babu d’igon sonshi a raina Baba, kuma kai kanka kace hankalinsa bai maka ba. Dr Zubair kuma matarsa zata iya ajalina lokaci guda saboda bak’in kishinta, Ummii ta baka labarin yanda take kiran wayana tana mini kashedi tare da barazanar aikani lahira da zarar na auri mijinta, to Baba me amfanin yin auren Idan babu zaman lafiya a ciki? Me amfanin auren da washegari zaku iya zuwa yin jana’izata saboda abokiyar zama ta kasheni? Don Allah Baba ka duba lamarina da idon rahama ka ji k’aina.”  Bata tashi a gurin ba sai da Baba ya amince da k’udirinta na cigaba da karatu a nan BUK. Laila wacce bakinta yak’i rufuwa tsabar murna ta shige d’akin Ummii tana tsallen murna.  Ganinta cikin farin ciki yasa ‘yan uwanta suka fara tambayarta me yake faruwa. A nan Laila ta basu labarin cigaba da karatun da zata yi, wanda Abul cikin murna ya rungumeta yana jindad’i ba don yasan cewa hakan na nufin mamanshi baza tayi aure ba, a’a, shi farincikinta shine nasa.  Ummii bata nuna murnanta ba sai dai ta mata fatan alkhairi ta kuma k’ara da cewa, “Allah ya kawo miki miji kiyi auren da bakya so d’in.”  Ko da Umma ta samu labarin cewa Laila ta koma makaranta sai da tayi k’aramar rashin lafiya tsabar takaici, sannan ta aika Nazifi yayi magana da Baba cewa a bata Abul tunda mamanshi na makaranta, ai kuwa sai Baba ya bada amsa kamar haka; “Ai zuwa makarantarta bashi zai hanata kula da yaranta ba, domin kuwa sai ta turasu makaranta kafin itama ta tafi, sannan suna dawowa kafin su tafi islamiyya itama zata dawo. Kenan kaga har gobe suna nan tare da ita kuma ita ke kula dasu.” Wannan shine silar komawar Laila makaranta in da take karantar Phamarcy tare da Mas’ud wanda yake aji biyu. Kullum tare zasu fita kuma tare zasu dawo gida, ko Mas’ud bashi da lectures, haka zai rakata makarantar ya jira har a tashesu sannan su dawo. Wai hakan da Laila tayi duk don ta kare kanta ne daga zargin mutane, amma a hakan sai take jin cewa wai idan suka shiga makarantar watsewa suke yi kowannesu yayi hanyar ajinsa, kenan har gobe mutane na zarginta.  Hakan yasa Mas’ud yayi wasa a jarabawarsa ta shiga aji uku, sakamako na fitowa kuwa ya samu maimaita aji, wato kenan ya dawo aji d’aya da Laila wacce ta shigo aji biyun. Maimakon yaci gaba da gyara courses d’in da ya fad’i sai ya nemi ya dawo aji biyu a matsayin sabon d’alibi kamar kowa. Hakan yasa komai tare suke yi da Laila babu abunda yake rabasu. A yanda ‘yan gidan suka san Mas’ud da ilimi, sunyi mamakin yanda aka yi masa maimaita aji. Basu samu labarin cewa ya zama sabon d’alibi ba sai da ya gama komai yanda baza a iya komawa baya ba.  Laila ta yiwa Mas’ud fad’a har tayi kuka tana cewa yana wasa da damarsa don kawai ya faranta mata. Baba kam ranshi ya 6aci sosai domin cewa yayi zai hana Laila makarantar yaga yanda Mas’ud d’in zai yi idan bata yi. Wannan karon abun mamaki Ummii ce da kanta ta bawa Baba hak’uri kan ya barsu suci gaba da karatunsa tunda Allah ne ya had’a jininsu har haka. Sannan ta k’ara da cewa, “Ko bayan ranmu nasan Mas’ud zai iya rik’e Laila da ‘yayanta ba tare da sun yi maraicin iyaye ba.” Bayan gama makarantarsu Mas’ud ya wuce yin Masters a Maiduguri bayan Baba ya masa dole, ita kuma Laila ta bud’e shagon Saloon a nan k’ofar gidansu domin Baba ya hanata yin aikin gwamnati. Duk cikin gidansu babu wanda yaso hakan sai Baba wanda shi ya rage garejinsa ya mata shagon wanda ake shiga ta cikin gida. Yawanci matan aure ne masu zuwa ganin shagonta yafi sirri sannan ta iya aikinta, hakan yasa Laila ta fara yin turaren wuta, humra, kulacca da dilka tana musu talle. Da ikon Allah shagonta ya samu k’ar6uwa har Amare ke zuwa ana musu gyaran jiki. Laila na tsaka da jindad’in wannan samun cigaban ne Babanta mai dafa mata ya kwanta dama bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi ta ciwon hanta. Mutuwarshi ba k’aramin girgiza mutanen gidan yayi ba wanda shine madogaransu. Daga nan kuma zaman gidan ya daina yiwa Laila dad’i wanda hakan duk silar Madu ne, magananshi d’aya kullum tayi aure ta daina zaman kanta da ire-irensu. Wata biyu da rasuwar Baba Laila ta k’ara bud’e shagonta aka cigaba da zuwa, amma kwana d’aya da haka Madu ya kulle shagon yace bazata sake yin wata sana’a ba sai a gidan mijinta. Ko da ta samu Ummii da maganan kan a yiwa Madu fad’a ya daina shiga tsabgarta, Ummii da take cikin takaba tace, “Nima bana goyan bayan kici gaba da zama haka, ba zai yiwu a shigo cikin gidan nan ana k’irga zawarawan ciki ba. Ki nitsu ki za6i miji kiyi aure.” Bak’in cikin da Laila ta shiga a ranar ba’a magana, Abul khair ne yayi ta rarrashinta bayan yaji me yake faruwa. “Mama tunda kince musu bakya son yin auren su barki kici gaba da yin sana’arki mana.” “Yaya Madu ba zai bari ba Abul, Baba ne mai kareni kuma mai son faranta mini amma kaga tun ba’a je ko’ina ba na fara ganin gurbinsa. Allah ya jikanshi yasa ya huta. Wata uku da haka Mas’ud ya dawo gida ya gama karatunshi gaba d’aya, ganin yayar tashi bata sana’arta ya tambayeta dalili, tsakaninsu babu 6oye-6oye don haka ta fad’a mishi komai. Kwana uku da haka aka raba gadonsu wanda Mas’ud ne jagora. Bayan an gama ne kowa ya d’auki rabonshi wanda dalilin hakane Laila ta tsira da shagonta ya zama nata halak malak kuma taci gaba da sana’arta. January 2020  Laila ce zaune a kan kujera tana rubutu a wani littafi dake kan cinyarta, lokaci-lokaci kuma tana duba wayar hannunta da alama abun cikin wayar take juyewa a littafin. Ji tayi an rufe mata ido wanda da farko ta tsorita, amma da ta ta6a hannun ta gane na wanene sai ta saka dariya tana ajiye littafin a gefe. “Kai Abul me haka?” Tace da d’anta wanda zai cika shekara ashirin da uku a watan gobe. Bai yi magana ba sai jin muryar Sabrin tayi tana cewa, “Happy Birthday Mama.” Da haka Abul ya bud’e mata ido tayi arba da k’aton cake d’in dake hannunta. “Happy Birthday Love.” Shine abunda Abul ya fad’a yana mai zagayowa ya zauna kusa da ita ya manna mata kiss a k’uncinta.  Sabrin ‘yar shekara ashirin ta ajiye cake d’in a kan center table dake kusa da Laila sannan itama ta zauna murna fal a fuskarta  Kallonsu Laila ke yi cikin tsantsar farinciki wanda ya hana bakinta rufuwa. “Wato bakwa ji sai da kuka mini birthday cake bayan na fad’a muku bidi’a ce ko?” Tace dasu tana mai hard’e hannunta kan k’irjinta. “Haba Mama na yau kad’ai ne fa, kuma ba party za’a yi a saka kid’a ba, kawai cake d’in aka miki.” Cewar Sabrin cikin shagwa6a. “Love, a yau da kika cika shekara forty ciff komai ma halal ne.” Wannan fad’in Abul khair kenan yana tashi daga gefenta sanin zata kai masa duka. Ai kuwa dukan ta kai masa amma sai ta shafi iska, dukansu suka saka dariya wannan karon har da Mas’ud da ya zama babban mutum d’an shekara talatin da bakwai. “Kai Tuzuru sai yanzu ne?” Fad’in Laila kenan cikin tsokana. “Na kusa nayi aure dai in huta da gorinki.” Ya bata amsa yana mai zama a gurbin da Abul ya tashi.  Bai shawarci kowa ba ya yanki cake ya kai baki. “Uncle Mas’ud dai bamu yi hotuna ba har ka yanka cake d’in.” Cewar Sabrin tana kwaye fuska. “Ohh, ohh Uncle yayi 6arna. I’m so sorry daughter, tashina kenan daga bacci ina jin yunwa. Zo ki zauna in muku hotunan sai ku 6oye gurin da na yanka.” Ya tashi tsaye yana mai jawo Abul ya zaunar dashi a gefen Laila. “Nifa babu wani hoton da zan d’auka rik’e da cake. Haba sai kace wata yarinya?” Wannan fad’in Laila kenan wanda a ganinta yin Birthday cake na yara ne.  Sai da kyar Mas’ud yasa ta yarda ya d’aukesu a hoto suka had’a da selfie, sannan suka nitsu aka ci cake d’in.  A ranar da yamma Laila, Abul, Sabrin suka nufi gidan Madu gaishe da Ummii. Ko da suka je suka samu Madu baya nan ba k’aramin dad’i hakan yayiwa Laila ba sanin halinsa har gobe bai canja ba. “Kina nan zaune a haka har yanzu ko?” Fad’in Ummii kenan bayan su Abul sun fita daga cikin d’akinta zuwa falo. “Ummii shi aure lokaci ne, idan Allah ya nufeni da yinsa bazan d’auki wannan lokacin ban yi ba. Kuma yanzu auren Sabrin ne a gabana.” “Ai kullum ba’a rabaki da abun fad’i. Shi wanda yake d’aure miki gindin ma gashi a yau babu shi. Hakan bai zame miki izina a kan rayuwa ba? Zamanki haka babu aure wani fa’ida ne dashi ko kwanciyar hankali? Allah ya kyauta.” “Idan lokaci yayi zan yi Ummii, lokaci nake jira.” Laila bata fasa fad’in hakan ba ko don hankalin Ummii ya kwanta. February Zagayawa take yi a hankali cikin Donutfairy super market, yayinda lokaci-lokaci kuma tana d’aukan abubuwan da take buk’ata tana ajiyewa cikin kwandon da take turawa. Tana gama sayayyan ta biya kud’i aka saka mata a ledoji har biyu. Da haka ta fita zuwa waje inda ta ajiye motarta, sai dai kafin ta isa ta tsaya cakk dalilin wani saurayi data gani jingine a jikin motar hannunsa cikin aljihun wandonsa. Zuciyarta ce ta buga da k’arfi domin wani d’an karkacewar da yayi ya tuna mata da Aliyu wanda duk duniya shi ta gani yake hakan. Sai a lokacin ta k’are masa kallo zuciyarta kuma ta tsananta bugu ba tare da ta kawar da idanunta a kanshi ba. Tana nan tsaye har hannunta ya fara gajiya, hakan yasa ta farga ta fara takawa zuwa gurinshi ba tare da tasan me zata ce dashi ba idan ta isa. Zuciyarta kuma bai daina lugude ba, bugu bana tsoro ba, sai dai na wani abu daban kwatankwacin irin wanda taji a farkon had’uwarta da Aliyu uban ‘yayanta. Tsayawa ta yi a gefenshi wanda hakan yasa ya lura da ita, da sauri ya matsa daga jikin motar yana cewa, “Yi hak’uri Hajiya, kawo kayan in saka miki a booth.”Wannan shine silar had’uwar wad’annan mutane biyu.

Mum Fateey👌

Back to top button