Ruwan Zuma Page 48 Hausa Novel
(48) “Haydar!!” Laila ta sake kiranshi with disbelief in her voice tana neman juyowa amma ya rik’eta k’amm ya hanata motsi. “Stop struggling Laila, Baby zai tashi.” Ya fad’a yana cigaba da shafa cikinta a hankali wanda ya lura ya tashi kad’an yayi tauri sosai. Sheshshekar kuka ta fara ta rik’o hannunsa dake shafa cikin nata ta rik’eshi a k’irjinta, hakan yasa Haydar ya juyo da ita suka fuskanci juna ba tare da ya bari ta bar jikinshi ba yace, “Me abun kuka Laila?” “It’s really you.” Ta fad’a tana shafa fuskarsa da jikinshi. “It’s me.” Ya juya kad’an ya kunna bedside lamp suka k’urawa juna ido, cikin sauri Laila ta tura kanta cikin wuyanshi tana shinshinarshi tana rufe ido. Bai hanata ba illa dariya da abun ya bashi domin yasan k’amshinsa na d’aya daga cikin addiction d’inta, shinshinarshi da take yi kuma yana mishi kamar cakulkuli ake mishi amma haka ya hak’ura har sai da tayi mai isarta sannan ta koma ta kwanta tana jan wata doguwar ajiyar zuciya tace, “Ka gujeni Haydar.” Shiru yayi bai amsa ba domin ya sani gudunta yayi da duk wani nashi don yaje ya warkar da zuciyarsa daga ciwon da aka saka mata. “I’m sorry amma ban zubar da cikin ba wallahi. Tun kafin wayewar gari nake jin kamar bazan iya zubarwan ba amma a hakan na fita naje asibitin. Abunda na fara sanar da Doctor shine ya duba mini lafiyar cikin da kuma girmansa don in sani in kuma sanar da kai cewa I will keep the pregnancy. Ka zo ka samu ana mini scanning wanda ya sakani hawaye dalilin ganin abunda yake cikina kamar wani beans, kenan shi zai girma ya zama d’an mutum gudan jininka. A wannan lokacin naji babu abunda nake so irin in bar wanann abun ya rayu in haifeshi in rik’eshi a hannuna ina kallon abunda muka haifa ni da kai. Haydar baka saurareni ba ka tafi, baka bani chance da zan yi explaining kaina ba. Kayi hak’uri da duk abunda na maka daga farkon zamanmu har rana mai kamar ta yau, don Allah ka mayar dani d’akina wallahi na maka alk’awarin haihuwa duk shekara har in kai menopause d’ina. I wouldn’t give a damn akan abunda mutane zasu ce saboda na gane kai ne farincikina basu ba. Please give me another chance, wallahi wallahi bazan sake kauce umurninka ba just stay with me don girman Allah karka sake guduna Haydar.” Ta tashi zaune tana k’ara rik’o hannunshi kamar an ce mata zai gudu, idanunta kuwa cike suke da hawaye wanda wasu ke gudu freely a k’uncinta. Haydar ya tashi shima ya zauna ya dunk’ula hannunsu guri guda ya sumbaci nata ya d’ago fuskarsa yana kallon yanda ta bi hannun da kallo kamar shine the most prized possession yace, “I’m not going anywhere Laila.” “Abun da ka fad’a kwanaki kenan Haydar amma still ka k’ara tafiya ka barni. Yaya kake son in yarda da maganarka alhali kana sa6a alk’awarinka.” “Saboda zaman da nayi babu ke Laila wallahi ban ta6a jin dad’insa ba ko na second d’aya. Idan na tuna cewa na rabu dake sai in ji kamar in yiwa kaina hukunci saboda nayi aikin gaggawa kuma nayi dana sani. A tunanina ko na dawo ba zaki yarda da aurena ba shiyasa nayi ta zamana har Allah yasa yau naji sak’on da kika bayar ga Mallam Nafi’u, wanda tun bayan tafiyana ban k’ara sauraron wa’azinsa ba sai yau. Ina cikin bin episodes d’in da nayi missing naji sak’onki wanda yasa na fito a lokacin ba tare da nayi la’akari da cewa dare yayi ba. Tun ranar dana tafi ina cikin Kano a wani hotel wanda su suke kawo mini abinci daga restaurant d’insu idan na buk’aci hakan, bana fita waje ko kad’an domin hatta sallah a cikin d’akin nake yi. Na nisanta kaina da duk wani abu na jin dad’in rayuwa sai ibada da nake yi ina jiran ranar da zan ji I’m ready to move on with my life. Wallahi Laila every minute without you ina jinshi kamar har abada ne, ina son dawowa amma idan na tuna bazaki kar6eni ba da kuma abunda nake tsammanin kin yiwa gudan jinina sai in ga gwara inci gaba da zama a can saboda bakya sona…..” “Wallahi ina sonka Haydar, ina maka son da ni kaina ina mamakinshi. You have no idea yanda sonka ke yawo a jinin jikina wanda ya hanani samun sukuni all this while da baka nan. Na fika shan wahala saboda kullum da hawaye a fuskata nake bacci, sai dai idan na tuna cewa ina tare d’anka sai inji sanyi a raina in gane cewa I’m not alone, someone is there for me. I’m sorry once again, I’m so sorry please forgive me.” With shiny eyes wanda suke sparkling dalilin hawayen daya taru a cikinsu Haydar ya kalli Laila yace, “I forgive you, ina fatan nima zaki yafe mini tafiya da nayi na barki da abunda yake cikinki.” “No, wallahi baka da laifi saboda na kaika bango ne kuma baka san cewa ban cire cikin ba. Laifin duk nawa ne kuma ni ya kamata in baka hak’uri in nemi gafarka. Please ka dawo dani matarka, please.” “Ke matata ce tun lokacin dana saka k’afa na shigo cikin gidan nan na kwanta a kan gadonki, na dawo dake d’akinki tunda na kai hannu jikinki. You are still my wife.” Ya fad’i hakan yana shafa fuskarta cikin tsantsar sonta da yake d’awainiya da zuciyarsa. Kwantar da kanta Laila tayi akan tafin hannun nashi sannan ta d’aga ido ta kalleshi tayi saurin had’e kansu guri guda tana kissing d’inshi, Haydar da yake restraining kanshi yaji ya kasa hak’uri ya rik’o wuyanta suka fad’a duniyar ma’aurata. Minti biyar da haka tace, “Haydar….don’t crush..my….my Baby.” “I won’t, I will be gentle Laila.” Bayan komai ya lafa Haydar ya jawota jikinshi yana shafa kanta cikin tsananin farinciki da yake ciki yace, “I love you and I can’t live without you Laila, please stay with me.” Hancinta ta saka a wuyanshi tana shak’ar k’amshinsa wanda a yanzu ya had’u da gumi kad’an dalilin k’ok’arin daya gama yi a lokacin, tace,“Ina nan tare da kai Haydar thou na ji Mallam ya baka shawaran ka k’ara aure, idan zaka yi bazan hanaka ko in tayar maka da hankali ba, sai dai ina tsoron kar ka auro budurwa ka wulak’antani a kanta ko kuma ka rabu dani saboda ni na tsufa. Amma in zaka zauna dani tsakani da Allah zan zauna da kai ko da uku ka k’aro a kaina.” Shiru Haydar yayi na wasu sakanni sannan yace, “In fad’a miki wani abu zaki rik’eshi a matsayin sirri har k’arshen rayuwarki kuma ba zaki gujeni ba?” Laila tashi tayi zaune tana jawo zanin da suka rufe jikinsu zuwa k’irjinta, amma Haydar na ganin hakan ya janye yana cewa, “Nafi son ganinki haka. Amma dad’ewan da nayi bana nan shi yasa naga sun k’ara girma ko dai idona né.” Murmusawa kawai Laila tayi tana buge hannunsa da ya kai k’irjin nata tace, “Cikin ne yasa suka k’ara girma. Now mu koma maganarmu na d’azu, me zaka fad’a mini? Sannan ka sani sirrinka sirrina ne, har abada bazan ta6a kwaye maka zani a kasuwa ba.” Gyad’a kai Haydar yayi ya dubeta with so much seriousness yace,“I’m Gerontophile Laila.” Tattare fatan saman goshinta Laila tayi cikin rashin fahimtar me yake nufi da wannan kalmar. “Menene Gerontophile d’in? Kamar ba common word bane.” Kallonta yayi sosai kana yayi ajiyar zuciya ya sunkuyar da kanshi k’asa yace, “Mutum ne who has a sexual attraction for people who are older than themselves. I like older women Laila, ‘yan mata basu ta6a burgeni ba wallahi balle har inji ina son tarayya dasu. Amma ke idan na tuna cewa kin girmeni sannan a hakan nake pinnng d’inki down ina faranta miki shi yake sakani farin ciki da nishad’i. Don Allah karki gujeni a yau dana fad’a miki deepest secret d’ina, ko Ammi bata sani ba and ina son ya tafi a haka saboda su baza su ta6a ganewa, k’arshenta tsorita zata yi tace aljanu ne suke d’awainiya dani. People like me exist Laila sannan bani na za6awa kaina hakan ba, haka na tashi na ganni.” Haydar da har lokacin kanshi na k’asa ya d’ago kanshi da yaji shirun yayi yawa, a ranshi kuma yana tunanin ko itama ta tsorita ne zata gujeshi. Sai dai ganinta yayi tana murmushi bakinta har kunne yasa shima fuskarsa ta washe yace, “Why are you grinning?” “Saboda yanzu hankalina zai fi kwanciya idan na tsufa, duk macen daka gani mai k’uruciya baza ta ta6a zama threat a gurina ba. I think we are one perfect couple shiyasa Allah ya had’amu ya kuma k’ara mana da albarkan samun zuriya. Wallahi baka san yanda wannan maganan ya d’auke mini wani k’aton nauyi a zuciyata ba, kullum idan na tuna cewa zan tsufa kai kuma zaka iya fara kula k’ananan yara sai inji kamar an yamutsa mini zuciyata. I’m happy that you are geron…. gerenta? Whatever! I’m glad.” Tana fad’in hakan ta rungumeshi tsam a jikinta tana fatan in ma hakan rashin lafiya ne kar Allah yasa ya warke ya zauna a haka, and yes, she is that selfish. “Hajjaju kina tsokanata kuma I don’t want to hurt you or the Baby.” Ya fad’i hakan yana ganin yanda take neman birkita mishi lissafi. “Waya fad’a maka zaka yi hurting d’ina ko Baby? Doctor yace a dinga yiwa Baby yayyafi ana bashi vitamin D.” “Then be my guest.” Ya amsa suka k’ara tafiya wata duniyar. Washe gari misalin k’arfe goma da wasu mintuna Laila ta farka ta ganta kwance a k’irjin Haydar wanda ke bacci sosai. Tsayawa tayi tana kallonshi wai wannan d’in duk nata ne ita d’aya, kyakkyawar fuskarsa da kuma k’arfin da Allah ya masa ya isa a kirashi da gwarzon d’a namiji domin duk wani k’ishinsa da ta dad’e tana ji sai da ya cire mata jiya. “I love you so much it hurts.” Ta fad’a a hankali kana ta tashi ta shige band’aki ta sillo wanka ta fito. Jikinta ta fara shafawa crème mai had’e da kulacca sannan ta bi da humra wanda yasa nan da nan d’akin ya bule da k’amshinta. Kwalliya ta zanawa fuskarta mai kyau da sauk’i sannan ta saka wata doguwar riga da Haydar yace tana mishi kyau. Jikinta ta k’ara feshewa da turare sannan ta juyo zata fita taga Haydar ya farka yana kallonta. “Ina kwana Baban Baby.” Cikin seconds uku ya iso gurin da take ba tare daya damu da rashin kaya a jikinsa ba.“Say it again.” Ya fad’a yana kissing wuyanta tare da shafa cikinta. “Baban Baby?” Ta tambayeshi tana zaro hannunsa daga cikin rigarta. “Eh.” Ya bata amsa yana cire mata kallabinta. “Baby yana jin yunwa, bana kai war haka ban karya ba fa.” Tayi saurin fad’a ganin zai k’ara janta zuwa wata duniyar. Yana jin hakan ya bar jikinta ya koma can gefe yace, “A bawa Baby abinci. Ni zan iya jiran nawa abincin sai anjima.” Yana fad’in hakan ya shige band’aki ya bar Laila a gurin wacce take jin kamar ta bishi. Sai dai tunawa da tayi cewa she needs real food yasa ta kad’a kanta ta fita zuwa kitchen. Tuwon da mai aikinta ta mata jiya shi ta d’umama ta sakawa Haydar a warmer sannan ta fito ta ajiye a dinning table tare da plate da serving spoon. Komawa kitchen tayi ta had’o tea sannan ta dawo ta fara cin tuwon tana kur6an tea d’in. Duk wannan abun da take yi murmushi da annuri bai bar fuskarta ba, haka kawai sai taji kamar tayi ihu tsabar murnar data samu kanta a ciki. Lokaci-lokaci kuwa tana duba k’ofar d’akin da Haydar yake ciki don ta k’ara tabbatarwa cewa ya dawo gareta. Tana gama cin tuwon ta wanko hannunta kana ta d’auko fruits d’in da Mas’ud ya kawo mata jiya ta fara sha bayan ta yayyankasu. Buga k’ofar falon da ake yi yasa ta tashi taje ta bud’e ta ga Mas’ud ne hannunshi d’auke da leda wanda ta tabbatar wani abun ya kawo mata. “Baka gajiya da d’awainiya.” Ta fad’a tana jefa kankana a bakinta sannan ta bashi guri ya shigo amma shi kuma ita yake kallo. “Kalti yau kina cikin farin ciki.” Shine abunda ya fara fad’a yana ajiye ledan a kan dinning table. Zama tayi a kujera shima ya zauna yana kallonta yana murmushi, kafin ta bud’e baki tace wani abu suka ji an bud’e k’ofar d’akinta Haydar ya fito sanye da jumfa da wando har da hula sai zuba k’amshi yake yi. Mas’ud sake baki yayi yana kallon ikon Allah yana nuna Haydar da yatsa amma ya kasa cewa komai. “Ya dawo jiya da dare.” Laila ta bashi amsa duk da bai furta tambayar ba. K’arshenta Haydar ne ya iso gurinsu ya rufe masa bakin sannan Mas’ud ya farga ya daki kafad’arsa yana cewa, “Ina ka tafi duk tsawon wannan lokacin?” Laila na ganin hakan ta taso ta shiga tsakaninsu tana cewa, “Calm down Mas’ud. Abun bai kai haka ba.” Ya ma rasa me zai ce illa tsayawa da yayi yana ganin yanda Laila ta kare Haydar shi kuma yana bayanta yana aiko mishi da gwalo. “Dukana zaka yi ne?” Haydar ya fad’a yana barin bayan Laila yaje ya zauna kusa da Mas’ud wanda har lokacin bai daina kallonshi ba. “Daa zan iya daa yanzu na fasa maka baki amma saboda Kalti zan barka, so welcome back the runaway husband. Wato kai haka rayuwarka zata k’are daga a kaika d’akin matarka sai ka daka yaji?” “Wai a hakan kai kawuna ne.” Mas’ud na jin hakan yayi dariya kana ya mik’a mishi hannu suka yi tafa cikin farin cikin ganin juna. “I’m glad you are back man. Karka sake mana irin haka please.” “Kuyi hak’uri na sakaku a cikin zullumi, hakan ba zai k’ara faruwa ba.” Shima ya fad’a sincerely. “Kalti ki bashi abinci ya rame da yawa.” Fad’in Mas’ud yana jawo warmer d’in ya bud’e. Ganin farin cikin da Mas’ud yake ciki yasa Haydar yaji wani abu ya zo ya tokare mishi a makwoshi kamar zai sakashi hawaye, saboda irin wannan soyayyar yake burin gani ana yi mishi tun tashinsa. Meyasa ya tafi ya barsu bayan an sanar dashi cewa sune danginshi da ya dad’e yana mafarkin samu? Mas’ud ne da kanshi ya saka mishi tuwon a plate ya tura gabanshi yana cewa, “Ka cinye duka, ina son ka murmure kafin Ammi ta ganka.” Laila dake tsaye a gefe tana kallonsu sai taji ta k’ara son Mas’ud domin shi mutum ne wanda idan ya soka to zai soka ne da dukkan zuciyarsa kuma baya iya 6oyewa. Ta lura ya k’ara k’aunar Haydar tunda aka gane cewa shi d’in jininsu ne kuma d’an cousin d’insu. Sai da Haydar ya cinye tuwon sannan Laila ta kawo mishi bowl da ruwa ya wanke hannunshi yana kallonsu duka yace,“Irin wannan so da kulawan da ake nuna mini sai yasa in k’ara gudu gobe.” “Don’t even try it.” Fad’in Mas’ud. Laila kuma tace, “Zaka k’arisani kenan?” Murmusawa yayi ya kad’a kanshi kana yace, “Ina Ammi take?” Nan suka nitsu Laila ta musu jagora zuwa falo suka zauna, shi dai Haydar bin su yake yi da ido domin bai ga dalilin da zai sa daga tambayar ina Ammi take ba sai su nemi ya dawo falo a zauna, kenan magana mai muhimmanci za’a yi. Kasa hak’uri yayi dalilin zuciyarsa data fara tsoritashi a kan cewa ko Ammi tana kwance ne bata da lafiya yace, “Me ya samu Ammi?” “Babu abun da ya sameta amma bayan tafiyanka abubuwa da yawa sun faru Haydar, ciki har da bayyanar mahaifinka.” K’ura musu ido Haydar yayi yana karantar su, ganin babu alamun wasa a fuskarsu yasa yace, “Da gaske kuke yi? Ina mahaifin nawa?” Zuciyarsa kuma tuni ta tsananta bugu amma a waje sai ya dake yana jiran amsarsu. “Alhaji Abdul yayanka ne babanku d’aya.” “No, no. Ta yaya? Yaya hakan zai kasance?” Ya cire hularsa ya ajiye a gefe yana jin gumi na tsatstsafo mishi ta ko’ina a jikinshi. A nan Mas’ud ya fad’a mishi duk abunda ya faru bai rage komai ba sannan ya k’arisa da cewa, “Yanzu Ummii da Ammi suna can Maiduguri.” Shi kuma Haydar kallon Laila yake yi da yaji labarin har gayyatar Alhaji Abdul tayi gidanta bayan duk munafurcin daya mata ya lalata mata d’anta, yace, “Meyasa zaki nemeshi Laila? Bakya tsoron ya k’ara cutar dake?” “Yayi nadama Haydar, yana k’aunarka yanda baka tsammani a yanzu. Try and get to know him shi da Babanka a nan zaka gane irin son da suke maka bana wasa bane.” A nan itama ta bashi tarihin Alhaji Abdul wanda ya fad’a mata har ta yarda da cewa ba zai ta6a gigin cutar dasu ba. Shiru Haydar yayi yana tunani sannan yace, “Bazan ta6a yafe mishi halin daya saka Abul a ciki ba, wannan cutar tafi kowanne bak’anta mini rai Laila. Ya cuci rayuwarsa wanda hak’uri yayi kad’an ya gyara 6arnan da yayi. Zan nemi mahaifina amma tsakanina da Abdul babu zumunci har abada.” Shiru su Mas’ud suka yi domin a yanzu da yake kan gadon zuciya ko menene suka fad’a mishi ba zai sauraresu ba. Amma idan lokaci yayi shi da kanshi zai neme Abdul d’in saboda su ‘yan uwan juna ne wanda ruwa ba zai wanke jininsu ba haka kuma wuk’a baza ta yanka ba. Suna zaune suna tattaunawa Haydar ya d’auko wayarsa dake cikin jakarsa ya kunna ta. Sak’onni ne suka fara shigowa babu k’akk’autawa wanda hakan ya hanashi kiran wanda yake son kira. Sai da suka gama shigowa ya duba yace, “Su waye suka turo mini messages haka?” “A cikinsu akwai wanda na zageka, so kar ka 6ata rai.” Fad’in Mas’ud yana sosa k’eyarsa. “Meyasa zaka zageshi Mas’ud?” Laila ta zaro ido tana dubanshi. Kafin ya bata amsa suka ga Haydar ya kara waya a kunnensa yana cewa, “Hello.” Alhaji Abdul da yake d’ayan gefen kasa magana yayi illah tashi da yayi tsaye ya nufi d’akin da Babanshi yake yana cewa, “Baba ga Haydar.” Hannu na rawa Baba ya k’ar6i wayar ya k’ara a kunnenshi yace, “Aliyu Haydar.” Kasa magana Haydar yayi dalilin ruwan daya taru a idanunsa ya juyawa su Laila baya sannan yace, “Na’am Baba, kana ina?” Mintuna talatin da haka Haydar ya shiga tangamemen gidan Alhaji Sammani wato Babansa shi da Alhaji Abdul. A bakin k’ofa ya tarar da tsohon wanda ko jira bai yi motarsa ta tsaya ba ya tako cikin sassarfa ya bud’e marfin gaban motar inda yaga Haydar yake zaune. Ai kuwa yana fitowa Baba ya rungumeshi tsam a jikinshi yana cewa, “Allah nagode maka, Alhamdulillah d’ana ya dawo gareni.” Shi kuma Haydar daurewa kawai yake yi amma kuka ne yaji yana son ku6uce mishi ganin wai yau gashi tare da mahaifinshi wanda a daa har ya cire rai da zai had’u dashi. Sai da suka tsagaita sannan Baba da kanshi ya mishi iso zuwa cikin falonsa ba tare da ya sake hannun Haydar ba. Alhaji Abdul da yake can gefe yana tsaye murmusawa kawai yake yi cikin farin ciki kana ya shige motarshi ya fita daga gidan zuwa gyaran abunda ya 6ata na biyu. Suna shiga falon Baba ya zaunar da Haydar kusa dashi kana ya k’ura mishi ido yace, “Kafi kama da k’anina Alhaji Shettima wanda ya kar6a maka aure, suna zuwa yanzu da duk ‘yan uwana.” Yana rufe baki kuwa suka ji k’aran bud’e gate nan da nan motoci zafafa suka fara shigowa suna parking a farfajiyar gidan wanda zai d’auki motoci fiye da ashirin. Lokaci guda falon ya cika da mutane manya da yara wanda Baba da kanshi yake nuna mishi su tare da sunayensu. Yawancinsu ‘yaya da jikokin Alhaji shettima ne tunda Baba Alhaji abdul kad’ai ya haifa kuma ya k’i aure har yanzu, Hajiya Hadiza k’anwarsu kuwa ‘yayanta 6 ne sai tarin jikoki. “Ga k’anina Alhaji shettima sai k’anwarsa Hajiya Hadiza, mu kad’ai iyayenmu suka haifa wanda a yanzu basu da rai Allah ya musu rasuwa. ‘Yayan Shettima goma sha uku da jikokinshi talatin da biyar. Sammani mai sunana shine babban d’ansa yana da ‘yaya bakwai, sai dai baya gari zai dawo yau daya samu labarin an sameka. Wannan k’anwarsa ce Aisha tana aure a nan Kano da ‘yayanta hud’u, sai……..” Haka Baba yayi ta k’irgawa Haydar ‘yan uwansa da kuma sunayensu, wani gurin idan yayi 6atan suna sai jikokin su gyara mishi suna mishi dariya wai yayi expire. Haydar dai bin kowa yake yi da kallo yana jin zuciyarshi kamar ta fashe tsabar murna da farinciki, suma ido suka zuba masa suna murnar ganinshi kowa na son yayi hira dashi amma hakan babu dama don yawansu. Hajiya Hadiza da tun shigowarta take zaune kusa dashi tace, “Aliyu Haydar ina mamanka?” “Tana Maiduguri gurin ‘yan uwanta.” Haydar ya amsa mata yana mamakin yanda yake d’ibi da ita kad’an musamman idanunsu da girarsu. Alhaji Shettima kamar yafi kowa murna don tun ranar daya d’aurawa Haydar aure da Laila yaji yana son yaron. Halin Alhaji Abdul na neman mata yasa suka tsani halinshi suke hantararsa, amma a yanzu da Haydar ya kasance nasu zasu jawoshi jikinsu ya gane cewa yana da zuriya. Kanshi ne ya fara ciwo domin mutanen sun mishi yawa gashi tun d’azu bak’inshi ya kasa rufuwa, Baba ne ya fara lura da hakan ya cewa ‘yan matan zuriyar nasu su shiga kitchen su musu girki. “Zamu dafa amma sai anyi alk’awarin aure.” D’aya daga cikin jikarsu Iman ta fad’a cikin tsokanan Kaka da jika. “Ku dai dafa sai ayi maganar auren, amma ni bazan auri wacce bata iya d’aura zani ba.” Ya mayar da martani wanda kowa ya gane da Iman yake yi wacce bata iya d’aura zani ba ko da pieces ne. Dariya sauran ‘yan uwanta suka mata ta koma gefen Haydar tace, “Kaga Babanka ko?” “Tsakaninku babu ruwana.” Ya bata amsa yana dariya. Kiran sallah da ake yi yasa Haydar da ‘yan uwansa maza wanda wasu sun fishi yayin da wasu kuma sa’anninshi ne suka wuce masallacin dake jikin gidan, iyayensu maza ma suka rufa musu baya. Matan kuma empty rooms d’in da ke gidan suka shiga suka bar Aisha babbar addarsu a falo tana musu order na abinci a wani restaurant. Hajiya Hadiza kam d’aki ta samu cikin tarin d’akunan da suke gidan tace kar a dameta zata yi bacci, jikokin da suka san halinta na masifa babu wanda yayi gigin zuwa inda take kowa ya kama sha’anin gabanshi. Kafin su Haydar su dawo gida har yayi aboki a cikin ‘yayan Alhaji Shettima wanda hankalinsu yazo d’aya kuma sa’annin juna ne sunanshi Yunus, a nan Yunus yake bashi labarin budurwar da zai aura wanda har an saka date next month. “Kace zamu sha biki.” “Ba sosai ba saboda bana son bidi’a yayi yawa a biki.” Yunus ya amsa yana murmushi. “Kuma hakan yafi, less bidi’a more albarka a aure. In bidi’a yayi yawa sai kaga ana ta tashin hankali saboda tun a auren albarkar shaidan aka nema bana Allah ba.” “Kuma gaskiyanka fa.” K’anin Yunus wanda kanshi ke rawa mai suna Na’eem yace, “Mu dai namu sai kaff yan Kano sun san anyi aure.” Dariya Haydar yayi yana jin kanshi cikin annushuwa wai shine yake having conversations da danginshi, shi kuma Yunus hararan k’anin nashi yayi yace,“Ka samu matar tukunna.” Da haka suka shigo cikin gidan Alhaji Sammani na tambayar ina Alhaji Abdul yake, kowa yace bai ganshi ba. Hakan yasa ya kirashi a waya yace yana son ganinshi yanzu. Minti ashirin da haka Alhaji Abdul ya shigo gidan ‘yan uwanshi na gaisheshi yana amsawa fuska babu yabo babu fallasa. Haydar kuwa yana ganinshi ya had’e rai sosai domin babu abunda yake tunawa sai lalata tarbiyyar Abul da yayi. Alhaji Sammani da Alhaji Shettima su suka ja ‘yan uwa biyun zuwa wani falo a uptairs suka ajiyesu guri d’aya domin sulhuntasu. Masu karatu zaku iya bawa Alhaji Abdul second chance?
Mum Fateey 👌

