Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 11 By Ayshercool

Bayanta manager ya bi da kallo, ta bashi tausayi sosai da sosai, sai dai yana addu’a Allah ya sa kar honorable ya cutar da ita.Kamar ɓarawo, haka walid ya diro a tsakar gidan, maimakon ya biyo ta ƙofa, ɗan mama yana zaune yana shan sigari a ɗan tsakar gidan.Bai kula shi ba, ya wuce ɗakin da viper yake, sai dai ya duba baya ciki.Walid ya dawo, ya kalli ɗan mama ya ce “Ina Viper?”Ɗan mama yayi dariya ya ce “Har ka gama fushin, ka dawo?”Walid ya ce “Kai ka san ba zan iya ba, ƙular da ni yayi ne, ina yi masa uzuri ne kawai na san kansa ya taɓu, yana ina?””Baya nan” ɗan mama ya bashi amsa kai tsaye.”Kamar yaya? Ina yaje?”Ɗan mama ya zuƙi sigarinsa sannan ya ce “Ni na isa na hana shi fita ne? Ko kuma na ce sai ya gaya mini in da za shi? Da dai kai ne zai iya ɗaga maka ƙafa”A fusace walid ya ce “Dan me zaka bari ya fita?””Au so ka ke na hana shi, ya karya ni, ko ya illata ni, kaɗaici ne ya dame shi, gidan babu kayan caji, sai na hayaƙi, shi ne ya fice. Yauwwa dama ina son gaya maka, ka daina kwashe kayan cajin nan gaba ɗaya, idan wani yayi rawa an bashi kuɗi, kai idan ka yi, na jaki zaka ci a hannunsa wallahi”Cikin takaici Walid ya ce “Wai so ka ke sai ya kashe kansa ne? Kana kallon allurar nan ba ta ɗaukar sa, farar ƙwaya ma fa ba ta yi masa komai, sai rikita masa ƙwaƙwalwa, idan ya haukace fa?” Walid gani yayi ɗan mama yayi tsuru-tsuru, yana rarraba ido, dan haka ya waiwaya bayansa, Al’amin ya gani a tsaye a bayansa.Bai kula su ba, ya zo ya raɓa walid ya wuce.”Master”ya kira shi.Al’amin ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, idanunsa sun yi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe ya ce “Me na ce maka a kan kirana da haka?”Walid ya ƙarasa kusa da shi, dai-dai kunnensa, ya yi masa raɗa.Viper ya kalli Walid ya ce “Kasheni ka ke so ka yi sannan hankalinka ya kwanta ko Walid?”Walid ya ɗage kafaɗa ya ce “Duk yadda ka gani”Viper ya hankaɗe shi gefe, ya wuce ɗakinsa, ya rufe ƙofa.Walid ya bishi ya leƙa ta taga ya ce “Me zaka yi ka rufe ƙofa?”Leda ya ciro daga aljihunsa, ya haɗa allura a sirinji, zai yi wa kansa.Walid ya ce “Al’amin, ba zaka daina yi wa kanka allurar nan ba ko? Ba za ta yi maka ba, ka haƙura mana”Al’amin ya tashi, ya je ya ja tagar ya rufe, ya bar walid a waje yana surutu.Sumayya kuwa tun da ta koma gida, mama ta lura da yanayinta, sai dai ta yi zaton ko gajiyar aiki ce, amma har dare ba ta walwala.Dan haka ta magantu, ta ce “Ƴar mama, wai ko babu lafiya ne?”Sumayya ta ce “A’a lafiyata ƙalau?”.”To faɗa ku ka yi da mutuniyar ne?””A’a bamu yi faɗa ba mama”Ba ta gaza ba ta sake cewa “To ko wurin aikin ne suka yi miki wani abun?”Sumayya ta ƙaƙalo murmushi ta ce “Hajiya mama, bamu yi faɗa da ƴar ki ba, lafiyata kuma ƙalau, kawai kin san yanayin aikin namu ne, kayi ta ganin abubuwa na ban tausayi daban-daban”.Mama ta ce “Ai baku ba sumayya, mu ma masu saurare, kusan kullum cikin zullumin kunna radiyon muke, sai dai ku ƴan jarida ku ne idonmu, ta bakinku kawai muke jin wasu labaran da jin halin da duniya ke ciki. Allah dai ya saka muku da alkhairi ya tsare mana ku baki ɗaya, daga ke har Nabilan aikin tainakon al’umma ku ke yi, Ubangiji Allah ya tsare ku ya kawo mazajen aure na gari”Sumayya kamar ta gaya wa mama, abun da aka umarceta a wurin aiki, amma ta san hankalinta tashi zai yi, zata iya hanata aikin ma, kuma Allah ne gatansu aikin nan ne gatansu, dan haka ta ja bakinta tayi shiru.***Sannu a hankali barrister Naja’atu take bin titin ƙauyen, sai tsaki take yi saboda yadda garin yake babu kyakkyawar hanyar shiga. Sai uwar ƙura da kwazazzabai a hanyar.A hankali ta cigaba da tuƙin har ta ƙarasa in da take son zuwa.Sai da ta shiga tsakiyar tsakar gidan, sannan ta yi sallama.Daga cikin ɗaki a ka amsa sallamar.Daga baya matar ta fito daga ɗakin, ta ce “Waye?” Ganin barrister Naja’atu ya sanya ta ɗan saki fuska, ta bata damar shiga ɗakin.Shame-shame taga rammaa a kwance a kan katifa, ta nemi wuri ta zauna a gefe.Ta kalli in da ramma take, sannan ta mayar da idonta kan maman ta ce “Na dawo ne na ji me kuka tsayar, kuma na ga haryanzu ba ta da lafiya, anya ramma ba shagwaɓa a wannan lamarin? ya ci ace kin ware ai, da auren ma aka yi miki ai da kina gidan miji, ko shi ma hakan zaki yi ta yi masa”.Fashewa da kuka ramma tayi, cikin tsananin baƙin ciki da takaici.”Meye kuma na kuka? Wannan abun da ki ke yi, sai mutane sun san halin da ki ke ciki?”Cikin sanyin jiki da damuwa, maman ramma ta ce “Tun da abun nan ya faru, take rashin lafiya, jiya mun je asibitin sha ka tafi, na garin nan, an ce ciki ne da ita” tayi maganar tana fashewa kuka mai taɓa zuciya.Sak Naja’atu tayi, tana kallon su.Ta numfasa ta ce “Wai wannan kukan na menene ku ke yi haka, kukan zai yi muku magani ne? Ai wannan ba abun ɗaga hankali bane ba”Cikin tsananin mamaki, maman rahama take kallon barrister Naja’atu.”Baiwar Allah, ce miki na yi fa, an ce mini ciki ne da ita, wanda ya dubatan ɗan garin nan ne, na san dole maganar nan ta fita, auren yarinyar nan ba zai yiwu ba, amma kina nuna bakomai bane ba, dan girman Allah a karɓowa yarinyar nan hakkinta”.Naja’atu ta ce “Baiwar Allah, ko fa an kai yaron nan kotu yayi prison, abun da zai faru ya riga faru, ba kuma zai goge ba, ɓacin suna kuma ya riga ya ɓaci.Matsalar mutanen mu na Arewa, kuna giramama al’ada da addini a kan ƴancinku. Da in da aka cigaba ne, zata iya haife abun da ke cikinta, idan tana so, and rise him as a single mother, har ta iya neman ya din ga biyanta wani abu a kotu, shikenan. But for now, za a iya zubar da cikin ta cigaba da harkokinta sai me? Is an adolescent crises kowa ma zai iya faruwa da shi”.Cikin mamaki maman ramma ta ce “Baiwar Allah kuma ke musulma ce?””Ƙwarai kuwa, muslma ce ni gaba da baya, mafita nake baku da shawara. Zan je na yi booking a saka rana a can cikin gari, private hospital, a cire cikin lafiya ƙalau za a cire shi, yanzu an cigaba nesa ba kusa ba, ku karɓi kuɗin ku ku rage zafi”.Rma ta fashe da kuka ta ce “Ni mama tsoro nake ji, an ce mutuwa ake yi, dan Allah ni dai a kai shi wurin alƙali, an ce kina taimako dan Allah ki taimaka mini, ji nake kamar na mutu na huta, ba a taɓa cikin shege a garin nan ba sai a kaina, dan Allah ki taimaki rayuwata, wallahi wanda zan aura ya ji labari ba zai aure ni ba, babu kuma wanda zai ce zai aure ni, cewa za ayi na zama ƴar iska” ta ƙarasa maganar kamar ta shiɗe.Barrister Naja’atu ta ce “And so what dan an fasa aurenki? Zaki iya zama duk abun da ki ke so a rayuwa ko da aure ko babu, waye ya ce muku aure shi ne limit na rayuwar ƴa mace ne? dan Allah ku fuskanci rayuwarku, ku daina bari ana cutar ku da addini da al’ada”.Cikin baƙin ciki maman ramma ta ce “Kin ga ya isa baiwar Allah, idan bawa bai riƙe addini ba haka zai ta rayuwa kamar dabba a gari, babu ƙa’ida babu hukunci? Wannan ai salon bawa yaro damar ya je yayi zina ne, ko ni da nake jahila a cikin ƙauyen nan, sam maganarki ba ta da tushe balle makama a wurina, dan haka ki tashi ki tafi kawai, bana buƙatar taimakon naki, cuta ce an cuce mu Allah ya isa kawai”Naja’atu tayi wani irin murmushi ta ce “Ƙarshen abun fa kenan, ki yi Allah ya isa, na biyo miki da masalaha amma kin ƙi, shikenan idan kin ƙi ji ai ba kya ƙi gani ba, duk abun da ya biyo baya wannan shi ne abun da ki ka zaɓa. Sai dai ina sake yi miki gargaɗi da babbar murya, kar ki kuskura ki sake shiga kafafen watsa labarai ki yi magana, idan kuma ki ka sake, ba ruwana”Ta tashi ta sake ajiye musu kuɗi, da complementary card ɗin ta, ta ce “Akwai lambar wayata a jiki, na san zai iya yi muku amfani, idan ku ka ga babu sarki sai Allah, domin kuwa barin cikin nan, dai-dai yake da zama da ajalinta, dan kome zai ɗauka, uban wanda ya aikata laifin, ba zai bari ba”Gaba ɗaya bin ta suka yi da kallo, har ta tashi ta fita, ramma ta fashe da wani irin kuka, tare da jin ƙarshen rayuwarta ya zo.Mahaifiyarta ta kalleta ta ce “Ki yi haƙuri ramma, ina tare da ke in sha Allah, na san ko menene ya faru, ni ce sila, da ban tura ki aikatau ba, da haka ba ta faru ba, amma babu yadda zan yi ne, ki yafe mini dan Allah” tayi maganar tana kuka ita ma.Sumayya na ta aiki a kan computer, sai dai hankalinta baya kan aikin sam, kawai dai tana yi ne, amma ƙasan zuciyarta tsoro da fargabar dalilin da ya sanya, aka ce ta je gidan honorable Indabo ta yi hira da shi take ji, idan a kan laifin da ta yi wancan karon ne, ai ta bayar da haƙuri, kuma lokacin tana farkon zuwa ne.Sallamar murtala ce, ta dawo da ita hayyacinta, tayi murmushin yaƙe ta ce “Uncle murtala, saukar yaushe?”Ya nemi wuri ya zauna ya ce “Agogo sarkin aiki, yakamata a ƙara miki matsayi a gidan nan fa”Ta waro ido ta ce “Ni a wa?””Ke a ma’aikaciya jajirtacciya mana, wai ya aka yi mutuniyar take ɗaga miki ƙafa yanzu, lawisa?”Sumayya ta ce “Hmm, Arfa ce ta ce na daina jin tsoronta, nima na nuna mata bani da kirki idan ta takura mini, shi ne fa ta sarara mini”.”Ai matar nan ƴar bala’i ce lamba ɗaya”Sumayya ta sake tattara nutsuwar sa a kan sa ta ce “Yauwwa ncle murtala, akwai matar da ka yi recording, ta zo an yi raping ƴar ta, an ce Barrister Naja’atu ta shiga case ɗin, ina aka tsaya ne?”Da sauri ya ce “Rufa mini asiri, ni da aka kusa korata a kan case ɗin, kuma lawyoyi da masu kare hakkin ɗan adam, sun yi casa a kan case ɗin, sai dai tun da ta shiga cikin lamarin, kowa ya ja da baya”Sumayya ta ce “Ikon Allah, to ai haryanzu ban ji a ina aka tsaya ba, wai ɗan waye ne yayi?””Taɓ ba zaki ji mutuwar sarki a bakina ba, nima ba ta faɗa mini ba matar, wai dai yaron ɗan masu kuɗi ne, wai ɗa ne ga wani ɗan majalisa, ba ta san sunansa ba, a gidan ƙanwar ɗan majalisar yarinyar take aiki, sun je gidan ta bi ba’asi, an hana su shiga, masu gadin da suka kai yarinyar asibiti ma duk an canza su”Cikin tausayawa Sumayya take girgiza kai ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, shikenan akwai Allah, amma kana ganin ita Bunkuren za ta yi wani abun kirki a kai? Meyasa ba za a bibiyeta ba, a ji a ina aka tsaya a case ɗin ba, atleast a gurfanar da shi a kotu mana”Ya miƙe tsaye ya ce “Lallai ƙanwata baki san ƙasar nan ba, ai dokar ƙasar nan a kan talaka kawai take aiki, ko ɗan kansila ne, ba za su hukunta shi ba, ita kanta barrister nan akwai ayar tambaya a kan ta, duk da a zahiri ta Allah ce, amma yadda ake tsoronta komai tayi, babu wani mai challenging ɗin ta, akwai wata a ƙasa”.”Gaskiya dai, Allah ya sa mu dace “Ya amsa mata da Amin.Nasir yana ta yi wa Nabila bayanin, irin cigaban da yake samu a neman viper, amma hankalinta ba ya kansa, jin sa kawai take yi, kawai ji take kamar ta gaya masa halin da ake ciki, amma ta fasa, dan ta san faɗa zai yi mata.Hankalinta bai dawo jikinta ba, sai da ta ji ya ce zai je Abuja.Ta kalle shi ta ce “Abuja kuma? Me zaka yi?””Harkar aiki mana, a ƙalla sati zuwa wasu kwanaki”Ta kwaɓe fuska ta ce “Har sati?””Eh mana, ko in tafi da ke ne?”Tayi murmushi ta ce “Wace ni, Allah ya bada sa’a”Kafin ya amsa, wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga ya saka a kunnensa, “To” kawai ya ce, ya ajiye wayar ya miƙe ya ce “Bari na shiga sashen mama, tana nemana”Nabila ta ce “To”Agogon hannunta take kallo, yau ko Abba zai jajjagata idan ya dawo bata nan sai ta fita, dan tuni ta ɓoye takalminta da hijjabinta a harabar gidan, za ta lallaɓa ta fice, yadda take ji a ranta, ko zata rasa rayuwarta, ba ta da wani burin da ya wuce ta ga an kama Aminu Viper, domin kuwa shi ne ƙashin bayan matsalar aikin daba da dillancin miyagun ƙwayoyi, gefe guda kuma ga dakon burin da take yi.”Nasiru sau nawa nake gargaɗinka a kan yarinyar nan? Ban isa in gaya maka magana ka ji ba ko?”Cikin son kare kai ya ce “Wallahi mama ba abun da ki ke tunani bane ba, magana muke yi kawai a kan harkar aiki””Ni ka yi maganar harkar aikin da ni mana. Wai ma yaya muka yi da kai, ina alƙawarin mu?””Mama dan Allah ki ƙara mini lokaci, sonake na kammala aikin nan na nutsu, kin san komai lokaci ne”A hasale ta ce “Zan kwaɗe ka da kai da lokacin, shekarunka nawa yanzu a duniya, me ka ke nema da Allah bai baka ba? Wato in saki jiki ka ce wannan shegiyar yarinyar zaka aura ko? To wallahi baka isa ba, idan ba ka kiyayeni ba, sai dai ka dawo ka tarar na aura maka duk wadda nake so”Yayi shiru ya sunkuyar da kai, shi bai ga aibun Arfa ba, kuma a zuciyarsa ji yake kamar zai samu chance ɗin da zata zama mallakinsa, rashin gaya mata abun da yake ji game da ita kawai, ba ƙaramin azabtuwa yake yi ba.Sanye take da face mask, tana rarraba idonta, ta ga ta ina zata ganshi.Liti ya kalli Walid ya ce “Ka ganta ko?””Eh, amma bana ganinta sosai, ta rufe fuskarta da facemask”.Liti ya ce “Bari na yi wa gali magana”Nabila na tsaye tana rarraba ido, wani matashi ya zo gabanta ya tsaya, ta ɗaga kai tana kallonsa.”Ki sauke takunkumin fuskarki”.Cikin tsiwa ta ce “Ban gane ba, ina ruwanka da ni?”Wayar hannunsa ya ɗaga mata, da take a kan kira, muryar liti ta ji.”Ki sauke takunkumin fuskarki, ko kuma na fasa haɗaku”Waiwayawa take yi, ta ga ta ina za ta ga liti, ta kalli matashin ta ce “Da kai zai haɗani?” Ya girgiza mata kai.Ta din ga waige-waige ko zata ga daga ina liti yake ganinta, har ya san ta saka facemask. Kafin ta waiwayo, gali ya bar wurin.Ta sauke facemask ɗin, tana rarraba ido.Zabura Walid ya yi ya ce “Kai, a ina ka samo wannan yarinyar?””Jiya ta zo ta same ni, wai ita ƴar uwar viper ce, in taimaka in haɗa su, na shiga area jiya na ɗan yi wuru-wuru, an tabattar mini ita aka kwatantawa dabar madaki, ta je nemansa, suka sakar mata karnuka, ban san waye ya kwatanta mata ni ba”.Walid ya ce “Tabbas! Yakamata a haɗa su”Liti ya ce “Idan kuma haɗin baki ne, ko wata maƙarƙashiya ce aka shirya masa fa?”Walid ya ce “Zan kula da komai, amma yakamata su haɗu, ka ce ta dawo jibi da safe””Kana ganin babu matsala?””Babu matsala”Nabila ta fara gajiya da tsayuwa, matashin ɗazu ya sake dawowa, ya miƙa mata wayar.Ta karɓa ta yi sallama.”Ki dawo jibi, ƙarfe sha ɗaya za’a haɗaki da shi”.Kamar Nabila ta yi zagi, dan haushi, amma ta danne ta ce “To shikenan, Allah ya kaimu” haka ta bar wurin jikinta a sanyaye, har ta fara tunanin ko dai raina mata hankali kawai zai yi.Haka ta koma gida, ba tare da ta ji za ta sare ba.Sumayya daga aiki gidansu Nabila ta je, dan su tattauna a kan umarnin da ta samu a wurin aiki.A ɗaki ta tarar da Nabila, tana bacci, dan daga wurin su liti da ta dawo, kwanciya ta yi.Tashinta tayi, Nabila ta tashi tana tsaki, saboda yadda ta tsani a tashe ta tana bacci.”Ke baccin uban me ki ke yi, bayan azahar, har kin dawo daga aikin ne?”Nabila ta yi miƙa ta ce “Ni ban je aikin ba ma””Allah ya shirya ki, tashi ki wanko fuskar ki, mu yi magana akwai case Arfa”.Nabila ta sake mayar da kanta kan fulo ta ce “Faɗi in ji””Dalla ki tashi ki saurare ni””Wai ba kunne ne yake ji ba?”Sumayya ta ce “Kin gane mutumin da muka gani a reception, ki ka ce kin tsane shi? Ɗan majalisa ne””Yanzu takanas ki ka zo gaya mini ɗan majalissa ne? Ai na sanixSumayya ta ce “Dalla ki tsaya ki saurare ni, Honorable Ma’aruf indabo ne ai”Nabila ta tashi zaune ta ce “And so?””Shi ne wai ni zan yi hira da shi, a madadin murtala, amma ya yi waya, wai sai dai na je gidansa na yi recoding ɗin program ɗin, shi ba zai samu zuwa ba”Nabila ta waro ido ta ce “Saboda me?””Wai ba shi da lokaci, Nabila tsoro nake ji, ko zaki raka ni? Jibi in Allah ya kaimu ne zan je,ba na son rasa aikina, kuma ina tsoron ya cutar da ni”Nabila ta ce “Kash, gashi kuma nima zan je wani aikin ne, da na raka ki aminiya. amma menene a ciki, ke zuwa gidan ɗan majalisa ba cigabanki bane?”A raunane Sumayya ta ce “Tsoro nake ji Arfa””Sumayya, wani abun fa dole sai mun cire tsoro, tsoronki yayi yawa, ki yi addu’a, duk abun da ya same ki, gidan radiyon will be responsible, babu wani abu in sha Allah, ai mun riƙe addu’a”Yanayin fuskar sumayyan ya tabattar mata da gaske tsoron take ji.Sai dai ita ba ta ga abun tsron kamar yadda sumayya ta ɗaga hankalinta ba.Nan ta din ga jan ta da hira, har ta saki jikinta suka cigaba da hira, suka ci abinci tare.Sai daf da magariba ta raka Sumayya ta tafi gida.Duk da ƙirjin Arfa na tsananta bugawa, amma ba ta ji zata iya fasa abun da ta ƙudurta ba, domin kuwa sai ta ga ƙwal uwar daka, jibin nan za ta shirya ta sake komawa wurin liti.

Paid book ne ₦500 via 0009450228Aisha Adam jaiz bank

Sai shaidar biya ta 08081012143Special 1k, wanda za su jira complete document shi ma 1k ne.

Ayshercool 08081012143

Back to top button