Hausa novels

Halysaah Page 43 By Khaleesat Haydar

Juyawa Abdul yayi ya fice daga kitchen din ba tare da yace mata komai ba ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake zuba idonta har ta dena hango sa, jingina tayi da kofar kitchen din ta kai hannunta fuskarta dai dai inda Meemah ta mareta don sai a sannan ta fara jin zafin marin, fashewa tayi da kuka tayi me isarta kafin ta fito daga kitchen din tana tafiya a hankali ta tafi ta zauna kan 1 seater dake parlorn tana share hawayen da yaki tsaya mata, abubuwan da Abdul yayi ma Meemah ne suka dinga dawo mata a kai don hakan yayi mugun shock dinta, but she just don’t want to believe senior sister dinsa yayi harrassing haka har da koranta, to ko dai ita ce Aunty Aminan da suke ce ma Meemah don taga sosai suke kama da ita, tana ta zaune parlon bayan wani lokaci sai gashi ya fito daga dakinsa, sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, ya karaso cikin parlon yace “Kin yi breakfast din ne?” Da Authoritative voice yayi tambayar yana kallonta, hakan yasa ta ɗan rikice kamar mara gaskiya ta girgiza masa kai with fear all over her face, sai kuma ta mike da sauri ta nufi kitchen ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, shayi rabin cup ta hada sannan debi Irish kadan a plate don tension yasa ta rasa appetite dinta gaba daya , sai kuma ta tuna shi ma bata basa breakfast din ba, tunanin ko ta kai masa parlor ta fara yi don a kwanaki ukun nan Bedroom dinsa take kai masa breakfast din kamar yanda ya umarce ta, kamar munafuka ta makale jikin kofar kitchen din tana kallonsa tana son tambayarsa ko ta kawo masa breakfast din nasa parlorn amma ta kasa don bata san me zai ce ba kar yayi mata masifa, wayarsa kawai yake dannawa bai ma san tana wajen ba, juyawa tayi a hankali ta koma kitchen din a sanyaye ta hada masa breakfast din ta fito da shi parlor, jikin kujera ta tsaya a hankali tace “Ga breakfast din nan” Daga kai yayi ya kalleta, gabanta ya dinga faduwa ta sauke idonta daga kallonsa, jin bai ce komai ba yasa ta karasa har gabansa ta duka ta ajiye masa breakfast din, yace “Ke ina naki?” Taki barin su hada ido tace “Yana kitchen” Yace “Dauko” Mikewa tayi ta tafi ta dauko nata ta dawo tana kallonsa, yace “Ajiye ki ci a nan” Bata masa musu ba kanta a kasa ta zauna gefensa da ya nuna mata ta fara tuttura irish din kamar dole tana satan kallonsa ta gefen idonta, a hankali taga ya jawota jikinsa taji gabanta yayi mugun faduwa, calmly yace “I am a monster to you right?” Da sauri ta girgiza masa kai zuciyarta na bugawa, yace “Gashi nan, kin maida ni dodonki” Ita kanta bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, yayi kasa da murya yana zame hulan kanta yace “Now tell me what u want from me, tell me what’s on ur mind…. amma before then ki sani bazan taɓa rabuwa da ke ba saboda ina son ki Khaleesat, rabuwa dake will be the last thing i will do on earth no matter what, You know i love you genuinely from onset, i loved you wholeheartedly and i gave u the best of everything I could, i loved you even before you become the woman you are today, i love you since when u were just a 15 year old teenager tun baki girma ba, yea i know about my flaws but loving you is all that matters, not in the sense that abubuwan da nake yi are right, i am obsessed with you Baby, may be you can change me in ur own way….” Khaleesat ta rufe idonta tana jin kamar ta fashe da kuka, jin kalamansa take kamar ana soka mata mashi a kirji, Ya dora forehead dinsa a nata murya can kasa yace “Why not give me a chance and forgive my flaws Khaleesat?” Bude idonta tayi hawaye suka hau zarya a idonta, har cikin ranta taji bata son jin maganganun da yake mata, a hankali yace “Forgive me, i know i wronged you in all ways, but don’t forget ina sonki, ina kuma sonki ne saboda Allah, they are many beautiful ladies out der buh i chose you Khaleesat” Lokaci daya gaba daya tunaninta ya tafi kan Housemate dinta, kasa daurewa tayi ta fashe da matsanancin kuka, ya daura kanta a saman shoulder dinsa patting her softly, ta dinga kuka kamar an aikota, shi dai bai ce mata komai ba, sai da tayi kukan me isarta sannan ta hakura don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya daga kanta yana kallonta taki yarda su hada ido, breakfast dinta ya ajiye mata a kusa da ita, ba musu ta fara ci a hankali da tunani iri iri a ranta, muryarsa taji ya daki dodon kunnenta “Yaushe zaki gama period?” Gabanta yayi mugun faduwa, ta ajiye cup din shayin dake hannunta ba tare da ta kallesa ba, a hankali tace “Ai ban dade da farawa ba” Yace “Yau kwana hudu da farawan ki” Da kyar ta dake tace “A’a, uku ne…. first day din ai bana yi sosai…” Yace “Saura kwana nawa ki gama kenan?” Sosai gabanta ke bugawa, ta sunkuyar da kanta cike da karfin hali tace “Kilan nan da kwana uku ko hudu” Jin bai ce komai ba ta daga kai a ɗan tsorace ta kallesa, taga kallonta yake without blinking, sauke idonta tayi tana wasa da karamin cokalin dake cikin mug din shayinta, ya dauke shayin ya mayar gefe, taga ya kai hannu shoulder dinta zai sauke siririn hannun rigar dake jikinta, sosai hankalinta ya tashi amma bata ce masa komai ba gabanta na ci gaba da faduwa, ya sauke rigan gaba daya yana kallon bare chest dinta, hawaye ne ya cika idonta taki yarda su hada ido, can dai tayi karfin hali muryarta na rawa tace “Toh baka sha shayin ka ba zai huce” Yayi kasa da murya yace “Wa ennan zan sha… ” Momy ce tsaye parlor tana kallon Meemah dake rusa kukan bakin ciki uwa er yarinya, ga trolley dinta a gefenta, bacin rai ne karara kwance fuskar Momy da idanuwanta suka ƙankance tana huci, mai aikin gidan ce ta shigo parlon rike da bowl din pepper soup din da tayi ma Momy, cikin ladabi ta risina tace “Hajiya ga farfesun nan ya kammala” a fusace Momy ta figi throw pillow ta jefa mata tace “Don ubanki wuce ki ban waje ke da farfesun, baki ga magana nake bane zaki shigo min parlor kai tsaye, yau ga jahilar mata kai” a tsorace mai aikin ta juya da sauri ta bar parlon ta koma kitchen ta kullo kofar, Momy tace “Na kusa daina daukan tsinannun masu aikin nan don sun isheni haka kuma, na kori wancan shegiyar da ta shigo min parlor da yan uwan Alhaji da suka zo daga kauye babu izinina yanxu kuma an kawo min wannan jakar da ko kwana biyu bata yi ba ta fara nuna halayyan dabbobi” Ita dai Meemah kuka kawai take tana fyace hancinta da handkerchief, tsabar kuka idonta har sun suntume, Momy ta kara kankance idanuwanta tana kallon Meemah tace “Shi Abdallahn ne yayi maki haka Meemah?” Meemah ta hadiye wani abu da ya tokare mata wuya don bakin ciki tace “Momy da kin ga tijaran da Abdallah yayi min akan yarinyar nan ko, hmmm, ki bari kawai Momy, Momy kare bazai ci abinda Abdul yayi min ba, bayan zagi da cin mutunci wai ni ya kora a gidansa, kora irin ta walakanci” Momy ta zauna kan kujera with disbelief, duk da AC dake aiki a parlorn sai zufa take yi dama ga ta narkekiya, tana gyara zama tace “Ko dai ya sha wani abu ne Meemah??” Cikin rawan murya Meemah tace “Babu abinda ya sha wallahi Momy don lafiyan Allah ya dauko ni a airport muna ta hira, tare fa da ni duk aka yi tracking yarinyar nan tunda akwai wani tsohon saurayina wanda aikinsa kenan, amma wai yau akanta Abdallah zai min irin wannan tijara haka tun ba aje ko ina ba, duka duka fa kwananta yau hudu da shiga hannunsa, amma ya rufe ido ya zazzageni ya ci min mutunci ya koreni” Momy tayi wani murmushin takaici tana girgiza kafa tace “Kin ga abinda nake ta gudu kika kasa ganewa kenan ai ko? Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai taɓa hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa” Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace “To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba” Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace “Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci? Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?” Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace “Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza” Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace “Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki” Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace “Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta” Meemah da kanta ya gama kullewa tace “Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban taɓa yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye” Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace “Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili? A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri’a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara” Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki. Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it’s past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace “Khaleesat” Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace “Um” Yace “Say something” Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace “Say something pls” Da kyar muryarta na rawa tace “Ban san me zan ce ba” Yace “Say anything” Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai taɓa rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace “Kawai alfarma daya zan nema wajenka” Murya can kasa yace “Say it Khaleesat” Tayi karfin halin cewa “I don’t want you to hurt anyone because of me….” Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace “Ohk u mean ur Body Guards that sue me?” Ita dai kuka kawai take, Ya ɗan yi wani murmushi yace “I don’t think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn’t der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem…” Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace “To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition…” Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace “The first condition is that…. zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu…” Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace “Baza ki yi ba kenan?” Muryarta na rawa tace “Ban ce bazan yi ba” Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace “Bani da number ai” Yace “Amma aunt dinki na da shi ai… Call her and ask her to send you the number” Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace “Bani da numberta offhand” Yace “Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki” Ta fashe masa da kuka sosai tace “Why are you doing this plss Ya Abdul” Yace “Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too…..” Tana kuka sosai tace “No plsss…” Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via +234 803 810 3096_

Back to top button