Hausa novels

Mejo Najeeb Page 16 By Autar Alheri

“Jirginsu nasauka suka samu dandazon yaransu suncika airport ɗin harda captain Jameel dakuma captain Ameer babban yaron general aliyu kenan suna jiransu….cikin takonsu na isa da taƙama suka sauko daga cikin jirgin cikin sauri captain Jameel yabuɗewa mejo Najeeb ƙofa inda captain Ameer yabuɗewa general aliyu Shima, aiko suna shiga suma sauran sojojin duk suka shiga Hakan yasa motocin tashi atare suna saka jiniya cikin gudu kamar zasu tsaga kwalta sukabar airport ɗin…Hakan yasa duk wanda ke airport ɗinnan hankalinshi yakoma kansu sedai tuni sunyi gaba abinsu….kowannensu gida yanufa suna shiga tangamemen get ɗin gidan yawan gale kanshi suka danna hancin motocinsu ciki tare da nufar Perking space….acikin gidan kuwa dukkan mutanen gidan na perlor ciki kuwa hadda sajad babban yaron mama wanda shikebin Munir acikin yaran gidan Shima jiyane yadawo daga wurin training.Baki Hajiya Umma tawashe tana faɗar “lale marhabin da mazan fama andawo kenan…suma duka yaran gidan murna sukashigayi ciki kuwa hadda mansura domin Allah yagani tana kwaɗayin ganinshi tayi kewarshi sosai kamar zataci babu..agefen ummi kuwa fargaba ce fall ranta domin ɗazu sukayi wayada ƙawarta juwaira tace mata Tanakan hanya shiyasa sam bataso yah najeeb yadawo yanzuba taso ace har juwaira tagama zamanda zatayi takoma bataga yaya najeeb ba domin tasan tabbas inyasan manufar juwaira akanshi to ƙaryarta taƙare…tanacikin wannan tinanin ne tajiyo ihun Siyana tana faɗar “oyoyo yah najeeb na yadawo oyoyo yah najeeb..Hakan yasa tadawo cikin nutsuwarta izuwa wannan lokacin kuwa tuni mejo yaƙaraso cikin perlor ana gaisawa dashi.Cikin girmamawa ƙannen nashi kegaidashi inda Munir da sajad suka bashi hannu sunayin musabaha daganan kowannensu yarun gumeshi suna murnar ganin yayan nasu.. sajad ne yabuɗe baki ahankali yace ‘yah najeeb I miss you so very much wlh yafaɗa yana share ƙwallar idonshi…bakinshi yaɗan ciza ahankali yanajin son yaron harcikin ranshi Yajima kamin sajad yaji saukar cool voice ɗinshi cikin dodon kunnen shi yana faɗar “miss you too my little bro ya school ɗin??? Tatambaya kamar bashine yayi maganar ba…ajiyar zuciya sajad yasauke kamun yaƙara ƙanƙame najeeb ɗin yace “alhmdllh yah najeeb amma ba daɗi wlh…se awannan karon najeeb yayi guntun murmushi kafin yace “to dama wayacema akwai daɗi…kafin sajad yayi wata maganar sukaji ihun Siyana tana faɗar “wayyo ita Allah yah najeeb yashareta yah sajad kawai yakeso…aiko duk wanda ke perlor seda yayi dariyarta…shiko dafe kanshi kawai yayi tare da duƙawa yaɗauketa bayan yacire sajad daga jikinshi kanshi yadafe kaɗan domin duk yagaji jima yakeyi duk sun haddasa mishi ciwon kai seda yaɗan yamutsa kyakkyawar fuskarshi kana yace “sorry angel daga Hakan yashiga gaida iyayen nashi.Cikin sakin fuska mama ta amsa mishi tana mishi barka da zuwa yayinda Hajiya Umma tamiƙe tsaye cikin murmushi tariƙo hannunshi suka haura pert ɗinshi da tuni Ummi tabuɗewa captain Jameel harya kaimishi laptop ɗinshi da wayoyinshi yaficewarshi…da kallo ƙurillah mansura tabishi harseda yaɓacewa ganinta kana tasauke ajiyar zuciya tana matse ƙwallar idonta tanason gaidashi amma tana shakku Hakan yasa batace mishi komaiba har suka ɓacewa ganinta…har cikin bedroom ɗinshi takaishi ta zaunar dashi abakin bed kana tashiga bathroom tahaɗa mishi ruwan wanka masu ɗimi tafito domin tasan tabbas yanzu wankan yafi buƙata, tana fitowa tace “my son jekayi wanka kahuta sekazo Kaci abinci kajiko? Kai kawai yaɗaga mata yana murmushi…itako hannun Siyana tariƙo tana faɗar”auta bari yayanki yayi wanka seki dawo kinji takarasa zancen tana saukowa da ita ƙasa…..shiko Mejo kayan jikinshi yarage tukunnah yamiƙe yasakawa ƙofarshi key kana yashiga bathroom ɗin nanma seda yasakawa ƙofar bathroom ɗin key sabida tsaro kana yacire boxes ɗinshi yafara wanka…sedai wani abin mamaki ko wankan begamaba yaji kamar sautin magana ƙasa ƙasa, shiru yayi yadakatarda wankan dayakeyi anan yaji ana faɗar “washh Allahnaa wayyoo sweet najeeb zanso ganin ranarda zanji jarumtarka ajikina wayyoo aranar Sena Suma uhmm ahhhh.. kowacece tafaɗa cikin shauƙi gadukkan alamu tafara lulawa duniyar begen najeeb ɗin…wani irin waro ido mejo Nejeeb yayi cikin mamaki da tsintsar kaɗuwa yajanyo towel yaɗaura tareda nufo ƙofar sedai yana ɗora hannu yabuɗe yaji ƙofar abuɗe domin yacire key Hakan nanufin wani key akasaka daga waje aka buɗe ɗakin har akashigo aka buɗe mishi bathroom ko yaya?? Yatambayi kanshi? Kuma bashida amsar tambayar..cikin hanzari yafito perlor amma bakowa, dafe kanshi yayi dake tsananin sara mishi yana tinanin wannan tashin hankalin acikin gidansu ace mace na leƙenshi wannan wanne irin bala’ine? Shiru yayi yana tinanin kalaman dayaji daga wannan muryar dayakasa gane kota wacece wai tanason jin jarumtarshi, innalillahi wa’inna ilaihiraji’un kaddai cikin ƙannenshine wata ke sha’awarshi, yasake faɗar Hakan aranshi Afili kuma yace “ya salam tokodai Basu bane koma wacece ai agidannan take tomiyasa??? Miyasaaa ? Yafaɗa yana kaiwa gadonshi naushi..cikin sauri sajad yaƙarasa shigowa jin ihun yayan nasu yana faɗar “subahanallah yah najeeb lafiya kuwa?? Miyasameka Hakan? Yatambaya ganin duk yayan nashi abirkice yana riƙo hannunshi dayake dukan bedside table dashi.Shiru mejo yayi yanasauke nunfashi tare da ɗora kanshi ajikin ƙannen nashi domin jiyakeyi tamkar zuciyarshi zata buga sabida wannan tashin hankalin atake jikinshi yaɗauki rawa sekawai kanshi yafara juyawa alamar ciwunshi nason tashi wata irin miƙa yafarayi yana karkarwa haƙoranshi suka fara haɗuwa…ido sajad yazaro ganin abinda kefaruwa yatabbatarda ciwonshine domin duk wanda ketaredashi yasanda wannan matsalar. Kuka yasaka yana faɗar innalillahi wa’inna ilaihiraji’un Allah yarabakada wannan ciwon yah najeeb…ciwo kuma wanne ciwo?? Hajiya Umma tafaɗa tana ƙoƙarin shigowa bedroom ɗin, sedai ayanayinda Taga Najeeb ɗin shine yabata amsar tambayarta batareda sajad yace komaiba illa kukanshi dayakeyi…..kuka tasaka cikin tashin hankali take Kiran Sunan najeeb tana shafa kwantacciyar sumar kanshi nason ganin yabuɗe idonshi dake lumshewa.. amma ina bayama jinta ɓalle ba’asin amsawa..ganin babuwani sauƙi Sega Allah yasa ta ɗauko wayarshi dake kan gadon tashiga Kiran doctor ziyad cikin kuka take gayamishi abinda ke faruwa…Allah sarki bawan Allah sosai hankalinshi yatashi amma ba yadda zeyi domin ciwon abokin nashi bana asibiti bane…ajiyar zuciya yasauke kamun yace”ganinan zuwa Hajiya Umma allah yabashi lafiya…. yanke wayar tayi kawai batareda tace mishi bakomaiba, Dede lokacinda Munir yashigo ɗakin shima Ummi nabiyedashi abaya ganin duk Suna’nan kuma sunji shiru basu dawoba, ganin halinda ake cikine yasa duka jikinsu yayi sanyi. sosai hankalin Ummi yatashi ganin abinda kefaruwa da yayan nasu Hakan yasa Itama tasaka kuka seya zamana babu me rarrashin wani a ɗakin Munir ne kawai yayi ƙarfin hali Shima dan karsuga gazawarshi ne amma Allah yasani hankalinshi yatashi ba kaɗan ba…idonshine suka fara kafewa Hakan yasa Ummi fita aguje tasamu mama nazaune a perlor tafaɗa jikinta tana rusar kuka.”Kee Ummi lafiyarki kuwa?? Miyafaru ne? Tatambaya hankali atashe “Cikin kukan take faɗar wlh mama yah najeeb bashida lafiya sosai dan Allah kizo akaishi asibiti karya mutu yabarmu wlh bashida lafiya taƙarasa tana sakin wani kukan metaɓa zuciya…tinda Ummi tafara magana Hajiya umma ke kallonta hartakai ƙarshe, jingina kanta kawai tayi ajikin kujerar datake kai tare da lumshe idanuwanta tace Allah yabashi lafiya Ummi kudena mishi kuka yayanku addu’ar ku yakeso bakukaba kinjiko. Tafaɗa tana shafa kanta…ɗaga matakai kawai Ummi tayi batareda tace komaiba sekuma tamiƙe dasauri kamar wadda aka tsikara tafita daga perlor mama jin sallamar doctor ziyad a general parlor, Koda tafito tuni ya haura pert ɗin mejo Najeeb ɗin Hakan yasa tamara mishi baya.Doctor ziyad nashiga yagansu duk sunkewayeshi numfashin shi yayi sama amma yakasa dawowa duka cikin ɗaga murya yace “Munir kuɗaukoshi muje asibiti mana…se alokacin duk suka kulada doctor ziyad ɗin aiko suka shiga rige rigen ɗaukar shi sedai kafin sugaiga tallaboshine yashiga sauke ajiyar zuciyar awahalce. Dakatawa sukayi dukkansu suna kallonshi har numfashin nashi yadedeta yafara ƙoƙarin buɗe blue eyes ɗinshi dasuka koma red lokaci ɗaya…mutanen dake kanshi yashiga bida kallo yayinda Shima ɗin kallonshi sukeyi cikin mugun al’ajabin wannan sihirtaccen ciwon nashi dabaya ƙaunar Akira asibiti…ɗan yamutsa kyakkyawar fuskarshi yayi kana yabuɗe baki ahankali yana faɗar lafiya?? Aikafin yarufe bakinshi Ummi tadayi mutuwar tsaye tasheƙo aguje tafaɗa jikinshi tareda ƙanƙameshi tana sakin marayan kuka wanda daga jinshi kasan daga kasan zuciyarta yake fita…ido yazaro ganin yadda yake dagashi se towel tawani maƙalƙaleshi yana ƙoƙarin cireta daga cikinshi yaji sajad yahaɗe daga ummin harshi Shima ya rungumesu yana kukan begama tantance wannan abun nasuba yaji Munir ma ya haɗasu duka yarungume kuma dukkansu kukan sukeyi..idonshi kawai yaruntse daƙarfi domin bayada wani zaɓin dayawuce karɓarsu koba komai suɗin jininshine kuma abin soyuwa agareshi haɗe hannayenshi Shima ya rungumesu dukkansu aiko Ummi najin Hakan tashiga magana cikin kuka take faɗar “please yah najeeb karka mutu kabarmu Kaine yayanmu jigonmu abin alfaharinmu dan Allah yah najeeb kabari aduba lafiyarka wlh Allah bazan iya jurar ganinka acikin wannan halinba balle awayi gari Babukai acikinmu narantse aranar zan iya haɗiye zuciya please katausaya mana taƙarasa zancen tana ƙara wa kukanta ƙarfi….wani irin abu najeeb yaji yatukare mishi maƙoshi tabbas ya yarda Ummi nasanshi ko acikin ƙanenshi duba da yadda yakejin bugun zuciyarta ayanzu amma miyasa zuciyarshi ke zarginta shimma mi Ummi tasani agun namuji da har zeyi tinanin itace ke mishi wannan abin? kanshi yadafe dasauri jin yadda ta tsananta kukanta, daƙyar ya iya buɗe baki cikin cool voice ɗinshi me daɗin sauraro yace “it’s ok Ummi stop crying please kinjiko I’ll going to hospital in sha Allah okay. “Kaitaɗogo ahankali inda dukkansu ma ɗagowar sukayi suna kallonshi jin abinda yace kamin Ummi tace “yah najeeb you’re promise me?? Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi kana yace “I promise. Murmushi taƙara yi tareda koma rungumeshi kana tamiƙe dasauri tafita daga ɗakin dukkansu ƙanen nashi murmushi sukayi inda sajad yace “thank you so much big bro..shidai bece mishi komaiba illa dungure mishi kai dayayi..Hajiya Umma kuwa ƙwallar idonta kawai tashare tare da shafa fuskar najeeb ɗin tafice se dakin yarage daga doctor ziyad se Munir dakuma sajad..duban kanshi yayi yaga yadda yake gasu kuma duk sun kewaye shi yasan dayayi wani dogon motsi towel ɗin jikinshi ma ze iya cirewa Hakan yasa yaɗago yana dallah musu harara..aikuwa suka miƙe suna murmushi suka bar ɗakin domin sarai sungane miyake nufi domin Najeeb fa akwai kunya da tsare gida sam bayasan reni ko kaɗan balle kuma ƙanenshi suga suturarshi..suna ficewa doctor ziyad yayi dariya yana kwanciya gefen gadonshi tare da faɗar kaide bazaka canjaba mejo Allah yashiryeka..ido yabishi dasu natambayar to Kai ubanme yazaunar dakai?…wata irin dariyace takuɓucewa doctor ziyad seda yayi abarshi me isarshi kana yace “Kaine kazaunar dani ai wlh sedai kada kasaka kayan ka tabbata ahakan domin ba inda zanje yana gama faɗar Hakan ya gyara kwanciyarshi.jin abinda yace ne yasa mejo miƙewa kawai yashige bathroom abunshi…!

Back to top button