Hausa novels

Halysaah Page 16 By Khaleesat Haydar

Ko da wasa Khaleesat bata ba Safiyyah labarin abinda ya faru tsakaninta da Ajay ba, amma fa bata da rest of mind gani take kamar zai iya dawowa gidan at anytime, upon all her restlessness bata ji tayi da ta sanin abinda tayi masa ba, dama haushi yake bata, Safiyyah na kallonta tace “Ke kwana biyu shiru banji kince ga abinda Abdul yayi maki ba ko dai ya fara canzawa ne? This is so unusual, ko baki gaya min ba in dai ya maki wani abu you are always moody in school, ta haka nake ganewa” Khaleesat na powering laptop dinta ta tabe baki tace “Ni ina naga wannan time din yanzu ga exams a gabana” Safiyyah tace “Atoh dai, wallahi naji dadin da kika fara daukar shawarata kina fita sabgarsa, sauranki abu daya yanzu” Khaleesat ta daga kai ta kalleta, Safiyyah ta gyara zama tace “Saura ki fara mayar masa da magana, in ya gaya maki daya ki gaya masa biyar” Ita dai Khaleesat bata sake ce mata komai ba tana neman softcopy na course din da za su yi studying tare da Safiyyah. Bayan tafiyar Safiyyah… Khaleesat ta wanke utensils da suka yi amfani da sannan ta wuce dakinta, wayarta ta dauka ta shiga WhatsApp don ganin ko Ummanta tayi mata reply din message da ta ajiye mata daxu, wajen karfe goma da rabi tana shirin kwanciya wayarta ya fara ring, dauka tayi taga Abdul ne ke kiranta, ta dinga kallon wayar, tun sanda Ummanta tace mata tana ganin kamar lkci aka tsayar take wani jin tsanarsa a zuciyarta, gashi yaki gaya mata ko da gasken an tsaida lkcn ko ba a tsayar ba don Ummanta ba wai ta tabbatar bane ita ma a gari ta ji, dama tana Nigeria din ne ta san gun warce zata je taji ko hakan ne ko ba haka ba, ɗaga kiran tayi kafin ya katse ta kai kunne, muryarta kamar me bacci ta gaishesa, ya amsa, a hankali tace “Ya aiki?” Yace “Lafiya lau” Shiru tayi bata sake cewa komai ba, yayi ƙasa da murya yace “I don’t know, kawai ina missing din ki ne yau, i want to be with you Baby” Ta kauda kai kamar irin yana kusa da ita din nan tace “Um” Yace “Yaushe za ku fara jarabawan?” Tace “Nan da wata daya” A hankali yace “Ohk, sai da safe, naga kamar kin fara bacci” Tace “Um, ina son tashi inyi karatu ne anjima shi sa na kwanta da wuri” Yace “To ci gaba da baccinki, sai mun yi magana” Daga haka ya katse wayar, ta jefar gefenta ta ci gaba da chatting da take da Ummanta. Washegari lahadi Khaleesat na zaune dakinta tana morning Supplications dinta taji ana kwankwasa kofar parlor, wayarta ta jawo tana duba agogo taga bakwai ya wuce, ta daure ta mike tana tafiya a hankali ta fito parlor, bayan ta karasa bakin kofar with calmness tace “Waye?” Taji muryar Housemate dinta yace “Good morning” bude kofar tayi ta koma gefe ya shigo, sau daya ya kalleta yace “How was ur night” Ta kulle kofar tace “Alhmdlh” Materials din hannunsa ya ajiye saman 1 seater sannan ya kwanta kan doguwar kujera, ita dai bin sa tayi da kallo taga har ya kulle idonsa yana gyara kwanciyarsa alamar bacci zae yi, tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ta karasa azkar dinta sannan ta kwanta. Har wajen karfe daya na rana Khaleesat bata fito dakinta ba, ta ɗan juya daga kwancen da take tana kallon kofar dakinta jin ana knocking, kiranta taji Housemate dinta ke yi, mikewa zaune tayi still tana kallon kofar amma bata sauka daga kan gadon ba, Calmly tace “I can hear you” Yace “Are you alright? Naga kamar baki yi breakfast ba ko?” Shiru tayi bata ce komai ba, bude kofar taga yayi, ta gyara blanket din jikinta tana kallonsa, ya tsaya daga bakin kofar dakin yace “Hope nothing?” Ta langwabar da kai tace “Nothing” Yace “To me yasa baki fito kinyi breakfast ba or are you fasting? Beside today is sunday” Ta kauda idonta tace “Kawai dai…” Sai kuma tayi shiru, ya karasa cikin dakin yace “Kawai dai me?” Kamar baza tace komai ba sai kuma dai tace “Ina jin ciwo a kafana ne” Yace “Ciwo a kafa kuma? Yana maki haka ne?” A hankali tace “Once a while” Shiru yayi jin abinda tace, can yace “Then what is the cause?” Ta ɗan kallesa, sai kuma ta bude hannu alamar bata sani ba, yace “Kun taɓa zuwa hospital a kan hakan?” Ta dai yi shiru without looking at him, sai kuma tace “It’s fine, i will get better before evening in sha Allah” Ya juya as if trying to diagnose without examination the cause of her leg pain at her age, sau daya ya kalli gaban dressing mirror dinta sai kuma ya juyo yana kallonta yace “Ok i get, Allah ya sauwake…” Ta ɗan kallesa, yace “Try getting a hot shower, you will feel better” Juyawa yayi ya fita daga dakin, a hankali Khaleesat ta koma ta jingina da pillow, ko tashi tsaye bata jin zata iya a yanzu dai, kilan zuwa can anjima ta ɗan ji relieve before she can stand up and do anything, kiran Abdul ne ya shigo wayarta ta kife wayar taki dagawa don ko magana bata so, after some minutes ta kalli kofarta jin knocking at the same time ya bude kofar dakin ya shigo ciki rike da cup din hot chocolate, sauke idonta tayi daga kallonsa ya karasa har side din da take ya duka yana mika mata Mug din hot chocolate din yace “Try drinking this, will get u pain reliever now” Ta amshi Mug din without looking at him a hankali tace “Thank you” Yace “You are welcome” Daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, yana fita kiran Abdul ya sake shigowa wayarta still taki dagawa daga karshe ma tayi silencing wayar, khaleesat na gama shan hot chocolate din ta ajiye cup din a bedside drawer sannan ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, kamar zata kira Safiyyah daxu wajen karfe sha biyu sai kuma ta fasa hoping the ache will subside, har ta fara bacci Housemate dinta yayi knocking wajen karfe biyu almost 20 mins bayan fitarsa daxu, sai da ta amsa sannan ya bude kofar, ita dai bata juyo ba, ya zaga ta inda take calmly yace “Are you sleeping Halysaah?” Ta bude ido tana girgiza kai, ya ajiye ledan abincin hannunsa da pain reliever da ya siyo mata yace “Baki yi hot shower da nace kiyi ba?” Tace “Zan yi” Yace “Ohk ga maganin sai ki ci abinci ki sha” Ta mike zaune without looking at him, a hankali tace “Thank you” Yace “Zan fita but i will come back around 6pm in sha Allah” Tana kallonsa tace “Toh makullin gidan fa?” Ɗan murmushi yayi yace “Ai a jikin kofar kika bar sa daxu da kika bude min da safe” Tace “Amma baza ka tafi da shi ba ai” Yace “To taso ki kulle kofar” Ta wani kallesa, er dariya yayi yace “Shi fa Ajay nasan yanxu kuma ya mance abinda ya faru tsakanin ku, may be sai ranan da ya kara ganinki zai tuna, but for now i am assuring you ya mance wallahi he is even busy with his upcoming defense, beside you misperceived him, Ajay is more than nice and calm, ba shi da matsala, kawai dai shaidan ne ya saka rashin jituwa tsakaninku tun a ranan da ku ka hadu” Khaleesat dai ta kyabe baki don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata taɓa yarda da abinda yake fadi ba, Jay yace “Baki yarda ba ko?” Ta buda ido sosai tace “To dama saboda me zan yarda?” Dariya kawai yayi yace “Take care of ur self Halysaah, in kin ci abincin ki sha magani, let me get you bottled water” Daga haka ya nufi kofa ita dai ta bi sa da kallo har ya fita, sai gashi ya dawo mata da ruwan gora mara sanyi ya ajiye a inda ya ajiye mata ledan abinci da magani wato bedside drawer, yace “See yah later” a hankali tace “Thank you, and pls do not mishandle the key” Murmushi kawai yayi ya gyada mata kai ya fita daga dakin ya kullo mata kofar, ta sauke idonta kasa, after some minutes ta dau ledan abincin da ya ajiye mata a hankali tana budewa don ganin abinda ya siyo mata. Karfe shidda saura Khaleesat na zaune kasan dakinta ta kwantar da kanta jikin gado tana voice note da Ummanta, zuwa sannan she is feeling very much better don har ta gyara dakinta ta wanke bandaki tayi wanka, parlor ne dai taji bazata iya gyarawa ba, wajen karfe hudu suka yi chatting da Safiyyah tace mata zata zo karfe bakwai, Khaleesat ta dan yi jim bayan taji kamar an bude kofar gidan, gabanta ne ya fadi bayan Ajay ya fado mata, ta ajiye wayar hannunta a hankali tana kallon kofar dakinta, after few minutes taji an yi knocking kofar dakin, she felt a bit relieved, with calmness tace “I can hear you” Taji muryar Housemate dinta yace “Can i open the door?” Tace “Okay” bude kofar dakin yayi yana daga bakin kofar a tsaye yace “Good evening Housemate, how are you feeling?” Tace “Da sauki” Yace “Are you sure?” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, ta dan kwantar da kanta gefen gado tace “It’s better than before” Yace “To Allah ya sauwake, where you able to go to the kitchen?” Ta gyada masa kai, yace “Ohk” Har zai kulle mata kofar sai kuma ya tsaya yace “Ko mu dan yi strolling as exercise, around the neighborhood, it will help you feel much better too” Khaleesat ta daga ido ta kallesa, yace “I will be waiting for you at the parlor, make sure to put on ur jacket cause it’s freaking cold outside” Yana fadin haka ya fita daga dakin, Khaleesat dai na ta zaune kamar me nazari, it took her almost 5 mins of deciding kafin ta mike a hankali, veil dinta kawai ta dauka ta yafa ta dau wayarta tana tafiya a hankali ta fito daga cikin dakin, tsaye ta gansa ya jingina jikin pillar dake kusa da study area yana danna wayarsa daya hannunsa rike da jacket dinsa, yana ganinta yace “Are you ready? Where is ur jacket?” Karasawa yayi inda take tsaye yace “It’s cold outside” Yana fadin haka ya ajiye mata Jacket dinsa kan kujeran dake kusa da ita yace “Use this, bari in dauko wani” Dakinsa ya koma ita dai ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo parlon with another Jacket, ya saka a kan rigar jikinsa yace “Mu je” Ta sauke idonta ta dau Jacket din nasa, Kofar parlon ya nufa ta bi bayansa har suka fita daga parlon, ya kulle kofar ya kalleta yace “Na lura kina son so much perfume ke dai” Ta girgiza kai tace “A’a ni ban sa ba yanzu” Yace “Ohk” A tare suke tafiya with nobody saying anything, tun ba su kai ko ina ba taji tana jin sanyi sosai, hakan yasa ta ɗan saci kallonsa sannan ta saka jacket din hannunta yace “Ai na zata baza ki sa ba kina forming big gal” Kawai dai tayi murmushi bata ce komai ba, tana jin kamshin turarensa da ya cikata na jikin Jacket din, dai dai yake tafiya da ita to keep same pace with her, slowly suke tafiyar with absolute silence har suka yi nisa away from home, Jay yayi breaking silence din yace “Soon za a fara snow” Tace “In sha Allah kafin nan mun gama Exams dinmu” Zai yi magana wayarsa ya fara vibrate ya ciro a aljihunsa yana duba me kiransa, ta gefen ido ta kalli wayar tasa taga Ajay, yayi silencing wayar ya mayar aljihunsa, ta tabe baki tace “Shi dole sai ya dinga damunka da kira ne as if you are with his kidney?” Jay yayi dariya yace “Kidney ai me sauki ne, cewa za ki yi kamar life dinsa na wajena dai, a rana sai ya kirani sau ashirin in banyi hankali ba” Khaleesat ta kyabe baki sai ga shi ya sake kiran wayar, Jay ya kara ciro wayar yayi picking ya sa Hands-free yana tafiya yace “What again?” Daga daya bangaren Ajay yace”I need ur laptop, zan duba references dinka, na mance zan shiga schl gobe, i am outside with my frnd now” Jay yace “Da laptop din na fita ai, kuma i am not coming back home anytime soon” Ajay yace “Gidan wannan mara kunyan ka koma kenan? Wai are you even okay Bruh? Me kake yi da wannan yarinyar da ya sa kake zama gidanta? Ko iskanci ka fara ne? In ma iskancin zaka yi why with that little local brat pls?” Jay that was trying not to laugh yace “Kai kar ka bata min rai fa” Ajay yace “On a serious note idan baka daina zuwa gidan nan ba i promise you am gonna report you back home kasan karamin aikina ne hakan ko?” Jay yace “In ka fasa, kai duk takurani da kake da yan iskan abokanka a can gida ban kai report ba sai ni da na bar maka gidan for peace to reign shi ne zaka kai karata? To references din ma baza a nuna ba, go and sort ur self out” Yana kai wa nan ya katse wayar ya mayar cikin aljihu, ita dai Khaleesat bata kallesa ba kuma bata ce komai ba amma har cikin ranta take jin Ajay bai mata ba, she doesn’t like him or anything concerning him, ta tsani mutum that is too pompous and proud of himself, Jay yace “Baya karatu fa, in ma wani aiki ne sai dai kai kayi ya gani sannan yayi nasa, har ma nasan yafi naka at the end” Khaleesat tace “To me yasa har yanzu ba a koresa ba daga makarantar?” Dariya sosai Jay yayi yana kallonta yace “Baya karatu doesn’t mean he is dull Halysaah, kinsan Genius? That is who Ajay is, he is naturally gifted, he graduated as one of the best medical student during our degree program in this state and masters, kuma kar kice wani karatu yake, mu ne dai sai mun yi karatun za mu wuce” Yana murmushi ya kare maganar, Khaleesat ta wani kyabe baki kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace “To ai gwara kai karatun kayi ka wuce, shi kuma banza kawai yake ci” Jay na dariya yace “Ai shi sa na bar masa gidan cause idan na ci gaba da biyesa da abokansa wucewa zai yi ya bar ni, su kansa abokan nasa ina tausaya masu biyesa da suke” Khaleesat tace “Shi ne yasa kake Co-living?” Yace “Yeah, shekaranmu na karshe kenan idan Allah ya yarda so i need much privacy to study very hard to earn my PhD, in kana tare da Ajay ba wani abun arziki da zaka yi in dai bangaren karatu ne, sannan baya barina inyi bacci sosai, nuisance ne shi fa, Ya Subhanallah” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta sauke idonta, yace “Year nawa kike yanzu?” A hankali tace “Year 3” yace “Kince Pharmacy ko?” Ta gyada masa kai, yace “Kin kusa gamawa kema ai in sha Allah” ita dai tayi shiru bata ce komai ba suna ci gaba da tafiya slowly, ita ce tayi breaking silence din after almost 10 mins da ya biyo baya tace “You know him back home?” Jay ya kalleta yace “Wai Ajay? Yeah he is my favorite, yanzu ma dai kin ga budurwa nake nema masa bashi da mashinshiniya ko daya wallahi” Khaleesat tace “Ashe bazai taba samu ba, ai he is way too rude and full of himself, wacece zata yarda ta auresa in dai ba auren dole aka mata da shi ba, ko makala mata shi aka yi?” Jay dai dariya kawai yake yana kallonta yace “Ya kai Saurayin ki?” Nan da nan mood dinta ya canza, taki ce masa komai tana ci gaba da tafiyarta, yana kallonta yace “Naga kin yi shiru ko compare and contrasting kike yi a zuciyarki? Tell me pls ya kai saurayinki?” Without looking at him tace “Kamar lokacin sallah yayi, and it’s getting dark already” Yace “Ke ina ruwanki da sallah tunda ba yi kike ba?” Khaleesat was dumbfounded jin abinda yace, ta kasa kallonsa kuma taki basa amsa still walking slowly, Roadside chair ta hango ta tafi ta zauna, ya karasa wajen yace “Ko har kin gaji ne?” Tace “To da bazan gaji ba, muna ta tafiya for almost an hour now” Yace “Akwai wani Eatry a area din nan, mu je sai mu yi dinner before going back home, the eatry isn’t far away from here” Khaleesat tayi shiru, ta san Eatry din da yake magana don sun taɓa zuwa da Abdul kuma abincin wajen shegen tsada ne da shi, yace “Let go” Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya, hakan ya sa ta mike ta bi bayansa, ya jira har ta iso inda yake sannan suka ci gaba da tafiya a tare har suka isa Eatry din, suna shiga ta kalli Jay that was grinning kamar yaga wanda ya sani a cikin Eatry din, lkci daya ta hango Ajay that was sitted da wata baturiya a cikin eatry din yana mata magana, ga abinci kala kala a gabanta, shi kuma ruwan gora ne kawai a gabansa, Khaleesat ta dauke idonta speaking calmly tace “I think zan tafi gida kawai, dama ba wani yunwa nake ji ba, i will order a Lyft in koma gida” Jay ya riko gyalenta don har ta juya zata fita yace “C’mon Halysaah, so kike ya kara raina ki, kina fita zai yi zaton tsoronsa ne yasa kika kasa shigowa kika fita and he will be very happy, kawai kiyi fuska ki tafi ki zauna” Khaleesat ta tsaya bayan ta ɗan yi nazarin abinda Jay yace, kuma fa haka ne zai yi zaton tsoronsa take, hakan yasa ta karasa Jay na biye da ita a baya ya jawo mata kujeran dake facing inda su Ajay ke zaune ta zauna, Jay ma ya zauna sannan ya kalli direction din Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, Jay ya daga masa hannu with smile all over his face alamar Hi, Ajay ya dauke kai kamar bai taɓa saninsa ba a rayuwa, Jay ya daga kafadarsa yana murmushi sannan ya dau menu dake saman table ya mika ma Khaleesat yace “Duba abinda zaki ci” Ta amshi Menu din tana kallo, cikin few minutes Jay ya saka masu order aka kawo masu abincin, duk da Khaleesat tana facing din Ajay ko da wasa bata yarda ta kallesa ba, tayi kamar bata san da shi a Eatry din ba, Jay kuwa cin abincinsa kawai yake with full concentration not minding her in his front, lkci lkci Khaleesat ke kallonsa, ta lura he doesn’t joke with food and sleep for anything, dariya ma ita yake bata, ita kam a hankali take cin abincin gabanta, ya daga kai ganin bata wani ci Crab patatoe Chips din gabanta ba yace “Should i fetch some of urs?” Ta wani kallesa tace “Do you have an extra stomach?” Bai san sanda yayi dariya ba yace “I don’t understand an extra stomach?” Tana kallonsa calmly tace “Naga duk kai ka kusa cinye abincin kan table din nan” Jay ya bude ido sosai yace “Har da sharri? Me da me na ci a table din?” Ta tallabi chin dinta tana murmushi tana kallonsa wanda har sai da dimples dinta ya lotsa, Mistakenly ta daga ido suka hada ido da Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, nan da nan murmushin dake fuskarta ya bace ta sha kunu, Jay bai ma san tana yi ba don tuni ya ci gaba da cin abincinsa har ma ya diba na gabanta, Khaleesat ta kalli wayarta dake vibrate kan table, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, Jay ya daga kai ya kalleta yace “Ba kiran ki ake ba?” A hankali tace “Na sani” Yace “Why are you not picking?” Tayi shiru, sai a sannan ta tuna fa ashe ya kirata severally bata daga kiransa ba, Jay yace “Ko de saurayinki ne?” Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, yace “Ki daga mana kar kiyi laifi” Sauke idonta tayi ta daga kiran a hankali ta kai kunne tare da sallama cikin sanyin murya…..07087865788✍🏻

Back to top button