Rahama Sadau Da Shatu Garba Mata biyu da suka fi shan ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta
Akwai ce-ce-ku-ce a Arewacin Najeriya game da yadda mata ke shiga gasa, musamman idan jikinsu zai fito fili. Wasu ’yan Arewa na barin ’ya’yansu mata su zabi fim a matsayin sana’a, wasu kuma ba sa bari. Har ila yau, yawancin al’ummar Hausawa na kallon Gasar Ƙawa a matsayin wata gasa marar kyau da ya kamata a hana ta a yankin.
Rahama Sadau da Shatu Garko wasu mata ne ‘yan Arewa. Rahma Sadau Jarumar Kannywood ce kuma ta fito a fina-finan Nollywood. Sau da yawa dai an sha sukar ta kan fitowar ta a Nollywood da kuma yadda ta ke nuna rashin kunya. Wannan suka dai ya kai kololuwa ne a lokacin da Rahama Sadau ta fito a wani faifan bidiyo na hiphop tare da Classiq, wani mawakin Hausa na jihar Bauchi. Wannan ya haifar da zafafan cece-kuce da ka-ce-na-ce, musamman yadda Classiq ya rungume ta a faifan bidiyon. An kuma ga Rahama Sadau tare da Akon, fitaccen mawakin nan dan kasar Amurka, jim kadan bayan bidiyon ta da Classiq.
KARANTA:
✓ Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko
✓ Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power
✓ Kano State School Of Nurses and Midwife Enterance Examination 2021/2022
A kwanakin baya ne Rahama ta saka hotunan ta a Instagram da Facebook tare da jaruman fina-finan Indiya da jaruman fim wanda hakan ya nuna cewa ta yiwu nan da nan ta fito a fina-finan Bollywood.
Ba a san Shatu Garko ba kafin nasarar da ta samu a gasar kyau. Lokacin da labarin nasarar ta ya bazu, mutane da yawa sun yi mamaki, musamman saboda sunanta na dauke da sunan karamar hukuma a jihar Kano. Sai dai abin da ya biyo bayan nasarar da ta samu daga Arewa shi ne suka da kuma barazana daga hukumar Hisbah, ‘yan sandan da’a da ke aiki a jihar Kano. Amma yayin da Shatu Garko ta zama Sarauniyar Kyau ta Nigeria, ta nuna farin cikinta duk da barazanar da ake mata.
Wadannan ‘yan mata biyu sun tsallaka kan iyakar arewacin Najeriya domin samun nasara a sana’o’insu. Sun tabbatar wa duniya yadda asalin mutum da jinsinsa ba abubuwan da ke tabbatar da nasara ko gazawa ba.