Novel Document

Mabaraciya Hausa Novel Complete

Description/Story:

Mabaraciya Hausa Novel Complete! Complete Hausa Novel Document Written By Sakna

 

Description Of Mabaraciya Hausa Novel Complete

Ni halittace wacce take tamkar hawainiyah, da take fitowa a launi daban daban.

A wanni wajen ma inaga nafi hawainiyar saboda ita idan ta sanja launi bata bayyana a wata siffah ta daban.

Wasu na kirana da matsoraciya,wasu kuma azzuluma, yayinda a wani wajen nake amsa kiran saliha, wani wajen kuma ni mai daukar fansa ca, wasu garesu ni mayaudariyace yayinda wasu ke daukata majinginarsu, wasu kuma sukan kirani da shu’umar macijiyah, yayinda wasu kuma ke yimin kirari da jajirtacciyah.

A yanda ainihin sunan yake a zukatan mafi akasarin mutane har gani kaina shine MABARACIYAH mace daya ƙwall acikin taron maza na almajirai………

Wata matace zaune a cikin taron mabarata wanda suke zama a bakin gidan bamu kudinnan domin samun abinda zasu sakawa cikinsu,duk wani lokacinma mutuwar zuciyace take kaisu.

Karar wayar nokia ce tayi kara a aljihun wata yar matashiya, wacce kusan dukka wajen tafisu mummunar shiga sosai.

Fitowa tayi da wayar da’aka ɗaɗɗaure da zare,da kyar ta daga wayar yanda hannunta yake karkarwa sosai.

Can kaman na minti ɗaya tasaka wayar a kunne amma batace komai ba, da alama wani abu ake faɗamata.

Sakin wayar tayi ta fadi a kasa tareda jera salati kala kala,

“Talatu mai ya faru kike wanann salatin lafiya kuwa?”

“Ahah kursiyyah, makwanciyata ce ta haya ta kirani wai ɗana bilyaminu dayake asibiti wai ciwonsa ya tashi,ance inbankai kudin aikin da wuri ba zai rasa ransa”

Wata ce daga gefe kana ganinta kaga jarababbiyah,

“Miye na damun kai oho, kefah kika ce yaronma shegene uhm”

Talatu tana jinta bata kula ta ba, karisawa tayi inda layin gaba suke ta faɗa musu abinda yake faruwa, ƙin yadda sukayi da ita saida na baya sukace da gaskene tukunna.

“Dan allah kuyi hakuri, ance idan ban kai da wuri ba zai rasa ransa, ku taimakeni na shiga gidan wajen alhaji dan allah,iya yaune kawai yake ganin mutane,inba hakaba bazan ganshi ba”

Kuka tafara wiwi, wanda hakan yasa na gaban jikinsu yayi sanyi suka barta ta shiga.

Securitynne suka bude mata kofar ta shiga tareda wasu masu neman taimako suma guda biyu da suke gaban layin.

Bayan kaman minti biyar da shigarsu sukaji danger alarma ta gidan ta buga.

Sauran masu neman taimakon hargitsewa sukayi,yayinda sauran masu tsaron kuma suka afka gidan da gudu.

Duddubawa sukayi inda karar ta fito,wani hayaki aka saki wanda duk da hasken rana ta allah amma mutum baya ganin gabansa.

Wani security ne ya kalli wata ƴar matashiya a cikinsu wacce bata wuce shekara sha takwas ba,ta fito daga cikin hayakin sai tari take.

“Lafiya khamriyyah naga kin fito ina yallabai ɗin”

“Ahhhh uhmm ban ganshi ba Ahamd,masu neman taimakon ma bangansu ba a ciki,inaga akwai matsala”

“Oh shitt, duk mai muke haka tafaru, akan haka zamu iyah faɗuwa jarabawarmu tazama SSS fah, duk da muna matakin karshe,barina ƙira Dec. Sadeeq yanzu nan”

Radio waya ya danna na security domin shaidawa headqauter su.

Can komai aka faɗamasa sai ya kashe wayar yana kallon ta.

“Yess wannan karon inaga zamuyi nasara khamriyyah, da suka tashi guduwa da shi sun ɗauki mota a cikin gidan, kuma akwai na’urah mai bin diddigi a jiki”

Saurin hawa mota suka yi,ahmad na tuƙawa da mic a kunnensa ana faɗamasa inda zasubi.

        **_____**_____**

Tafiya suke motar cikin matsanancin gudu,kayan jikinta yagygygye tafara cirewa tana zubarwa a motar, ta kuma yiwa wacce take tuƙin magana, wacce itama yagaggun kayanne a jikinta.

“Ki taka da sauri, mukai akan lokaci,sonake kowanne tafiya da motar nan zata yi ta dungayi ta barazanar ƙarewar numfashinsa na karshe a duniyah”

A bakin wani kogi suka tsayah bayan sunyi tafiyah mai nisa a cikin jeji.

Fitowa akayi dashi kansa a rufe da wani buhu,durkusarshi tayi a bakin ruwan dake gaban ta,tana sanye da baƙaƙen kaya sun yayyage kaman na mahaukata ,wanda tasamu damar sakasu a motar.

“Safiyyah, miƙomin buhun nan yanzunna”

“Toh shugaba”

Cirewa buhun dayake kansa tayi tareda tsugunnawa suna kallon juna.

“Ka ganeni Brr. Shehu ko kuma na tuna maka”

Jikinsa ne yafara karkarwa kaman an jona masa shocking.

“Dan… al Allah kiyi hakuri na tuba, ki tunafah inada iyali da suke jiran komawa ta gidan, mai yasa zaki zalunceni akan wata buƙata taki?”

“Hhahahah zalunci shine abicina brr. Shehu, kuma yanzu kaima zan ciyar dakai shi ”

 

Karbar buhun tayi daga hannun matar sai motsi yakeyi,

“Kasan menene a cikinnan? nasan baka saniba, to macizaine masu mungun dafi da aka tunzurasu na tsawon sati guda,neman inda zasu huce sukeyi,…… yanzu zamu saka kanka a ciki su samu abinda zasu juye dafinsu a ciki”

Ihu yafara kan gari ya gari jin abinda take faɗamasa yana cikin buhun, saidai ko a jikinta saima ƙara nishaɗi da hakan yabata,

“Kasam menene Brr.,ina son naga na kama mutum babba yakusa haifata inayimasa abu yana ihu yana neman taimakona, sannan inason yin basaja a cikin masu nemana ko wanda nake nema,wanann duk yafi bani nishaɗi,naga kana nemana ko kuma kana tsorona amma ina gabanka, a matsayin bakowa ba batare da saninka ba, hhhh wannan shine aikin MABARACIYAH, matsoraciyah kuma abar tsoratarwah…

Mabaraciya Hausa Novel Complete txt

File Name   Mabaraciya … Hausa Novel Doc.
Title   Mabaraciya Hausa Novel Complete
Author    Saknah
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    300KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦500
Phone No   07068390570
Download Mabaraciya Hausa Novel Complete By Saknah

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button