Hausa novels

Gargadar So Chapter 118 By M Shakur

Baba nama Ammi ihu data taresa cikin bacin rai yace “Mijinta zata sama bindiga akai sabida wani katon banza da wofi iyye hauka Hawwa zatayi ne? Akwai wanda yafi mijinki daraja da kima da iko awajenki ne?Bakison aure kinfi son zaman gida? Billahillazi yaron nan ya sakeki idan kin zauna a gidana Allah ya tsinan albarka saidai kije kiyi zaman kanki koki shiga duniya, shegiyan yarinyar mai zuciyan arna! Ni ku banni na mammake tambadaddiyar konaji dadi” Baba yayi kanta Hawwa tasaki Umma tahau gado taje chan karshe tana kuka cus Baba can injure her ayanda ranshi yabaci, sosai Umma da Ammi suka rike Baba dake nishi kaman zai mutu sabida bakin cikin Hawwa, muryanshi har rawa yake yana shaking irin na wayanda suka tsufa din nan yace “da aurenki ki bude baki kina cewa mijinki eh kinason wani sabida ke sokuwa ce, katuwar banza ko Miemie autan gidan nan bazatai kalan sokoncin nan ba, eh mijinki da babu abinda baya miki, kullum tsakaninki dashi saidai kice kin tsaneshi eh, Hawwa ni zaki tozarta ki ciwa mutunci? Ni zaki zubama toka a idanu? Sabida kinga yaro na sonki yana bibiyanki kaman wata sarauniyan mata shine kika sami waje kina shuka iskanci kinama yaro kaman kece uwarsa harda zagin iyayensa, kai wlh idan ban kashe yarinyarvnan ba bazanji dadi ba” Baba ya fizge hannunshi zaihau gadon Umma takama Baba dasauri tayi ihuuu sosai tace “Malam dan Allah, dan Allah kayakuri, Malam kayakuri ka zuciya dayawa, Malam idan tana dauke da juna biyu fa iyye? Baka daki Hawwa da ba sai yanzu? Dan Allah Dan Allah Malam kayakuri”kirjinshi Baba ya daka yace “kinsan me Hawwa tayi kuwa? Zan iya kara kallon yaron nan kuwa? Dan ubanta batasan kishi yake ba yasa yake dukan watsastsen makirin yaron nan Aliyu, idan tahanashi yaki hanuwa meya hanata kama mijin nata kaman yanda kika kamani yanzu eh? Miyahanata yin haka? Amman saidai kisamai bindiga aka kice zaki harbesa akan wani katon banza ke gaki yar sanda, to bari kiji na rantse da Allah dagayau baki ba aikin yar sandan! Kika kara zuwa wannan aikin ban yafemiki ba Hauwa’u! Abarma maza aikin, kaico! Nagama jin haushin Ni’ima yau da raina Allah ya nunamin tawa diyar zata iya abinda yafi na Ni’ima ban kunya tir da hali irin naki, Hawwa yau naji takaicin da kika kasance diyata!” Ya fizge jikinshi daga Umma yajuya yafita kai Baba ya zuciya bakadan ba, Hawwa ta taho wajen Ammi tana kuka sosai ganin Baba yafita tace “Ammi dan Allah kuyakuri wlh na rantse bazan kara abinda nayib……” hannu Ammi tasa takaimata mari bataso tacigaba da marinta hakan yasa takalli Umma tace “bani dorina!” Umma zatai magana Ammi tace “bani dorina nace Umma banson wani magana” Ammi takalli Hawwa dake wani kalan kukan ban tausayi tace “zamanin mu duk girman mu iyayenmu na cin kaniyan mu idan munyi kuskure ko bayan mun haifi yara goma, ban bari Babanki yadakeki ba sabida namiji ne shi karfe yadaga but that doesn’t mean ni bazan hukuntaki ba, Hawwa magana da wa’azi basa aiki akanki ko? You feel kaman kin girma you are out of reach ko? Zakici gidanku” daidai Umma na shigowa rike dawata yar karaman dorina karamaHawwa tazabura zata gudu Ammi tawani riketa duk karfin Hawwa takasa guduwa, hannayenta biyu Ammi takama tahada ta zubamusu dorina tace “hannayen nan dakike dukan mijinki dasu kina dauramai bindiga aka duk randa kika sake attempting yi wannan bulallan zaisa kituna mahaifiyarki ta taba hukuntaki akan haka” Ammi ta shauda mata guda biyu a hannun masu kyau Hawwa nawani irin kuka cus sun shigeta dorinar da zafi, Ammi ta saki hannunwan da gudu Hawwa tai baya zata gudu Ammi kawai tarike kafafunta gam ta hadesu Hawwa takai hannuwan takama hannun Ammi dake rike da dorinan tace “Ammi kiyakuri, baki taba dukana ba ko Baba bai taba dukana ba dan Allah kiyakuri, wlh zafi Ammi dan Allah” fizge hannunta tayi Ammi ta zubamata bulala biyu akafafu tace “this is for saka kafafun nan a hanya kifice daga gidanki batare da izinin mijinki ba next time idan zakiyi haka remember this” Ammi tasaki kafan kawai Hawwa taga Ammi tarike fuskanta dasauri takulle bakinta cus tasan next thing is her mouth, Ammi tace “ai baki isa release bakin dayafi iya rashin kunya da zage zage da maganganu marasa dadi, saki bakin nan!” sakin bakin Hawwa tayi ta tsorata da Ammi sosai, Ammi babu tausayi ko wani abu ta kaima bakinta duka mai kyau da lafiya saiga jini a lips nata cus sun datse da hakoranta Ammi tace “good jinin dama nakeso ya zuba, stupid girl mara tarbiya mai bama iyayenta kunya, mai zagi da dukan mijinta” Ammi ta yarda dorinan akasa tajuya tafita daga dakin itama fuuuu Umma tawuce wajen Hawwa data rungumeta sosai tana kuka tana bata hakuri tana mata kuma fada.Azaure Ammi taga Baba yazauna flat akan simenti ya yarda sandanshi a gefe yabuga tagumi idanunshi sunyi jaaa gwanin ban tausayi ahankali Ammi ta zauna kan kujeran wajen tace “kayakuri Malam na zaneta yanzun nan kafin nazo nan nahukun tata, dan Allah kayakuri yanzu yaza’ayi bazamu barta anan ba, muka barta mun nuna munyi supporting bad dabi’unta ne hakan ba halinta dattaku bane” Muryan Baba yayi rauni yace “Zainabu kunyan Ibrahima nakeyi Zainabu kinsan yanda yaron nan ke sona kuwa”? Baba yayi shiru saikuma ya matse hawaye yace “na gayamiki ai yakawomin takardun babban gida ya sayamin nakoma ciki nacemai a’a bazan taba barin gidan nan nawa ba har abada, Zainabu na gayamiki yakawomin katuwar mota da driver dazai dunga kaini duk inda nakeso wlh naki amsa nagayamai badan kudinsa nake sonsa ba and sabida ya auri yarinyata basaiyamin abubuwa ba, namai tatas naki amsa, na nunamai idan yacigaba yanamin irin abubuwan nan zan batarai dashi, Zainabu still yakara zuwan mini da maganan zai kaimu aikin Hajji dukanmu da yaranmu, daganan yanaso yawuce dani turkey amin aiki asamin kafan karfe nadinga tafiya da kaina batare dana amfani da karafunan nan ba, wannan ne kadai maganan Khaleel dana aminta na yarda ko jiya saida yagayamin zai aiko ranan asabar har gida azo amana passport nakira su Hafsa dasu Aminu da ke dasu Ramla duk suzo gida amana baimasan zakizo Abuja jiyan ba a asibiti yakemin magana” Baba yayi shiru yasake share hawaye yace “Zainabu kunyan Ibrahima nake yaron daya girmamani ya daukeni tamkar ubansa, yayi kuka ajikina yarikeni, Ibrahima baitabamin kallo kaman baban matarsa ba saidai mahaifinsa, Hawwa tarasa wanda zata ciwa mutunci sai shi, dakuma iyayensa, nima ai na takurawa yaran wasu nasama yaran unguwa ido saida Allah yasa y’ata taki auriwa nazo na gyara kuskurena, Point din is ai nima ba mutumin arziki bane, banda aiki sai zama kofar gida na sama yaran mutane idanu ina Kai karansu wajen iyayensu ni maisa wasu yaran basu zageni ba? Iyayyenka ko bokayene babu wanda ya isa ya zagan maka su, Zainabu Hawwa ta kama yaron mutane taita bugu iyye? Lahaula fi sha’atillah! Hasbunallahu wa ni’imal Wakeel! Zainabu takama yaron mutane tanata bugu tana sharara masa mari? Zan iya rantsuwa iyayensa basu taba marinsa ba wai kinga yanda mahaifin Ibrahima ke sonshi kuwa? Ina ganin ko ihu baitamaba yaron nan ba balle har akaiga mari amman Hawwa taita zubamasa mari takama yaro tana bugu tana jibgansa? Zainabu idan na cemiki ban tsani Hawwa ba nai karya nayi karya!” Ammi ta runtse idanu ahankali, yace “Wlh wlh da Aminu zai auro yarinyar dake hali sak irin wanda Hawwa na tayi wlh sainasa ya rabu da yarinyar nan, ba matan aure bace amman yau Hawwa! Hawwa na fa danake gani tafi duka yarana hankali take abubuwan nan sabida taga yaron sangartacce kaman baida wayau dukya haukace a sonta shine take haka kome?” Baba ya tambayi Ammi ranshi abace yace “uban me zaimasa ta tsaya tama kula Baban Yaseer Aliyu da aurenta? Ai bayan gaisuwa bai kamata tama tsaya sauraransa ba kwata kwata kamata yayi ta tada mota tabar wajen” Baba ya girgiza kai yace “Zainabu na rantse miki banjin inada karfin dazan iya kallon idanun Ibrahima ba ko kadan diyata tariga ta tozarta ni nan nan kafin ta yardan masa su hada shimfida saida mukasa baki eh wani kalan zuciya ke ga Hawwa”? Baba yace “kinga kucemata tafito tabarmin gida billahilazi ko ruwan gidana aka bata tasha sai nahau sama na fado kasa da mutum tazo tabar gidana idan zaki tafi da ita zaria ne chan muku amman nidai Hawwa bazata zauna gidana ba!” Dasauri Ammi tace “Malam nasan ranka yabaci amman dan Allah ka fahimceni, na farko dai bazan taba daukan Hawwa na tafi da ita zaria ba yoo ai nama daure mata gindi kenan! Kawai so nake ka kira Khaleel yanzu yasa abarmu mu shigo idan mun kaita abada hakuri asa tabashi hakuri tunda bai riga yasaketa ba” Baba yace “naje nabada hakuri gobe tasake marinsa? Gobe tasake bugunsa? Koko gobe tama harbesa gabaki daya”?.

Back to top button