Wannan magana tabbas haka take babu kokwanto a cikinta na cewa “kulli nafsin za’ikatul maut”, dukkan mai rai sai ya dandana dacin mutuwa. Idan kuma aka ce mai rai kowa yasan ba iya dan adam ake magana akai ba hatta mala’iku suna da rai, aljanu suna da rai, tsuntsaye suna da rai, dabbobi suna da rai, kwari suna da rai da dai sauransu, kuma duk wanda Allah Ya busa ma wannan ran wata rana komai daran dadewa sai ya cire kayansa.
Hakazalika duk wanda Allah yasa masa rai har kuma ya kaddara yazo wannan duniyar to tun kafin ma ya fito daga cikin mahaifiyarsa ya shigo wannan duniya Allah Ya riga yasan rana da kuma lokacin da zai koma, idan kuma lokacin da aka dibar wa mutum ya cika ko dakika daya ba za a kara masa ba, wannan dai abinda muke fada wani abu ne da kowa ya sani, kawai dai muna cika umarnin Allah ne daya umarcemu da mu tunatar, domin tunatarwa tana amfanar da mumuni.
A halin yanzu dai Allah ya karbi ran daya daga cikin fitattun jarumai a masana’antar fina-finai ta Kannywood wacce ta dade sosai tun shekara da shekaru ana damawa da ita a masana’antar mai suna Fatima Usman wacce ake yiwa lakabi da Fati Slow Motion.
Mutuwar jaruma fati slow motion tazo da wani irin yanayi da ba a saba da shi ba a masana’antar ta Kannywood, domin kuwa bama a Nigeria ta mutu ba, ta mutu ne a can wata kasa a wani gari da ake kira Abasha, wanda shine birni na hudu mafi girma a kasar Chadi, kuma birnin na Abasha yana iyaka da Sudan.
Acan garin ne na Abasha wato a kasar Chadi Allah ya nufi da mutuwar fati slow, kuma acan din ne aka yi zana’idarta dan ba’a dawo da ita Nigeria jihar Kano ba.
Tsohuwar jarumar Kannywood, kuma tsohuwar matar jarumi Sani Danja Mansura Isah itace ta fara wallafa wannan labari na mutuwar fati slow a shafinta na instagram.
Ga kuma wallafar da tayi kamar haka:
Idan zaku iya tunawa a baya dai kimanin shekara daya zuwa biyu da suka wuce, fati slow tayi tashe a dalilin wata rigima data faru a Kannywood, har ma fati slow din take cewa tana shan kebur, wato dai tana fama da tsananin talauci, daga karshe har Naziru sarkin waka ya bata kyuatar kudi naira miliyan daya.
Ya kuma bawa dattijuwar jarumar nan mai sun Mama tambaya wacce ake yiwa lakabi da Ladin cima kyautar naira miliyan biyu, kuma duk a lokaci daya sarkin wakar yayi masu wannan kyuatar, da fati slow da Mama tambaya.
To bayan wannan wallafar ta Mansura Isah ne dai, sai sauran jaruman Kannywood din suka ci gaba da yada wallafar akan shafukansu kamar jarumi Ali Nuhu shima ya yada wallafar akan shafinsa na instagram, da Abubakar bashir maishadda, A’isha Humaira da dai sauransu.
Inda kowa keta yiwa fati slow din addu’o’in na neman rahamar ubangiji, dan haka muma addu’armu ita ce Allah yayi mata rahama ya kuma yafe mata kurakuranta, mu kuma idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da kyau da imani Amin Summa Amin.
Kalli cikakken bidiyon yadda aka gudanar da zana’idarta 😭😭😭