Novel Document

Wata Kishiyar Complete Document

Description/Story:

Wata Kishiyar Complete Document Written By Maryamah Mrs Am

 

Description

 

WATA KISHIYAR

Alkhairi ce ko Sharri?

 

Na Maryamah_Mrs AM

 

Page 1

 

Lagos Nigeria

 

Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar idan bazan makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani conference meeting da aka turani daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu nisan tazara tsakanin unguwar tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani cewa ” not now please” azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani waiwayawa, megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali Yara kuma suna ce masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya saka masa da ya rasu sati biyu kafin na haifi Aliyun.

 

Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara’a amma dai ai yanayimun nidai. Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da gajeran murmushi nace “Baban Ali ka ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan a jaka ashe batayi ba (Amna Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da Mahaifiyarmu ta sake aure).

 

“Uhm” kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata tareda ratayata na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita

 

“Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe” muryarsa ta doki kunnena,

 

“To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse” na sa kai na fice daga dakin. Already Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da yara suka biyo ni suna yimun.

Wata Kishiyar Complete Document

Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai wani abune ya faru a bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan nayi waya da yan uwana kuma ba abinda akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai kawai zakuje Gombe ba. Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi.

 

A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin bari na kwana a Kanon dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan kwana ba nasan bazasuji dadi ba musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci abincin da Aliyu ya kawo min, ina zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana cikamun zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da sauran wani damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su.

 

Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu shekaru 13 ya shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha Allah yana da qoqari tamkar Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad su Shidan nan sune rayuwata ban kuma hadasu da komai ba.

 

Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi, sauqin dana samu tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din nan bacci zan shaqa. Sallamar Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa dan shi dama be fiya zama ayi irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya Amsa yana nufar dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima ganin kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze shige dakin ga kuma fita da yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi dakinsu matan ma haka.

 

A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa “Ashe baka nan, na tambayi yara sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki”

“Uhm” ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin Hasala amma fa ina da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya tambayeni ya hanya koda yake dama duk satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban kula shi ba nasan qiris yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki tareda cewa “Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo ka juyemun to bazan tanka ba”. Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum fada kamar ko yaushe kuma akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad, Ahmad da Abdallah Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za’a kwanta shine a sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace sedai dan uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu muka karanta Azkar din bacci naja musu qofa tareda kashe fitila.

Wata Kishiyar Complete Document

Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na shiga dakina, jikina na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake nema yasakani kashe fitilar da ya bari a kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata gajiya na sake saukar mun.

 

“Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe” ya sake fada, sena gyara kwanciyata ina cewa “Allah ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa surutu zamuyi tayi dan dai yasan abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba kowanne ba se yayi corresponding hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka ana tsakiyar Term yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk sanda nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban farka ba se Qarfe 7 harda Rabi na safe.

 

Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta danne ni banajin ko juyi nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai baccin ya sake ni bane na fito palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter. A tare suka gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi

“Kunyi karatun Asuba ne” na tambayesu suka amsamin da eh

Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma bacci. Kafin na fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka na zauna kan Dining ina shan Tea ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa 12 harta gota na rana.

 

Wata Kishiyar Complete Document

 

File Name   Wata Kishiyar… Hausa Novel 
Title   Wata Kishiyar Complete
Author    Maryamah Mrs Am
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    14/10/2024
File Size    1.31
Format Size    TXT
Book Price
Phone No
<em>Download Wata Kishiyar complete Document By Maryamah Mrs Am

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


  • Proceed with your download Wata Kishiyar Complete Document by clicking the below button

 

 

Be With Us

Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button