Uncategorized

Muhimman abubuwa 11 da ya kamata mu sani game da watan Ramadan

 

1. Azumin watan Ramalana daya ne cikin rukunan Musulunci guda biyar.

2. A cikinsa ake samun daren Lailatul Qadri wanda falalarsa tafi na darare dubu, kimanin daren shekara 83 da wata hudu.

3. Tun daga farkon watan zuwa karshen ake bude kofofin Aljannah a rufe kofofin Wuta a sanya Shaidanu cikin dabaibayi.

4. Azumtar Watan Ramalana ke sanyawa a gafartawa Mutum abin da ya gabata na kura-kuransa.

5. A cikin Watan Ramalana a Daren Lailatul Qadr Allah ke saukar da bayanin abin da ya hukunta faruwarsa na shekarar bana zuwa shekara mai zuwa kamar yadda Al’qurani ya ambaci hakan a Suratul Qadri. (INNA ANZALNAHU FI LAILATIL QADRI)

KARANTA: “Alfanun Azumi guda 8 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam”

6. Sadaka a watan Ramalana ta fi lada. An tambayi Annabi kan wace Sadaka ce ta fi? Sai ya ce: “Sadaka a Watan Ramalana”.

7. A cikinsa Allah ya saukar da Alqur’ani dungurungum zuwa Baitul Izzah a sama ta farko, daga nan aka saukar wa Annabi Muhamamdu SAW a rarrabe.

8. Shi ne watan da in ka yi tsayuwar Sallah don neman lada a dararensa Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka kamar yadda Annabi ya ce.

9. A cikin kowane dare na Watan Ramalana ne Allah ke ‘yanta bayinsa masu dumbin yawa daga cancantar zaman Wuta zuwa Aljannah.

10. Shi ne watan da yin aikin Umara a cikinsa yake daidai da Aikin Hajji da Manzon Allah kamar yadda Annabin ya fada a Hadisi.

11. A wannan Watan ne Annabi ya fi yawan kyauta kamar yadda Imamul Bukari ya ruwaito a Hadisi.

Back to top button