Hausa novels

Halysaah Page 204 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 204…Washegari karfe biyar na yamma Khaleesat suka sauka garin Abuja, their Flight to Kano was is in less than an hour, wannan ne yasa basu bar airport din ba suna jiran lokacin, Khaleesat na zaune kusa da Hadiyah cikin airport din, lokaci lokaci take ɗaga kai ta kalli Ajay da hankalinsa ke kan wayarsa da yake dannawa, haushin hakan taji har cikin ranta ganin duk attention dinsa na kan wayarsa ko kallon inda take baya yi, ta ɗan kalli Jay dake zaune not too far away from Ajay shi ma dai wayarsa yake dannawa, mikewan da tayi tsaye yasa Ajay ya daga kai ya kalleta, Jay ma ya daga kai ya kalleta, Ajay na ganin mood dinta ya ajiye wayarsa, ta tafi inda yake ta zauna gefensa amma taki kallonsa, shi dai kallonta kawai yake, sai kuma yayi kasa da murya yace “You need something dear?” Shiru tayi taki cewa komai, ya matsa kusa da ita a hankali yace “Jeeddah” Nan ma taki cewa komai sai ma kauda kai da tayi, Jay duk yana kallon ikon Allah, haka ma Hadiyah dake ta kallonsu, Ajay ya kai hannu jikinta yaji her temperature is normal, ya tashi ya koma daya side din da ta mayar da kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace “To yi hakuri wife” Shi dai kawai ya bata hakuri ne ba don yasan fushin me take ba, tana cika tana batsewa da kyar ta bude baki tace “Ni na gaji, ina son in kwanta” Ya kwantar da murya yace “Ai mun kusa boarding flight din mu to Kano, nan da 30 mins za mu tashi in sha Allah” Kamar zata yi kuka tace “Ni bazan iya tafiyar ba na gaji, i just want to lie down, bacci nake ji” A hankali yace “Duk baccin da kika yi a jirgi wife” Ta wani hade rai tace “Yaushe nayi bacci a jirgi?” Yace “Ohk na tuna baki yi ba” Ta tura baki ta jingina da kujeran da suke zaune, Ajay dai kallonta kawai yake, can ya juya ya kalli Jay, after some seconds ya mike ya tafi inda yake zaune, Jay ya daga kai yana kallonsa, Calmly Ajay yace “Can we reschedule our ticket to tomorrow?” Jay yace “Why?” Ajay ya ɗan sosa kai yace “Erm, naga kawai yamma tayi ne” Jay yace “Idan muka fasa tafiyar sai me zai faru?” Ajay yace “Zan mana booking hotel ne mana” Jay dai kallonsa kawai yake daga sama har kasa don yasan duk tsarin matarsa ce, but considering her condition sai bai ce komai ba, Ajay ya mike ya koma kusa da Khaleesat yana danna wayarsa zai masu booking hotel, in 40 mins time suka isa hotel din da yayi masu booking, tun a hanya Khaleesat ta fara bacci har suka iso hotel din, da kyar Ajay ya lallabata tayi wanka a hotel room dinsu sannan tayi sallah ta ci abinci a nan inda take zaune ta fara bacci, ya fito daga wanka ya sameta a haka, dukawa yayi ya dauketa ya kwantar da ita saman gado ta ci gaba da baccinta. Ba su suka bar Abuja ba sai ranan Lahadi all because of Khaleesat don ranan asabar ce ma Ajay tayi she don’t feel like traveling, mamaki ya kusa kashe Jay ranan lahadi da Ajay yace masa ai mota za su bi kawai, da Jay ya tambayi dalili sai ce masa yayi ai tafiyar mota yafi dadi, Jay yasan ba kowa ne yasa su bi mota ba sai Khaleesat, still dai yayi considering condition dinta suka kama hanyar Kano a mota, ai ko ta ji jiki a hanya kafin su karasa Kano, tun da ta fara laulayi bata yi amai ba sai ranan, all through the journey tana kwance jikin Hadiyah duk ta jigata, gashi duk maganar da Ajay zai mata sai tayi masa jaraba sai kace shi yace su bi mota, daga karshe taki kulasa ma gaba daya a motar, duk abinda take so sai dai tayi ma Jay magana, a haka suka iso Kano da yamma sosai don tafiyar tasu bai yi sauri ba duk saboda ita don sai da ta sa suka tsaya a kaduna wai tana son ta huta kamar dai ita ke driving din, Jay was so patient a wannan tafiyar tasu don ma dai ita ce, da wata ce daban da tuni yayi tafiyarsa ya kyalesu. Wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da take, mikewa zaune tayi ganin Ajay baya dakin, ta kalli flask din ruwan zafi da Hadiyah ta ajiye mata da kayan shayi tun zuwan su gidan, sauka tayi daga saman gado ta dau hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita zuwa downstairs, kwance ta samesa kan 3 seater, duk da ba bacci yake ba yana ganin ita ce ta sauko kasa ya rufe ido kamar me bacci, tana tafiya a hankali ta karasa kusa da shi tana kallonsa, sai kuma ta durkusa kasa ta kamo hannunsa a hankali tace “Me yasa zaka kwanta a nan” Bai yi niyyar bude idonsa ba amma jin jikinta da zafi yasa ya bude ido ya mike zaune ya dagota ta zauna kusa da shi yace “Are you okay?” Ta kwantar da kanta a jikinsa ta gyada masa kai a hankali tace “Na tashi ban gan ka ba a daki, i want to take tea” Tashi yayi zai tafi kitchen tace “Hadiyah ta kai min kayan shayin daki” Ya dawo ya dagota suka wuce sama. Khaleesat na shafa mai bayan tayi wanka wajen karfe sha daya na safe Hadiyah ta shigo dakin rike da breakfast, Khaleesat ta kalleta tace “Are you going out?” Hadiyah tace “Ehh za mu fita ne da Ya Jawwad, za mu je gaida yayar Abbana she is kano, naga baki jin dadi ne shi yasa ban ce ki shirya mu je ba, beside kin ma ce gidan kawarki zaki je yau” Khaleesat tace “Ni fa lafiyata qlau ba abinda yake damuna” Hadiyah tayi murmushi tace “Dama ai lafiyarki qlau kawai stress din hanya ne ya sa kike ta bacci, wani unguwa aka kai kawar taki ne?” Khaleesat tace “Wallahi ban ma sani ba, bata replying chat dinta, but I will call her zuwa anjima” Hadiyah tace “To shikenan, in dai kika ji shiru ban dawo ba ta zan kwana ne gidan Gwaggo na, duk yanda ake ciki dai i will call you, ga breakfast nan na kawo maki” A hankali Khaleesat tace “To nagode, but i will miss you so much” Hadiyah tayi er dariya tace “Sai kace warce zata je wani gari, idan ma zan kwana bai wuce inyi kwana daya ba kar ki damu” Khaleesat ta langwabe kai tace “To shikenan, ki gaida min ita don Allah” Hadiyah tace “In sha Allah, kuma don Allah ki dena ma yayana wannan masifar da kike masa duk kwanan nan” Khaleesat ta zaro ido tace “Yaushe nayi masa masifa?” Hadiyah tace “Oho dai, duk da mun san ba laifin ki bane” Hadiyah bata jira cewar Khaleesat ba ta fita daga dakin tana murmushi…. Ko da Khaleesat ta kira layin Safiyyah cousin sis dinta ce ta daga tace wayar na gida sai dai ta kira Ya Mustapha, Khaleesat ta duba ko tana da numbersa amma taga bata da shi yanxu, sake kiran cousin din Safiyyah tayi ta turo mata number Ya Mustapha, karfe sha biyu Ajay yayi dropping khaleesat a dai dai address din gidan da Mustapha ya turo, Khaleesat na kallonsa a hankali tace “Karfe nawa zaka dawo?” Yace “Duk sanda kika ce ranki shi dade” Tace “To idan na gama zan kira ka” Yace “Alright My love” Ta ɗan hade rai tace “Amma ina zaka daga nan?” Yayi murmushi yace “To bari kawai in jira har lokacin da zaki fito” Yana fadin haka yayi baya da kujeran motar zai kwanta, dariya ta fara yi, ya dinga kallonta babu ko kiftawa, tayi me isarta sannan ta tallabi kuncinta tana kallonsa tana murmushi tace “Idan nace ka zauna nan ka jira ni sai ka zauna” Shi dai ya kasa dena kallonta, after some seconds ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace “I want a baby girl like you pls Jeeddah” Ta ɗan bude ido tace “Ni ce ma zan ba kai na babu girl din kenan?” Sauke Idonsa yayi, a hankali tace “Ai kace za mu je Umrah kwanan nan, idan muka je sai inyi addu’an Allah ya bani cikin baby girl” Ya daga idanuwansa ya kalleta, yace “Wannan dake jikin ki fa?” Tayi shiru tana kallonsa, ya kamo hannunta yana kallonta yace “You mean you don’t know u are pregnant with my baby?” Ta turo baki taki cewa komai, ita abinda yasa taki yarda tana da ciki all this while taga bata ji abinda taji a cikinta na farko ba, babu kasala babu tashin zuciya, sannan tana cin abinci, baccinta ne kawai ya karu, ya lakaci hancinta yace “Yi duk tunanin da zaki yi amma ki sani idan kika haife wannan babyn you still have 7 more to go in sha Allah… Zaki haifa min girls shidda masu kama da ke, biyu su yi kama da ni” a hankali Khaleesat tace “Ni dai ina son namiji” Shiru yayi yana kallonta, can ya sauke idonsa yace “Bana sha’awan duk abinda zai hada zuri’ata da sarauta wataran Jeeddah, shi yasa bana fatan samun ɗa namiji, in sha Allah lineage dina will have nothing to do with the throne of our Emirate for their peace of mind, yanda bazan yi sarauta ba bana fatan jini na yayi, kin ga idan Allah ya bani iya yara mata babu ruwansu da harkan Emirate, za su yi rayuwarsu babu kalubalen da ya shafi gidan sarauta” Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta sauke idonta a hankali tace “Haka ne, nima bana son abinda ya same ka ya samu yaran mu, Allah Ubangiji ya bamu yara mata” Yayi kasa da murya yace “Masu albarka Jeeddah” Tana murmushi tace “In sha Allah” Dai dai nan aka bude gate din gidan Ya Mustapha ya fito, Ajay ya bude motarsa ya sauka suka gaisa da shi, Khaleesat ma ta gaishesa ya amsa mata da fara’a, a haka ta shiga cikin gidan ta bar su a kofar gidan, sallama tayi ta shiga babban parlon gidan tana murmushi ta zauna tana jiran ganin ta inda kawarta zata billo, furnitures masu suna furnitures aka zuba a parlor, Banda kamshi babu abinda ke tashi a gidan, shiru dai bata ga Safiyyah ta fito ba, ta kusa 10 mins zaune sai ga Mustapha ya shigo Parlon ganinta a zaune ya nuna mata hanyar dakuna yace “Tana can ciki ai Khaleesat, ki shiga, her Bedroom is the first one by ur right” Khaleesat tace “Toh” Mikewa tayi ta nufi corridor din da ya nuna mata, ta ga dakuna hudu a jere, ta bude dakin farko dake bangaren damanta tayi sallama, Safiyyah dake kwance ta mike zaune da sauri tun ma bata san Khaleesat ba ce, Khaleesat dai kallonta take ganin yanda idonta suka kumbura sosai alamar ba karamin kuka ta sha ba and she looks stressed, gashi duk a firgice take, nan da nan ta fasa tsokanarta da tayi niyyar yi, Khaleesat ta karasa kusa da gadon ta zauna gefenta tana kallonta da damuwa tun kan tace komai Safiyyah ta dora kanta saman shoulder dinta ta fara shesshekan kuka, Khaleesat ta ma rasa me zata ce, ga jikinta taji da zafi sosai, ta kalli magungunan dake kan bedside drawer, after some seconds ta kwantar da murya tana patting bayanta tace “Haba Sophie ni fa na zata kin hakura tuntuni, what’s the meaning of this please, sai kace warce aka hada da stranger su yi aure, haba you are too matured for this mana” Safiyyah dai hawaye kawai ke zuba idonta cikin rawan murya tace “Ni ban taɓa sanin shi mugu bane sai yanxu Khaleesat, Wallahi mugu ne shi” Tana fadin haka ta fashe da kuka sosai, Khaleesat bata san sanda tayi murmushi ba jin abinda Safiyyah tace, after some seconds ta dago kanta, fuskarta dauke da mamaki tace “Ban gane shi mugu bane Sophie, me yayi maki na mugunta?” Safiyyah ta dinga kuka taki ce mata komai, Khaleesat tace “Ni dai tunda kuka zaki yi tayi bari in yi tafiyata dama Ya Junaid na kofar gida zai maki Allah ya sanya alkhairi, kawai bari in tafi zan bari bayan kwana biyu in dawo” Safiyyah ta rikota da sauri tace “Don girman Allah ki rufa min asiri kar ki tafi ki bar ni” Khaleesat tace “To na ji, ince Ya Junaid din ya shigo?” Safiyyah ta fara wani sabon kukan a hankali tace “Ai bazan iya fita parlon ba” Khaleesat ta ɗan bude ido tace “To saboda me?” Safiyyah ta kasa cewa komai hawaye wasu na bin wasu a idonta, tuni Khaleesat ta ɗago komai, ga abun dariya amma ba daman yi, ga dukkan alama Safiyyah ta gano Mustapha ba mace bane kamar yanda take kiransa idan iskancinta ya tashi, Khaleesat ta kasa daurewa tace “Hope yanxu dai kin dena yi ma Ya Mustapha kallon mace?” Safiyyah ta daure fuska ta jefa mata wani kallo, Khaleesat ta fashe da dariya har da kyakyatawa.

Back to top button