Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 31 Book 2 Complete Novel

   

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)


KARANTA ZAFAFA 2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


            •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•                                      bayan Jahad ta kammala wankan ta canza kaya ixuwa doguwar riga, hawa tayi itama saman gadon kusa da hosana suna daf da juna tace “hosana me kike tunani game da hafsat da mommynsu? Anya ba wani abu suka shirya mana ba? Kada fa ace so suke yi su kashe mu ko su zubar damu shiyasa suka tsara mana hakan,’ tayi maganar cikin nuna damuwa a fuskarta,

  Hosanna tace “jahad ni nasan abunda mommynsu hafsat ta shirya mana, fuska biyu tayi mana wlh, so take ta nuna mana kulawa sosai don mu saba da ita yadda in yaya Omar yazo yace zai tafi damu muƙi binsa saboda sun nuna mana kulawa………’  dakatawa tayi da maganar jin alamun tunkarowar mutun ɗakin da suke ciki,

  Hafsat ce ta shigo ciki fuskarta ɗauke da murmushi tace “sannunku My sisters ya jikin naku”? Ta tambaya ayayin da take samun wuri saman room sofa ɗin tazauna,

   “Alhamdulillah da sauƙi” suka bata amsa atare, mayar da idonta tayi gefen kujerar da take zaune leda ce  ajiye wadda taba Jahad ta ruƙe mata bayan ta fito daga store, hannu tasa ta ɗauki ledar tana cewa “Lahh Jahad wannan ae naku ne na siya maku, Chocolate ne da sweet ko bakwa so ne”? ta tambaya tana kallonsu,

   Suka haɗa baki wurin cewa “muna so,” sannan jahad ta sauko daga saman gadon tasanya hannu biyu takar6a tana fadin “mungode Aunty hafsat,” 

 Murmushi hafsat tasaki tare da cewa “Naji daɗin sunan nan da kuka kira ni dashi, amma nafison ku kira ni da Sister Hafsat akan aunty hafsat zanfi jin daɗin hakan,” 

Murmushi su kayi su dukan su, kafin daga bisani Jahad ta curo musu chocolate cookies ɗin data siya musu, guda biyu ta curo ta ɗauki ɗaya sannan ta miƙa ma hosana suka 6are suna sha, 

   Har lokacin idon hafsat na akansu kallonsu  takeyi gwanin burgewa, dama tun ranar farko data fara cin karo dasu sun burgeta kawai baƙin hali ne irin nata yasa bata nuna ba,

  Ɗagowa su kayi jin alamar shigowar mutun, AUNTY BABBA ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi tana kallonsu tace “Ya jikin naku My daughters?

   haɗa baki su kayi wurin cewa “da Sauƙi Alhamdulillah,” 

Jinjina kanta tayi kafin daga bisa ni ta kuma cewa “Yakamata ku fito mana kuzauna a palour ko kallo ne kuyi zai ɗebe muku kewa kuma zaku samu nishaɗi,” 

   Amsa mata sukayi da “Toh” sannan suka sauko daga saman gadon hannun jahad ruƙe da ledar choculate ɗinsu, 

   A falon suka samu wuri saman gujera mai mazaunin mutun biyu su ka zauna tare da mayar da hankalin su Wurin kallon shirin da akeyi a tashar Bollywood, tuni kallon ya ɗauke musu hankali saboda daɗin dramar da suke yi ta india, dama kuma ga chocolate ɗinsu suna sha sai abun yaƙara nutsar dasu gaba ɗaya,

   AUNTY BABBA  kuwa wuri tasamu ta zauna agefen gadon tana fuskantar hafsat tace “Sannu Madam,”

  tashi hafsat tayi zaune tana cewa “Mommy dama ina son magana dake! Wannan canjin dana gani a tattare dake shin dagaske ne? Ko duk shiri ne? ta tambaya tana kallonta don jin amsar da zata bata,

   ɗan ƙayataccen murmushi AUNTY BABA tasaki tare da cewa “Hafsat kenan ! Ke naso ki fara faɗamun gaskiyar lamarin nan shin dagaske ne yanzu kin fara jin tausayin yaran nan? 

   “Mommy da gaske ne, natausaya musu sosai saboda bugun rashin imanin da kika yi musu, kuma ayanzu bana son wani yaƙara ƴunƙurin cutar dasu daga ni har KE !

   Ajiyar zuciya aunty babba tasaki tana mai jinjina kai tace “Shin ya maganar matar da kika amsar ma kuɗi kusan miliyan shidda? Mayar mata su zakiyi kenan…..?

   Hafsat tace “wannan ni tashafa mommy, zan san yarda zanyi da ita, in ma bazaiyiyu ba just zan mayar mata da kuɗinta ne,” 

ɗan ta6e baki AUNTY BABBA tayi daga bisani tace “Shikenan Daughter but lemme remind u something, kin manta da uban bashin da Ake bin ki kenan u ave to think about it, how can u pay all ur debt? Dole ki buƙaci kuɗi ………………..tana kai ƙarshen maganarta, ta tashi ta fuce tana faman sakin shu’umin murmushi aranta tana cewa “Yarinya kenan! Naki wasa ne,” 

**********💪💪💪***************

 misalin ƙarfe 5 da rabi na marece a lokacin suna dab da kammala aikace-aikacen su na girki, sai ga OMAR ya shigo cikin gidan kai tsaye kitcen ya nufa in da suke, Hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin OMAR don atsorace take dashi,

 bai shiga kitchen ɗin ba tsayawa yayi daga waje ba tare da yace komai ba, 

Sehrish ce tace “Aunty Azmee ga yaya Omar nan,” azmee na jin haka cikin sauri ta fito izuwa inda yake tsaye da murmushi a fuskarta tace “Omar ashe kaine ina fata lafiya dai ko,” 

  Jinjina kansa ya ɗanyi ayayin da idonsa ke kallon sehrish wadda ke acikin kitchen taƙi ɗagowa su haɗa ido dashi, har time ɗin ya gaza gasgata abunda idonsa ke nuna masa,

  ɗan gyaran Murya yayi tare da mayar da idonsa kan na Azmee yace “Sannuku da ƙoƙari, ina fata dai ban katse maku aikin ku ba”

   Azmee tace “A’a wlh Ae ma mun kammala girkin gyaran kitchen ɗin ne kawai ya rage mana yanzu,” 

 OMAR  Yace “Okey, dama aiki ne nake son kuyi mun ke da waccen Yarinyar ta cikin kitchen,’ 

  Jin hakan yasa sehrish ɗan ɗagowa suka haɗa ido dashi cikin sauri ta sunnar da kai ƙasa,

   Azmee tace “Wane kalar aiki kenan Omar?

   “Zan baku makullin gidan Uncle ABUSUFYAN so nake Kuje can ku duddubamun gidan duk wani abu da ake buƙata kawai inaso ku rubuta mun shi,”

  Murmushi azmee ta saki tare da yin ƙasa² da murya tana cewa “To fa, kodai Abusufyan ne zai dawo nigeria da zama ne?

  Kamar daga sama taji muryar Omar yace “Bashi bane zai dawo, wasu marayu ne nake son zubawa aciki, so inaso agyara mun gidan da duk wani abu na more rayuwa da mace zata buƙata acikin Sa, sannan bayan kun kammala wannan aikin inaso ku shirya zuwa Yi masu siyayyar kayan sawa da sauran abubuwan buƙata na mata,’

   Azmee tace “wannan ai aikin lada ne, insha Allah Omar zamu yi komai yadda kake so,”

    “Hakan yayi mun, bari na ɗauko maki key ɗin gidan ku tabbatar kunje yau, zansa Junaid ya kai ku a motarsa,” ya yi maganar yayin da yake wuce wa izuwa sashen Abbansu,

         Hannu yasa ya ciro wayarsa daga cikin aljuhun wandonsa, contact ya shiga tare da dannawa Abban nasu kira, kamar jira yake omar ya kira sa awaya sai gashi ya ɗauka,

 Ƙara wayar Omar yayi a kunnansa    yana cewa “Abba gani nashigo bedroom ɗin naka, wurin ina key ɗin yake”?

    “Ka duba cikin side drawer ɗita gida na tsakiya suna anan ciki makullan na zuba su,” 

   “Ok to ngde Sosai Abbana, take care of your self for me,” 

  yana jiyo sautin muryar Abban nasu Mai haɗe da Murmushi yana cewa “Nima haka ka kulamun da kan ka,” 

   “Insha Allah,” Omar ya faɗi tare da rejecting kiran, ya mayar da wayar tasa cikin aljihunsa,

   Kai tsaye inda Bedside drawer ɗin Abban nasu take ya ƙarasa tare da zuƙunnawa ya janyo gida na tsakiya acikinta, Sai ga makullan sun bayyana hannu yasanya ya ɗauka sannan ya fito daga ɗakin nasa,

   Kitchen ya nufa azmee na ganinsa ta fito, ƙarasawa yayi tare da miƙa mata key ɗin yana cewa “Ga shi nan ku tabbatar kunyi aiki mai kyau, yanzun nan zan ma junaid magana yazo yakai ku can gidan,” 

  Azmee ta amsa masa da cewa “Toh insha Allah,” sannan Omar ya fuce daga main palour izuwa filin buga ball ɗinsu tunkan ya isa yake faman kwalawa junaid kira wanda ke acikin filin kwallon sai faman buga ball suke yi su uku shi da wasu daga cikin security ɗin gidan,

   Jin kiran Omar yasanya shi dakatawa da yin kwallon ya wurgar masu da ita sannan ya fice daga cikin ragar izuwa inda Omar yake, 

       tsayawa yayi agabansa tare da zuƙunnawa ya dafe guiwarsa sai faman haƙi yake yi daker ya iya cewa “Yaya Omar gani,”

   Hannu omar yasa tare da bugun bayan junaid yace “Bana hana ka buga ball dayawa har haka ba? Tun fa ɗazu dana shigo nasame ka, cikin waɗancan gardawan sai faman wahalar mun dakai suke yi,” 

   Murmushi junaid yasaki tare da ɗagowa tsaye yana cewa “Yaya Omar zandaina ne, amma yanzu tana sanya ni nishaɗi sosai,” 

  Jinjina kai Omar yayi tare da dafa kafaɗarsa yace “ko don saboda lafiyarka junaid, yakamata kadaina yawan buga kwallon ɗin nan da kuma yawan yin guje-guje,’

   Cikin girmamawa junaid yace “insha Allah yaya Omar zandaina,” 

  dafa kafaɗarsa omar yayi sannan yaci gaba da cewa “ka shiga ciki ka shirya zaku fita tare da Azmee da wannan Yarinyar inaso ka kaisu Gidan Uncle Abusufyan, zasu yi mun aiki ne kaima sai ka taya su,”

  Cike da zumuɗi junaid yace “To shikenan yaya Omar, bari naje yanzun nan nashirya nakaisu,”

   “Yawwa My boy,” Omar  ya faɗi tare da wuce wa gaba, 

   Shige wa junaid yayi da gudu cikin babban falon kamar ba wanda aka gama ja ma kunne akan yin gudu ba,

   A lokacin azmee da sehrish sun kammala gyara kitchen ɗin, kowan nan su ya wuce ɗakinsa domin kimtsawa, 

  Da gudu yake tattaka Matattakalar benen adai-dai lokacin SGR ya fito shima yana ƙoƙarin saukowa down, jikinsa na sanye da jallabiya fara mai gajeran hannu abun ba’a magana,

    tsayawa yayi yana jiran isowar junaid Domin yayi masa kyakkyawan ruƙo, sai da junaid yakai ƙarshe sannan ya lura dashi, ɗan zaro ido yayi tare da dakatawa da tafiyar gabansa na faɗuwa, sarai yasan cewa sun hana shi gudu shi kuma abun ajinin sa yake yadda kasan wanda aka sanya Ma battery haka junaid yake,

    Tun kafin Babban yayan nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa “Bazan ƙara ba wlh, na daina” ya faɗi yana ɗan raku6e fuska yana kallonsa wuri da ido, 

    Sgr yace “Junaid na ta6a sa hannu na ajikinka, da sunan zan buge ka ga?

   Girgiza kai yayi tare da cewa “a’a babban yaya, baka ta6a ba kuma bana fata, ai nasan ma bazaka ta6a buguna ba,” ya faɗi da murmushin nan nasa,

    Sgr yace “meyasa kake tunanin cewa bazan iya bugunka ba,”?   

    ɗan cizon red lips ɗinsa tare da cewa “Because…….You love me so much……’ ya ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin sauri yana dariya, bin shi da kallo kawai Sgr yayi, tunawa yayi da wata magana da aka ta6a faɗa masa cewa

*Kowa ne ɗan adam yana da lagwansa, kaima haka ga lagwagonka nan, wato ƙanin ka JUNAID, Yakamata ka kula dashi sosai, Saboda duk wanda zai kawo maka hari acikin maƙiyanka, to ina da tabbacin cewa zasu 6ullo maka ne ta wurin JUNAID, So you’ve to be very careful,”!

     Jikinsa ne ya ɗanyi Sanyi amma ta wani 6angaren yana jin cewa bazai ta6a barin hakan ta faru ba A matsayinsa na SURGEON GENERAL RAFAYET, 

   A babban falon ya zauna saman doguwar kujera mai mazaunin mutun uku, ya kishingiɗa tare da ciro wayarsa yana daddanawa,

  Shigowa Omar yayi cikin babban falon ganin SGR yasa shi sakin fara’a yana cewa “Ashe kana ciki yaushe ka shigo,” 

   tashi zaune Rafayet yayi jin muryar omar,

   Kallonsa yayi tare da cewa “ban jima da dawowa ba, what of u ,”? ya tambaya yana kallonsa,

  Zama Omar yayi saman Sofa ɗin da sgr yake suna ɗan fuskantar juna yace”Nima yanzun nan nashigo, bansan kana aciki ba ae dana shigo, dama inaso nace kunyi waya da EVA? tana so tayi magana dakai sosai tayi mun magana ɗazu, its better ka kira ta if not kasan halinta ƙaramin aikinta ne kaganta a Nigeria,”

   ɗan ta6e baki sgr yayi tare da cewa “naga missed Calls ɗinta, na manta nabi kiran nata that’s why,”

  Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa “Har yanzu baka yanke shawara bane game da ita? Pls bro kodan saboda Uncle Donald yakamata ka sassauta mana….’

  Wani irin kallo Sgr yake binsa dashi kafin yace “Uncle ya riga da yasan tsarina, ko shi kansa ya tsawatar mata akaina amma taƙi ji so ni banson ya zanyi na fahimtar da ita ba,” 

    Omar yace “matsalar kenan, ni abunda yafi damuna taurin kanta, in banda ƙarfin hali irin nata taya zata ce dole sai kai zata aura? a ƙalla EVA ta baka kusan 10years aduniya, har yaushe ne zata daina wannan mafarkin? ya tambaya yana kallonsa,

  Sgr yace “Omar da ace zan iya canza ra’ayi na akan mace ,to ina mai tabbatar maka da cewa ita ce mace tafarko da ta cancanta ta mallake ni, saboda kusancin dake a tsakani na da ita……………….”

  Karaf!! Maganar Sgr ta sauka a kunnan Sehrish wadda fitowarta kenan ta nufo cikin babban falon, har ta kammala shiryawa tsaf, ta zumbula jalbaba ajikinta har ƙasa maroon colour, hannunta na ruƙe da hand bag, ƙafarta kuma na sanye da flat shoes launin hijab ɗinta, fuskarta sam babu makeup ƴar hoda ce kawai ta shafa sai ta murza man baki a la66anta, amma ba ƙaramin kyau tayi ba, tsayawa tayi jiki amace tana sauraron firar tasu sam tagaza motsi, har sai da Marshal Omar ya ɗago da idonsa ya kalle ta, gabansa ne yaji yayi mugun bugu sam yagaza ganewa wannan ruɗanin dake a fuskar yarinyar nan, Sehrish bata lura da kallon da Omar keyi mata ba, juyawa Sgr yayi don yaga me Omar yake kallo ne karaf idonsa suka sauka ana sehrish wadda itama idon nata na akanshi, from up to down ya kelle ta kafin yace “Ke zonan,” gabanta ne taji ya faɗi rass tayi firgit tana kallonsu, hankali atashe ta tunkare su gabanta na ɗarr!ɗaarr ta ƙarasa inda suke dab da Babban yayan nasu daya kira ta, Hannu yasa tare da ruƙo jalbabar dake ajikinta, saboda tsananin tsoro sai da sehrish ta kusa sakin fitsari tuni jikinta yasoma kerma kaf!kaf !!kaff!

     cikin sanyayyiyar muryar nan tasa ta natsastsu yace “Menene wannan haka ajikin ki,”? Ya tambaya in serious matter batare da ya aza idonsa akanta ba,

  Murya na rawa sehrish tace”hi..hij..hijabi ceeee…’

   “Masallaci zaki je ne”? Ya tambaya yana jiran amsa,

    “A’a fita zamu tare da aunty azmee,”

    Cire hannunsa yayi tare da nuna mata hanya yace”maza ki koma, ki cire wannan abun, bana son sake ganin shi,” cike da mamaki Omar ke kallon sgr har dai yagaza yin shiru yace “Rafayet nan fa ba Us bane Nigeria ce, kuma wannan shine best outfits da yace mace musulma tayi, Domin rufe surar jikinta daga jan hankalin mutane akanta saboda tsaro,’

  girgiza kai sgr yayi tare da cewa “ban yarda da wannan shigar ba, shin Omar taya mutun zai iya motsi acikin wannan abun”? Ya tambaya yana nuna hijabin jikin sehrish,😂

  Fashewa da dariya Omar yayi kamar kamar me, ganin yarda Sgr ya haƙiƙance akan hijabin dake ajikin yarinyar, shi a ganinsa takurace kuma mutun bazai iya motsi acikinta ba, daƙer ya dakatar da dariyar tasa ya kalli sehrish tare da cewa “Ki faɗa masa yarda kike motsi acikinta may be ya fahimta,”

   ɗan murmushi sehrish ta saki ita kanta abun ya gama ɗaure mata kai, ɗagowa da hannayenta tayi tare da cewa “Ga hannun hijabin nan, tun da na fiddo da hannun acikinsa lafiya lau nake motsi acikinta,” ta ƙarasa bayanin tana kallonsa

   Jingina bayansa yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa “Its Okey, u can go,’ har ta juya zata tafi Omar yace “Ya Sunan ki ne?

   Juyo wa tayi ta kallesa da murmushi a fuskarta tace”SEHRISH”

  Omar yace “masha Allah suna mai daɗi, amma menene ma’anarsa? ya tambaya yana kallonta,

   *kyawawan halayyu na mutun,” 

ta bashi amsa,

  *ina fata zaki nuna mana waɗannan kyawawan ɗabi’un acikin gidan nan, har ma ki zama alkhairi agare mu,” omar ya faɗi da ɗan murmushi a fuskarsa, duk Sgr na sauraronsu duk da ya ci gaba da dannar wayarsa,

   Sehrish ta amsa masa da cewa “Insha Allah,” sannan ta wuce 

  Sai lokacin Sgr yace “Ashe kana surutu har haka Omar?

  Kallonsa Omar yayi tare da cewa”Yarinyar ce tana tattare da wani abun al’ajabi a fuskarta shiya sanya Na sake mata,”

     “Ba kowace baƙuwar fuska yakamata ace kana sakemawa ba irin haka ba, Mata Basu da tabbas they’re trouble makers,” acewar Babban yaya,

   ƴar dariya Omar yayi batare da cewa komai ba,

    Sehrish kuwa kitchen ta wuce ta zubo musu coffee tare da snacks a plate Cikin tray sannan tadawo inda suke tare da ajiye masu saman Table, Omar yace “thank u miss Sehrish,” 

   Murmushi tayi masa sannan ta juya ta nufi ɗakin azmee tunkan ta ƙarasa ɗakin nata sai ga Azmee ta fito itama ta kammala shiryawa cikin atampha ja, ta aza babban mayafi milk colour launin takalminta ƙafarta, atare suka fuce suna jiran isowar junaid,

   Ba da jimawa ba sai ga junaid ya fito daga upstairs yana saukowa down sai faman zabga murmushi yake yi, jikinsa na sanye da haɗaɗɗiyar shadda gezner blue colour mai maiƙo sai faman ɗaukar ido yakeyi kai kace wani sabon ango ne, shaddar tasha aiki a wuyanta tsantsararre, hannunsa na ruƙe da wayarsa haɗe da key ɗin motarsa,

      Lokacin daya ƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin, gaba ɗaya Marshal Omar da Sgr suka bishi da kallo, 

    Zagayawa yayi inda babban yayan nasu yake yana isa ya manna mashi kiss agefen fuskarsa sannan yace “Zan fita, saina dawo,” ko amsa bai jira ba cikin sauri ya lalla6a ya fuce yana cewa “yaya Omar kayi masa bayani, mu mun wuce ,”

   Girgixa kai kawai SGR yayi sam ya kasa magana, wato junaid yasan cewa zai iya dakatar dashi daga fita shine yayi dabarar tserewa,

    Murmushi Omar yasaki tare da cewa “Junaid kenan ! komai nasa  na burgewa, ya cika ƙiriniya ga shegen wayon tsiya, saboda kada ka hana shi fita shiyasa ya gudu bai jira amsarka ba,” yayi maganar yana kur6ar coffee ɗin da sehrish ta kawo masu a cup,

    “Ina zasu je ne”? Sgr ya tambaya yana kallonsa, Omar yace “Gidan Uncle Abusufyan na aikesu, inaso zanyi amfani da gidan ne akwai wasu marayune da zan zuba acikinsa kwanan nan,” 

    Sgr yace “Omar kenan, meyasa baka sanarmun ba? ko ni ba’a buƙatar gudummuwata ne? ya faɗi yana kallonsa,

   Murmushi Omar yasaki dama sun saba indai irin haka ne, muddin akace aikin lada yasamu, to har rububi suke yi wurin bada taimakonsu, kowa burinsa ace da dukiyarsa za’ayi amfani wurin bada tallafi sam basa gajiya da irin wannan (Kaji masuyi don Allah) Shiyasa dukiyar tasu kullum hau hawa takeyi kamar kamar me, a ƙalla su kansu basu son adadin gidajen marayun da suka buɗe ba a kasashe daban daban kuma suke ɗaukar ɗawainiyarsu da komai, Manyan asibitoci kuwa da suka buɗe ba iyaka, wanda suma duk kyauta ne ake duba marasa lafiya acikinsu, ga makarantu na marayu da marasa hali da suke dasu ba adadi, wannan ba komai bane ba, kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke yi na taimako, Ya Allah ka bamu arziƙi mai albarka wanda zamu amfana dashi kuma ƴan uwanmu musulmai suma su amfana dashi, ba irin arziƙin da mutun zai mallaƙe ba, ka ga ko cikin gidansa fama ake dashi basa ciyuwa balle na waje su samu😧

*****GIDAN ABUSUFYAN*******

Haɗaɗɗiyar daula, Aljannar duniya tun daga kan Tanƙameman gate ɗin gidan Golden colour & brown sehrish ta saki baki tana kallo Ikon Allah, Ba don daga gidan Abban sojoji ta fito ba da sai tace wannan gidan a dubai yake, tsayar da motar junaid yayi abakin gate ɗin sannan ya fito daga cikin Motar, ya nufi jikin gate ɗin, tunkan ya isa ya danna madannin da ke ajikin key ɗin gidan a hankali gate ɗin ya soma zugewa da kansa daker daker yake tafiya saboda gidan ya jima ba’ayi amfani dashi ba tunda Abusufyan yabar Nigeria a fusace gidan yake ahaka garƙame, ganin zai 6ata musu lokaci yasa junaid sanya hannunsa yana ƙoƙarin turasa da ƙarfinsa don yayi saurin f

Buɗewa, aikuwa nan take zufa tasoma wanko masa kamar wanda aka watsa ma ruwa a fuska dama jiki bana wahala ba, muryarsa kamar zaiyi kuka yace “Aunty Azmee wai bazaku fito ba mu tura, Wlh ban iyawa ni kaɗai,”

   Jin hakan yasa su fitowa daga cikin motar suna faman tikar dariya, azmee tace”Haba junaid wannan fa ƙaramin aiki ne, sai kace ba Namiji ba haba karka ban kunya mana, Be a Man,’ 

   Kallon azmee yayi yana faman sauke haƙi yace”In dai saina tura wannan jibgegen gate ɗin zan zama namiji, to Allah abarni a jinsin mace yafi mun,” 

   Fashewa da dariya sehrish tayi har tana dafe ciki jin abunda junaid yace, harara ya watsa mata yana hura hanci,

   Azmee na isa jikin gate ɗin tace”Matsa ka gani junaid, ni bari in zama Namijin, ni kaɗai zan tura sa,”

   Jin haka yasa junaid matsawa suka bata wuri don ta jaraba, gefen Sehrish ya tsaya suka zuba ido suna kallon azmee,

   Hannu tasanya sannan ta soma tura gate ɗin nan take ya tafi da gudun gaske ya ƙarasa zuge kansa,

   Zaro ido Junaid da sehrish su kayi cikin tsananin mamakin ƙarfi irin na AZMEE, 

   A ruɗe junaid yace”Aunty azmee taya hakan ta faru? Ni nakasa turasa amma ke kina aza hannu gate ɗin ya buɗe,”

   Murmushi azmee ta saki tare da nuna masa damtsen hannunta tace “Tsohon ƙashi kenan! ba irin naku ba na ƴan shila,” 

   Fashewa su kayi da dariya su duka kafin daga bisani suka koma cikin Motar, junaid ya shigar da ita cikin gate ɗin kai tsaye yayi parking ɗinta a harabar gidan

  

    *Shin Kuna tunanin Cewa Omar zai samu damar ɗauko su hosanna da Jahad daga gidan Aunty babba*?😟

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button