Uncategorized

Wata Sabuwa: Jarumi Kannywood yayi Kira Da Ayi Sulhu Tsakanin Nura M. Inuwa Da Abdul Amart

Jarumi a masana’antar Kannywood wato Aminu A. Dagash yayi rashin jin dadin yadda alaƙa ta yi tsami tsakanin manyan abokan juna kuma aminai wato Nura M. Inuwa da Abdul Amart Mai Kwashewa, shi dai jarumin yayi kira ga manyan masana’antar da su yi wa Allah su shiga wannan maganar wata ƙila ko Allah zai sa a samu daidaito tsakanin abokan biyu. Su dai abokan biyu ada kafin wannan danbarwar ta faru sun kasance suna aiki ne tare a ƙarƙashin kamfanin su mai suna Abnur Entertaiment.

Ga abin da shi Aminu A Dagash din ya rubuta a shafinsa na instagram,

aminu_a_dagash Abnur Amintattun mutane biyu da duniya ta gamsu da nagartar amincinsu. Abdul & nura, bazamu bari din kakkiyar kwarya ta fashe ba, Kuma ace ta gagari dinki ba. Aminu Mannir k-eza said @abdulamart_mai_kwashewa @nura_m_inuwa

Also Read:

Ummi Rahab ta zama ta ɗaya a wadanda suka mallaki Iphone 13 Pro Max

Gaskiyar Magana Akan Aure Hadiza Gabon da Malam Ali Pantami.

Bayan wallafa bayanin da Aminu A Dagash ɗin yayi, masoya da magoya bayan Mawaƙi Nura M Inuwa da ma na Abdul Armart din sun nuna rashin jin dadin su, inda suma suka yi fatan Allah ya shiga lamarin nasu, Ya kuma daidaita tsakaninsu ayi sulhu domin shi sulhu alkhairine.

Duk iya kokarinmu na sanin abin da ya haɗasu ba mu samu ba, amman ku ci gaba da bibiyar wannan shafi namu da sannu zamu kawo maku dalilin da yasa alakar aminan biyu ta yi tsami.

Back to top button