Mallama Juwariyya

Domin Sabbin Ma’aurata: Ladubban Daren Farko Da Yadda Ake Yinsa

Mallama Juwairiyya Bin Usman

Abubuwan Da Ya Kamata Sabbin Ma’aurata A Kan Yadda Yin Ladubban Daren Farko

Daren angwanci wani dare da ake farinciki, idan an wayi gari cikin sa rana ce da masoya basa iya mantata a matsayin ranar fari ciki. Zaku kasance a wani hali mai tattare da shauki da zumudi na kasance warku a matsayin abu daya, daren daraja ga ma’aurata kenan.

Da zarar an kai amarya gidan mijinta ango kenan, Iyayenta da kawayenta za su barta a daki tana jimamin kasancewar ta a wannan yana yi na kasancewar ta amarya.

A kan so bayan an watse ambar amarya ta tashi ta dan gyara abin da take ganin bazai kayatar mata da ango ba a wasu guraran kawayen amarya suna tsayawa har sai an kawo ango. Wannan baya cikin al’ada an fison abar amarya daga ita sai ango su ci amarci.

 

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Sabulun Da Zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Da Kuma Maganin Kuraje

 

Kai ango ka shigo ku yi abinda addini ya yarda dashi na sanar da ita yadda addini yake, kuyi sallah ku nuna godiya ga Allah ku ci daga abinda Allah Ya baka a wannan dare domin more amarci.

Na biyu shine kokarin tafiyar da kunya tsakanin ma’aurata kasancewa sababbin ma’aurata duk baki suke ga wannan harka ta ibadar aure, dole ya kasance akwai kunya da ‘yar fargaba kan daren, don samun cikakkiya nasara daren farko, sai ma’aurata sun rage jin kunyar dake tsakaninsu, Ya kasance suna tattaunawa kan batun ibadar aure, da yadda suke fatan daren farkonsu ya kasance.

Da kuma dokinsa dasa kyawawan tunani cikin zuciya game da shi tun kafin zuwan ranar a nan aikin ango ne ya rika bi a hankali, cikin wasa da raha da zolaya ta hanyar amfani da kalmomi makimanta ba masu nauyi ba, kuma ya kasance suna cike da shauki, har yaga Ya zakulo amaryarsa ta rage jin kunya, in ma dai ba ta daina ba, fada matan zai sa ta zama cikin sanin abinda ka iya faruwa, haka kuma yana da kyau ma’aurata su nema tare da karanta littafai dasu kai bayani kan ilimi ibadar aure don a fahimce su.

Karanta>>> Domin Dawo Da Martabar Nonuwanki Cikin Sauki.

Shirya Jiki Da Jini: Domin dai jiki da jini kamar inji ne ga fetur din gabatar da ibadar aure: don haka yana da alfanu ga ma’aurata su inganta lafiyar jikinsu da ta jininsu ta hanyar cin abinci mai kyau da gyara jiki musamman ganyayyaki da ya’yan itatuwa da yawan motsa jiki da sauran shirye -shirye makamanta wadannan yin kyakkyawa zato game da juna: ango Ya sani abubuwa da yawa na iya ballewa mace murfin budurci ta daga cikinsu akwai;

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

1. Jinin haila mai nauyi

2. hawa sama, itace, gini da sauran su.

3. tsalle-tsalle, kamar wasar tsalle-tsalle da sauran su.

4. Yawan hawan keke ko doki

5. Hawa jaki da dai sauran su.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Ya kamata iyaye su dinga hana yara mata irin wadannan matsalolin don haka haramun ne Ya kawo wani mummunan zargi game da matarsa har in ya same ta ba da murfin budurci ba ana iya samun matsala. Ma’aurata su sani cewa ba lallai bane su samu nasara a daren farko su domin gajiyar hada-hadar biki da fargabar yin wani muhimmi abu Na Karo Na farko Na iya haifar da kaduwar jiki har tasa ango yaji Ya kasa.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Don haka ba lallai bane ko dole sai an gabatar da ibadar aure a daren farko, in aka daga shi zuwa wani dare, bayan jiki Ya huta, abin yafi kayatarwa sannan ga sabon angon da ya san yayi sabo da zinar hannu, Ya kamata yayi kokarin dainawa a kalla wata uku kafin daren farko, kuma Ya sababbin ma’aurata su sani, haramun ne gare su yin tunane-tunanen alfasha kamar kallon finan-finan alfasha.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Ladubban Yadda Ake Yi A Daren Farko

Da farko idan zaka shiga dakin amaryarka, zaka shiga ne da alwala. sannan zaka nemi dan wani abinci mai daraja, misali: kamar kaza ko tsire da sauransu idan kashiga zaka umurceta itama taje tayi alwala sannan kuyi wa Allah godiya a bisa cika musu burinku da yayi. Kuyi addu’o’in a bisa kanku da dukkan al’ummar da suka amsa gayyatar ku suka halarci wajen daurin aurenku daga nan sai ka dafa kanta ko goshinta sannan ka karanta wannan addu’a

Allahumma Innee As’aluka Khairaha Wa Khaira Ma Jabaltaha Alayya Wa A’uzubika Min Sharriha Wa Sharri Ma Jabaltaha Alaiyaya (ko kuma ma jubilat alaiha) (Abu dawud Ya ruwaito DA ibnu maajah da nisa’i)”

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Daga nan kuma sai kuci wannan abinda ka shigo dashi ku dan sha wani abu amma ba’a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin daga nan kuma sai ku kusanci juna, tare da gabatar da yan’wasanni da juna kafin kufara gabatar da ibadar aure, kuma akwai addu’o’in da ake karantawa daidai lokaci jima’i.

Allahumma jannibnash shaitan wajannibish -shaytana ma razaktana

Karanta>>> Hadin Karawa Mace Ni’ima, Sha’awa Da Kuma Karin Dandano

ANNABI (S.A.W) yace “idan aka kaddara samun ciki a wannan saduwar to shaitan ba zai iya cutar dashi ba har abada (bukhari DA muslim suka ruwaito).

Wannan shine cikakken bayani kan yadda ake yin daren farko tsakanin ma’aurata, da kuma ladubban abubuwan da addini yazo dashi. Da fatan kun ilimantu.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Back to top button