Uncategorized

Macijine Shi Page 13-14 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 13/14

____________________”Wayyo Allah na Mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar tallafinka,ahhhhhhhhh !!!fattu ta kwalla ƙara mai tsananin ƙarfi lokacin da taji hannun maigari na ƙoƙarin taɓa mata dukiyar fulani tana mai buge hannunsa daga kan ƙirjinta.

Ɗaga hannu maigari yayi cikin fushi ya sake ɗauke fattu da wani gigitaccen mari,dan ya fuskanci tana ƙoƙarin kawo masa cikas akan ƙudurinsa,shikuwa ya rantse yau bazai bar wannan damar ta wuce shi ba.

“Dan ubanki ki tsaya nayi- nayi abinda ke gabana,wllh yau ko ubankine bukar zai zo gurin nan bai isa ya hanani aiwatar da ƙudirina akanki ba”mai gari ya faɗa yana ƙara ƙoƙarin maida hannunsa gurin dake tsole masa idanu,wato  breast ɗin fattu.

Saidai kafin hannunsa ya sauƙa ga inda yayi nufin ,yaji  wata irin shaƙa da tunda yake arayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin irin makamancin wannan shaƙar a aduniya ba.

Ta ko ina yaji shi aɗaure dam-dam kamar ƙullin buhun goro.

Cikin azaba da fizgar magana mai gari yace “wayyo Allah hannuna,na shiga uku wayyo zan mutu”  ya faɗa idanunsa azazzare kamar zasu fito tsabar azaba.

Cikin hanzari fattu wacce idanunta ke rufe, ta riga ta gama fitar da rai ta sadaƙar cewa yau shikenan ta rasa budurcinta ,dan ta san ba mai zuwa ya ceceta ,koda tayi ihu ba mai jin sautin ihunta,sakamakon ruwan saman da ake tsugawa.ba zato ba tsammani tajiyo ihun maigari lokacin da maciji yayi sama dashi  ya cilla shi can gefe guda ,bayan tabbatar da cewa mai gari ya suma.ji kake ƙasss-ƙasss,hannu da ƙafar mai gari na bangaren dama sun karye.

Da sauri fattu ta kalli inda akayo jifa da mai gari dan tabbatar da cewar shiɗin ne kokuma yaya.aikuwa cikin wani irin farin ciki da murna ta yunƙura da ƙyar ta zauna tana kuka da dariya,sai kuma ta tafi gareshi cikin rarrafe tana zuwa inda macijin ke tsaye yana huci ya ƙure mai gari da ido,da alama yana son ganin maigari ko zaiyi wani motsin ne yaje ya ƙarasashi,duba da yadda yake ta uban huci ya kafe mai garin da ido.

Fattu na zuwa ta wani kwaƙume  macijin zuwa jikinta ,ta ƙanƙameshi tana kuka kamar ran ta zai fita,kukanta na dalilai biyu ne,dalili na farko shine ganin macijinta na nan araye ba mutuwa yayi ba,kuma masu neman shi basu ganshi ba.na biyu kuma yadda yazo ya kawo mata ɗauki adaidai lokacin da ta fidda rai da  cewar zata rasa abu mafi muhimmanci arayuwarta.

“Ina ka shiga mai taimakona?na shiga damuwa na rashin ganinka, naji tsoron ko sun kamaka sun kashe ,dan Allah karka ƙara yin nesa dani na tsawon lokaci irin haka,kalli yadda suke son kawar min da budurcina, bansan me na tsare musu ba ,kowa nufinsa ya cutar dani,kai kadai ke sona,sai baffana ,bana son na rasa ɗaya daga cikinku ,kune rayuwata,farin cikina da jin daɗina,mai taimakona ina sonka har cikin zuciyata, ba ruwana da kasancewarka wata halitta ta daban,Dan kafiyemin halitta irin tawa sau dubu”duk cikin kuka fattu ke faɗin Waɗan nan maganganu,yayi da take ƙanƙame da macijinta kamar zata maida shi cikinta.yadda ta ƙanƙameshi, kai kace uwace ake ƙoƙarin rabata da ɗanta.

Ahankali macijin nan ke sauƙe wani irin numfashi kamar yana hurawa fattu iska mai sanyi ,da alama dai rarrashinta yakeyi,dan yadda yake huro iskar yana wani rufe ido da buɗewa shine zai fahimtar da kai cewar rarrashinta yake .

Zare jikinsa yayi daga ƙwaƙwumar da fattu tayi masa ya zagaye west ɗinta ,Amma Sam bai matseta ba ,sannan ya shigo da kanshi ta ƙirjinta yana kallon fuskarta yadda hawaye yayi faca -faca kan kyakkyawar fuskar tata.kallon -kallo ake tsakanin fattu da macijinta ,kallo yake mata irin na tausayawa dan abin mamaki ne sosai idan kaga yadda ya wani marairaice fuska yana ƙifta idanunsa tare da ɗan matso da kansa saitin fuskarta,sai kuma ya kwantar da kan nashi saitin da hawayenta ke tsiyaya, ta ɓangaren dama, sannan yayiwa ɓangaren hagun ma haka.

“Dariya mai haɗe da kuka fattu take yi cike da tsantsar ƙaunar wannan halitta ,hannu ta sanya ta share hawayen daya ƙara zubowa tace “na daina kukan mai taimako tunda baka so ,bazan ƙara ba ka gani ma ko “ta faɗa tana mai ƙara shafe idanunta ,saidai wasu hawayen na ƙara zubowa.

Zare jikinsa yayi yana mai hawa kan wuyanta zuwa kanta saiya leƙo da kansa ta saman kanta ,idan ta ɗago da nufin kallonsa saiya silale ya koma wuyanta ya ɓoye kansa abayanta.

Dariya fattu take cikin farin ciki da ganin cewar wai wasa yake mata dan ta sami nutsuwa ta daina kukan ,dan haka lokacin daya ɓoye abayanta sai tace “wayyo ni fattu mai taimakona ya ɓata, ya zanyi da rayuwata ,ina kake abinsona shikenan masu son cutar dani zasu sami dama akaina wayyo ga mai gari nan ya taso”ta faɗa cikin yanayi kamar tana son yin kuka .aikuwa cikin sauri macijin nan ya haye kan cinyarta yana mai fasa kai da wani kalle -kalle ya miƙa kansa can ya dawo dashi can yana huci.

Dariya fattu tayi tace “nima ramawa nayi tunda ka boyemin ” ta faɗa cikin shagwaɓa kamar wacce ke gaban baffanta ko innarta.

Juyowa macijin yayi yana kallonta sai kuma ya ɗora kansa daidai saitin zuciyarta yayi lamo ,tare da rufe idanunsa.ahankali ta sanya hannu tana shafa kyakyakywan jikinsa mai matuƙar santsi da laushi.kusan minti biyar suna haka,yayinda ake tafaman zuga ruwan sama ,can gefe kuma mai garine shame shame akwance baya motsi.kallon mai gari fattu tayi ,sai taji tsoro ya cika zuciyarta,kodai shima mutuwa yayi, dan ita tama manta da batunsa aɗakin sam,idan kuma ya farka ya ƙara dawo mata fa ,gara fa su gudu daga ɗakin nan tun kafin jama’a su ankare dasu.

Cikin muryar tsoro tace “mai taimako ya kamata mu gudu gida karya farka ko wani yazo ya gammu dashi ahaka”ta faɗa tana kallon macijin dake kwance akan ƙirjinta,da alama kuma yana jin daɗin kasancewarsa ahakan.

Ahankali ya ɗago kansa tare da silalewa ƙasa yayi hanyar ƙofar fita daga bukkar,wacce mai gari ya barta abuɗe tsabar jaraba na cinsa.

Binsa fattu tayi da sauri ,harta fita saikuma ta dawo ta ɗauke tocilan nan ta mai gari ,dan taga garin yayi baƙi ƙirin kuma har lokacin ruwa ake.

Suna fita fattu ta kama sauri -sauri gudu-gudu ,tana tafe tana haska tocilan ɗin nan ,yayinda mai taimako ke biye da ita cikin salon nashi gudun ,saidai suna tafe yana zagayeta ,dan bata kariya ta kowacce kusurwa.

Suna zuwa gida kai tsaye fattu ɗakin baffa ta nufa,tana zuwa ta shiga ɗakin ahankali tana haska tocilan ɗin hannunta.Allah sarki baffa yana kan sallaya ya ɗaya hannunsa sama yana ta addu’a,juyowa yayi dan ganin hasken da ake haskowa.

“Waye anan”ya faɗa yana kunna tashi tocilan ɗin.

Ai da sauri ya miƙe tsaye yayi kan fattu,yana mai cewa”fattu kece alhmdllh fattu na ba abinda ya sameki,?ina mai garin?waye ya fito dake?baffa ya jero mata waɗannan tambayoyin alokaci guda yana mai shafa kanta cikin farin ciki .

Ahankali fattu ta kalli gefenta ta ƙasa inda macijin nan ke nannaɗe ya fasa kansa yana kallon baffa.tace “baffa wannan ne ya taimakeni, kuma shine macijin daya hukunta su jauro “ta faɗa tana haska macijin da tocilan.

Da sauri baffa yaja baya yana faɗin”subhanalla fattu wannan ai MACIJINE ,meye haɗinki dashi,matsa daga gareshi maza karya cutar dake” baffa ya faɗa cikin tsoro yana mai kamo hannun Fattu.

“Baffa ka kwantar da hankalinka ,ba abinda zai min ,domin mun jima tare dashi,zauna baffa in baka labarin haɗuwata dashi ,sannan baffa macijin nan yana cikin matsala ,dan da alama anyi amfani dashi wajen yiwa wani asiri.

Zama baffa yayi ahankali kan sallarsa ,idonsa akan macijin nan ,daya matso kusa da fattu wacce ke zaune kusa da baffanta,kallon ikon Allah baffa keyi, yadda macijin nan yayi kane-kane akan cinyar  fattunsa ya waniyi lub kamar jariri akan cinyar mahaifiyarsa.

Kallon fattu baffa yayi ,yaga ko ajikinta saima hannu data ɗora akan bayan macijin tana shafawa.

“Ina jinki fattu faɗa min komai dan hankalinta ya kwanta”

Nan fattu ta fara bashi labari tun daga farko har kawo yanzu.

Sannan ta ɗora da cewa “baffa dan Allah mu taimaki wannan macijin dan wllh yana cikin matsala ,bakaga yadda ya koma ba lokacin dana ke masa karatu,mu cire masa wannan masifar dake jikinsa”ta faɗa tana nunawa baffa waɗannan layun dake wuyan macijin.

Cike da mamaki da al’ajabi baffa ke kallon macijin ,wanda ya ƙara kafewa jikin fattu yana kallon baffa da kuma fattu.baffa yace “haƙika akwai wani ɓoyayyen al’amari dangane da wannan macijin ,kuma in sha Allah zamu taimaka masa iyakar ƙarfin mu,tun kafin mai gari ya farfaɗo ya ɗauki matakin kashe macijin nan ,yanzu kije kiyi alwala ki dawo,dan  mu fara aiki akansa.

Cike da ɗoki fattu ta amsa da” to baffa na ina godiya agareta sosai”sannan ta ajiye macijin gefen baffa tace “mai taimako ai kasan baffana ko?to katsaya agurinsa yan zu zan dawo kaji”ta faɗa cikin murmushi tana shafa bayansa.

Kallo ta kawai yayi kafin ya kwantar da kansa ajikin gangar jikinsa dake nannaɗe.

Bayan fattu tayi alwala ta dawo dakin ne ta gabatar da sallolin dake kanta ,sannan tayi addu’ar samun nasara akan ceton macijin nan ta shafa.sanna ta juyo gurin baffa wanda ke ta tofa addu’a cikin wata ƙwarya ,zama ta gyara tana mai kallon baffa da jiran ya kammala addu’ar sa.

Shikuwa macijin nan yana ganin fattu ta zauna ya silalo ya dawo kan cinyarta ya kwanta,gaba ɗaya jikinsa asanyaye yake,kamar wanda yake tsoron faruwar wani abu.kallonsa fattu tayi tace “mai taimako ba abinda zai sameka ka kwantar da hankalinka ,in Sha Allahu zamu cire maka duk wani sihiri da akayi amfani dakai wajen yinsa”ta faɗa tana mai shafa lallausan san jikinsa mai santsi.

Miƙa mata kwaryar nan baffa yayi yace karɓi wannan fattu ki yayyafar masa ajikinsa ,kinayi kina karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi, duk abinda zaki gani karki tsorata kinji ?”baffa ya faɗa yana mika mata kwaryar,dan shikam ya gama fahimtar abubuwa da dama aka. Macijin nan.

Karɓa fattu tayi cikin nutsuwa ta fara karatun tana kuma shafa masa ruwan rubutun nan ajikinsa.

Ikon Allah,ai da fara shafa masa ruwan nan ajikinsa ya fara wani irin motsi da jijjiga ,yana murɗewa ,baffa kuma saiya ci gaba da addu’a yana tofa masa.

Ahankali hannun Fattu ya kai kan waɗaɗan na layin dake wuyan macijin nan,aikuwa damƙarsu tayi da Bismillah ta fizge da ƙarfin gaske.

Wata irin ƙara da guguwa ne suka turnike dakin gaba ɗaya baka iya ganin komai sai duhu…..

Masu karatu mutara gaba dan jin ya zata kaya.

Takuce dai Mrs babi💘💘

Back to top button