Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 86 Complete Novel

 *Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Wuraren ƙarfe shida na marece,ta fito daga cikin toilet,jikinta na sanye da towel fari ta ɗaure shi a saman ƙirjinta,da alama wanka tayi aciki,jahad ta samu zaune saman gadonsu,hannunta ɗauke da wayarta tana ɗan daddanawa,tsayawa tayi a ƙopar toilet ɗin ta ruqe ƙugunta tare da ɗan ɗaure fuskarta tace”Jahad!bana hanaki ɗaukarmin waya ba?kin manta abunda ya faru ran nan?kika kusa kashe mun waya gaba ɗaya!,yanzu da ace ta lalace dashi kenan wa zai siyamun wata”?
Fuskar jahad ɗauke da murmushi tace”Daddy mana!ae yace zai siya mana Phones gaba ɗayanmu,hada ke ma zai canza maki wata,hada ma laptop xai siya mana,”
Washe baki Sehrish tayi tare da cewa”Wai dagaske”?

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Eh,mana,shi da kanshi ya faɗi hakan,Kuma yace next week zamu koma school da kanshi zai mayar damu,don kada wani ya ɗaga mana yatsa,”ta ƙarasa maganar fuskarta dauke da dariya,sehrish kuwa tunda jahad tayi maganar school ba kowa ya faɗo mata aranta ba,face ƙawarta AMRISH,lokaci guda ta faɗo mata acikin ranta,nan take kuma taji gabanta ya faɗi rass,
Ganin fuskarta da alamun damuwa atattare da ita,yasa jahad kiran sunanta”Sehrish,meya faru ne?maimakon inga kina farin ciki?ko baki son komawa school ne?baki gaji da zaman kashe wando ba acikin gida?
Muryarta asanyaye tace”ba haka bane jahad,kawai na tuna da wata school friend ɗita ne,Nayi missing ɗinta sosai,Yarinyar tana sona sosai,itace take ƙarfafa mun guiwa akan in ringa yin karatu,in daina bacci a class,Gaskiya banyi mata adalci ba,sam na manta da ita,ni nasan cewa amrish ta neme ni har ta gaji,”
Jahad tace”Eyya,gaskiya baki kyauta mata ba,gashi sunan ku shigen iri ɗaya ke da ita,ni tun kafin ma in ganta har naji ina sonta,saboda tana son ƴar uwata sosai,Amma meyasa ba zaki jaraba kiranta ba tunda ga waya ko baki da numbarta ne?
“Ina da numbarta,kinsan kwanakin nan hankali na duk ba’a kwance yake ba,tun lokacin da muka daina zuwa school,ban ƙara bi takan wayar ba,sai ma na ganta a hannunki ne sannan nake tunawa da cewar ina da waya,Allah sarki Amrish ɗina,bansan wani hali take ciki ba,gashi bansan gidansu ba,”
Mikewa jahad tayi ta nufi wurin da Sehrish take tsaye,mika mata wayar tayi tare da cewa”Ki jaraba kiranta mana,sai mu gaisa,”
Kar6ar wayar Sehrish tayi,ta shiga cikin contacts ɗinta,ta lalubo numbar amrish,sae dai kash tana kiran layin taji wayar akashe,ɗayan layinta na Airtel ta kira shima akashe yake,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
“Bansan meyasa ba’a samun layinta ba,amma mu bari da anjima sae mu jaraba kiranta mu gani kilan ta kunna wayar,”tayi maganar tare da miƙa ma jahad wayar ta kar6a,sannan ta koma gefen gadon ta zauna,ita kuma ta wuce gaban wardrobe tana lalubar kayan da zata sanya,
Turo ƙopar ɗakin nasu hosana tayi,da sallama abakinta,juyowa sehrish tayi tana kallonta haka itama jahad,
Nuna Sehrish tayi da yatsanta manuni,kafin tace”RISHI KIZO INJI DADDYN MU YACE KI SAME SHI A ƊAKIN SHI,KADA KI WUCE MINTI BIYAR”
Rasss!taji gabanta ya faɗi,
“Hosana dagaske ni daddy ke kira?kuma ni kaɗai yace inzo”?
“Eh,ke kaɗae yake son gani,”
Cikin sauri ta juya tare da zura hannunta cikin wardrobe ɗin,ta lalubo wasu pakistan riga da wando,rigar fara ce,har guiwa daga ƙasanta kwalliyar duwatsu ne,wandon kuma pink colour ne,bai da kwalliya ajikinsa,irin falazun nan ne burgujeje,mayafin kayan ta yafa Shima pink colour,gaban madubi ta koma ta ɗauki flower bomb ɗinta,ta feshe jikinta dashi,sai da ta fara kallon fuskarta a mirror ta ɗan sakarwa kanta murmushi,sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin,
Jahad tace”Allah yasa alkhairi ne!kullum in daddy zai kiramu atare yake kiranmu amma yau ke kaɗae kawai yake son gani,”ta ƙarasa maganar tana nuna bayan sehrish da hannunta,
Murmushi kawai ta saki kafin ta buɗe ƙopar ta fuce,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Da sauri da sauri take tafiya don karta wuce minti biyar ɗin da Hosana tace,tana ƙarasawa baƙin ƙopar ɗakin takai hannu kenan zata buɗe,taga an ja ƙopar daga cikin ɗakin,da alama wani ne zai fito,zubama dogayen yatsun hannunshi ido tayi,farare tass ya ruƙe handle ɗin ƙopar dasu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga ɗakin,nan take ta gane Cewa BABBAN YAYA NE,mamaki ta shiga yi mai ya kawo babban yaya a ɗakin daddynsu?bayan sa6anin da suka samu a tsakaninsu,ko sun shirya ne,?
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,SGR ya ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin Abusufyan,wankan suit ne ajikinshi farare,kyau iya kyau,
Tsayawa yayi cak kamar an dakatar dashi,Sehrish kuwa tuni gabanta ya shiga faɗuwa,tun daga ƙasa har sama yabi ta da kallo,Yarinyar ko ƙafaɗarshi tsayinta bai kai ba,
Daƙyar sehrish ta iya buɗe baki tace mashi”Ina yini”
Tamkar bazai amsa mata ba,don har sai da ya wuceta ya ɗan yi nisa sannan taji yace”Lafiya,”yana faɗin hakan ya ƙara gaba,su babban yaya irin wannan shan ƙamshi haka,
Jiki asanyaye ta shiga cikin ɗakin da sallama abakinta,A zaune ta samu Uncle abusufyan,daga gefen gadonshi,juyowa yayi tare da kallonta fuskar nan tashi ɗauke da murmushi yace”Daughter,”
“Na’am daddy,ta amsa mashi tare da ƙarasawa,ta samu wuri saman sofa ɗin dake fuskantar gadonshi ta zauna,suna facing ɗin juna ita dashi,sannan tace”gani daddy hosana ce ta sanar dani cewa kana nema na,”
“Eh hakane,ni na ce ta kira mun ke,”
Natsuwa tayi tana jiran jin me zaice mata,sae faman wasa takeyi da yatsun hannunta,
“Gobe yaushe”?yayi tambayar yana kallonta,
..fuskarta ɗauke da murmushi tace”Friday,” jinjina kanshi yayi tare da cewa”Masha Allah,Juma’a babbar rana,zaifi kyau in aka kafa tarihi aranar juma’a,ina tunanin kamar zai yi wuya a manta dashi,ko ba haka ba daughter?
Dariya sehrish tayi kafin tace”gaskiya ne daddy,juma’a itace babbar rana,duk abunda ya faru a ranar friday,zaiyi wuya a manta dashi,”
Abusufyan yace”Shiyasa nake so gobe na ɗaura maki aure,ko bakya so”?
Da sauri tasa tafukan hannunta tare da rufe fuskarta,tana dariya,
“Na ƙosa na fara ganin ƴan jikoki na,” cikin zolaya yayi mata maganar,
“Dan Allah daddy,ka daina faɗin haka wlh kunya nake ji,” cikin shagawa6a tayi maganar har lokacin bata zame tafin hannunta daga saman fuskarta ba,
Miƙa hannu Abusufyan yayi tare da janyo drawer chest ɗinsa gida na tsakiya,ya ɗauko wani small box Golden Colour mai shegen kyau,sae faman ƙyalli yake yi yadda kasan da Zallar Zinari akayi shi,
Ruƙo shi yayi a hannunshi yana jujjuya shi,ɗan ɗagowa yayi yana kallon sehrish wadda ta rufe fuskarta,
Gyaran murya yayi mata tare da cewa”Buɗe fuskarki mana,” a hankali ta zame hannunta daga kan fuskarta,kai tsaye idanunta suka sauka kan small box ɗin dake hannun Daddynsu,ɗan zaro idanunta tayi tana ƙare mashi kallo,akwatin ya burgeta sosai,jikinshi sae ƙyalli yakeyi mai matuƙar ɗaukar ido,da jan hankali,cike da zumuɗi tace”daddy wannan fa?wlh yayi kyau sosai,ban ta6a ganin irin shi ba,”
Ƴar dariya Abusufyan yayi tare da cewa”koya burge ki ne”? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Jujjuya akwatin yayi tare da cewa”Sadakin wata Ne,aka biya da Gold,”
Waro ido waje sehrish tayi cike da mamaki tace”daddy!dagaske ka ke dowry ne aka biya da Gold,but daddy who’s she? Dariya abusufyan ya kuma yi ganin yadda tabi ta ruɗe da jin abunda yace,
“Dagaske nake ba wasa ba,sadakin wata Mai sa’a ce,Jinin nasara,”
“Daddy,can i see it pls”?

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Miƙa mata small box ɗin yayi hannunta har kerma yake yi wurin kar6arsa,janyewa Abusufyan yayi fuskar nan tashi ɗauke da dariya yace”Da hannun hagu kuma?hannu biyu zaki sa ki kar6a,sannan in zaki kar6a ki tabbatar da kinyi bismillah,don Abun yayi albarka,”
Murmushi sehrish tayi tare da gyara natsuwarta,sannan ta miƙa hannanyenta duka biyun,tayi bismillah kafin ta kar6e shi daga hannun abusufyan,wani irin sanyi ne taji ya ratsata,jujjuya akwatin ta shiga yi tana ƙare mashi kallo,yana da nauyi duk da ƙarantar shi,hakan ya tabbatar mata da cewar,abune mai daraja acikinsa,ƙoƙarin buɗe akwatin ta shiga yi,da sauri Abusufyan ya dakatar da ita”kada ki buɗe shi,ki adana shi a wurinki,bana so kowa ya gani,kuma kada kowa yasan inda kika ajiye shi,”
Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,
“Amma daddy,sadakin wata ne fa?kuma naji ka ce in ajiye shi a wurina,saboda Me”?
Bai bata amsa ba,sae ma kwantar da bayanshi da yayi saman gadon nashi,ya ɗan kishingiɗa,ya aza kansa saman pillow,yana kallonta,ta zuba mashi ido tana jiran jin amsar da zai bata,
Ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abusufyan,ya jima ahaka suna kallon kallo shi da Ƴar tashi,kafin yace”Zaki samu amsar tambayarki,amma ba yanzu ba,ki bani lokaci zan neme ki,yanzu zaki iya tafiya,”ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanyar fita daga ɗakin,
Tamkar wadda aka zarewa lakar jikinta,haka ta miƙe jiki ba kwari,wani irin faɗuwar gaba kawai take ji,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,tana tafiya tana waiwayen daddyn nasu,daya zuba mata ido yana kallonta,tabbas akwai wani abu da yake 6oye mata,sai da takai bakin ƙopar ɗakin,tana ƙoƙarin buɗe kopar ta fita,taji ya ambaci sunanta
“SEHRISH” da sauri ta juya tana kallonshi,

“Game da abunda ya faru tsakaninki da babban yayanku,Nasan ranshi ya 6aci sosai,ya baki Umarnin kiyi mashi aiki,amma na hanaki a matsayina na mahaifin ki,inaso kije ki bashi haƙuri,’
Waro ido waje sehrish tayi a ɗan tsorace tace”daddy in bashi haƙuri fa ka ce?wlh tsoro nake ji,jiya ranshi ya 6aci sosai,idan na kuskura naje wurinshi yau karya ni zaiyi nasan,”
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,fuskarta tamkar zatayi kuka,
“Don’t worry ur self,SGR bazai ta6a gigin bugunki ba,saboda ba halayyarsa bace,”
Haɗiyar yawu tayi,tana sauraronshi,ɗan dakatawa yayi da yin maganar,kafin ya ɗaura da cewa”daga yanzu inaso,ki cigaba da aiki a ƙarkashinsa….’ tunkan ya ƙarasa maganar Sehrish tace”Amma daddy,ka hanani zuwa part ɗinsa fa”
“A yanzu na soke wannan!inaso ki yi mashi biyayya,ki bishi sau da ƙafa,komai yake so kiyi mashi kawai!part ɗinsa kuma koda wani lokaci zaki iya zuwa ki shiga,even in the midnight,indai ya buƙaci ganinki ki je kawai,”
Gaba ɗaya Abusufyan ya gama ruɗar da ita,la66anta har kerma sukeyi wurin cewa”dad..dy!bangane me kake nufi ba,dan Allah ka fahimtar dani,”
“Ki tafi kawai kiyi duk abunda nace maki,idan lokaci yayi zan sanar maki,”
Juyawa tayi tare da zura ƙafarta,tabar bedroom ɗin nashi,lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu,ya ƙurama ceilling ɗin sama ido yana kallonshi tamkar mai karanta wani abu ajikinshi,tunani ya shiga yi acikin zuciyarshi,ya shiga tariyo abunda yaji a kunnuwansa,
_Na amince zan aureta,bana son abun ya ɗauki lokaci,bana son taron mutane,kuma banaso kowa ya sani,saboda ba auren dundundun bane,nan da wata uku zan sake ta,zan aureta ne ba don ina sonta matsayin matata ba,sae don tayi mun aiki kafin na bar nigeria_
Hannu Abusufyan yasa tare da ɗaukar wata takarda dake ajiye saman side drawer ɗinshi,zuba ma takardar ido yayi yana kallonta,Agreement paper ce (Takardar yarjejeniya)mai ɗauke da signatures na mutun uku,”
Ajiyar zuciya ya sauke tare da zura ta cikin drawer chest ɗin daya fiddo akwatin nan da ya bama sehrish ya sanya takardar aciki ya ajiyeta,sannan ya mayar da ita ya datse,rufe idanunshi yayi bakowa bane ya faɗo mashi arai ba face ABU,nan take yaji kewarta ta lullu6e shi,Allah sarki abu,tana raye kota mutu?

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

A 6angaren Sehrish kuwa bayan fitarta daga bedroom ɗin Abusufyan,a ƙopar ɗakinsu ta tsaya,warware mayafin da ta laga akanta tayi,sannan ta lullu6e small box ɗin dake hannunta don kada wani ya gani,tura ƙopar ɗakin tayi sannan ta shiga daga ciki,babu kowa acikin ɗakin,sautin ruwan da taji ne daga cikin toilet ya tabbatar mata da cewar Jahad ce ke wanka,cikin sauri ta lalla6a gaban dressing mirror ɗinsu,ta zuƙunna gaban drawer ɗin dake ɗauke da mirror ɗin,ta janyo gida na ƙarshe,ta tura small box ɗin acikinsa can ƙurya ta turashi,sannan ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,miƙewa tsaye tayi har lokacin bata daina mamakin abubuwan da Uncle ya faɗa mata ba,abun ya ɗaure mata kai sosai,
Safa da marwa ta shiga yi acikin ɗakin,takasa zama saboda yanayin da ta tsinci kanta aciki,

*Boss Bature*

❤🤍❤
AMRISH,

Tun jiya da daddare data farka,tana bullayi asaman gadon bayan an samu nasarar ceto rayuwarta,doctor yayi mata allurar bacci bata ƙara farkawa ba,yini tayi a kwance tana bacci kamar matacciya,hankalinsu zeenatu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,musamman Mommyn Amrish ɗin,bata ta6a tunanin amrish zata rayu ba,amma cikin ikon Allah sae gashi taji sauƙi sosai,poison ɗin da tasha bai kaiga yi mata illa ba,sunyi gaggawar kaita asibitin kuma likotoci sun taru akanta wurin ceto rayuwarta,wannan ne yasa bata jigata ba sosae,amma still da sauranta don ba ƙaramin galabaita tayi ba,yanzu haka ma ƙarin ruwa ne aka sanya mata,

Mommynta na zaune asaman plastic chair din dake agaban gadonta,fuskar nan tayi jawur da alama ba ƙaramin kuka tasha ba,ga rashin baccin da basu samu ba adaren jiya,gaba ɗaya hankalinta na akan Amrish dake kwance magashiyan tana bacci,

Zeenatu na a zaune daga gefen gadon da amrish ɗin take kwance,duk sunyi zuru suna kallonta,tunda safe Sofia ta koma gidansu,ita kaɗae ta rage saboda tace bazata koma gidansu ba har sai Amrish taji sauƙi sun koma gida,

Suna cikin zaman nan,kwatsam Amrish ta buɗe idanunta ta zazzaresu a wani irin firgice ta sanya hannu ta fizge robar ƙarin ruwan da akeyi mata,hankali atashe Zeenatu tace”Mommy amrish ta farka!ta cire ƙarin ruwan da aka sa mata,”jin wannan maganar yasa Mommyn yin firgit ta dawo cikin hayyacinta daga zurfin tunanin da ta shiga,sai dai kafin suyi wani yunƙuri,tuni Amrish ta diro daga saman gadon,ta watsa aguje,zeenatu na ƙoƙarin tarota,takai mata wani kakkwaran naushi a saitin Cikinta,nan take zeenatu ta zube ƙasa hannunta dafe da cikin,ta fasa uwar ƙara tana faɗin”Wayyo Allah na!cikina!nashiga uku,
Ko waiwayonta amrish batayi ba,hanyar fita kawai ta nufa,da gudu ta fice daga ɗakin,bin bayanta Mommyn tayi tana yarfa hannu a ruɗe take faɗin”Help!help!!dan Allah jama’a ataimaka a taro mun ita!mara lafiyace zata gudu,’
Da gudu wasu nurses suka bi bayan amrish,hada wasu daga cikin masu zuwa dubiya,
“Amrish dan Allah ki tsaya!wai meke damunki ne!bakiji ina magana ba!ina zaki je ne!,” hankali tashe mommyn ke magana,amma ko sauraronta amrish bata yi ba,duk wanda ma yayi ƙoƙarin tarota bugu take kai mashi kamar ƴar wrestling,gashi wani irin ƙarfine da ita kamar na Doki,in ta daki mutun sai ya kusa zaucewa,duk yadda suka so su kama amrish,amma abun yaci tura,domin kuwa 6att suka neme ta suka rasa acikin asibitin,saƙo da lungu babu inda basu duba ba,amma babu ita babu alamarta,ko mai kama da ita ma babu,nan fa hankalin kowa ya tashi,hatta security guards ɗin dake tsaron gate ɗin asibitin,sae da aka tambayesu,sun tabbatar da cewar basu ga fitarta daga asibitin ba,sae dai ko a wani wurin ta 6oye,Hatta Cctv footage sae da aka bincika,amma ba aga ta hanyar da Amrish tabar cikin hospital ɗin ba,kuma ba’aga wurin da ta 6oye ba,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,yarinya kamar mai iskokai?babban abunda zai baka mamaki ƙarfin daya zo mata,mutumin dake kwance magashiyan a gadon asibiti,amma ya tashi farat daya da irin ƙarfin nan a jikinshi❓

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Saboda tsabar tashin hankalin da Mommyn Amrish ta shiga,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume,sai dai nurses suka cuccu6eta aka shiga da ita ciki,suka kwantar,itama zeenatu sae da suka kwantar da ita don kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba,naushi ɗaya tayi mata aciki,amma sae da jini ya zuba a bakinta,

*ANA WATA GA WATA!JAMA’A INA AMRISH TA SHIGA NE*?😳😳😳

*Aunty Babba*

Fitowarta kenan daga cikin toilet tana faman dafe cikinta,ɗagowa tayi tana kallon hayaam dake zaune gefen gadon ta zabga uban tagumi da hannayenta biyu,Hafsat kuwa na asaman gadon kwance ta lullu6e da bargo jikinta sae kerma yake yi,wani irin zazza6ine mai zafi ya rufar mata,tunda rana tagaza motsa jikinta,abun gwanin ban tausayi,

Kwatsam!sukaji an banko ƙopar ɗakin nasu,dafe ƙirji Aunty babba tayi tana kallonshi,sae faman huci yakeyi yadda kasan mayunwacin zaki,da ƙafarsa ya tura ƙopar ɗakin ta rufe,hayaam na ganinshi a razane ta haye saman gadon,jiki na rawa ta wuntsila daga ƙasan gadon ta 6oye,tana faman zazzare ido,
Cikin inda inda ta ambaci sunan shi”I..ishaq!”
A zafafe ya ƙarasa inda take,kwakkwarar damƙa yakai ma wuyanta,ya shaqeta sosai,yadda ko ihu bazata iyayi ba,saboda tsabar raɗaɗin da taji nan take ta saki fitsari a wando,wani irin gumi ne ya shiga tsattsafowa daga gefen fuskarta,idanunta sunyi jawur cike tab da kwalla,ƙwayar idon tamkar zata zazzago ƙasa,
A ruɗe hafsat ta fasa uwar ƙara,ganin abunda daddynta ke ƙoƙarin yi,gadan gadan so yake ya kashe Mommynta,da gudun gaske ta duro daga saman gadon tana kuka,
“Kafin ki kashe su!Ni zan fara kashe ki!muguwa kawai!Nayi danasanin aurenki laila!nayi danasanin saninki da nayi,Nayi danasanin haɗa zuri’a ɗaya dake,Allah ya isa tsakani na dake!Na tsaneki!kin fita araina!ban sonki!bansan ganinki!”daƙyar sautin muryarshi ke fita saboda tsabar 6acin rai,a fusace ya buga kanta jikin bango,nan take Aunty babba ta baje ƙasa a sume,’
Juyawa yayi tare da aza idanunshi akan hafsat dake tsaye tana faman zabga uban kuka fuskarnan tayi jaga jaga da hawaye hada majina,nunata yayi da yatsan hannunshi sannan yace”dake da uwarki!ku tattara kayanku ku bar gidan nan!tun kafin inyi sanadin mutuwarku!muguye kawai waɗanda ba Allah aransu,”

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Hannu hafsat ta aza akanta tana ambaton”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’Un!”
Juyawa ishaq yayi da sauri zai bar ɗakin,da gudun gaske ta ruƙo rigar jikinshi tare da zubewa saman guiwowinta tana kuka tana yi mashi magiya akan,karya koreta,
“Daddy dan Allah kayi haƙuri ka yafe mun!wlh ba laifina bane,nasan mun cutar dasu,amma inaso ka sani daga baya na ƙaunace su,Daddy ka yarda dani Mommy itace take azabtar dasu,kuma itace tayi silar barin….’bata ƙarasa maganar ba sakamakon bugun daya kai mata da ƙafarshi,da sauri ta dafe gefen bakinta daya buga wurin har ya fashe,jini ya shiga ɗiɗɗigowa,dogon tsoki ishaq yaja tare da cewa”Kada ki kuskura ki ƙara kirana da sunan daddy!don ni ban haifi wata ƴa mai suna hafsat ba!tunda har kin za6i ki bi mugun hali irin na mommynki,don haka gaki ga ita,duk in da zata je ƙafarki ƙafarta,karku kuskura Dare yayi maku acikin gidan nan!don wlh sai kunyi danasanin haihuwarku da akayi acikin duniyar nan!don bazan raga maku ba,tamkar ban sanku ba,haka zan hukunta ku!kuma idan ta farka daga suman da tayi ki sanar da ita cewa NI ISHAQ NA SAKE TA,!!!!

Wani irin bugu zuciyar hayaam tayi ji kake daramm!!kamar an buga ganga,nan take ido ya raina fata,sae faman mazurai takeyi abayan gadon da ta la6e,Na shiga uku Ni hayaam An saki Aunty laila!Shikenan komai ya ƙare komai ya lalace!mun gama yawo!!

Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu tamkar zai 6alle ƙofar ya fuce,Amani dake la6e tana sauraronsu da gudun gaske ta watsa,sae cikin ɗakin da suka sauka,Tana shiga cikin ɗakin ta daka tsalle,bakinta awashe saboda tsabar dariyar mugunta hada hawaye ke fita a idonta,Amal dake zaune saman gado tana buga game a wayar amani,ganin yadda amani keta dariya kamar wata zautacciya,yasa ta ɗan dakata da buga game ɗin tare da cewa”Aunty Amani meya sanyaki farin ciki har haka”?
Daƙyar ta iya dakatawa da yin dariyar tace”Amal ba zaki gane bane,Wani buri da nake dashi ne ya cika ayau ɗin nan!!waɗanda suka jima suna ƙuntata rayuwarmu,tun yau zasu fara gir6ar abunda suka shuka,” tana magana tana dariya,
Murmushi kawai Amal tayi tare da mayar da hankalinta kan game ɗin da take bugawa,

General ishaq na fita daga ɗakin,hayaam ta lalla6a ta fito,yadda kasan lagwanin fitila haka take tafiya,jikin taƙaura yayi la’asar wannan hada magriba ma,zuƙunnawa tayi gaban Aunty babba dake baje ƙasa,ta fashe da wani irin matsanancin kuka,Hafsat na kuka itama tana kuka,babu mai lallashin wani,kowa takansa yake yi,
Cikin shessheƙar kuka hafsat ta soma magana”Allah ya isa tsakanina dake Aunty hayaam,kun cuci rayuwata duk don saboda ku ne mommy ta aikata abunda ta aikata don taga ta cika muku burinku,gashi nan yanzu abun ya shafe ni,kunja daddyna ya kore ni,Ni bansan ku wasu irin mutane bane!sam baku da zuciya kare ya lashe,kun nace kun liƙe dole sai kunyi arziƙi da gumin wasu,ku bazaku tashi ku nemi na kanku ba,sam babu Allah aranku,mugunta kawai kukasa agaba,shiyasa har yau babu wani cigaba acikin lamurranku!wlh yanzu ma kuka fara gani!indai bazaku koma ga Allah ba,,ku tsaya a iya matsayin da Allah ya ajiye ku,ku daina hangen na wasu,wannan dogon burin da kwaɗayin abun duniyar ba inda zai kai ku face ya jefa ku ga halaka…..”
Itadae hayaam bata tanka mata ba,saboda bata da abun cewa,har wani zazza6i take ji ajikinta,saboda tsabar tashin hankalin da take ciki,komai ya jagule masu,

Miƙewa hafsat tayi,jiki ba ƙwari ta ƙarasa tare da janyo trolley ɗin kayansu da suka zo dashi,janshi tayi izuwa gaban wardrobe ɗin hayaam,ta buɗeta,kayansu dake aciki tashiga fitowa tana ninkesu,Cikin trolley ɗin take jerasu,

Miƙewa hayaam tayi tana tunanin inda zata samu ruwa ta yayyafa ma Aunty babba,saboda babu ruwa acikin ɗakin,kuma tana jin tsoron ta fita waje suci karo da mutumin,tana cikin wannan tunanin ta tuna da akwai fanfo cikin toilet,da sauri ta shiga ciki a tafin hannayenta ta tarbo ruwan,da sauri da sauri tazo ta yarfa mata shi a fuskarta,dogon numfashi Aunty babba taja,tun kafin ta buɗe idanunta ta shiga fadin”Ruwa!Ruwa!” jin haka yasa hayaam yin tunanin ta fita waje ta samo mata ruwan,buɗe kopar dakin tayi cikin sanɗa ta fito tana tafiya acikin corridor din dakunan nasu,cikin sa’a ta taras babu kowa a main palour din,ƙarasawa tayi wurin fridge ɗinsu,ta bude jikinta na kerma ta ɗauko robar ruwa,da gudu ta koma cikin ɗakin,

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Ƙarasawa tayi tare da taimaka ma Aunty babba ta tashi zaune sannan ta miƙa mata bottle water ɗin,A tsiyace ta 6alle murfin robar,ta kafata a bakinta,yadda kasan zata haɗa da robar duka ta cinye,abun kamar yaƙi,ta damƙi robar,sae kwankwaɗar ruwan take,kwatt!kwatt!!har sae da ta shanye ruwan duka tass,sannan ta saki robar ƙasa,sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi,hannunta na dafe da kakkauran wuyanta sae faman Murzarshi takeyi,wurin sae raɗaɗi yake yi mata kamar an barbaɗa mata attarugu,idanuwan nan nata sunyi jawur luhu luhu,sae da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta kalli Hayaam tare da cewa”hayaam meya faru dani ne?ya akai na ganni akwance ƙasa?
Kafin hayaam ta buɗe baki tayi magana,tuni hafsat ta katse mata hanzarinta da cewa”Mommy!kina nufin cewa kin manta duk abunda ya faru?idan ma kin manta bari na tuna maki,Dadddy ne ya damƙi wuyanki ya shaqeki,sannan ya bugaki ajikin bango har saida kika suma,”
Shiru aunty babba tayi tana tariyo abunda ya faru,
“kuma yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan,kada mu bari dare yayi mana,bayan haka kuma ya dankara maki saki ɗaya”rai a6ace hafsat ke maganar,
Wata irin mahaukaciyar dariya Aunty babba ta kwashe da ita kamar wata zautacciya,hakan ba ƙaramin mamaki ya basu ba,miƙewa tsaye tayi tana gyara ɗaurin ɗankwalinta tace”Da sauƙi ma,Ni nayi tunanin wani mummunan hukunci zai yanke mun,sai me don ya kore ni?sakin ma da yayi mun wlh ko ajikina,yayi a banza Ae akwai sauran igiyoyi guda biyu,Ni nasan cewa muddin Abbansu yaji cewar ya sake ni,sae yasa ya mayar dani,Ae ni wlh gaba takaini gobarar titi A jos!” To fa,
sakin baki hafsat tayi galala tana kallonta,ba ita kaɗae ba hatta hayaam abun ya ɗaure mata kai,sunyi tunanin cewa in taji ishaq ya sake ta,xata haukace masu ne,amma sae gashi ko ajikinta!zuciyar ta bushe,
Sae faman tiƙar dariya takeyi kamar sabon shiga a fagen hauka,lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta,tare da kallon hayaam tace”Maza ki tattara kayanki,don atare dake zamu tafi,”
Hankali tashe hayaam tace”Ni kuma?saboda me zamu tafi atare”?
Shu’umin murmushin nan nata tasaki kafin tace”Saboda inaso,muje wurin bokan nan baba ibliss!wannan karan ba fashi,Dole in kawo ƙarshen auren Amani!kamar yadda zanyi zawarci itama haka nakeso tayi shi,sannan waccen mahaukaciyar yarinyar da tayi silar tona mun asiri har ishaq ya sanya hannunshi ya shaqe mun wuyana na kusa sheqawa barzahu wlh saina yi Ajalinta!!!sannan kuma aurenki da Sgr ba fashi!Wlh ko ta halin ƙaƙa!ko suna so ko basa so sai an ɗaura shi!In har kika ga ba’ayi auren nan ba!To sai dai in bana a doron duniyar nan!ko kuma shi RAFAYET ɗin Ya daina numfashi ne acikinta!sai dai kowa ya rasa wlh!da alama har yanzu basu san wacece Ni ba!zan nuna masu true colour ɗina!Ni dasu shege ka fasa!!” tana magana tana fitar da huci,
Mugun abu kokayi bacci?yace idona biyu 👀!ANA WATA GA WATA,

Zuru hafsat tayi tana kallonta,abun yafi ƙarfinta,lamarin Mommyn nata sae addu’a,tunani ta shiga yi anya Mommynta bata fara shaye shaye ba?kodai tana da iskokai ne?

Suna cikin wannan tsayuwar,aka kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,a tsiwace Aunty babba tace”Wanene”?
“OMAR NE” koda jin muryar marshal Omar nan fa kowa ya shiga taitayinsa,
“Hayaam je ki buɗe mashi ƙopa,muji dame yazo!in shima zuwa yayi don yaci mutunci na to bismillah!kowani shege dai dai nake dashi,”kamar wata ƴar daba haka take maganar,
Buɗe mashi ƙopa Hayaaam tayi,tun daga irin kallon da taga Omar ya watsa mata tuni tashiga ƴan kame kame tana sunnar da kai,
Shiga cikin ɗakin nasu yayi,yayin da idanunshi ke akan Aunty babba wadda ke tsaye ta ruƙe qugu,sae faman jijjiga jikinta takeyi kamar wata ƴar bori,
Janye idanunshi yayi daga kanta ya mayar dasu kan hafsat,wadda ke tsaye ruƙe da trolley ɗin kayansu,ganin yana kallonta ne yasa ta ɗukar da kanta ƙasa cike da jin kunyarshi,
“Ina zaki je ne”? Yayi maganar fuskarshi a ɗaure,
Muryarta na rawa tace”dad..dy ne yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan kada mu kuskura mu bari dare yayi mana anan,”
“Ban da ke!su kaɗai zasu tafi,”
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,har ta gaza rufe bakinta saboda tsabar farin ciki,”

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Mayar da idanunshi yayi kan Aunty babba dake tsaye ruqe da qugu yace”Major na awaje yana jiranku,idan kun kammala shiryawa ku same shi,Nayi mashi magana zai kai ku hotel ɗin da zaku kwana kafin gobe da safe sae ku wuce maiduguri,Amma fa in kuna so kenan,sannan kuma….’ya ɗan dakata da yin maganar tare da zura hannunshi cikin aljihun jeans ɗin dake ajikinshi ya zaro bendir ɗin kuɗi na ƴan dubu dubu,a ƙalla zasu yi dubu ɗari ɗaya,ya miƙa masu,jiki na rawa hayaam ta kar6e kuɗin tana yi mashi godiya,
…murmushi Marshal Omar ya saki tare da cewa”No,ba sai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,’
Yana kai ƙarshen maganar ya juya tare da fucewa daga dakin yana dariya gami da girgiza kanshi,
Bayan fitarshi aunty babba ta buga tsoki,tana faman hura hanci tace ma hayaam”maza ki shirya mana kayanmu,naji ana kiran sallar magrib,zae fi mu lalla6a mu fuce daga gidan batare da kowa ya ganmu ba,nasan duk sun tafi salla,”
Amsa mata hayaam tayi da toh,sannan ta juya tare da shigewa cikin toilet,
Hankalin hafsat ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana faman sakin murmushi,dama babban tashin hankalinta shine idan tabi su Aunty babba maiduguri bazata iya rayuwa cikin gidansu ba,sau ɗaya ta ta6a zuwa,bataji daɗin zama agidan ba,muggan talakawa ne,babu wani abu na more rayuwa acikin gidan,sae ma abun haushi da takaici da zaka taras,
Kusan minti Goma shabiyar sai ga aunty babba ta fito daga cikin toilet ɗin,da alama wanka tayi,xanin atampar jikinta ne tayi ɗaurin gaba dashi,ya jiƙe sharkaf saboda ta ɗauraye shi acikin toilet da ta shiga,
Batare da 6ata lokaci ba,suka shirya tsaf ita da hayaam,dogayen riguna suka sanya ajikinsu,sannan suka aza mayafi daga sama,kama hanyar fita daga ɗakin sukayi,ɗan juyowa aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace”sannu hakima yayi maki dai dai wato hankalinki kwance zaki rabu da Mommynki ko rakiya babu”?
Miƙewa hafsat tayi tare da bin bayansu,suka fuce daga cikin ɗakin,ta ƙopar baya suka bi don kada wani yaga fitarsu,a waje suka samu Major tsaye jikin motarshi,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,yana ganin sun fito da sauri ya buɗe masu motar,
“Allah ya kiyaye hanya mommy,in sha Allah gobe da safe kafin ku wuce maidugurin zan kiraki a waya,”
Harara aunty babba ta watsa mata kafin tace”Munafuka!Hada wani raku6e fuska kamar irin zakiyi kewata ɗinnan!Ae kada ki damu ki sha kuruminki in dai ni ce zan dawo ne!nan bada jimawa ba,”tayi maganar tare da kutsa kai ta shiga cikin Motar,
“Aunty hayaam Allah ya tsare hanya,Ni dai zan wuce ciki,”
Murmushin yaƙe hayaam tayi,tare da janyota ta rungumeta,daga bisani ta shiga cikin motar,batare da 6ata lokaci ba,Mojar ya shiga mazaunin driver,yayi ma motar key,yaja ta da gudun gaske,Fashewa da kuka hayaam tayi tana leƙen gidan ta cikin gilashin motar,aunty babba sai lallashinta takeyi tana cewa”ke fa banzace,menene abun kuka anan?karki wani damu kanki,Ae babu inda zamuje,ko cikin garin nan bazamu bari ba,Ni nasan me nake shiryawa,AI YANZU WASAN YA FARA,
Cikin shessheƙar kuka hayaam tace”Aunty laila bazaki gane bane,wlh banson inyi nesa da gidan nan!ji nake kamar zan rasa shine gaba ɗaya,na kwallafa raina akan Sgr,duk da bana ganinsa amma zaman da nakeyi acikin gidan nan,yana kwantar min da hankalina,at lease muna kusa da juna,ko ba don haka ba,A yanzu ni banajin zan iya rayuwa acikin gidanmu,kwara nan gidan wlh,kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwana a mai kyau,duk da atakure nake kwara nan ɗin da can gidan mu,Jarabar mammy kaɗae ta isa ta Ramar da mutun,babban takaici na,korar wulaƙancin da nayi ma Sofwan nasan cewa yanzu kona nemi taimako awajensa bazai kulani ba,”hannu tasa tana share hawayenta,
Tsoki aunty babba taja mtsww kefa matsakarki kenan!nace maki ki kwantar da hankalinki,ba inda zamuje amma duk kin bi kin tashi hankalinki,sannan in dai akan sgr ne ni nayi maki alƙwarin cewar saina mallaka maki shi,in dai kika ga sgr bai aureki ba to ki tabbatar cewar rayuwarshi a tazuranci zata ƙare,kuma naji kina maganar wani sofwan,uban me zaiyi mana?Ko kin manta cewar Muna da jari atare damu?daga ke harni babu namijin da zai kallemu ya kawar da kansa,Allah ya bamu hasken fata,ga dogon gashi,duk wani abu dake jan hankalin ɗa Namiji ae muna dashi Allah ya bamu,Kinga kuwa muna da hanyar da zamu samu kuɗi,don biyan buƙatunmu,’
Gaba ɗaya duk wannan surutun da sukeyi a kunnan Major,ya kasa kunne yana sauraron su,Sae faman ƙumshe dariya yakeyi acikin bakinsa,abun ban haushi abun ban dariya,

*Boss Bature*

❤REESHRAF❤

A hankali take hawan upstairs ɗin,yayin da zuciyarta ke tariyo mata abunda daddynsu ya sanar da ita,na cewa taci gaba da aiki a part ɗin SGR,kuma tayi mashi biyayya sau da ƙafa,me hakan ke nufi?small box ɗin da daddynsu ya bata,dowry ɗin wanene?ya sanar dani cewa sadakin wata ne,amma dai koma wacece wannan ba ƙaramar mai sa’a bace,halan tafi kowa kyau a duniya ne?shiyasa Aka biya sadakinta da Gold,dama ni wlh,’
Kamar wata zautacciya,sae faman surutai takeyi ita kadae abunta,

Ƙarasa hawa up din tayi,kai tsaye ta wuce part ɗin babban yaya,bata tashi jin faduwar gaba ba,sae da tazo ƙopar shiga falonsa,sannan ta tsaya tana karanto addu’o’in neman tsari,duk don kada ta fuskanci hukunci a wurinsa,bayan ta kammala addu’ar,ta shafa asaman fuskarta da kuma jikinta,kafin tasa ƙafarta ta shiga cikin falon cike da kwarin guiwa,sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu shi acikin falon,sae dai daddaɗan ƙamshin turarensa,mai ratsa zuciya,bin falon nasa tayi da kallo,kusan 3 days kenan babu gyara,dama da shirin aiki tazo,wuce wa cikin bedroom ɗinshi tayi,nan ma babu shi aciki,da alama basu dawo daga sallar magrib ba,may be sae after isha,ko kuma ƙarfe goma sha biyun dare daya saba dawowa gida,
Shimfiɗeɗen gadonshi tabi da kallo,zanin gadon duk yayi squeezing,ga blanket ɗinsa ma nannaɗe asaman gadon,bai ɗaukeshi ba,
Hannu tasa tare da zame mayafin sarin dake ajikinta,ta ɗaure shi a qugunta,kwantacciyar sumar kanta na ɗaure acikin ribbon,saman gadon ta haye tare da sanya hannayenta tashiga ƙoƙarin tattaro bedsheet din nasa,Zancen zucin da takeyi ne ya fito fili,
“Matar babban yaya ta shiga uku,na tausaya mata Allah,mutun kullum fuskarshi a daure,kamar ta sa,babu fara’a ko kaɗan,in tayi mashi laifi kuwa zata sha zallan kwaɗi,in kuwa ta fusata shi,ɗaukar ta zaiyi kamar haka,
Tayi maganar tana tattaro bargonsa,ta ɗaga bargon sama tare da yin wurgi dashi,sannan tace”Ya jefar da ita,ko kuma yayi mata irin yadda yayi mun jiya,kamar wata ɗiyar Roba haka zai ruko wutsiyoyin gashin kanta,ya ɗaga ta sama!yana jujjuyata,
Tana cikin wannan sambatun nata,taji anyi mata gyaran Murya,a wani irin firgice ta juya don taga WANENE..

 

Back to top button