Zamantakewar Aure

Yadda Ake Hadin Tsumi Mai Motsa Sha’awa Da Karin Ni’ima

Yadda Ake Hadin Tsumin Ruwan Kankana Mai Motsa Sha’awa Da Karin Ni’ima:

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

✦ Kankana

✦ Kwakwa

✦ Aya

✦ Dabino

✦ Garin citta

✦ Garin mazarkwaila

✦ Madara ta ruwa

Zaki samu kankananki mai kyau sai ki yayanka sai ki cire kwallon sai ki hada da sauran kayan hadin ki markada amma ban da madara bayan ki markada sai ki tace ki zuba madarar ki dunga sha.

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Yadda Ake Hadin Garin Sallaja Ga Macen Da Take Fama Da Karancin Ni’ima:

Yar uwa idan kina fama da karancin ni’ima ko kina da matsalan rashin gamsar da maigida to ga dama ta samu.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

✹ Garin sallaja

✹ Garin gyada

✹ Garin habbatus sauda

✹ Garin dabino

✹ Garin aya

✹ Madarar peak

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya har su hade sai ki dunga diban cokali biyu kina sha da madara.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Yadda Ake Hadin Tsumin Saiwar Kankana Don Samun Karin Ni’ima:

Yar uwa idan kina fama da matsalan rashin ni’ima to ga naki don wannan hadin dai sai alasan barka.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

★ Saiwar kankana

★ Saiwar zogale

★ Garin Kanunfari

★ Mazarkwaila

★ Zuma

Zaki samu saiwar kankana da na zogale sai ki tafasa idan ya tafasa sai ki tace sai ki maida ruwan kan wuta sai ki zuba mazarkwaila da kanunfari sai ki dafa na yan mintoci sai ki sauke ki tace sai ki zuba zumanki ki sa a frige don kar yayi saurin lalace ki sha.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Yadda Ake Hadin Kwababben Lalle Don Mtse Gaba Da Gamsar Da Maigida:

Zaki samu kayan hadi kamar haka;

☞ Garin Lalle

☞ Miski

☞ Man hulba

Zaki samu miski mai kyau sai ki hada da man hulba guri daya ki gauraya sai ki kawo garin lalle ki zuba a ciki ki kwaba sosai sai ki dunga diba kina matsi da shi bayan sallan isha idan ya samu kamar awa daya sai ki wanke da ruwan zafi.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

 

COMPLETE TREATMENT FOR ALL TYPES OF UTI (Urinary track infection

MAGANIN DUKKAN NIN CUTUKAN SANYI NA MATA.

• Kaikayin gaba.

• Kurajan gaba.

• Fitar farin ruwa.

• Daukewar Sha awa.

• Gushewar Ni’ima.

• Kullewar mara.

• Ciwon baya.

• Fitsarin jini.

• Fitsari Mai fita da zafi.

• Warin Gaba.

• Da sauransu..

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

 

Duk mace Mai fama da 1daga cikin to ga yadda zata yi.

• Garin bagaruwa cukali 3

• Kanwa cukali 2.

• Gishiri cukali 1.

• Tafarnuwa kunso 1.

Sai azuba ruwa daidai yadda za iya shiga azauna, sai atafasa sosai in ga gas ne minti 30 ,inko a itace ne awa 1. Amma tafarnuwa a kadaka ta ko agoga ta.

Kana atsiyaye atace azauna ciki na tsawon minti 15 Amma fa da dumi ba da zafi ba.

Sannan kuma Asami man zaitun.

• Man tafarnuwa.

• Man kwakwa.

• Tafarnuwa.

Sai atoyasu ayanyanka tafarnuwa aciki.

Daganan sai ta samo audiga adangwali man ayi matsi ba za acire ba sai bukatar Hakan ta taso.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

 

NA SHA.

✓ Kankana na ₦100.

✓ Tsamiya sili 4.

✓ Tafarnuwa kunso 1 babba.

✓ Turmeric (kurkur) gada 4.

✓ Jar Albasa Rabi.

✓ Citta gada 1.

✓ Ruwa pure water 6.

Sai atafasa sosai kana atsiyaye atace arinka Sha. Amman fa Wannan hadin Banda Mace Mai ciki ko Mai shayarwa ko kankanin yaro baya Sha.

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

 

Mace Mai ciki ga nata.

Kankana na ₦ 100.

Tsimiya sili 4 Amma fa sabowar.

Tafarnuwa kunso 1.

Duk macen da take haka to zata waraka daga Dukkan matsalulin sanyi duk tsananin sa da yardar ALLAH. Masana magani sunce ba ayi wani magani ba Kamar sa.

Nan take zataga alamun In Sha Allah.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Back to top button