Uncategorized

Abdul Jala Chapter 5 Complete Hausa Novy Complete

 

Da sauri maryam takarasa bakin gadon da Aliyu yake kwance yana ta fidda jini ta hanci tabaki ga wani wahalallen numfashi da yake saukewa da kyar, da gudu take ta zube a gabansa

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Aliyu meya sameka haka”

Shine abinda maryam tafada cikin kuka 

Jalila ma da gudu ta tafi gurin abbanta cikin karfin hali ya rungume Jalila tareda janyo maryam kirjinsa

  “Noor kiyi hakuri na taho kano ban gayamiki ba Usman ne yakirani jikin innarmu yayi tsanani shine na taho muka samu accident a hanya”

“Sannu abu Jalila Dan Allah ka warke ka tashi mucigaba da rayuwa u are my life habibi”

  “Is not complicated dear kawai internal injury ne kuma likitoci zasuyimin aiki zan warke insha Allah

Dama haka kike matukar sona noor irin wannan rikicewa haka I love u too my dear u mean a lot to me maryam”

Yafada cikin karfin hali da son kawar wa da maryam damuwa

  “Abu Jalila is not time for joke lafiyarka tafiyemin komai nikam, inaso mu rayu tare kacigaba dabani farin ciki nida baby Kaine garkuwarmu kai ka dai ka ragemin “

Tafada tana zubda hawaye 

“I love u too ummu Jalila, kije kuduba inna se ki turomin Dan uwana zamuyi magana”

Harta yunkura zata tashi

“Maryaman Aliyu”

Ya kira sunanta dawowa tayi ta zauna ta kuma riko hannunsa

“Dan Allah ko bayan raina kar abinda matar usaman take miki yasa ki raba zumuncin dake tsakanin yayanmu”

Gyada masa kai tayi sannaan

Ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar fita,

Usman yana waje a bakin kofa yanajin duk hirarsu gwanin ban tausayi, haka usman ya dinga share hawaye kaman karamin yaro

Jiki a sanyaye Tafito daga dakin Usman ya nuna mata dakin da aka kwantar da inna 

Usman ya koma dakin da Aliyu yake yaje gaban gadon Aliyu ya zauna ya riko hannunsa

  

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“Dan uwana ya jikin naka ya kake ji yanzu”

“Yayana mutuwa zanyi bazan rayuba inaso in barmaka amana ne da duk duniya bame rikemin se kai”

Aliyu ya fada yana Jan numfashi da kyar 

Yacigaba da cewa

“Dan Allah karkabari babyna tai kukan maraici, ko aure maryam tayi ban yadda ta tafi da yata agolanci ba, inason baby tayi karatu me zurfi, na addini Dana zamani

idan ta isa Shiga Jami a inaso takoma hannunka kasan tarbiyar ya mace seda tsayayyen namiji,”

Yayi tari jini yana fitowa daga bakinsa 

Usman ne yake share masa jinin yana masa sannu,

Sannan ya cigaba da cewa

“Kar kayi yinkurin raba baby da maryam yanzu, seta isa shiga Jami a nakeso takoma hannunka, sannan ka tabbatar in baby ta girma maryam takoma garinsu tanemi yafiyar iyayenta, nasan kafin nan sun huce daga fushin dasuke da ita baby taga dangin mahaifiyar ta

Tunda kaga mu kenan bamu dayawa,

Yayana bana so iyalina suyi maraicina in baby na ta isa aure kazaba mata miji nagari karka manta ka rike alkawarinmu dan uwana,

Kacewa innarmu ta yafemin, kagayawa maryam da diyata da soyayyarsu zan koma ga Allah”

Ya kalli Usman dake ta zubarda hawaye INA kaunarka Dan uwana”

Tarine yakuma sarke Aliyu yana numfashi da kyar 

Kalmar shahada ya dinga nana tawa, sekuma yayi shiru jikinsa ya saki 

Usman rungume gawar Aliyu yayi ya fashe da kuka seda yayi me isarsa sannan ya mike ya nufi dakin da aka kwantar da inna mairo, maryam ya gani a gabanta tana bata ruwa tana shan ruwan da kyar wani yana dawowa

Yana shigowa inna ta dago kai ta kalleshi tare da fadin ya mutu ko Usman, Aliyu na shima ya tafi,”

Ta fashe da kuka tacigaba da fadin

” Allah ya karbi bakuncinka Aliyu na yafe maka duniya da lahira

Maryam kikula da kanki ki rike mana Jalila kaima Usman kakula da amanar da Dan uwanka ya bar maka, maryama  karki manta da abunda nagaya miki inna mairo tayi maganar tana kuka tare da numfar fashi.

Lokacin da Aliyu yayi hatsarin aka kawoshi asibitin da inna take, an  turota a wheel chair ta dubashi,, tunda ta Ganshi taga halin da dannata yake ciki ta karaya jikinta ya kuma rikicewa,

Duk abin naan da ake Zainab bata taka kafarta Asibiti ta duba jikin inna Mairo ba balle Aliyu da ba Sa shiri

Da gudu maryam ta fita ta koma dakin da Aliyu yake ta tarar da shi an rufeshi da bargo dagaske dai Aliyun ta ya mutu 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un maryam ta dinga maimaitawa tare da silalewa kasa sumammiya

Kafin akawo motar daza a dau gawar Aliyu inna mairoma ta cika

*************************

    Ummi na zuwa nan a duniyar  tunani ta fashe da wani matsanancin kuka tare da furta Allah ya jikanka Aliyu na”

ta fada hankali.

  “Ummina kiyi hakuri idan magana ta ce tabata miki rai kiyi hakuri banyi Dan in bata miki rai ba “

Jalila tayi maganar daga inda take kwance ba tare da ta juyo ba Ummi bata CE mata komai ba taci  gaba da kukanta daga karshe ma ta fita ta dauro alwalaa ta tada salla

Washe gari da safe Jalila ta fuskanci still umminta bata walwala fuskarta ta kumbura saboda kuka

Jalila aikace² kawai take ba tare da ta kula ummin na ta ba seda tagama komai ta hado musu breakfast ta shiga dakin ta tarar da Ummi ta baje hotuna a gabanta tarike guda daya tanata kuka

Ajiye tray din hannunta tayi ta karasa gaban Ummi ta Sa hannu ta zare hoton da yake hannun ummin nata ta duba

Hotonta ne ita da Aliyu sun kalli juna suna dariya

Jalila ta dago ta kalli umminta, “

“Ummina soyayyar ce ta motsa kika Sa hoton abeena a gaba kina kuka,?”

Jalila tai maganar tana dan murmushi wanda iyakacinsa lebenta, saboda in da Sabo Jalila tasaba da ganin umminta ta dau hoton abeenta tasa agaba tana kuka, kokuma hoton family ta

Jalila ta cigaba da cewa

“haba ummina idan ina ganin karaya a fuskarki me kike tsammani daga gareni duk lokacin danaga hawaye a idonki karaya nakeyi ummina bana son ganin hawayenki kaddararmu kenan semu karbeta a haka muciga ba da hakuri Allah shiyasan abunda yake boye”

Jalila Tafada jikinta a sanyaye tana sharewa Ummi hawaye yayinda itama take zubda hawayen

Dukda karancin shekarun Jalila, in tana magana tana tsara zance daki² dukda tarin kuruciya dake dawainiya da ita wani lokacin tana tunani irin na manya

Riko hannun Jalila Ummi tayi tare da ajiyar zuciya, 

“babyna Kidena kuka nima na dena ina tuna abubuwan dasuka wuce ne a baya Jalila bazan manta da halaccin mahaifinki ba a gareni, da kakaninki sunmin halacci ina miki fatan samun managarcin miji me kaunarki kaman mahaifinki sukuma Allah ya kai rahama kabarinsu”

“Ameen Ummi”

Sukayi breakfast bayan sungama ne Jalila takuma Cuban umminta tace

“ummina amma meyasa ba kyason muje garinku, nifa nagaji da cin zarafin da akemin akan danginki ni ko Yaya suke ina so nagansu a haka ko basu da addini ina sonsu ummi”

Jalila Ummi takira sunanta 

Jalila ta dago ta kalleta ba tare da ta amsa ba

“Meyasa kika dawo gida hutunku be kare ba nasan akwai damuwa me ya faru”?

Turo baki Jalila tayi

“To ni Ummi meye be faru ba, wannan Yaya mairon tazo tana cin zarafina,  tun ina yarinya bana gane kyamar da take min har na girma nagane ba ta dena   ba why?”

Ajiyar zuciya Ummi tayi 

“Nasan abun da matukar wuya amma kiyi hakuri, kaman yadda kikace qaddararmu ce haka”

    

“To Ummi su mutane basu San kaddara bane dan mutum ya musulinta daga baya se yazama laifi yazama aabin kyama, wannan wane irin abune

Ummi ni mukoma danginki ya fiye min wannan cin zarafin Indai zasu bari muyi addinin mu, gara mu zauna a cikinsu da hujja insan ni jikar kiristoci ce, a fada da hujja tun INA zanin goyo bansan komai ba Ummi mutane ke nunamin kyama saboda kawai daga baya kika tuba, ina kema a da musulma ce uminna enough is enough am tired asarar hawayen damuke yayi yawa”

    Ummi kallonta kawai takeyi gaba daya setaga Jalila ta juye takoma mata Aliyu sak irin halinsu daya Jalila akwai saukin kai ita dai batta da Neman magana tana da kawaici amma bata iya fushi ba gaba daya hargitsewa take sekace Aliyu

  Janyota Ummi tayi jikinta ta zaro wani hoto

“Baby na kinga hoton ki kina Jaririya kamanki daya da kakarki, wani lokacin kuma in kikai abu senaga kaman mahaifiyata”

  “Haba Ummi yakike kokarin basar da maganar damukeyi, Ummi I mean what I said fa tun kafin ki haifeni kike fuskantar wannan matsalar, Ummi irin wannan cin mutunci da hausawa keyiwa Wanda suka musulinta daga baya har ina”

  “A’a Jalila yan adamne mu in an mana ba dai² ba se muduba Alkhairan mutum kinsan wani Abu, baby na Alkhairan mahaifinki Dan uwansa da kakaninki gareni se in manta da laifin da wasu daga cikin hausawa maraasa fahimta suke min kinemi yardar Allah bana mutum ba

Kiduba tunda mahaifinki ya rasu dan uwansa yake dawainiya damu bamu taba kukan babu ba, a garin nan kalli yadda Mike zaune da kowa lafiyaa, indai bazaki dinga duba alkhairan mutane ba se sharri to bazaki taba yi musu adalci ba”

  Nannauyar Ajiyar zuciya JALILA ta sauke 

“Am proud of u ummina kinsa jikina yayi sanyi, to shikenan amma meyasa ba kyason zuwa Gida?”

“JALILA inason zuwa amma sekinyi aure in muka je yanzu bazasu kara bari in taho ba nikuma nafiso sekin yi aure semuje ki gansu,  tsawon lokacin danayi ba tare dasu ba zuciyata na tare da su, nafiso koni zasu rikeni ke yazamana kina dakin mijinki shizesa hankalina ya kwanta”

Ya mutsa fuska Jalila tayi

“Ke kullum zancenki aure²”

  “To ai shine cikar mutuncin ya mace nidai fatana kirike mutun cinki a rayuwa Jalila kizama ya tagari abar Alfahari, kuma kizama garkuwa ga mijin dazaki aura ko ya yake,”

“Insha Allah ummina bazan baki kunya ba”

Ummi ta cigaba da cewa

“sannan kirike zumunci da yan uwanki Jalila kar abunda mahaifiyarsu da danginta kemana yasa ki gujesu wannan shine abinda mahaifinki yaita gayamin kan ya rasu”

“Naji amma bazan kuma zuwa kano ba in sun damu dani su suzo inda nake”

Dan zaro ido Ummi tayi

“Meyasa?”

“daf nake da wataran in wankawa Yaya Mairon  nan mari wallahi,”

“Jalila ni ban koya miki wannan tarbiyyar ba, duk abinda hakuri bebaka ba rashinsa baze Baka ba”

“To Ummi tuba nake”

Ta fada tana mikewa tsaye 

” ga wannan azzalumin shima Dan giya yadda ya dinga cin zalina bazan kuma zuwa kano ba”

Tayi maganar a hankali 

“Me kikace ?”

“Ba komai Ummi, cewa nayi siyama bata zo nemana ba tunda na tafi bamuyi waya ba”

Tafa Dan kar Ummi ta gane me tace

  “Tazo amma jiya da safe kafin Ku iso seda takuma zuwa nace mata baki dawo ba”

Murmushi Jalila tayi tareda cewa 

“Allah sarki Aminiya”

Jalila tafada tana murmushi

Allah sarki babyna kin makara komawarki kano yazama dole Ummi tayi maganar a zuciyarta

   

Sallama akayi Ummi ta amsa Jalila kam bata tsaya ba data ji me sallamar ta fito da gudu daga dakin suka rungume juna dame sallamar

“Aminiyata nayi missing dinki”

Tureta siyama tayi ta Dan hade rai 

“eh shiyasa naga kullum semunyi waya, nakiraki ba kya dagawa duk cikin missing din nawane”

A hankali Jalila tai mata magana 

“Sorry aminiya Akwai labari”

Gyda kai siyama tayi ta Shiga suka gaisa da Ummi sannna ta fito suka koma dakin Jalila,

Dakin da dashi da babu kusan daya a gurin Jalila Dan komai Nata yana dakin Ummi se dai in sunyi fada seta koma dakinta kokuma in kawayenta sunzo

Suka shiga suka samu guri gefen katifar dakin suka zauna

  “Bari Azumi baki San meyafaru bane amma ni kaina nayi missing dinki”

“Wallahi kika kuma cemin Azumi tashi zanyi in tafiyata ya za ayi a samun siyama ki dinga wani cemin Azumi kamar wata tsohuwa”

“Yi hakuri aminiya siyama na dena”

“Kin temaki kanki, wato kikaje kano kika tare kin manta da batun haddar islamiyya, gashi baki ba da uzurinki ba kinsan malam nazeeru ba afuwa

Waima ya akayi kika dawo Ummi tace min se hutun school ya kare zaki dawo”

Jalila ta nisa

“Kinga yanzu bar batun malam Nazeeru nasan yadda zanyi dashi”

Jalila ta kwashe kaf abunda yafaru zamanta a kano ta gayawa siyama ciki hada dramar su da Jalal,

Jin siyama take kamar Yar uwata ta jini basa boyewa juna komai

Jalila tacigaba da cewa

“Siyama bazan kuma zuwa kano ba,”

Jalila ta fada in a serious tone

  

” aikuwa ke zuwa kano ya kama zaman Kaduna banaki bane”

Siyama ta bata amsa

“Azumi ki kiyayeni dagaske nake bani ba kano”

” kina kuma cemin Azumi zan dinga cemiki matar Jalal”

“Allah ya kiyaye, ya za ayi in gayamiki magana kina Neman jamin bala’i Dan giyane fa, naji bazan kuma cemiki Azumi ba amma meyasa kikace dole in koma kano”

“Yanzu a ce yaya Jawwad ne yake abinda Jalal yake kikaji abinda Ilham tace zuba ido zakiyi kenan??”

“Allah ya kiyaye Yaya na ba irinsa bane bahaka muke ba

Narasa dalilin dayasa ya mannewa Yaya Jawwad”

  

“Aminiya babu Wanda yafi karfin kaddara”

“Siyama abinda Jalal yake ba kaddara bane son zuciya ne”.

     Jalal ne kwance akan wani makeken gado ya tada kai da hannunsa yana ta baccinsa cikin nutsuwa fuskarsa tayi fes kaman Wanda yake jinya, gashi ya rame sosai

Wata matace da Wasu mutane a bayanta suka shigo dakin da Jalal yake kwance, suka zagaye gadon da yake duk sun rufe fuskokin, su matar tasaka kaya tundaga sama har kasa ta rufe ko ina da bakaken kaya

Hannunta ta mika baya daya daga cikin mutanen dasuka zo tare ya mikomata wata zukekiyar wuka se kyalli takeyi 

Ta zo kan Jalal ta saita cikinshi da tsinin wukar nan ta daga wukar sama

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

  

“Karki caka masa, dan Allah

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!!”

Shine abinda Jalila tafada da karfi ta farka daga mummunan mafarkin da take Wanda ya kasance tsakiyar dare

Da gudu Ummi ta yanke sallar da take ta taho kan gadon ta dago Jalila

“Lafiya me yasameki Jalila,?”

“Bakomai Ummi mafarki nayi”

  “Kinyi adduar kwanciya bacci?”

  Gyada kai Jalila tayi alamar eh

“Alwala fa”

“Itama nayi Ummi”

“Jeki sake alwalar sekizo ki kwanta”

Mikewa Jalila tayi taje ta yo alwala ta dawo ta kwanta tayi shiru tana kuma tunanin mafarkin da tayi

A hankali Ummi ta zo ta rungume Jalila tana mata 

addu a, amma har yanzu kirjin Jalila bugawa yakeyi da sauri²

  Washe gari da safe suna karyawa, amma hankalin Jalila yana kan mafarkin da tayi jiya Ummi ta lura da ita dan haka, ta yanke shawarar  tambayar Jalila mafarkin da tayi take ihu cikin dare

“Jalila mafarkin me yasaki ihu cikin dare jiya”?

“Ba komai”

Jalila tabata amsa

“Kaman ya ba komai kin firgitani”

“Ummi ni dai nasan nayi mafarkin tsoro amma na manta me nagani”

Kallonta Ummi ta yi 

“Baby kenan adinga addu’a dai”

“Inayi ai Ummi amma zan kara insha Allah”

“Yayi kyau kici abinci kidena wannan tunanin”

Gyada kai Jalila tayi ta Dan cakali abincin ta bari

Uniform din islamiyyarta ta dakko tana gogewa, amma duk kokarin ta, ta cigaba da harkokinta tana tuna mafarkin nan se gabanta yayi mummunar faduwa

“Subhanallah”

Shine abinda Jalila take fada in ta tuna mafarkin, haka ta karasa gugar tasaka uniform din islamiyya tana zaman jiran siyama ta karaso su tafi islamiyya

Qur’anin da Daddyn Jalal yabata ta je ta dakko tasamu guri tazauna tana kallonsa tana shafawa se jujjuya shi take a hannunta 

Sallamar Siyama ta ji amma bats motsa daga inda take ba Siyama suka gaisa da Ummi a tsakar gida

“Ummi ina Jalilan take?”

“Tana cikin dakinta yau narasa meyake damunta yau tun safe tana daki”

“To Ummi bari ingani kinsan ta wani lokacin se a hankali”

“Aikam halin Jalila ai se hakuri”

Dakin Jalila ta shiga ta tarar da ita tana ta jujjuya Qur’ani a hannunta

“Aminiya lafiya dai yau kuwa,wannan Qur’anin fa me kyau, kice har babban guzuri kika taho mana da shi”

Ita dai Jalila ba tace mata komai ba ta mika mata 

“Masha Allah gaskiya yayi kyau box din da yake ciki ma gwanin sha awa bari in sashi a Jaka mutafi da shi Islamiyya munyi sabon Al Qur’ani

“Bani”

Jalila tasaka hannu ta karbe Al Qur’anin daga hannunta Jalila 

“wannan ba na zuwa islamiyya bane kallonsa kawai zan dinga yi”

“Kamar ya “?

” kamar yadda nagaya miki”

“Allah yabaki hakuri naga yau tambotsai kikeji”

Jalila bata kuma kulata ba ta dauki hijjabinta ta saka ta maida Qur’anin cikin cover dinsa ta adana shi 

  Suka fito

“Ummi zamu tafi”

Siyama tayi maganar tana risinawa

“To adawo lafiya Allah yayi Albarka”

“Ameen Ummi”

duk wannan maganar da ake Jalila batace uffan ba

Har sunkusa fita Ummi tace

“Ke madiga ina taki Jakar makarantar?”

“Ban gan taba sena dawo zan duba”

Tafada tana sunkuyar da kai 

Girgiza kai kawai Ummi tayi sukuma suka tafi

Daga office dinsa ya dinga jiyo hayaniyar  Jalila ta dawo daga ajin dake gaban office dinsa

Tsaki ya ja ya kalli dayan malamin

“Aifa bismillahi wannan baki abun maganar ta dawo yanzu bamu da sakat saboda surutun dalibai”

Daya malamin ne ya kalleshi

“Lallai kam malam naziru indai Jalilace baki abun magana, ga surutu ga Neman magana, inda take birgeni kwakwalwarta tana Ja sosai, kuma duk tsiwarta intai laifi akwai bada hakuri”

“Hmm kaidai bari kawai idan nafara lissafo maka halin yarinyar nan ai se dai addu’a”

Murmushi daya malamin yayi sukayi musabiha ya bar office din

Mamakine ya cika shi kodai kunnensa beji dai² ba yaji ana Jalila ta dawo amma yaji ajin shiru kaman an cinyesu se Dan surutu da suke kasa²

  Har yayi gaba ya dawo ya leka Ajin aikuwa itance amma fuskarta Sam ba walwala ta koma gefe tayi shiru se Siyama dake gefenta tana mata magana

Kai tsaye ya dawo kofa ya shiga ajin gaba daya suka nutsu

“Baku San me yakawoku nan bane Ku dakko Qur’anin Ku kufara tilawa,”

Ya kai dubansa kan Jalila 

“Ke yau kwananki kusan goma bakizo makaranta ba, kuma baki bada wani uzuri ba”

Siyama tai saurin cewa 

“Malam Naziru nafa gaya maka..”

“Ke rufemin baki marasa da’a ina magana zaki katseni”

Ya maida dubansa ga Jalila 

“in anjima zanzo karbar hadda duk na kwanna Goman nan sekin bani haddasu

Kukama Ku dakko Qur’anin Ku nace”

Kowacce kokarin dakko Qur’anin Sa yake banda Jalila wadda kamar an dasata

“Ke ina naki Al Qur’anin”?

Ya dakamata tsawa

Qur’anin hannun Siyama ta nuna masa

Ya kalli siyama ” ke ina naki?”

Itama Qur’anin ta nuna masa “rainamin hankali zakuyi kenan?”

Fita yayi be dade ba se gashi da wata katuwar dorina yana zuwa ya fara takan Siyama ya zaneta sannan ya nufo inda Jalila take 

Zumbur ta mike ta fara ja da baya

“Dawo nan ki tsaya, fara bani haddar yanzu zan karba”

Yafada yana muzurai yana nuna mata gabansa

“Ni wallahi banyi haddan nan ba kuma in kada keni da wannan bulalan suma zanyi”

  “Ai ko mutuwa zakiyi yau sena zaneki Dan kun rainamin hankali wai Qur’anin Ku daya Ku biyu”

Aikuwa Jalila ta dage ta kwala ihu tare da fadin 

“Malam babba kazo ka temakeni, danka ze kasheni, za a daki amanarka Dan Allah kazo”

Daga ajin da dattijon yake zaune yana biyawa dalibai karatu ya jiyo ihunta tana kiran sunansa 

Malam babba shine mamallakin makarantar malam, Naziru kuma dansa ne dabasa jituwa da Jalila

Wataran ya daketa tayi suman karya, aka kaita Gida lokacin Abban su Jawwad yazo, hankalinsa ya tashi sosai yazo har makarantar ya samu malam  babba akan dukan da akayiwa Jalila yayi yawa, malam babba yaita bashi hakuri, shine Abban Jawwad   “yace malam ga yata nan Amana dan Allah a hannunka marainiya CE adinga hakuri da halinta”

shikuma yace ya karba, indai za a daketa har cikin zuciyarsa yakeji bayason kukanta

Itakuma Allah be hada jininta da malam Naziru ba, kusan kullum Seya nemi abinda zesa ya daketa

Tashi yayi da sauri ya taho ajin dayake jiyo ihunta yaganta ta makale a lungun ajin tanata kuka ga kuma malam Naziru a tsaye da bulala

“Naziru lafiya nakejin kukan ‘yata”

Nan malam Naziru ya shiga gayamasa abunda akayi da Wanda ba ayiba

“To ina nema mata afuwa bana son ana samun ita kuka dukda Yar tawa tafiye Jan magana”

Gyada kai malam Naziru yayi ya fita daga ajin zuciyarsa fal bakin cikin rashin Zane yarinyar nan.

Malam babba ya hada litattafan makaranta yabawa Jalila sannan yace ze aikomata da Jakar makaranta

Itakam siyama har aka tashi daga Islamiyya kukan dukan da akayi mata take Dan tana tsoron bulala, mafi akasari in Jalila tai lefi akanta abun yake karewa.

Da aka tashi Har Gida Jalila ta  raka siyama tana ta bata hakuri

Kwana biyu  Jalila tacigaba da harkokinta hankalinta kwance amma data tuna mafarkin nan se ta ji jikinta yayi sanyi 

Tana kwance a dakinta gidan bakowa tanata tunani bacci ya kwasheta Ummi bata nan ta tafi kasuwa

Jeje ne zaune yana ta busa shisha, shikuma Jalal yasaka Bluetooth a kunnensa ya jingina da kujerar da yake kai

Jeje yadan taba shi alamar yanason zeyi magana da shi cire Bluetooth din kunnensa yayi yana kallon Jeje alamun ina jinka

Jeje yai gyaran murya

“Man wai ya batun tafiyarmu Dubai ne naji ka shiru”

Lumshe ido Jalal  yayi 

“Tafiya tana nan daddy ya turomin kudi nayi arranging din next week ne insha Allah”

“That’s good my man but a yanmatan nan baka ganin yakamata mu tafi da wasu abun zefi dadi inda mata a harkar”

Hade rai sosai Jalal yayi murya a kaushashe yace

“Amma kasan a tsarina babu mata ko? bana gayyatowa kaina ciwon kai, in kaga bazaka ba seda mata to  kawai ka zauna, ba Y’ar Wanda zan dauka in tafi da ita”

Lallai gayen nan, amma a hankali da matan zamu kafa maka tarkon dabaka Isa ka tsallake ba, tarkon daza mu rikeka a wuya jeje yai maganar a zuciyarsa

A fili kuma yace

“As u wish my boss abar maganar mata mutafi kawai”

Jalal bekuma tanka masa ba Yakoma ya jingina da kujerar da yake

“Are u serious Jalal wai damaa dagaske kake tafiya Dubai zakayi, mahaifiyarka fa bata so mahaifinka ma ba a son ransa zaka tafi ba meyasa bazaka hakura ba? Haba Dan uwana kayi tunani mana”

Jawwad ya karasa maganar a sigar rarrashi

“Ina ruwana da rashin yaddata data yadda da karta yadda duk matsalarta ne, daddy kuma tunda ya yadda ya turamin kudin ai ya yadda kenan”

  “Haba Jalal duk abunda kayi ba da yadda iyaye ba kosa albarkarsu ba karshen al’amarin lalacewa”

“Indai albarkarta ce banaso ta babana ta isheni”

JALAL yai maganar yana hade rai

A fusace Jawwad ya kalleshi

“JALAL uwa uwace komai lalacewarta balle babu lalacewa a iyaye meyasa kai baka yafiyane? Kamanta mana komai ya wuce hawayenta masifa ne a rayuwarka”

“Idan na tsallake nabar Nigeria seta manta dani kafin na dawo kaga ta huta ta dena hawayen”

“Haba Jalal mahaifiyarka CE fa meyasa kafiye taurin kai ne meyasa baka yafiyaa me”?

“Dole kace haka tunda ba kai kake irin rayuwar danake ba, ba kai ka samu kanka a halin da nake ciki ba, mutane na kyamarka shiyasa kake cewa in manta komai ya wuce, 

Idan nabar kasar nan seta ganni zatayi kukan ai lokaci² nazo inga daddy”

“Jalal anya Kasan soyayyar dake tsakanin d’a da uwa kuwa baka tunanin halin daza ta shiga in ka tafi?” 

Jawwad ya fada yana kallon Jalal da yake shirya kayansa a trolley

Be dago kai ya kalleshi ba yabashi amsa

“Kai kasanta ita soyayyar d’a da uwar, gobe insha Allah zan bar kasar nan kudena ganina balle ranku ya cigaba da baci akaina”

Jalal ne da Jawwad ke zaune suna hira gwanin sha’awa sunayi suna dariya suna cin yayan itatuwa a wani lambu me matukar kyau da korayen bishiyu

Wani mutum ne ya zagayo ta bayan su Jalal ya rife fuskarsa ba a iya gane waye, yabawa Jalal wani abu, Jalal ya karbi abun yafito da shi ya dubi kirjin Jawwad ya zaro wata siririyar kibiya Yar Karama ya sokawa kirjin Jawwad din saitin zuciyarsa, nan take Jini ya balle, sekuma Jalal ya yadda kibiyar ya rungume Jawwad yana kuka, wannan matar ce ta rannan tazo tafara Jan Jalal,

Nan da nan gurin Yakoma baki bishiyoyin gurin suka bushe,

Ta dinga janshi zuwa wani katon rami ita da wani mutum

Jalal mikowa Jawwad hannu yake 

“Dan uwa ka temakeni kar kabari sujani cikin Ramin nan”

Jawwad dafe da Inda Jalal ya sokamasa kibiya jini na zuba yake fadin 

Bazan iyaba Dan uwa 

Jalila!Jalila!!Jalila!!!

Kitema kawa Jalal karki bari su jashi cikin ramin nan

Siyama dake sallama a tsakar Gida ta jiyo kukan Jalila da Sauri ta karasa Inda take jin kukan nata

Tana kwance akan gadon Ummi ta hada gumi se kace tayi dambe da zaki ga hawaye a fuskarta,

se jujjuya kai take tana fadin

“A’a nima bazan iyaba Yaya Jawwad bazan iya temaka masaba nima zasu hada dani”

Subhanallah siyama tafada tare da jijjiga Jalila

A firgice Jalila ta farka daga mummunan mafarkin datake tana haki

“Jalila lafiyanki kuwa meyasameki? ina ummi?

Tun dazu na shigo nake sallama ba Wanda ya amsa me yasaki wannan kukan”

“Bakomai”

Tabawa siyama amsa

“Kamarya ba komai kalli fa yadda kika hada gumi ga kuka kinayi”

Siyama tafada tana nunata

Mikewa Jalila tayi ta tafi gaban mudubi

Ta kalli kanta taga yadda ta hada gumi ga hawaye, idonta har yayi ja kaman ta wani tana kuka

Wayarta ta ta dakko ta dawo inda ta tashi ta zauna 

“Aminiya waime yake damunki ne akwai matsala ne?”

Girgiza mata kai Jalila tayi tana duba wayarta lamabar Yaya Jawwad tayi dialing bugu biyu ya daga sekuma tayi shiru tarasa mezata CE

Jalal ne ya katse shirun ta hanyar Sa wayar a hands free  sannan ya yimata sallama

“Salamu alaikum warahmatullah sisyna yakike ya Ummi”

Ajiyar zuciya tayi

Alhamdilillah yana raye

“Me kikace?”

  “Duk Muna lafiya ya maama da Nana”

“Muna lafiya sisyna, ya karatu”

“Yaya Jawwad”

Takira sunansa

“Na’am sisyna ya akayi?”

“Kana inane?”

“Akwai matsalane? yau weekends muna gida ina tare da yayanki Jalal ina ta fama dashi wai se ya tafi Dubai ya barni, in ya tafi kuma wai baze dawoba

  Dan karamin tsaki Jalila tayi sannan tace 

” to Yaya seme? kabarshi yaita tafiya daga nan har bangon duniya ya tafi ai gara hakama tunda baze karatu ba kaman sauran mutane ba seya tafi yayi abunda ya dace dashi kaima ka nutsu ka maida hankali akan naka karatun”

Cak ya tsaya da hada kayan dayake saboda yanajin duk abinda Jalila take fada saboda Jawwad a hands free yasaka wayar wannan Jarababbiyar yarinyar bazata fasa aibata shiba kenan

Shikam Jawwad saroro yayi yama rasa meze ce

Da kyar Jawwad  ya hadiye yawu yayi gyaran murya

“Sisy bana gayamiki addu’arki Jalal yake bukata ba shima fa dan uwanki ne kidena fadan maganganu marasa dadi akansa kinji ko”

“To naji nadena ka gaida maama da Nana”

Haka dai suka gama wayar da Jalila

Jawwad ne ya kalli Jalal sannan ya kira sunansa da nufin yaba shi hakuri akan abinda Jalila take masa

Daga masa hannu Jalal yayi

” gara in bar muku kasar hankalinku ya kwanta hankalin kanwarka ya kwanta kar in lalata ka” yacigaba da abunda yake

“Jalal bahak…..

Daga masa hannu Jalal yayi

” no need to say anything “

“Aminiya wai bazaki gayamin meke faruwa ba”?

Siyama takuma tambayarta

” ke kin isheni nace miki ba komai amma kin isheni kibarni inji da abunda yake damuna!”

Jalila tayi Wa siyama maganar a hasale

Dan zaro ido siyama tayi

“Sorry Allah yabaki hakuri laifina ne danazo inda kike kuma na damu da damuwarki dama zuwa nayi in gayamiki dazu malam babba yace agayamiki akwai musabaka next week insha Allah”

Tana zuwa nan ta tashi tafita tabawa Jalila guri

Sam Jalila jinta take wani iri wannan wane irin mafarkai takeyine akan Jalal

A haka Ummi tadawo ta tarar da ita wani iri kaman Mara lafiya tana nuna mata abubuwan data siyo amma hankalinta baya kanta

“Baby waime ke damunkine?”

“Ummi marata ce take ciwo kuma na sha magani”

Dayake tana cikin period ta wayance da hakan

“Allah ya sawwake”

“Ameen”

Ummi ce tayi musu girkin dare 

“Wai har yanzu marar ce tashi kici abinci ki kuma shan magani”

“Ummi na koshi da abincin”

“Baby kin fiye taurin kai shiyasa bana son rashin lafiyarki kin fiye gaddama tashi ko tea kisha”

Tea din kawai ta sha ta nemi guri ta nema ta kwanta amma fargabar yin baccin take saboda bata San mezata kuma gani ba

Se jujjuya mafarkan da tayi takeyi a zuciyarta dayake bacci barawone haka yayi awon gaba da ita dukda tarin fargabar da take ranta

“Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi………..

Ni bazan iyaba wallahi, idan suka kashe nifa, niba abunda zan iya yatafi ina ruwana

“Ke Jalila wai meye hakane

Ba magana nake miki ba”

Tashi Ummi tayi taje ta jijjigata a firgice ta tashi tana rarraba ido

“Wai meyake damunki a yan kwanakin nan kusan kullum sekin tayar min da hankali in dare yayi ko dai gamo kikayi da Aljanu”

“Niba wasu aljanu kawai tsorata nake”

Jalila tafada tana ya mutsa fuska

“Au tsoratanne kawai, to tunda kawai ne kika kuma min kuka a cikin bacci bulala zan saka in zaneki ta shi kije kiyo alwala kiyi salla ki dau Qurani ki karanta Allah yasa kina Azkar”

“Ummi bana salla”

“To jekiyo Alwala kibiya Wanda kika haddace”

Ba musu taje tayo alwala tazo taita bitar Qurani da ka bacci kam gagararta yayi se dai juye²

  Yauma kamar kullum haka ta tashi jikinta kaman Mara lafiya ko abincin kirki takasa ci ga idonta daya kumbura saboda rashin bacci Ummi kallonta kawai take dakinta ta koma ta nemi guri ta kwanta tayi shiru

(Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi!!!)

Tas kalaman da akayi mata a mafarki suke dawo mata kwakwalwarta Wanda yayi dai² da wani mugun bugawa da zuciyarta tayi da karfi, kanta ya Sara

“Nashiga uku ni Jalila wannan wani irin bala’i ne meye hadina da wannan mutumin ake tsoratani akanshi wani tsautsayin ne ya kaini kano wanannan wani irin jarabane ana nema a haukatani why?”

Tafada tareda yin jifa da pillows din kan katifar ta yage bedsheet din kan gadon ta kifa kanta akan katifar

“Dan Allah ji abinda nake kamar mahaukaciya Ta Yaya zan hanashi tafiya ina nan yana can how? Be duba amincinsu da Yaya Jawwad yafasa tafiyar ba se ni da bama shiri to ni ya zanyi?

Kawai shirmen mafarkine kimanta kicigaba da harkokinki

Wani bangare na zuciyarta ya gayamata,

aikam ta yadda da abinda zuciyarta ta gayamata na ta manta shirmen mafarkine

Ga bacci a idonta kanta har ciwo yake amma bazata iya ba saboda fargabar inta kwanta me zata gani

Duk yadda taso ta manta takasa zuciyarta se bugawa take da sauri² hankalinta yaki kwanciya

” Nashiga uku ni Jalila meke shirin faruwa dani haka ya zanyine?

Ko ingaya Ummi me

Karki kuskura hakan be dace ba mussaman intaji abinda yayi miki bazataji dadi ba, wani sashi na zuciyarta ya gargadeta 

Siyama ce ta fadomata a rai, dan haka da sauri ta mike taje ta wanke fuskarta tasaka hijjabi ta fito, ta tarar da Ummi tana saka a dakinta

“Ummi inaso zanje gurin siyama”

“Adawo lafiya kigaidamin da ummanta saura ki dade inkika dade kin kori gaba kinsan halina”

Gyada kai Jalila tayi ta fita ta nufi hanyar gidansu siyama

Haka nan take tafiyar kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, haka takarasa gidansu siyama.

    makeken Gida ne Wanda yayi matukar haduwa da tsaruwa baban siyama yana da kudi sosai custom ne daga shi har Maman siyama mutane ne masu saukin kai kuma sun yaba da hankalin Jalila shiyasa suka kyale kawancen nasu

Siyama Sam bata da girman kai a makarantar boko suka hadu da Jalila tun primary suke tare makarantar ‘yay’an masu kudi ita Jalila takeyi saboda Jajircewa da rikon amana na baban su Jawwad

Kawancensu har tsakanin iyayensu mata Wanda yakai har kasuwanci sukeyi tare, umman Siyama ta San komai game da rayuwar ummin Jalila ta dauketa kaman Yar uwatta ummin Jalila bata fiye shiga harkar mutane ba amma tana mu’amala sosai da umman Siyama

A tangamemen parlour Jalila ta tarar da Umma (mahaifiyar siyama)

“Hajiya Umma brk da rana”

“Anya Jalila zan amsa gaisuwar nan taki, kinyi tafiya ba sallama kin dawoma bakizo mun gaisa ba balle insa ran tsaraba to ni nayi fushi”

Umman tafada cikin zolaya

“Haba Umma tuba nake yau ai gani Nazo”

“Bawani kinzo dai gurin Siyama sekije tana daki,

Nikuma zamu gauraya dake naganki wani iri ko baki laafiya ne”?

“Hajiya Umma kenan, lafiyata kalau, bari inje gurin siyama, Ummi tana gaisheki “

“Ina amsawa”

Jalila ta mike ta haura sama dakin siyama

Siyama ce kwance akan katafaren gadonta tayi rub da ciki tana game a waya,

Sallama Jalila tayi, siyama ta amsamata ba tare data daga kai ta kalleta ba

“Aminiya gurinki nazo akwai matsala”

Banza siyama tayimata tacigaba da abinda take

“Aminiya magana fa nake kika min banza”

Jalila ta maimaita

“Ni a wa zan San matsalarki, ni na isa ko kin manta wulakancin dakika yimin A gidanku”

Siyama ta bata amsa ba tare da ta dago ba

“Ohh God am sorry aminiya lokacin ina cikin tashin hankaline, Dan Allah kimin afuwa ki saurareni, right now ma a cikin wata matsalar nake siyama jinake kaman zanyi hauka, yanzu haka zuciyata bikiji bugun data keyi ba”

  A razane siyama ta mike zaune tana kallon Jalila 

“Kaman Yaya? Meyafaru?”

Ajiyar zuciya Jalila tayi sannan ta labarta mata duk halin da ake ciki

“Ni yanzu babban tashin hankalina aminiya ni bansan ta Yaya zan hana shi tafiyar nan ba yana kano ina Kaduna,

Tunda na fara mafarkan nan bana nutsuwa se inji kaman zan haukace”

“Easy, don’t said that again please karki kuma batun hauka

Kinga maganata ce fito  dama nagaya miki zaman Kaduna bana kibane inkika temake shi kanki kikayiwa kamar kin temaki Jawwad ne”

“Kinga ni ba wannan surutun ba kigaya min mafita siyama kaina ya kulle”

“Aikuwa dole kibude shi, shi tunanin naki, yaya Jawwad zaki kira ki zigashi akan kar yabarshi ya tafi saboda besan meze faruba in ya tafi zuciyar Yaya Jawwad zzaki karya yadda zaki ingiza shi ya hana shi tafiya”

“Siyama bana tunanin hakan me yiwuwa ne, nasan Yaya Jawwad zeyi iya yinsa kan yahana shi tafiya tunda kika ga ya hakura to abun yafi karfinsa,

Dama da ganin idon nan na Jalal zeyi azababben taurin kai”

“A’a Jalila ki dai gwada kigani, kema ai taurin kan yana damunki”

Mummy ce take ta rusa kuka 

“Yanzu Jalal dagaske tsallakewa zakayi kabarni, kai kana ganin hakan shine dai² a rayuwarka bani da kowa se kai zaka Sa k’afa ka tafi, har kana fadin inka tafi bazaka kuma dawowa ba”

“Idan na tafi hutun mune ni dake gaba daya ki huta dasaki bacin rai danakeyi”

Ilham ce tafito tazo gabansa 

“Haba Yaya Jalal yanzu in…

” ke!!!!! Kikasake kika Sa min baki sena tattakaki ina ruwanki dani mayya kawai”

Ya fice daga parlour lambar Jeje yakira 

“Karka manta fa kazama cikin shiri karfe hudu insha Allah jirginmu ze tashi”

Ya katse wayar ya tafi dakinsa 

“To siyama bari in jarraba amma nikam na karaya Allah kabani iko “

“Ameen don’t waste time yi sauri”

Siyama ta fada a gaggauce

Lambar Jawwad Jalila ta kira 

Aikuwa tayi sa’a ya dauka

“Barka da rana yayana”

“Yawwa autar Ummi ya ummina ya Gida”

“Lafiya kalau, amma yanaji muryarka wani iri ko duk Dan tafiyar Yaya Jalal dinne”

“Kedai bari sisy na Daren Jiya banyi bacci ba Jalal ya kafe wannan karon tun tasaowata tare muke dashi jinsa nake wani bangare na zuciyata amma ze tafi ya barni gani nake Lamar da wasa yake”

Ajiyar zuciya Jalila tayi

“Ya tafinne?”

Jalila ta tambaya

“A’a jirgin karfe hudu zebi yau zetafi”

Cikin Jalila ne yayi wata kara ta kalli agogo karfe daya da rabi

“Yaukuma ?”

Tafada a tsorace

Siyama ce ta kalleta ta girgiza mata kai alamar kwarin gwiwa

“Eh yau sisy haka dai yacemin, yau ban yi tsammanin Dan uwa zetafi ya barni ba”

Jalila ta numfasa tace

“To waime yasa ze tafine?”

“Cewa yayi gara ya tafi mummy ta dena ganinsa, yadena sata bacin rai”

“Allah sarki mummy ko yazataji idan ya tafi, ya daddynsa zeji in ya bude ido yaga baya kusa dashi,

Yaya Jawwad abokinka bashi da tausayi baka tunanin me ze faru Idan ya tafi kasar da babu me Sa shi babu me hanashi,

Baka tunanin wasu abokai ze hadu dasu a can, 

Allah sarki nasan dole mummy ta zubda hawaye inya tafi, kuma Kasan hawayenta matsalane a rayuwarsa, Yaya yakamata kahana shi tafiyar nan, ka temakawa rayuwarsa daga masifar hawayen uwa

Yanzun ma karkayi mamaki abokanan banzarsa ne suka ziga shi shine zeyi tafiyar”

Da sauri Jawwad ya tashi zaune tare da furta

“Abokanan banza Jeje”

“Mekace Yaya”

“No bakomai zanyi kokari inkuma jarraba hanashi tafiya nagode sosai da gudunmuwarki kanwata, da na hakura amma kin tunatar dani wani abu me mahimmanci nagode”

Sukayi sallama

Jalila tayi ajiyar zuciya

“Good dear kinyi yadda yakamata sekace Jarumar film”

“Hmm ba wannan ba aminiya Allah yasa ya yadda kar yayi tafiyar nan”

“Ameen insha Allah bazeyiba Addu’a zamuyi tayi”

“Allah ya amsa amma nakaraya saura awa biyu ya tafi fa”

“Ba komai calm down mucigaba da addu’a Allah ya bawa Yaya Jawwad sa’ar hanashi tafiya”

“Ameen”

Jalila ta amsa a sanyaye

Da sauri Jawwad ya tashi ya nufi gidansu Jalal kai tsaye part din Jalal ya nufa yaje ya tarar yashiga wanka

Gefe ga katuwan trolley dinshi ya hada ta tsaf 

A hankali Jawwad ya shafa trolley yayi ajiyar zuciya, ya nemi guri ya zauna yana jiran fitowarsa ya shafe akalla mintuna sha biyar yana jiransa sannan ya fito daga wankan

“Kana nan banji shigo warkaba ai”

JALAL ya fada yana goge jikinsa da Dan karamin towel

“Jalal”

Jawwad yakira sunansa da dan sauri Jalal ya kalleshi saboda da wuya ya ambaci sunansa

“Baka saba yimin karya ba yanzun ma bana fatan kayimin kaida wa zaku tafi dubai”?

Jalal ya danyi shiru sannan ya yi magana

” nida Jeje ne”?

Da sauri Jawwad ya kalleshi Jeje fa kace Jalal

“Jalal kasan me kake cewa kuwa yanzu kaida shi zaku tafi,

Ka fifita tafiya kabar iyayenka saboda wannan Dan iskan Mara mutuncin

Kazabi ka tsallake kawai katafi garin da banaka ba, ka zauna,

Dama nasani he is behind all what u are doing”

“No Jawwad don’t blame him u know who is behind all this kasani kasan komai karka Dora masa, nan da wani dan lokaci shi  jeje ze dawo nizanyi zamana a can in karatun Yakama in cigaba a can”

“Jalal kasani ba kaunarka yake ba, baze bari kayi kyakykyawa rayuwa ba kullum burinsa ya kuma rusaka”

“Ouhhh don’t mind me bros, kabani gudunmuwa a rayuwata bazan mantaba, bana tunanin ko ciki daya muka fito da kai zansamu fiye da haka ,

Amma gara in barka kaima ka huta, kanwarka bata son  mu’amalarka dani banaso mutane sucigaba damin kallon zan bata maka rayuwa kamar yadda tawa tasamu illa,

Banason mutane sucigaba da kyamata da miyagun halayena

Gara inje rayuwar da naga dama Inda ba Wanda yasanni balle ya damu dani”

Cigaba da shirinsa Jal yayi yasaka kananan kaya wando jeans da T-shirt blue, ya taje sumar kansa ya daura agogo sannan ya dakko bakin glass yasaka 

Yayi kyau matuka, duk abin nan da ake Jawwad yana zaune yana kallonsa,

“Dan uwana kazama me min addu’a aduk inda kake kaman yadda kake min abaya Jawwad bazan manta da kai a rayuwata ba”

Jalal yafada jikinsa a sanyaye

“Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni,

Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,

Da second daya bantaba kyamarka ba amma sekai akan wani dalili naka Mara amfani

Zaka tsallake ka barni,

Akan wannan Mara imanin zaka tafi kabar kasarka ta haihuwa iyayenka yan uwanka ka tafi, wannan shine sakamakon abota wannan shine yan uwantakar dake tsakanina da kai

This is what I deserve from you nagode da kauna Jalal”

Jawwad yayi maganar cikin fada

Jalal ya tako gaban Jawwad ya dafa kafadarsa idonsa dauke da kwalla, muryarsa na rawa yafara masa magana

“Am sorry dan uwana baka cancanci haka daga gareni ba but am sorry ba yadda na iya”

Yaja trolley dinsa yayi waje da sauri

“Siyama nifa wallahi gabana faduwa yake ganinake wallahi seya tafi

Bakisan halin Sa da taurin kai ba”

“No kwantar da hankalinki, kome zezo da sauki insha Allah yanzu kira Yaya Jawwad din muji ya ake ciki”

“Anya zan iya magana kuwa bakiji bugun da zuciyata take ba”

“Calm down kirashi kiji”

Layin Yaya Jawwad takuma kira

Sedata kusa tsinkewa sannan ya daga

“Yaya Jawwad ya ake ciki ne yafasa tafiyar kuwa”

“Jalila ya tafi bashi da niyyar fasawa ya tafi yau ze bar kasar nan”

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please

More comments more typing……

Love u all my fans

Back to top button