Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 28 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

Dedicated to Aunty kubra

E28

Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji

Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar,

Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata,

Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla,

Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace”MEKE FARU WA NE’?_

Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa”mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su”

Shiru angel ta É—anyi ta ruÉ—e ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a Æ™asa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta É—ago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, Æ™anÆ™ameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faÉ—in” angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daÉ—i, xafi yake yi mini raÉ—aÉ—i nake ji,

Ƙura ido angel tayi tana kallon É—igon Jinin dake ajikin wandon Parveen Nan take ta gane cewa Jinin al’ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya É—aure mata kai,’ shessheÆ™ar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta,

ÆŠago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaÉ—unta”Kiyi haÆ™uri kiyi shiru parveen zanje in faÉ—a ma tsohuwa,” takai Æ™arshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa,

“Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su,” amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi Æ™opar É—akin tsohuwa takai hannu ta bubbuga Æ™opar, almost 3 times tana knocking Æ™opar, Kafin tajiyo motsinta,

Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda,

“Meke faruwa ne nake Jin koke koke” tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu,

Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa”ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buÆ™atar magani da kuma pads É—in da zasu sanya”

Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duÆ™ar dakai Æ™asa tana sakin wani irin shu’umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai,

“Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba”?

Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana

“I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room” har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara,

“Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za’a zo a É—auke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani Æ™ato ba,” zuciyarta a harzuÆ™e takai Æ™arshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buÉ—e Æ™opa daga can saman benan…………………….

A matuÆ™ar kiÉ—ime angel ta juya tana kallon stairs É—in, hatta su Batool a ruÉ—e suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su Æ™arasa saukowa sautin takalmansu ya karaÉ—e kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya Æ™arfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases É—in, haÆ™iÆ™a hankalin angel yayi matuÆ™ar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi, juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace” na roÆ™e ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alÆ™awarin zan kula dasu,” idanuwanta cike tab da Æ™walla takai Æ™arshen maganar,

Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace”Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za’a zo a É—auke shi akai shi inda za’a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a Æ™arÆ™ashina suke ba, dukan mu Ma’akaita ne dake aiki gidan kurkukun Æ™addara, Kuma a Æ™a’ida wani baya shiga hurumin wani………”

kalaman tsohuwa sunyi matuÆ™ar girgiza angel, kafin ta yi yunÆ™urin buÉ—e baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faÉ—in Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ‘ a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin É—auka su kayi masu ta hanyar ruÆ™e waist É—insu suka yarfa su saman faffaÉ—an kafaÉ—unsu, bayin Allah Sai kuka suke Yi suna Bugun bayan giants da hannayen su, Nan take zuciyoyinsu Batool suka karaya Jikin kowan nan su yayi sanyi, har ma basu san lokacin da suka fashe da matsanancin kuka ba, Juyawa giants su kayi atare suka soma tafiya dasu É—auke saman kafaÉ—unsu suka nufi stairs É—in,

Da gudun gasken Angel ta tunkaresu Tana Æ™arasawa bayansu Ta cafko hannayen parveen dake abayan giant É—in dake É—auke da ita, da iya Æ™arfinta na Æ™arshen ta janyota gaba É—aya ta faÉ—o ta baya, baiwar Allah jikinta sai 6ari yake yi, É—agowa tayi tare da rungume angel ta Æ™anÆ™ameta tana kuka tana faÉ—in”dan Allah angel kada ki bari su tafi dani, saboda basu dawowa da mu, bana so nabar Cikin Æ´an uwana bansan inda zasu kai mu ba, Ina ji araina kamar na tafi kenan…….” Giant É—in dake a É—auke da Parveen Ya tsaya Tsak wanda ko ba’a faÉ—a maka ba, zaka shaida cewar A fusace yake, domin su ba’a katse masu aiki, Da gudun gaske su Hanna da su Javed suka Æ™araso Inda su angel ke a zaune Æ™asa suna kuka,

Kallonsu kawai take yi idanuwanta sun rune ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ci, Na raba ta da ƴan uwanta da ake ƙoƙarin yi,

Cikin shessheÆ™ar kuka Batool tace” Dan Allah ki daina kuka Parveen, tsohuwa ta faÉ—a mana cewa Cuta ba mutuwa bace, Sai in kwanan mutun ya qare, Zasu yi maki magani ne zuwa gobe idan ku ka ji sauÆ™i zasu dawo mana da ku,” Ita kanta batool ta karaya sosai ta yi maganar ne kawai donta Æ™arfafa mata gwiwa,

Zufa ta ko’ina Ajikin Parveen Muryarta na kerma tace”Koda ace ban dawo ba, Idan an kawo abinci, ku dinga ajiye mini nawa” Hawaye sharkaf akan fuskarta tayi maganar, angel dai takasa cewa komai, Zuciyarta ta gama karaya,

Kafin wani ya kuma cewa wani abu, Giant É—in yakai Hannu da niyar ya É—auki parveen, a tsorace ta Æ™ankame jikin angel tana faÉ—in” kada ki bari su tafi dani, bazasu dawo dani ba, idan har kuna sona dagaske ku taimake ni, kada ku bari araba ni daku……” Æ™anÆ™ameta angel tayi ajikinta, Giant É—in ya damÆ™i qugun Parveen, ta Æ™arfi ya fisgeta daga Jikin angel ya É—aura ta saman kafadarshi Ya juya Cikin zafin nama Ya haura saman benan, Sauran Giants É—in guda Biyu dake a É—auke da rubina da Deeja suna abakin Æ™ofar fita suna jiran Æ™arasowar shi, yana daga cikin dokar aikinsu Basa tafiya dole sai suna atare da juna, wani irin jiri ne Ya rufe idanuwan angel, anan Æ™asa ta kwanta idanuwanta na zubar da hawaye, Suna Jiyo sautin muryar parveen cikin shessheÆ™ar kuka take faÉ—in cewa”Angel dan Allah kiyi mini addu’a, Kuma idan gobe ba’a dawo dani ba, ku ajiye mini abinci na”

Wannan maganar ta parveen ta yi matuÆ™ar kashe masu sassan Jikinsu, A nan suka wuni zuÆ™unne suna kuka, Mutun biyu ne acikinsu basu zubar da kwalla ba, Danish da Haris Saboda sun sa ma ransu cewa Za’a dawo masu da Æ´an uwansu ne, duk da haka sun yi matuÆ™ar damuwa da halin da su Parveen suka shiga, Na raÉ—aÉ—in ciwo ga kuma maraicin da zasu Yi na raba su da Æ´an uwansu,

Tsohuwa dake a tsaye Bakin ƙopar ɗakinta, Ko a ha6ar xaninta bata sanya damuwar Halin da yaran suka shiga ba, Sai da taga Sun sassauta da yin kukan tukunna Ta dogara sanda ta nufi inda suke a zuƙunne ta tsaya tana kallon fuskokinsu da suka jiƙe sharkaf da hawaye

“Idan ku ka yi haÆ™uri, Za’a dawo maku da Æ´an uwanku ne da zarar sun samu warakar Lalurar dake damun su, Kuka bazai ta6a yi maku maganin komai ba, Illa iyaka ya Æ™ara haddasa maku wata damuwar, Shawarar da zan baku shi ne, Ku sanyawa zuciyar ku haÆ™uri da juriyar rashin Æ´an uwanku, kada ku cusawa kanku damu…….” bata Æ™arasa maganar ba angel ta yunÆ™ura ta miÆ™e zaune idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, muryarta a zafafe ta soma magana

“Har kina da bakin zuwa ki bamu haÆ™uri akan mu yi shiru mu daina kuka? Wlh tun da nake 6anta6a ganin Muguwar mace azzaluma irinki ba!

Ɗan zaro ido tsohuwa tayi da kwala kwalan idanuwanta tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa,

“Kince ke uwa ce agare su, meyasa da naje na faÉ—a maki cewa Cikinsu na ciwo, baki zo kin duba jikin su ba? Koda sannu ne kiyi masu Amatsayinki na mahaifiyarsu, Amma bakiyi hakan ba, sai dai wasu Æ™attai suka zo suka É—auke su da sunan zasu duba lafiyarsu, bayan ke ya dace kiyi hakan a matsayinki na Ƴa mace, duk da bani da ilmi akan abun amma auntyna ta ta6a faÉ—a mini cewa Menstruation lalura ce ta mata da suke yi a kowani wata, zaki iya taimaka masu idan kinso basai an kaisu wani wuri ba……” cikin shessheÆ™ar kuka takai Æ™arshen maganar, Su batul duk sunyi zugudum suna sauraronsu,

“Banta6a jin tausayin wani É—an adam ba aduniyar nan ba, kamar wadannan bayin Allah, wai su haka rayuwarsu zata Æ™are? A tagayyare basu da me share masu hawayensu, basu da kafaÉ—ar da zasu É—aura kansu akai suyi kuka a lallashe su, Wannan wata irin Makauniyar Æ™addara ce? Tayi tambayar idonta akan tsohuwa dake a tsaye ruÆ™e da sanda, baka Iya gane awani hali take Ciki, domin kuwa fuskarta a haushine take, tsufanta da muninta sun Æ™ara bayyana

Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta
“Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaÉ—ai kika sa agaba, wlh rantsuwar É—an musulmi idan har ba’a dawo mana da Æ´an uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne’

Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana

“Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara….” a ruÉ—e angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta,

Cigaba da magana tsohuwa tayi”ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAÆŠANÆŠA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun Æ™addara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara,” tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura Æ™ofar É—akinta ta shige taja Æ™opa ta garÆ™ame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruÉ—ani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun Æ™addara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za’ayi dasu? danginsu basa Æ™aunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa?

Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel,

“Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa “ALLAH”

biji biji take gani acikin idanuwanta, daÆ™yar ta samu ta iya zuÆ™unna agabansu, Muryarta a disashe tace”kuyi haÆ™uri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, ” miÆ™ewa kowannansu Yayi, Suna jan Æ™afa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su É—aya bayan É—aya tayi masu addu’a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu’a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata É—azu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife Æ™asa, cikin shessheÆ™ar kuka angel ta furta “NAYI DANA SANI” Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiÉ—arta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta É—aga sama Ta soma yi masu addu’o’i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu,

A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu’a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen,

A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye,

Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita,

Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish,

Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi”Danish” a hankali ya buÉ—e idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta,

“Ka tashi lafiya”? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta É—an sauke kafin tace” Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa” ya amsa mata da toh,

Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace

“Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse Æ™opa ta ciki na sanya jam lock”? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, É—an tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips É—insa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa,

“Ba ka yi mini kama da maÆ™aryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet É—in sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko’ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet É—in, wanda nayi Imanin bata ainihin Æ™opar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba” Cikin tuhuma take yi mashi maganar,

muryar shi a sanyaye yace” Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet É—in shine kaÉ—ai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba”

Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne,

Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi,

Mayar mata da martanin murmushin yayi Calmly yace” kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne”?

Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta Æ™ara da cewa”na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa”

Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata

“Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alÆ™warin hakan,” É—agowa tayi tare da kallon shi,
“Taya akai kasan cewa zasu dawo”? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi,

Murmushin gefen fuska ya É—anyi, Can kuma yace”Kin manta anzo an É—auke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne”

Girgiza kai angel tayi”amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an Æ™ara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an É—auke ka daga Cikin mu”? ta jefa mashi tambayar,

“Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka É—auke ni bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene,”

Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa,

MiÆ™a hannu danish yayi tare da ruÆ™o nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata”angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone……..” kalaman shi ba Æ™aramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na É—an wani lokaci,

Æ™ayataccen murmushi ta saki tana motsa lips É—inta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana É—aya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra’ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata Æ™ara bari faÉ—a ya haÉ—a su ba, Shi ma haris É—in bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta,

“What are u thinking about”? Jin voice É—in danish yasa ta É—anyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta,

” baki bani amsa ba,” ya tambaya yana sauraranta,

“Dama ni ban ruÆ™e ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar Æ´an uwana ne jini,” ba Æ™aramin daÉ—in kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes É—inshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne,

Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba,

Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu,

Sun É—auki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna,”

“Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa”? Batool ce tayi mata tambayar,

“Taya xan iya runtsawa, alhalin Æ´an uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne…..” kukane ya ciyota, da sauri ta duÆ™ar da kanta Æ™asa, sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata Æ™ara karya masu zuciya ne, sai dai duk Æ™oÆ™arinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da É—aukar su parveen da akayi ba,

Dafa kafaÉ—unta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace”pls angel, u should stop shedding your tears, kina Æ™ara sanya mana damuwa ne, ke da kike Æ™arfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan”? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar,

Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba, bata fahimtar me suke tattaunawa,

Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace “Nadaina batool, bazan Æ™ara ba, kema kada kiyi kuka” jinjina kai batool tayi”Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haÉ—a hannu wurin taimaka ma sauran Æ´an uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu Æ™arfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani,

Ga Link na Tiktok Ɗina kuyi following dina, Zan yi posting na vedio din Prisners da kowa na kurkuku👇 facebook page kuma Hafsat Bature

tiktok.com/@boss_bature

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button