Uncategorized

Abin Farin ciki: An saki sakamakon jarabawar Neco a jihar Kano kowa ya je ya duba

 Tun kusan sati biyu da suka gabata Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar dalibai sai dai bata saki ta jihar Kano da wasu jahohi dake arewacin Nigeriya ba, to amman cikin ikon Allah sai hukumar ta sanar da sakin jarabawar a jiya.

 Hakan ya biyo bayan kokarin da gwamnatin jihar ta yi na daidaita kudaden jarabawar NECO.

 Kwamishinan Ilimi na jihar, Muhammad Sanusi-Kiru ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar, Aliyu Yusuf ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a jihar.

ALSO READ: Yadda za ku duba sakamakon jarabawar ta Neco

 Sanusi-Kiru ya ce fitar da sakamakon zai baiwa daliban damar samun damar shiga Jami’o’i da sauran manyan makarantun da suka zaba.

 Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su sanya dabi’ar nuna godiya ga abin da gwamnati ke yi duba da irin kalubalen da ake fuskanta kan karancin albarkatun da take da su.

 Don haka kwamishinan ya yabawa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jiha, Hon Murtala Sule Garo da dukkan shuwagabannin kananan hukumomi 44 bisa goyon bayan da suka bayar ta wannan hanyar.

 Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na ci gaba da tallafawa fannin ilimi.

 Idan dai ba a manta ba hukumar jarabawar ta hana sakamakon dalibai sama da 80,000 a jihar saboda gazawar gwamnatin jihar Kano wajen cire basussuka.

Back to top button