Hausa novels

Ruwan Zuma Page 43 Hausa Novel

(43)   “Suwaiba kece?” Fad’in Ummii bayan ta zauna a kan kujera da taimakon Madu. “Nice Kalti.” Kuka Ummii ta fara yi yayin da Ammi ta tako ta zauna a gefenta itama tana kukan. “Ina kika shiga ko sau d’aya baki waiwayi gida ba?” Shiru Ammi tayi dalilin kukan daya ci k’arfinta, Madu dake zaune a gefe sai yanzu ya gane wacece ita. Zuciyarshi ta buga da k’arfin gaske shima ya zauna a gefensu yana kallonsu yana mamakin wannan al’amari. Can kuma ya d’auki waya ya kira Laila amma wayarta a kashe take, hakan yasa dole ya kira Mas’ud yace mishi ya d’auko Laila ta zo taga abunda taurin kai ya haifar mata. “Haydar d’anki ne na cikinki Suwaiba?” Ummii ce ta yi wannan tambayar tana share hawayen fuskarta. “D’ana ne na cikina Kalti. Wallahi d’ana ne.” “Wannan aure an yishi cikin rashin sani cikin duhu. Kash!” Fad’in Ummii tana kama kanta.  Mas’ud yana shiga asibitin ya hango Laila na tahowa yayi saurin yin kanta ranshi a 6ace ya fara magana, “Wallahi kin bani mamaki, duk k’ok’arin da mutumin nan yake yi a kanki baki gani ba sai da kika saka mishi da mummunan abu, you are my sister amma wannan karon I hate what you did. Kuma Allah ba zai barki ba saboda kin zalunceshi Kalti.”  Laila kallonshi tayi sau d’aya kana taci gaba da tafiyarta ganin hankalin mutane na komawa kansu, Mas’ud kuma fad’a ya dinga mata yana bin bayanta har suka isa bakin motocinsu. Ganin ko sauraron shi bata yi yasa a zuciye ya fad’a mata sak’on Madu, “Ummii tana nemanki yanzu-yanzu a gida.” Bai jira me zata ce ba ya shige motarshi ya barta a gurin yana jin zafi a zuciyarshi don ya lura babu ko d’igon nadama a fuskarta. Bai san yaushe yayarsa ta zama muguwa haka ba kuma wannan karon zai nuna mata laifinta ko da hakan zai jawo mummunan fad’a tsakaninsu.  Haydar ne ya fara isa gidan Madu ya kira Ammi a waya, jin muryarta yayi tana kuka tana cewa, “Ka shigo cikin gidan.”  Nan take zuciyarshi ta bashi cewa had’uwa tayi da Madu ya mata rashin mutunci, ai nan take fuskarsa ta k’ara had’ewa da tsananin fushi yana ayyana me zai yiwa Madu.  Da sallama ya shiga falon ya samu Amminshi zaune a k’asa  kusa da Ummii tana share hawayen fuskarta, nan ya tabbatar da abunda yake zargi domin shima Madun gashi can a gefe yana kallonsu fuskarsa babu yabo babu fallasa. “Me ka yiwa mahaifiyata?” Shine tambayar da Haydar ya fara yi yana shigowa yayi kan Madu. “Me zai sa in yiwa mahaifiyarka wani abu?” Madu shima ya mayar mishi da tambaya yana mamakin tsaurin idon yaron. “Ali zo nan.” Fad’in Ammi tana yafutoshi.   Wani mugun kallo ya aikawa Madu irin ‘bamu gama ba’, sannan ya matsa gurin Ammi ya durk’usa yana tambayarta me aka mata, ya ma manta a gaban surukarsa yake domin ya k’i jinin abunda zai ta6ata don a yau ya gane cewa babu mai sonshi sai ita kad’ai.  Ummii kuma kallon Haydar kawai take yi tunda ya shigo, sai yanzu ta gane dalilin da yasa tun farkon ganinta dashi bata kushesa ba, illah ma d’aura Laila da tayi akan mishi biyayya, ashe jikanta ne jininta.  “Babu abunda aka mini Haydar, ga dangina da kake son sanin ina suke.” “Ban gane ba Ammi.” Ya fad’i hakan yana zama mai kyau cikin rashin fahimta. “Kalti Falmata k’anwar Babana ne, a gabanta na tashi tun kafin tayi aure, kamar mahaifiyata na d’auketa saboda irin so da kuma kulawan dana samu a gurinta.”  “Ammi me kike nufi? Kina nufin sune dangin da kike gudu kuka kika k’i fad’a mini?”  Gyad’a mishi kai tayi wanda hakan yasa idanunshi tara hawaye ya d’aga ido ya dubi Ummii yace, “Ke dangin Ammi ce?” “Eh, ni Kakar ce Haydar.” Ta bashi amsa tana shafa kanshi cike da tausayinshi don tasan ba zai ji dad’in labarin mahaifiyarsa ba ko kad’an. “Ina mahaifina yake?” Ya k’ara wata tambayar yana kallon Ummii don ya lura ita baza ta 6oye mishi ba.  Ummii ta kalli Ammi wacce nan take kanta yayi k’asa tace, “Ban san waye mahaifinka ba Haydar, amma mune dangin mahaifiyarka gaba da baya.” “Ammi ina mahaifina?” Ya juyar da kanshi gareta yana tambayarta abunda ya rantse bazai sake tambaya ba. “Mu bar maganar ba yanzu ba.” Tace dashi ta k’i had’a ido dashi.  A nan ne Mas’ud ya shigo tare da Laila suka tsaya suna kallon ikon Allah ganin Ammi wacce ke share hawaye ga Haydar zaune kusa da Ummii. Guri suka samu suka zauna suka fara gaishe da ‘yan falon ba tare da sun tambayi me yake faruwa ba saboda sun d’auka akan zubar da cikin da Laila tayi ne.  Madu ne ya fara magana yace, “Laila kin ta6a jin labarin ‘yar Kaala Abdi wacce ta bar gida?” “Na sani, meyasa kake tambayana?” Ta amsa cikin rashin fahimtar inda maganar tashi zata dosa. “To gata nan itace Uwar mijinki, d’anta kika aura.” Ya fad’i hakan kamar mai karanta jarida babu alamar emotion a muryarsa. Nan Mas’ud da Laila suka mayar da dubansu ga Ammi tare da Haydar, sai yanzu suka ga dalilinsu na zama kusa da Ummii. “Ummii da gaske ne wai itace?” Mas’ud ne ya samu k’arfin halin magana Laila kam kasa cewa komai tayi sai bakinta da yake motsi alamar addu’a take yi. “Haka ne. Jininku ce ‘yar uwarku, Haydar kuma d’a yake a gurinku.” Madu murmusawa yayi yana kallon yanda Laila ta daburce tana had’a d’aya da biyu suna bata amsar da baza taso furtawa ba, wato mijinta shege ne. “This escalates quickly.” Fad’in Mas’ud yana kallon ‘yan falon kamar bai gaskata abunda yake faruwa ba, wannan wani irin abu ne kamar a film? “Ammi tunda ba zaki sanar dani waye mahaifina ba ki fad’a mini dalilin da yasa kika guji gida da kuma danginki. Me suka miki? Sannan meyasa kika kasa komawa gida duk tsawon wannan lokacin alhali kin san inda suke? Meyasa kika rabani dasu?” “Saboda ko na koma ba zasu k’ar6eni ba.” Ta bashi amsa cike da nadama. “What really happened? Ammi don girman Allah wannan karon karki 6oye mini komai tunda da alama kowa yasan labarinki nine ban sani ba.” Ya fad’i hakan with desperation in his voice. “Baza ka so jin labarina ba Haydar, k’azantar dake cikinta da yawa yake.” Ta fad’i hakan itama cikin rok’onsa.  “Suwaiba ki sanar dashi saboda babu amfanin 6oyewan.” Fad’in Ummii tana dafa kafad’unta. Ammi ta dubi Haydar taga hankalinshi gabad’aya na kanta cikin son jin labarinta. Share hawayen fuskarta tayi ta dubi Ummii tayi magana ta yarensu wanda Haydar bai ji ba, hakan kuma k’ara masa takaici yayi amma bai ce komai ba. Sai ji yayi Ummii ta fara magana, “Suwaiba itace ‘ya ta farko a gurin Kaala Abdi wanda mahaifiyarta ta rasu gurin haihuwarta. Ko da Kaala Abdi ya k’ara aure sai ya kasance bai k’ara haifan d’iya mace ba sai maza zallah. An haifeta lokacin da nake da shekaru tara, da yake a cikin gidanmu yayana yake, sai ya kasance kullum tana hannuna ina kula da ita tunda rainonta ya dawo gurin mahaifiyarmu. Zan yi mata wanka, in saka mata kwalli sannan in goyeta muyi ta zaga gidanmu ana cewa Suwaiba d’iyata ce. Bani kad’ai ba, hatta Kaala Abdi ya d’auki son duniya ya kwallafa mata ba tare daya san cewa ita ce kad’ai ‘ya mace da zai haifa ba. Hakan yasa Suwaiba ta taso cikin so da kulawa matuk’a wanda ya kai ga kowa yayi dana sanin aikata hakan. Lokacin data kai shekara takwas a lokacin halayyanta ya fara canjawa dalilin yaba kyawunta da ake yi ga mutanen gidanmu har ma dana waje. Sannan ko a cikin yara tayi fad’a da wani nice mai bata gaskiya koda kuwa itace bata da gaskiya saboda k’aunar da nake mata. Da ta fara girma sai tayi wanka tayi kwalliya ta samu guri ta zauna kowa yazo sai ya yabata, hakan yasa da naga kin fara irin haka naji tsoron ko kema zaki zama kamarta ce Laila, nayi tsammanin bada hannu da nayi wajen gur6acewar tarbiyyar Suwaiba shi zai dawo kan zuriyata. Hakan yasa na zareki a jikina, a zatona duk ranar da kika 6ace bazan shiga halin da Kaala Abdi ya shiga ba bayan 6acewar ‘yarsa.” Ummii ta k’arisa maganan tana kallon Laila wacce idanunta ya tara hawaye dalilin an mata hukunci akan abunda bata ma san tayi ba.  Ummii taci gaba, “Tana da shekara goma ta fara tara samari a k’ofar gida wanda hakan yasa kowa ya farga aka hanata tsayuwa dasu dalilin k’ank’antan shekaruta. Sai dai hakan bai mata dad’i ba dalilin an hanata abunda take so wanda a daa duk abunda take so ake yi mata. Takurar da yayi yawa sai ta fara fita ba tare da an sani ba, hakan kuma yaci gaba da faruwa har ta kai shekara sha uku sannan magana ta fito fili kan tana zuwa d’akin samari suna amfani da ita suna bata kud’i. A yinin bikina aka kamata tare da wani saurayi wanda uban yaron ne ya kawosu dukansu har gaban Kaala Abdi yace a musu hukunci yana kuka. A ranar an ga tashin hankali domin Kaala Abdi duka ya mata sai data suma ya farfasa mata jiki. Shima saurayin aka mishi bulala d’ari kamar yanda shari’ar musulunci ta tanadar. Bikin da aka k’arisashi babu armashi kenan aka kaini gidana nan cikin unguwarmu, sai dai gaba d’aya hankalina yana kan Suwaiba saboda a lokacin da ake mata bulala sai da aka rik’eni. Kwana uku da haka Kaala Abdi ya aika gidan su yaron kan cewa ya basu aurenta idan ta gama istibra’i za’a d’aura musu aure. Duk yanda na kai ga son zuwa gida in dubo jikinta ba’a barni ba dalilin al’ada irin tamu ta hana Amare fita daga yin aure, sai dai kullum k’annena na zuwa suna fad’a mini halin da take ciki. Sati d’aya da aurena aka kawo mini labarin cewa ta gudu an nemeta an rasa.” Ummii ta share hawayen fuskarta taci gaba, “Duk laifina ne da nake kareta idan tayi laifi za’a mata hukunci. Kuma nayi dana sani ba kad’an ba shiyasa kaf yarana ban nuna musu wannan son ba gudun kar hakan ya faru dasu, duk da cewa wani lokacin k’addara ce daga Allah ba don iyaye sun kasa bawa yaran tarbiyya nagari ba. Kaala Abdi sai daya samu cutar shanyewar gefen jiki bayan guduwanta, sannan ya hana kowa cigiyarta yace a bari duniya zata koya mata hankali. Har sai dana haifi Mas’ud sannan Allah ya bashi lafiya, cigiyarta kuma munyi a 6oye har muka hak’ura dalilin ko sau d’aya ba’a ji wani yace ya ganta ba sai yau data bayyana don kanta.”  Tsit d’akin yayi ana kallon Haydar wanda yake zubar da hawaye yana kallon Amminshi tamkar wata halitta yake gani ba ita ba. “Hakane Ammi?”   Gyad’a mishi kai tayi yayi saurin sunkuyar da kanshi yana 6oye fuskarshi daga garesu. Bai yi tsammanin labarin haka bane, ya d’auka kurciya aka mata, ya d’auka korarta aka yi daga gida ko kuma a gidan marayu ta girma ta gudu. Bai yi expecting ita da kanta ta gudu ta barsu ba, sannan bai yi tsammanin zata aikata zina ba. Kenan shi shege ne, dalilin da yasa bata son fad’a mishi kenan?  “Na aikata laifi mafi muni a rayuwata Haydar, hakan yasa abunda nayi yake bibiyata har na so rasa raina tare da naka a lokaci daban-daban. Kuma yanzun ma ba tsira nayi ba, ina tsoron sanar da kai ka nemesu su kashe mini kai.” “Ki fad’a mini.” Shine abunda ya fad’a yana d’ago kanshi yana share hawayen fuskarsa cikin dakewa.  Laila dake gefe nan take ta fara jin tausayinshi domin babu wanda zai so yaji shi shege ne. Kenan itama shegen ta aura, kuma a matsayin d’anta yake tunda Ammi ‘yar kawunsu ce (cousin). Ji tayi kamar ta isa gurinshi ta rarrasheshi, ashe shi d’in wani sashe ne na jikinta da gaske ba gamuwar jini bane kad’ai. “Ban san ya aka yi na tsinci kaina a halin da nake ciki ba, kawai na san da cewa a gida kowa yana sona, k’anin matar Babana ne ya fara nuna mini hanyar lalata tun ina k’arama ba tare daya bari na fad’awa kowa ba. A haka na tashi cikin gur6ataccen rayuwa ba tare da nayi tunanin abunda nake aikatawa babu kyau ba, bayan kowa ya sani ni da kaina na yanke shawarar gudu da naji labarin za’a had’amu aure da wanda aka gannì tare dashi. Kud’in da nake tarawa na kwashe babu wanda ya lura na tafi tasha na shiga mota, saboda gudun kar a sameni yasa ban tsaya a gari d’aya ba nayi ta hawa mota ina yawo har kud’ina ya k’are a Pot Harcourt. A nan ne tsoro ya shigeni dalilin bani da gurin kwana sannan ban san ina zan je ba. Wani gurin sayar da abinci naje na raku6e a bayan ginin ina kallon mutane masu shiga da fice. Sai da duhu ya fara yi na k’ara tsorita, dalilin nasan bazan kwana da rai ba muddin na kwana a tasha, hakan yasa na fara kuka wanda ya k’ara jawo hankalin mutane kaina. Kamar daga sama naga wata mata musulma tana mini magana da hausa wanda bana ji sosai sai yarenmu na Shuwa kad’ai. Jin tayi yaren Shuwa yasa nayi saurin tashi na isa gurinta ina fad’a mata damuwata tare da neman ta taimakeni tun kafin in fahimci me take son fad’a mini. Sai dana gama magana ta nuna mini so take yi in tashi in bar gurin saboda ina tara mata jama’a wajen sana’arta, A nan na gane ita ce mai gurin. Cigaba da rok’anta nayi kan cewa zan mata kowanni irin aiki ne in ta bani gurin kwana. Da kyar ta yarda a kan cewa zata taimakeni, a madafinsu na zauna tare da sauran ma’aikatanta har lokacin tashinsu yayi suka kulle gurin muka dawo gidanta wanda gida ne na haya mai d’auke da d’Akuya k’anana ashirin da biyu, kuma duk gidan matane. Ban jima tare da ita ba na fad’a rayuwar da kowa yake yi a gidan nima aka bani d’akina daban ina biyan haya idan maza sun biyani. Babu buk’atar in fad’i duk abunda ya faru a wannan zaman amma duk abunda yake faruwa da karuwa wacce ta bar gidansu ya faru dani. Mata sun dakeni idan na kwace musu samarinsu, maza sun dakeni idan na nemi rabuwa dasu ko fad’a ta shiga tsakaninmu, wulakanci na rayuwa babu wanda ban gani ba amma hakan bai saka na koma gida ba. Shekarata sha biyu a pot harcourt na dawo Kano dalilin wani Alhaji dana biyo wanda tun had’uwarmu naji ina sonshi. A farkon had’uwarmu shima ya nuna yana sona amma da aure dalilin shi baya bin karuwai, dama abokinshi ya rako d’aukan mace a gidanmu ya had’u dani. Ganin na k’i yarda da batunshi yasa ya biye mini muka fad’a ga halaka. Bayan sun gama aikin daya kawosu pot harcourt sai ya nemi in bishi zuwa Kano, a nan ya nema mini gida na zama tamkar matarshi duk da cewa ya so muyi aure tun farkon had’uwarmu amma na k’i. Watana uku a Kano watarana yazo gidana cikin gaggawa yace in tattara kayana in tafi Abuja matarshi ta samu labarinmu, ban k’ara awa d’aya ba na bar gari na tafi Abuja zuwa wani gidansa da yasa wani ma’aikacinsa ya kaini. Sai da nayi sati uku bai zo ba wanda har na fara tsoron ko matarshi ta kasheshi a yanda yake bani labarin tana da zafin kishi, hakan yana d’aya daga cikin abunda yasa yake son aurena domin idan ni matarshi ce duk kishinta zata hak’ura ta barmu. A ranar daya dawo na lura da karaya a hannunshi yake fad’a mini ban jima da tafiya ba matarshi ta shigo gidan suka yi fad’a har ta kwad’a mishi Tv ta gurd’a mishi hannu. A nan yake rok’ana kan in amince in aureshi domin babu wanda ya bashi gaskiya akan abunda ya faru sannan mutuncinsa na zubewa a idon jama’a. Nice mace d’aya daya ta6a nema sannan bayana ban ta6a ji ko ganin ya nemi wata mace ba. Da na nuna rashin amincewata sai ya nemi mu rabu, son da nake mishi yasa naji tsoron rabuwa dashi domin ko na rabu dashi zuciyata baza ta barni in zauna lafiya ba, hakan yasa na amince da aurensa.” Dakatawa Ammi tayi kana taci gaba, “A ranar daya zo ya koma Kano akan sai na gama Istibra’i kafin a d’aura mana aure. Wata uku da haka ya dawo ya nemi in koma gidanmu ya nemi aurena a can amma nak’i yarda, hakan yasa aka d’aura mana aure a nan Abuja ba tare da dangina ba. Sai a wannan lokacin na gane cewa rayuwar da nayi a baya bata da fa’ida, dalilin kwanciyar hankalin dana samu kaina a ciki a matsayina na matar aure, Alhaji yana nuna mini so na hak’ik’a wanda ni kaina na sani. A wannan zaman ne na samu cikinka Ali, wallahi kai ba shege bane. Farin cikin da muka yi a ranar dana gane ina d’auke da juna biyu ba’a misaltawa dalilin Babanka bashi da ‘yaya da yawa. Cikina yana munzalin wata bakwai Babanka yaje Kano akan zai dawo bayan sati biyu, washe gari ina kwance naji ana kwankwasa k’ofa maigadi ya bud’e, daga nan ban k’ara jin motsi ba sai ji nayi ana kwankwasa k’ofar falo. Ban kawo komai a raina ba saboda makwabtana suna shigowa nima kuma ina zuwa musu. Ina bud’ewa naji naushi a fuskata wacce tasa na fad’i tsabar gigicewan da nayi. “Munafuka algunguma ashe da gaske har ciki kika d’auka.” Shine abunda na fara ji a lokacin da nake k’ok’arin dawowa cikin hayyacina. Maza biyu na gani tsaye a kaina gefensu kuma mace ce wacce na tabbatar matar Alhaji ce. Daga nan duka na dinga ji ta ko’ina amma na dunk’ule guri d’aya gudun kar a bugi cikina, duk kuka da ihun da nake yi kuwa babu wanda ya kawo mini d’auki saboda babu mai jina. Sai da suka jikk’atani sannan tasa suka d’aureni a jikin kujera tare da toshe mini baki don in daina rok’arsu gafara. Ina gani ta d’auko wuka na fara girgiza kaina ina hawaye, tsaga mini k’afafuwa tayi da wuk’an jini na zuba a jikina sannan daga baya tace zata yanka cikina ta ciro d’an cikina. A nan ne ta cire mini tsumman da suka toshe bakina na fara bata hak’uri ina rok’anta kar ta kasheni ko d’an cikina. A nan ta bani za6in in 6ace daga rayuwar mijinta ko kuma ta kasheni a wannan lokacin, banyi k’asa a guiwa ba na yarda da cewa zan tafi saboda nasan Wallahi zata aikata kasheni. A gabansu na had’a kayana na fita daga gidan, daga nan kuma Zaria nayi ina jinyar jikina a wani hotel. K’udin hannuna yana k’arewa na fito gari neman aiki har na samu wanke-wanke da shara a wani gida saboda bana fatan sake komawa rayuwata ta baya. A haka na haifeka na saka maka sunan Aliyu Haydar ba tare da sunan uba ba, kana da shekara d’aya maigidan da muke zaune a gidansa ya rasu wanda hakan yasa na rasa aikina na dawo ina yawon neman aiki da gurin kwana. A nan ne kuma na had’u da wannan abokin Alhaji daya had’amu ya fad’a mini cewa Alhaji yana nemana in zo ya mayar dani gida. Tuna irin kisan gillan da matarshi zata mana yasa na fad’a masa zan shirya kayana gobe mu koma. A ranar ban kwana a Zari’a ba sai Lagos. A can naci gaba da zama ina talle a bakin titi bayan na samu gida a Squatters wani unguwa na kazo nazo. A Lagos na saka Haydar a makaranta har zuwa lokacin da na gaji da zaman garin naso komawa arewa dalilin fyade da wani ubangidana ya mini. Garin neman kud’in mota na had’u da Alhaji a yayin da yake mik’awa Haydar kud’i bayan mun yi k’aryar cewa ni makauniya ce. Ina ganinshi na ja Ali muka gudu muka 6ace masa, daga nan kuma muka koma Jos da zama har Ali ya gama secondary school. Duk da cewa bana fita cikin gari in ba ya kama dole ba amma sai naji kamar tsawon zaman da nayi a Jos zai sa a gane inda nake. Hakan yasa rana d’aya muka bar garin muka dawo Kano saboda nasan Alhaji bazai ta6a tsammanin zan dawo cikinta ba. Sannan duk nemana da zai yi ba zaiyi a cikin Kano ba. A nan na sayi gidan da nake ciki na fara tallan k’osai da doya a bakin hanya har Ali ya gama university, kuma ya had’u da Laila ya aureta ba tare da sun san cewa su ‘yan uwan juna bane. Wannan shine rayuwata a tak’aice bayan na tafka kuskuren da bana yiwa ko mak’iyina fatan irinsa.” Jikin kowa a d’akin yayi sanyi musamman Haydar da bai ta6a kawowa a ranshi cewa mahaifiyarshi ta ta6a rayuwar karuwanci ba, ko a daa da yake tambayarta cewa ko shi shege ne bai sa a ranshi ita ta kai kanta ba, yafi zaton fyad’e aka mata aka koreta a gida shiyasa bata son fad’a mishi. Ashe labarin rayuwarta yayi munin da har abada ba zai so ya k’ara zama a labarta mishi ba.  Ummii ce ta fara magana da cewa, “Tun farko kin yi kuskuren barin gidanku, sai dai za’a alak’anta hakan da yarinta da kuma sangartar da kike taso a cikinta. Allah ya yafe miki kura-kuranki ya kuma gafarta miki. Sai dai da tun wancan lokacin da kika tuba kin waiwayi gida, wallahi babu mai korarki ko da kuwa da cikin shege kika dawo Suwaiba. Wannan labarin data bayar kar wani ya fitar dashi, duk wanda ya tambaya a fad’a mishi yawace-yawacen da tayi na garurruwa ba tare da an labarta k’azantar da yake ciki ba, sai kuma labarin aurenta da kuma abunda ya sameta har ta bar mijin don kare kanta da d’an cikinta. Madu kira mini Kaala Abdi in sanar dashi wannan kyakkyawan labarin.” Ummii ta gama maganar fuskarta cike da tsantsan farin ciki. “Don Allah karki fad’a mishi zai kasheni idan ya ganni.” Fad’in Ammi cikin tsoro. “Sanin daa kika yiwa Babanki, amma daga baya shi da kanshi ya saka cigiyarki, kuma har rana mai kamar ta yau bakinshi bai daina furta sunanki ba. Girma ya zo masa Suwaiba kuma yayi nadamar rashin nemanki da wuri da yayi.”  Haydar daya lura hankalin kowa ya koma kan Ammi ya mik’e ya fice daga falon, Laila ce kad’ai taga fitansa tayi saurin bin bayanshi tana kiran sunanshi amma bai waiwayo ba har ya fita daga gidan bayan ya jefar da key d’in motarsa a k’asa. Yana zuwa bakin k’ofar gidan ya tsaya yana kallon bakin titi. A nan Laila ta sameshi tana cewa, “Ina zaka je Haydar?” Hannu ya mik’ar mai achaba ya tsaya kana ya dubeta yace, “Babu amfanin kasancewata tare daku, sannan nasan zaku kula da Ammi. A yau na rasa wani part na rayuwata sannan na samu wani sashe na rayuwata wato sanin wanene ni. Kuma nasan a yanzu da kika ji labarin mahaifiyata zaki fi tsanar had’a zuriya dani, don haka ni Haydar na sakeki.” Yana gama fad’in hakan ya hau acha6a suka tafi y bar Laila a daskare a gurin kafin ta fad’i a k’asa sumammiya.

Mum Fateey 👌

Back to top button