Novel Document

Haske Complete Hausa Novel Free Document

Haske Complete Novel Document By Salma Ahmad Isah

Description/Story:

Haske! Complete Hausa Novel Document

Written By Salma Ahmad Isah 

 

Description

*Shimfiɗa…*
Akwai wasu ƙaddarorin da kan zo da wani irin duhu, wanda zai mamaye rayuwar ɗan adam, ta yanda ko da tafin hannunsa ba zai iya gani a cikin wannan duhun ba.
Kuma an ce HASKE ne kaɗai ke maganin duhu.
Ɗan adam kan shiga halin neman HASKEn da zai yi amfani da shi wurin gusar da wannan duhun dake bibiyar rayuwarsa.
Shin menene duhun?
Wasu tarin ƙaddarori ne waɗannan da ke tafe da matsanancin duhu?.
Shin a ina wannan HASKEn yake?
Sannan kuma menene wannan HASKEn?

*Shekara ta 2000.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*01:40 Na dare.*
Wata matace ke tafe cikin sassarfa, sanye take da atamafa kalar ruwan goro, wanda akewa laƙabi da me dalma. Hannunta riƙe da wani abu, wanda ke duƙunƙune cikin zani.
Kanta ta ɗan ɗaga ta kalli sararin samaniya, ta ga yanda hadari yake gangamuwa, ga kuma iska me ƙarfi da aka fara, sai cida da tsawa da ake har da walƙiya.
Ƙafafuwanta ne suka taka birki, a lokacin da ta kawo gaɓar ruwan shiga yankin Makoko. Tarin kwale-kwalen dake bakin ruwan ta kalla, sannan ta kalli abun da ke hannunta. Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tana faɗin.
“Ba zan iya aikata haka ba!”
Sai kuma ta shiga juyawa tana kallon kewayen wurin da take, babu kowa sai gilmawar karnuka. haka ta nufi wani kwale-kwale dake cikin tarin kwale-kwalen dake wurin, ta shiga cikin kwale-kwalen ba tare da tsoro ba, ta tsuganna tana aje abinda ke hannunta.
Kafin a hankali ta kai hannunta kan zanin, ta buɗe shi, nan take fuskar jaririya sabuwar haihuwa ta bayyana, don da alama yanzu ta zo duniya, saboda ko jinin haihuwarta bai bushe daga jikinta ba. Fuskar yarinyar ta ƙara rufewa da zanin, ta ɗora wata sarƙar ƙafa a kan zanin. Sannan ta miƙe ta fita daga cikin kwale-kwalen. Ta dawo ta bayansa, ta shiga turashi cikin ruwan, har ta samu nasarar turashi gaba ɗaya. A kan idonta kwale-kwalen ya shiga yawo a kan ruwan. Ya na nufar gidajen katakwayen dake saman ruwan. Sai da ta share ƙwallar idonta tukkuna, sannan ta juya da gudu ta bar wurin.
Ma somin ƙaddarar kenan, a ganinta ta kawo ƙarshen matsalolin, tun da har bata kashe jaririyar ba kamar yanda aka umarceta. Tun da har yarinyar ta yi nesa da gidan, wata ƙila komai zai ƙare.
Tana wannan tunanin ne ba tare da sanin cewa yanzu ne komai zai fara ba, dan kuwa barin yarinyar da ta yi a raye, shi ne musabbabbin buɗewar ƙofofinsu wasu tarin ƙaddararo da ko ita kanta bata san da aukuwarsu ba. Saboda ta kashe maciji ne batare da ta sare kansa ba. A yanzu ne komai zai fara!.
*Present day…*
*Shekara ta 2024.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*06:30 na Safe.*
“Wai Shola ba za ki fito ki tafi wurin aiki ba?… Kin kusa makara fa!”
Cewar wata baƙar mata cikin harshen yarbanci, yayin da take zaune a kan dandaryar katakon da aka kafa ginin gidanta da shi. Daga can cikin ƙaramin ɗakin gidan, muryar wata matashiya ta bata amsa cikin faɗin.
“Takalmi nake sakawa Gigi!”
Matar ta girgiza kanta tana dawo da dubanta kan mijinta dake kwance a gefenta. Fuskarsa ta ɗan leƙa ganin idonsa a rufe, zatonta bacci yake. Amma a zahirin gaskiya ba baccin yake ba, idonsa biyu, tunanin rayuwa ne yasa shi a gaba.
Damuwar halin da gidansa ke ciki ita ce ta sako shi a gaba, ba dan ‘yarsa ɗaya Shola ta duƙufa wurin nemo kuɗin da zasu ci abinci ba, da tuni gidan nasu ya jima da durƙushewa. A da shi ne yake kula da gidan, amma tun bayan iftila’in hatsari da ya afka masa riƙon gidan nasa ya koma hannun ‘yarsa DIYA, wanda sukewa inkiya da SHOLA.
“Ga ni na fito”
Cewar Shola, bayan da ta fito daga tilon ɗakin gidan nasu, a tare suka dubeta, daga Gigin har mijinta da ya buɗe idonsa.
Sanye take cikin wani baƙin wando me faɗi, sai wata farar oxford shirt. Kanta yafe da baƙin gyale. Ƙafafunta sanye da fararen canvas da suka fara jin jiki. Wannan shi ne kayan da ta saba sakawa idan zata je wurin aiki. Fara ce sosai, tana da matsakaicin jiki, idan za ka mata adalci, a kallon farki idan ja mata za ka kirata da bafulatana.
Gigi ta yi murmushi.
“Ga guntuwar shinkafar jiya, ki ɗan taɓa kafin ki tafi”
Shola ta girgiza kanta tana sauƙowa daga kan mattattakalan katakon gidan nasu.
“A’a Gigi, ni idan na ci ku me za ku ci?, kawai ku ci, idan na je wurin aiki zan samu abun da zan ci”
Gigi ta miƙe tana fitowa daga gidan katakon nasu, ta tsaya kusa da Sholan dake kiran sunan Ekene, wanda yake zaune a gidan dake gaban nasu, dan ya zo ya fitar da ita bakin gaɓar ruwan unguwar tasu, dan ba’a zirga-zirga a unguwar sai da kwale-kwale.
“Ya kamata ki taɓa wani abun Shola”
Diya ta juyo ta kalleta.
“Karki damu da ni Gigi, ko biredi ne zan siya na ci, ke de ki kula, na bar miki ɗari biyar a ɗaki, wata ƙila za ku buƙace ta”
Gigi ta yi murmushi tana shafa kanta, tare da saka mata albarka.
“Shola ga ni”
Cewar Ekenen da take kira, bayan da ya fito daga ɗakinsu na katako.
“Na kusa makara Ekene! Ka zo ka fitar da ni”
Ta faɗi tana dubansa. Saida ya ɗaga busassun hannayensa ya yi miƙa, kafin ya sauƙe yana jan wata baƙar tsohuwar singlet da ke rataye a jikin wata gwafa ta gidansu. Sannan ya zagaya ta inda kwale-kwalensa yake, ya cinto shi daga jikin wani ƙarfe da ya ɗaureshi, sannan ya shiga yana ɗaukan marar kwale-kwalen, ya zagayo da shi har zuwa ƙofar gidansu Shola.
Shola ta yi wa Gigi sallama, sannan ta hau kwale-kwalen. Ekene ya fara tuƙasu. Diya ta ci gaba da kallon irin wahalar rayuwar da ake a yankin nasu. Kaf gidajen yankin na katako ne, kuma a saman ruwa suke, dan gaba ɗayan unguwar ma kanta malale take da ruwa, shi yasa ko ina zaka sai ka hau kwale-kwale.
Sosai ake shan wahalar rayuwa a yankin, yawancin mazaunan yankin masu zuwa cirani ne, sai ‘yan gudun hijara, da kuma wanda ƙaddara ta zama silar zuwansu wurin. Yankin nasu ya haɗa tarin ƙabulu, da kuma mutane masu mabanbanta halaye. Kowa ta kansa yake a wurin, babu ruwan wani da rayuwar gidan wani.
“Mun iso!”
Cewar Ekene, sanda suka iso bakin ruwan. A hankali ta miƙe, hannunta riƙe da jakarta. Godiya ta masa tana fita daga kwale-kwalen. Hanya ta yanka ta so ma tafiya. Kafin ta samu isowa tashar bus ɗin da ta saba hawa.
Tafiyar munti 55 ce ta kaita cikin Victoria Island. A wani bus stop suka tsaya, ta fito daga motar bus ɗin, tare da sauran mutanen da suka shiga motar. A ƙafa ta fara takawa, har ta iso Cactus restaurant. Wurin da take aikin raba abinci kenan.
Memakon ta shiga ta ƙofar gaba kamar yanda kowa ke shiga, sai ta zagaya zuwa backyard ɗin ginin restaurant ɗin, ta shiga ta ƙofar kitchen ɗin restaurant ɗin dake baya.
“Shola sai yanzu kika iso?”
Ɗaya daga cikin masu girkin wurin ta tambayeta, yayin da take ƙoƙarin saka apron ɗinta dake rataye a jikin wani hook. Zaren apron ɗin ta gama ɗaurawa tana faɗin.
“Eh Wallahi, sai yanzu na samu isowa”
“Diya! Diya!”
Tun daga nesa suke jiyowa muryar Orisa cikin ƙwalla kiran sunan Diya. Kafin Diyan ta amsa, Orisa ta bayyana a cikin kitchen ɗin.
“Wai ya aka yi kika makara?…. MD ya zo yana ta faɗa!”
Orisa ta faɗa mata cikin harshen yarbanci, Diyah ta saka jakarta cikin wata loka tana amsa mata da.
“Yau ban farka da wuri ba ne!”
“Lalle kam, ke har wani lokacin miƙe ƙafa ki yi bacci kika samu?”
Orisa ta tambaya. Diya ta miƙe tana kallonta.
“Orisa mutum idan be huta ba ai sai ya samu matsala, mu yini muna aiki mu koma gida kuma a ce ba za mu yi bacci ba?”
Orisa ta gyaɗa kanta.
“To yanzu dai ba zan ce za ku tsaya kuna yi ba. Ga wani plate ɗin brown spaghetti can, ki ɗauka ki kai teburi na sha takwas”
Cewar Ifunaya, shugabar sashensu na masu kaiwa abinci.
“Ok”
Diya ta amsa tana raɓa Orisa, plate ɗin brown spaghettin ta ɗauka ta ɗora a kan wani tray me kyau, ta nufi ƙofar shiga cikin restaurant ɗin.
Da misalin ƙarfe tara na dare ta kamo hanyar dawowa gida, bayan da ta tashi daga aiki, hannunta na dama riƙe da wata farar leda. Kafaɗarta kuma saƙale da jakarta. Kasancewar a yankin nasu ba ko ina ne me wutar nepa ba, yasa take amfani da hasken wayarta, wurin haska hanya.
Kuma har zuwa lokacin akwai sawun mutane a waje. Ranta ne ya ɓaci asanda ta iso bakin ruwan yankin nasu, ta iske babu masu yin fito, sai de tarin kwale-kwale a bakin wurin. Ga shi Ekene tsabar talauci da ya masa kanta ko waya ba shi da ita, bare ta kirashi dan ya zo ya fitar da ita.
Haka ta duba ɗaya daga cikin kwale-kwalen da ta san me shi, ta fara tura shi zuwa cikin ruwan, kafin ta ɗale ciki tana ɗaukan marar fiton sa, ta fara tuƙa kwale-kwalen.
Ganin hasken fitila kunne a tsohon gidansu da ya kusa durƙushewa ya sa ta fahimci cewar har yanzu basu kwanta ba. A kan matakalar katakon ƙofar gidan nasu na ƙarshe ta dire,sannan ta ɗaure kwale-kwalen a jikin wani ɗan katako dake jikin gidan nasu.
Sannan ta ɗebi kayanta da ta aje su a cikin jirgin, ta fara taku a hankali, saboda yanayin jimawar da katakon ginin gidan ya yi, ya sa ba sa taku da ƙarfi, dan abu kaɗan ne zai iya sawa ya karye, saboda wasu wuraren ma sun karye ɗin.
A tilon ɗakin nasu ta tarar da su, Gigi na zaune tana wa Papi firfita, sun kunna mosquito coil, sai wata dundurusun fitilarsu mara haske sosai dake ci. Ɗakin babu komai sai wasu lamitssatssun katifu guda biyu, dake yashe a ƙasan ɗakin, sai ‘yan wasu jakkukkunansu na kaya. Dan basu cika tara tarkace a ɗakin ba, gudun kada katakon gidan ya ɓalgace.
“Ba ku yi bacci ba?”
Ta tambaya tana cire viel ɗin jikinta, Gigi ta kalleta tana faɗin.
“Tukunna dai, zafi ne ya hana mu kwanciya”
Diya ta dawo bakin ƙofar ɗakin nasu, ta ɗauke labulen ɗakin, saboda iska ta ɗan samu ta shigo ciki. Ta dawo ta ɗauki kwandon soso da sabulunta, ta fita waje.
Ɗan siririn banɗakin gidan ta shiga, da wani ruwa rabin bokiti ta samu ta ɗan yi wanka, sannan ta fito, jikinta ɗaure da zani, ta dawo ɗakin ta saka wata doguwar rigarta. Sannan ta zauna kusa da Gigi, tana jan ledar da ta shigo da ita.
“Papi na samu kuɗin siyan maganinka, amma ɗaya aka samu, sai a yi maneji”
Papi ya kalli tilon ‘yar tasa, ƙwalla na shirin taruwa a idonsa, a shekarun da suka wuce ya tsinceta, shi ya kula da ita har girmanta, sai ga shi a yau ita ce take kula da shi, rayuwa kenan.
“Allah ya miki albarka Shola”
Ta sunkuyar da kanta tana amsa masa da amin.
“Yau me kuka ci da rana?”
Ta faɗi tana fitar da sauran kayan da ke cikin ledar, Gigi ta aje muficin hannunta tana faɗin.
“Taliya muka ci”

Haske Complete Hausa Novel Free Document

File Name   Haske… Hausa Novel Doc. 
Title   Haske Complete Novel
Author    Salma Ahmad Isah 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    01/01/2025
File Size    200KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦800
Phone No   08130172702
Download Haske Complete Hausa Novel Document By Salma Ahmad Isah

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button