Description/Story:
Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3! Written By Aisha Aliyu Garkuwa
Description
Yana surutai, sai dai jin mgnar tashi a wani irin gigice.
tana son ta saita nitsuwarta ta tabbatar wa kanta abinda takeji amman ina sai take jin abin a bai-bai.
Sama da 50 minute suka ɗauka suna abu ɗaya, gaba ɗaya sun gigice, duk wani tunaninsu ya kau, wannan daren yakasance musu wani dare na mussaman, dan kuwa sun shayar da junansu, zuman soyayya, surutai da sambatu kuwa babu irin wanda basu yi ba sun nuwa juna asalin soyayyar da sukewa junansu.
Ahankali ya kwanta ajikinta, yana sakin wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, kusan atare suke fitar da numfashi, gaba ɗaya tayi laushi, dan ya mugun gajiyar da ita ƙwarai, saidai kuma zaƙin daya shayar da ita, bazai faɗu ba, dan har yanzu awata duniya ta daban takejin kanta.
Kissing goshinta yayi, cikin zuciyarsa yace. “Allah Ya miki Albarka my shugar na, tabbas keɗin ta dabance acikin mata, ni’imarki daban take, komai naki is perfect, I love you with all my heart.”
Ɗan mirginawa gefenta yayi, hannunsa yasa yaɗan riƙe bayansa dake masa ciwo, dan yayi mugun gajiya, wanda sai ayanzu ne kuma yakejin gajiyan, sabanin ɗazu dayake ta kwasan garaɓasa baiji gajiyan ba. Kusan mintuna goma suka ɗauka suna maida numfarfashi, ahankali ya soma ɗanjin ƙarfi ajikinsa, kallon Zaleehan yayi, wanda ta riga da ta rufe jikinta da blanket, kyawawan idanunta alumshe suke, da’alama itama ta jigata sosai.
Towel ya jawo ya ɗaura ajikinsa, dayake wheelchair ɗinsa na gefen bed ɗin, shiyasa bai wani sha wahala ba wajen yunƙurin tashi, hawa kan wheelchair ɗin nasa yayi, cikin nutsuwa ya wuce bathroom,
da kansa ya haɗa musu ruwan wanka acikin wani haɗaɗɗen jakuzzie, saida ya tabbatar da ya shirya musu komai na wanka, kafun ya dawo cikin ɗakin, hannayensa yasa ya ɗagota jikinsa, ɗan shagwaɓe masa fuska tayi, tare da turo bakinta gaba, cikin sakalci tace.
“Dan Allah kabarni saida safe wallahi na gaji sosai, ni bazan iya wanka yanzu ba, jikina duk ciwo yake min.”
Dogon hancinta ya ɗan ja, cikin body language ɗinsa yace.
“Ehem dole ki faɗi haka ai, bayan kin gama moreni, har da ihunki.”
Hararan wasa tayi masa tare da sake turo masa baki gaba.
Ɗaukanta yayi suka wuce bathroom.
Bayan sunyi wankan tsarki shida kansa yayi mata wanka, koda suka fito ma shiya tayata ta saka rigan bacci, sake kimtsa gadon nasu sukayi.
Tana rungume ajikinsa haka suka kwanta, da yake agajiye suke sosai basu wani jimaba daddaɗan bacci ya ɗaukesu.
Ƙiran sallan asuban da yaji raɗau acikin kunnuwansa ne ya sashi ɗan ɓude idanunsa, baiyane yayi salati, tare da ɗan janye jikinsa daga nata ya tashi zaune, miƙa yayi, tare da jawo wheelchair ɗinsa ya hau kai.
Toilet ya shiga ya ɗauro alwala, yana fitowa ya saka wata farar jallabiya tare da ɗaura ƙatuwar rigar sanyi, ƙarasowa jinkin gadon yayi, ahankali ya shiga ɗan bubbuga ƙafan Zaleeha’n, cikin magagin bacci ta bude idanunta, ganin haka ya sashi juyawa ya nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Ganin fitansa yasa akasalance ta tashi ta wuce toilet.
Shikuwa Saifuddeen koda yabar cikin hotel ɗin,kai tsaye masallacin dake kusa da hotel ɗin ya nufa, Sultan Ahmed Masjid, acan yayi sallan Asuba, tare da ɗaukan Alƙur’ani ya ɗan taɓa karatu, jin bacci acikin idanunsa ne ya sashi hawa kan kekensa, ya koma zuwa cikin hotel ɗin nasu.
Zaune ya samu Zaleeha akan sallaya tana karatun Alƙur’ani, gaba ɗaya zazzaƙan muryarta ya karaɗe ɗakin, kallo ɗaya ya mata ya saki murmushi, komawa kan gadon yayi ya kwanta, dan bayaso ya katse ta daga karatun da take. Ko mintuna 10 baiyi da kwanciya ba bacci ya ɗaukesa, Zaleeha kuwa koda ta kammala karatun idanu ta zuba masa, hakanan yanayinsu na jiya da dare ke dawo mata, idanunta taɗan lumshe, tare dason jiyo abun da taji kaman yana faɗa jiyan, tabbas idan kunnuwanta basu mata ƙarya ba, jiya tajishi kaman yana wasu irin surutai, saidai kuma sanin cewa shiɗin baya magana yasa take ƙoƙarin ƙaryata kanta.
Hijabin dake jikinta ta cire sannan ta haye saman gadon ta kwanta, abayansa, tare dayin pillow da kafaɗansa. Taɗan jima ahaka kafun bacci ɓarawo ya ɗauketa.
Ƙarfe 10 dai-dai suka farka atare, wanka suka sakeyi, koda suka fito waya ya ɗauka inda yayi musu oder’n takeaway. Bajimawa kuwa aka kawo musu, saida sukaci abincin, kafun Zaleeha ta kimtsa kanta cikin wata haɗaɗɗiyar gown me taushi, da ɗan kwalin kayan ta yane kanta, sannan ta ɗaura wata jibgegiyar rigar sanyi akai, shiɗinma dai kayan sanyi ne ajikinsa.
Sunyi matuƙar yin kyau, kasancewar ƙarfe 11:30 dai-dai zaiga Doctors din da zasu duba shi, hakan yasa suka fito hannunsu sarƙe acikin na juna.
A compound ɗin hotel ɗin, suka samu drivern da Dr.Acash ya turo musu, wanda shine zai kaisu asibitin.
Babu ɓata lokaci kuwa suka shiga, driver’n yaja suka tafi.
Har ƙofar babban asibitin. *Acibadem Hastanesi Hospital Instanbull* drivern ya sauƙesu, already sun samu waƴanda zasu musu jagora zuwa cikin asibitin na jiransu, hakanne ma yasa basu wani sha wahala ba suka samu ganawa da manya manyan Doctors, awani ɗan falo Zaleeha ta zauna, inda shi kuwa aka wuce dashi wani ɗaki na musamman, Dr.Acash Prasat da kuma sauran doctors ɗin suka kaishi, inda suka duƙufa akansa, suna duba larurar tasa.
Sama da 40 minute suka ɗauka suna checking ɗinsa, wanda ahakane suka hango babban nasaran dake tattare dashi, dan kuwa daga yanzu zuwa ko yaushe zai iya miƙewa ya tsaya akan ƙafafunsa har ma ya taka, kaman yanda duk wani me lafiya ke takawa.
Cikin son ƙarfafa masa guiwa, tare da horas dashi, Dr. Acash ya miƙa masa hannu, babu musu kuwa ya kama, ɗan ɗagosa Dr Acash ɗin yayi take kuwa sai gashi ya miƙe ya tsaya akan ƙafafunsa, saidai ƙafafun nasa naɗan rawa kaɗan-kaɗan, tafi sauran Doctors ɗin sukayi, dan su kansu sunji daɗin hakan. Ahankali yaɗan ɗaga ƙafansa na dama ya taka ta, ƙoƙarin ɗaga ɗayar ƙafartasa yayi itama ya takata, wani irin fitinenne daɗi ne ya rufeshi, a haka sukayi taku bakwai zuwa tara ya sake ɗaga kafar zai taku na goma, saidai jin tayi masa nauyi yasashi komawa ya zauna.
Tafi sukayi mishi sosai kana suka bashi shawarwarin.
Magunguna suka rubuta masa, tare da basa ƙarfin guiwan cewa yasa aransa cewa ko da yaushe zai iya taka ƙafafunsa yayi tafiya mai tsawo kamar da, sannan kuma yana ɗan gwada miƙewa tsaye yana tsayawa akan ƙafafunsa, da sannu ƙafafunsa zasu ware ya samu a rinƙa riƙeshi yana ɗan takawa.
Kana sunce akwai alluran da za’a ke mishi duk bayan sati ɗaya, ana biyu kuma yazo nan asibitin a sashi a na’urarsu mai ɗan yiwa bayansu tausa, lissafin dai zai kaisu watanni uku rak, za’a gama mishi komai.
Godiya ya musu sosai, kusan dai awa biyu suka share acikin asibitin kafun ya fito suka tafi.
Daga asibitin Wani haɗaɗɗen gardeen Goztepe Garden Park instanbul.
Sukaje Wurine mai ɗan karen kyau da daɗin yanayi dasa shauƙi da nishaɗin ko ina an ƙawatashi da koraye da jajayen fulawi, ga wasu kujeru masu kyan gaske kana mutane kowa sabgar gabanshi yakeyi kowa ka gani da shigar kayan sanyi, kusan anan suka ƙare rabin wuninsu na ranan, dan sai dare sannan suka koma hotel ɗin bayan sunyi sallan isha a blue mosque sosai dai suka ɗan zazzagaya….
File Name | Nakasa Ba Kasawa Bace 8… Hausa Novel Doc. |
Title | Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3 |
Author | Aisha Aliyu Garkuwa |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 17/08/2024 |
File Size | 200KB |
Format Size | TXT |
Book Price | 500 |
Phone No | 09097853276 |
Download Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3 By Aisha Aliyu Garkuwa
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.